JAMI'IN DAN SANDA 16
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_16
.........................zaune suke cikin wani k'ayattacen falo wanda babuce kawai babu acikinshi , ga sanyi AC da wani daddad'an k'amshi na tashi , kowanensu Yana hakimce akan kujera ,kallo Daya zaka masu kasan cewa lalli wad'an nan alhazan sunci sun tada kai da nera suturar jikinsu ma in ka kalla kasan ba k'ananan mutane bane , 'dayan 'bangaren kuma ,yan jagaliyar su ne a tsaitsaye kowanensu rike da zungureriyar bindiga fuskar nan tasu ba alamar imani ,
Alhaji Manu da Alhaji Musa da Alhaji Buba shahararrun yan kasuwa ne wanda sukayi suna a cikin garin na Lagos har ma da kewayenta, masu kud'i ne na gaske wanda ake damawa dasu suna da kamfanoni shaguna gidajen abinci da gidajen mai da sauransu , duk wanda ya sansu da wadan nan abubuwan ya sansu sai dai ta k'ark'ashin k'asa sud'in sun kasance azzalumai ne ga k'asar tasu don sun kasance manya manyan masu shigo da miyagun kwayoyi kayan maye kala kala ,duk wanda yake hark'allar Miyagun kwayoyi to zaka samu a k'ark'ashinsu ya ke ta nan ne suke samun mahaukatan kud'ad'e ,yayinda gefe daya suke shigo da gur'bataccen magungunan asibitin daga k'asashe daban daban ,wad'an da sun kasance masu cutarwa ne ga lafiyar mutum duk wanda yayi amfani dasu a hankali a hankali zasu rinƙa kassara rayuwarshi batare da ya sani ba ,su kuwa hakan ba damuwarsu bace tunda biyansu akeyi sunacin dudduniyar k'asarsu,
Ta dayan bangaren kuma suna nunama jama'a cewa su mutanen kirki ne ta hanyar yin sadaka gina masallatai makarantu bada tallafi ga mabuk'ata wannan yasa mutane da yawa suke son su dayi masu kallon mutanen kirki , wanda dama su haka sukeso bawai don Allah sukeyi ba a'a sai don ganin sun kauda idon mutane daga kansu ,
Wannan yasa hankalinsu yayi mummunan tashi lokacin da inspector Abdulrahaman yasan sirrinsu wanda yayi barazanar tarwatsa muguwar manufarsu ,
Har gida sukasa akayi masu kiranshi , batare da wata damuwa ba ya amsa kiran nasu , inda suka bashi mak'uddan kudade akan ya janye idonshi daga kansu sannan karya kuskura ya tona masu asiri inba haka ba kuwa zasuyi duk yadda zasuyi don suga bayanshi ,
, alokacin sam Abba bai wani damu da barazanarsu ba kuma kai tsaye ya gayamasu bazai amshi ko sisinsu ba sannan bazai fasa kai wannan case din kotu ba tunda yanada duk wata hujja a hannunsa , haka nan ya juya yayi tafiyarshi yabarsu baki sake,
Tun daga lokacin suke bibiyarshi tare da yimashi barazana kala kala , da farko sunki kasheshi ne saboda sunason su sani shi da gaske yanada wasu hujjoji akansu kamar yadda ya fada kokuma yafad'a ne don yayi masu barazana , in da gaske ne taya zasusan shirinshi da inda yake da hujjojin,
Sai dai abunda basu sani ba shine abba bashida wata hujja k'wak'k'wara sai goga gashi shikuma goga yaki bada hadin kai dukda irin azabar da ake gana mashi , wannan yasa lokacin da suka gayyaceshi yaje anan ya shirya masu tarko don kuwa duk maganganun da sukayi dashi ya nad'esu tsaf a wayarshi ,
Alokacin da suka samu labarin daukar da Abba yayi ne wanda ita kadai ce hujjarshi yasa suka yanke shawarar kashe shi kawai
Alhaji Manu Yana kan kujera Yana zuk'ar taba duk ya had'a d'an k'aramun gajimare a wajan , meeting sukeyi akan wasu kaya da zasu shigo dasu , do neman hanyar da zasu wuce da muggan makaman batare da wata matsala ba,
D'aya daga cikin masu tsaron k'ofar ne ya shigo ya d'an rank'wafa alamar girmamawa yace " sir kana da bak'o yana waje yace yanason ganin ka ne,"
Saida ya share sama da minti ukku sannan ya dubi security yace "wanene wannan "
"Inspector Haruna ne"
"Ok kace ya shigo "
"To sir" juyawa yayi ya fita daga falon,
A hankali inspector Haruna ya shigo yana wani dudduk'ewa yana washe baki sai faman zabga masu kirari yake yana mik'a gaisuwa ,
Dukkansu ba wanda ya dubi inda yake , tun yanasa ran cewa zasu bashi izinin zama har yafara sarewa ganin sama da 15mnt ba wanda ya kalleshi acikinsu sai faman shaye shayensu sukeyi suna tada hayak'i,
Yawu ya had'iye da k'yar ganin yadda Yan jagaliyar ke yi mashi muzurai kamar wasu zakuna,
"Mike tafe da kai "? Cewar Alhaji Manu
"am am dama Alhaji zancan kud'i da kukace zaku bani ne *Naira miliyan ashirin* to naji shiru har yanzu gashi har anyi watanni , ga wannan ciyon da naji a kaina lokaci da wannan had'arin ya faru ya fara damuna sosai har yanzu fama nakeyi dashi kuma likita ya tabbatar mun da cewa nasamu matsala acikin kaina ne.doli sai anyimun aiki kuma kudin sunada yawa sosai yace rashin yin aikin nan zai iya haifarmun da babbar matsala anan gaba san."..................... "Kai dakata don Allah kazo sai zuba kake sai kace wani Radio , yanzu kai in Banda cewa d'an mahaukaciya ne kai taya kake tunanin zamu baka kudi har miliyan ashirin , ubanmi kamana da zamu baka wannan uwar dukiyar , to kaji da kyau ko sisi bazamu baka ba , inace tun farko munbaka one million to kaje sun isheka inba hakaba abunda yasamu dan uwanka kaima zai iya samun ka, " cewar Alhaji Manu,
Alhaji Musa da Alhaji Buba kuwa ko kallonshi basuyi ba , ganin hakan yasa ya tashi jiki a sanyaye ya fita daga falon , tafiya yakeyi yana hada hanya gaba d'aya sun rusa masa babban burinsa ,tuni ya riga da ya shirya yadda zai gudanar da sabuwar rayuwa idan har suka bashi kudinshi miliyan ashirin kamar yadda suka mashi alk'awari , wani irin tururi zuciyarshi keyi yanajin wani irin bakinciki , d'ayan gefe kuma ga matsalar da yasamu yayin yimasu wannan aikin don saida ya share wajan sati Daya a asibