YAR AMANA 19-20
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
*PAGE 19-20*
............ Sai da suka isa har gaban Daddy Sanan ABUDULJABBAR ya cika hanunta ya zauna, itako 'YAR AMANA cikin tsoro ta saci kallon Daddy, sai taga fuskarsa ba alamun wasa dan haka kuwa tini ta fara neman gurin da zata zauna sai dube-dube takeyi, ABUDULJABBAR ne ya kamo hanunta ya zaunar da ita ta qarfi akusa dashi, sanan yace " Daddy Sannu da hutawa"Cikin fishi daddy ya juyo ya kalleshi yace " kariqe sanunka ABUDULJABBAR bana so ina son insan wanan wacece?" ya fad'a yana nuna 'YAR AMANA
"Daddy kayi haquri da gaske nake maka matata ce"
"Tayaya ta zama Matarka ABUDULJABBAR ? Wa ya aura maka ita ina so insani?"
Nan ABUDULJABBAR ya kwashe labarin komai da ya faru atafiyarsa har zuwa aurensa da 'YAR AMANA.
Cikin Mamaki Daddy yace " tayaya zan yarda da haka ABUDULJABBAR menene shaidarka?"
ABUDULJABBAR kuwa wayarsa ya ciro a aljihun jallabiyarsa Ya kunna hoton bidiyo rikoda ya miqawa daddy, nan daddy ya kar'ba ya fara gani Gashi nan lokacin da ake d'aura auren ABUDULJABBAR da 'YAR AMANA, domin kuwa a lokacin da ake d'aura auren ABUDULJABBAR ya ciro wayarsa ya d'auki komai saboda tsaro
Miqawa ABUDULJABBAR wayarsa daddy yayi Sanan yace "sannu da qoqari ABUDULJABBAR lalle kaid'in ka cika d'a nagari managarci, domin kayi taimako dan Allah, amma su wa 'yanan wasu irin mutanene haka daga taimako sai yazama matsala? Amma ba komai domin ba musan alherin dake lulu'be da auranan ba.
Sbd haka ABUDULJABBAR ka riqe matarka AMANA domin kuwa yanzu amanar ahanunka take, kuma ya zama dole ka 'boyewa matarka da Mummyn ka wanan lamarin domin kuwa kasan halinsu sbd haka kabari har zuwa gaba sanan susan komai"
ABUDULJABBAR kuwa cewa yayi "nagode Daddyna domin kai d'in mahaifine na qwarai mai fahimtar 'ya'yansa kuma zanyi aiki da shawarka"
"Yauwa ABUDULJABBAR Allah yayi muku Albarka, sanan Daddy ya dubi 'YAR AMANA yace " Sannu NUSAIBA ki saki jikinki kinji domin nan gidan kune"
'YAR AMANA kuwa da take 'boye kanta abayan ABUDULJABBAR dan anata shirmen tsoron daddy takeji, cewa tayi " Amma Kad'on Aljani, shi wanan Aljanin mai kirkine har ya fika kirki gashi kuma kyakyawan dattijo"
Daddy kuwa cewa yayi "aljani kuma a ina me take cewa ne ABUDULJABBAR?"
"Daddy ai ita dukkanmu kallon Aljanu take mana sbd shirmenta da qauyancinta dan aganinta wai duniyar Aljanu na kawota"
Murmushi Daddy Sanan yace "NUSAIBA mu ma mutane ne irinki kinji ko? Karki sake qiran kowa da Aljani a gidan nan domin dukkanmu mutane ne irinki kawai de mu 'yan birnine kuma kema wata rana zaki zama kamar mu, sanan akwai mamanki da yayarki suma zaki gansu harma da qawarki IKIRAM kinji amma fa karki qirasu da Aljannu domin dukkanmu mutane ne"
Sanan Daddy ya dubi ABUDULJABBAR yace " sai de fa kayi ta haquri domin kasan da Akwai banbanci, sbd haka kasata amakarantar boko da Isilamiya"
Godiya ABUDULJABBAR yayi wa Daddy, shi kuwa Daddy nan ya sanar da ABUDULJABBAR akan FINAH na asibiti ba lafiya, nan ABUDULJABBAR yanemi sanin me yasa meta, amma Daddy yace " ni baisan komai ba saide in kaje asibitin"
Sanan Daddy yace " maza kakai NUSAIBA d'akin IKIRAM domin tare za surinqa kwana, kafin nanda wani lokacin, sanan ba ruwanka da mahaifiyarka akan maganar NUSAIBA kawai kabarni da ita nasan ta inda zan 'bullomata"
Godiya sosai ABUDULJABBAR yayi wa daddynsa domin kuwa shikam yayi dacen mahaifin da ba kowa yake da irinsa ba sbd haka a kullum yake cikin godewa Allah
Kama hanun 'YAR AMANA yayi sanan suka nufi d'akin FINAH a gurguje ya kwashe komai na 'YAR AMANA a d'akin ya miqawa 'YAR AMANA buhunta da Baffa ya bata wanda suma basu san ko menene bane aciki domin ba wanda yabud'e ya gani acikin su, tsohon kayan 'YAR AMANA kuwa da tazo da shi ajikinta fita yayi yaje ya zubar da shi a dosbin d'in gidan, sanan ya dawo ya kama hanun 'YAR AMANA ya kaikata d'akin IKIRAM a gurguje ya d'auko doguwar rigar IKIRAM ya bata tasaka sanan ya tatara kayan FINAH Ya mai da mata, domin yana tsoron kar Mum ta zo gidan, gurin 'YAR AMANA ya koma ya sameta agurin da yabar ta wato akan gadon IKIRAM, tsaya wa yayi akanta yace " 'Yar qauye ki tsaya anan zanje indawo karki kuskura kifita inkinji fitsari ko wani abu ganan bayi nan ki shiga"
Itako 'YAR AMANA baki ta murgud'amar tace ni sunana ba 'yar qauyeba sunana 'YAR AMANA"
zaro ido ABUDULJABBAR yayi yace " ni kike murgud'awa baki yaushe kika rainani aini ba ahaka dani zanaki zanyi"
'YAR AMANA kuwa tana jin zancen dukka jikinta yayi sanyi Sanan tace " dan Allah kad'on Aljanu kayi haquri wlh ba halina bane kawai sunan da ka kirani dashi ne bana so shi yasa"
"Murmushi ABUDULJABBAR yayi wanda 'YAR AMANA bata ta'ba gani afuskarsa ba sai taga ya mata kyau sosai, shi kuwa cewa yayi to " Shikenan amma kiringa kiyayewa kinji ko? Kuma nima kidena cemin kad'on aljanu, inba kyaso na qira ki da 'Yar qauye"
'Daga kai tayi alamun to.
ABUDULJABBAR kuwa fita yayi yana cewa " idan qanwata IKIRAM tazo zata baki abinci kici". 'YAR AMANA kuwa kallon bayan sa tayi Sanan tace "itama Aljanarce?"
Shide bai kula taba ya fice abunsa, yana fita yaga daddynsa shima ya fice da mota
Shima ABUDULJABBAR ko kayansa bai tsaya sanja wa ba ya nufi gurin da yake ajiye motocinsa, key ya kar'ba ahanun d'aya daga cikin security's d'insa sanan ya shiga motar sa ash colour, qirar jeep, ya mata key Maigida ya bud'emar qofar ya fice agidan aguje kai tsaye asibitin su da suke zuwa yana nufa, yana danna kan motar sa cikin asibitin bayan ya shiga yayi parking ya fito daga motar sa kenan sai ga Abban FINAH Alhaji Halliru yazo zai shiga motar sa, yana amsa kiran waya, ABUDULJABBAR ne ya tsaya ajikin motar sa ya kananad'e hanunsa a qirjinsa, Inda yake fuskantar Abban FINAH, Abban FINAH kuwa baima kula da ABUDULJABBAR wayarsa yakeyi yana cewa " ai nafa d'ama Alhaji Biliyaminu har yanzu fa ba'aji labarin wanan shegen yaronba, domin yanzunan ma ina asibiti FINAH ba lafiya kuma mahaifiyar Yaronne awajenta, kuma na tambayeta labarin yaronata amma cemin tayi har yanzu bai dawo ba kuma wayoyinsa basa shiga, kaga kuwa ga dukkan alamu aikin yaranan yayi kyau sbd haka yama kama ta muqara musu kud'i"
ABUDULJABBAR kuwa da yake jin duk abunda Abban FINAH yake fad'a kuma ya gane duk inda ya nufa dan haka sai yace "Abba Ina yini ya mai jiki"
Azarane Abban FINAH ya juyo yana kashe wayarsa yana cewa "ina zuwa Alhaji Biliyaminu"
Alhaji Halliru kuwa idonuwansa ya ware ya dubi ABUDULJABBAR sanan yace "kaine?"
"Eh Abba nine kaganni ko ban mutu ba aini ABUDULJABBAR ASHIRU MAINA, nafi qarfin mutum wlh dan haka sai ka gaya musu ina raye sbd haka lokaci bai qure muku ba wajen maida dukiyar da kuka sata idan kuma ba haka ba..... Kawai sai ABUDULJABBAR ya murza ya tsun hanunsa asetin fuskar Alhaji Halliru sanan yayi shigewarsa cikin asibitin d'ayan hanunsa kuma riqe da key d'in motar sa.
Abban FINAH kuwa da qar yasamu yabar gurin jiki asa'bule inda yakira abokan arqallarsa awaya yace musu su had'u a guest house d'insa.
ABUDULJABBAR kuwa kai tsaye office d'in babban likitan ya nufa wato dr Musa, dama kuma dr Musa abokin ABUDULJABBAR ne bayan sun gaisa ne dr Musa ya raka ABUDULJABBAR d'akin da FINAH take, da sallama suka shiga d'akin Mum na kallon ABUDULJABBAR tatashi tace " ABUDULJABBAR yaushe kadawo duk nabi na damu domin kuwa ina ta qiran Nombobinka basa zuwa"
"ABUDULJABBAR kuwa cewa yayi " lafiya lau Momi na dare ne yayi shi yasa kawai na tsaya na kwana, amma Mum me yasami Nafisa ne haka har kuka kwana asibiti, Nan Mum ta bashi labarin abunda ta sani, sanan ya nufi gadon da FINAH take kwance, zama yayi abakin gadon ya kamo hanunta ya riqe yace "sannu my Nafisa" murmushi FINAH tayi tace "yauwa dear amma me yasa baka dawo ba ajiya domin kuwa harda rashinka shi yasa ciwon nan ya kwantarni asibiti"
Itako Mum fita tayi ta basu d'akin, ai kuwa nan FINAH taita narkemar shiko ABUDULJABBAR haushinta ma yakeji sbd da daddynta amma sbd son da take mar kawai sai yaji yana tausayin ta amma ba dan haka ba da daga asibitin nan sai gidan ubanta tinda bashi da hali.
Tin asibitin FINAH ta nunawa ABUDULJABBAR tsantsar jarabarta domin kuwa tana ganinsa tini ta manta da ciwon tarungume shi nan tashiga nuna masa soyayyar iri iri, shi ko yana kawar da kai da yaga abunata ma yana nema ya wuce gona da iri sai ya tureta ya tashi ya fice ad'akin, itako FINAH sbd baqin ciki sai da kwalla ta fito mata sanan tace " ABUDULJABBAR nagaji da rashin mutunci da jan aji da kakeyi min tabbas lokaci yayi da zanyi maganin ka"
________________________
Shiko ABUDULJABBAR office d'in dr Musa ya nufa nan dr Musa ya haushi da fad'a yana cewa " ABUDULJABBAR ya kana da hankali da ilimi zakabar matarka tana amfani da magungunan nasara mai sa illa a mahaifa domin jin dad'in junanku, sanan ga uban kwayoyin rashin haihuwa da take d'irka harma da Allurai tabbas mahaifar matarka saura kad'an tatashi aiki domin kuyi mata illa da yawa, sbd haka ABUDULJABBAR kaji tsoron Allah kabar 'yar mutane ta haihu, kar ka cuceta sanan daga baya kazo kace haihuwa kakeso, bayan kuma ka gama nakasata domin munga hakan da yawa"
ABUDULJABBAR kuwa idon sane ya cika ds kwalla sanan yace "FINAH, FINAH kin cuceni ashe duk tsawon shekarunan kece kike cutata? na d'auka har yanzu Allah ne bai bamu raboba, wlh dr inappropriate son haihuwa kuma bansan FINAH duk tana yin wa 'Yanan mugayen laifukanba, ni yanzu ya zanyi wani mataki zan d'auka akanta?"
"Aure zaka qara abokina shine kawai mafita kuma shine hukuncin da zaka d'auka akanta ita kuma ita tasani domin kanta tayiwa ba kaiba"
Haka de dr Musa da ABUDULJABBAR suka gama tatataunawa sanan ABUDULJABBAR ya bar asibitin ransa a'bace, kai tsaye ya nufi makarantar su IKIRAM domin ya d'aukota.........
Please kuyi haquri da wanan wlh ina busy ne shi yasa
Dan Allah in kinkaranta kiyi min shere asauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH, WA A TUBU ILAIKA* 🤲
No comments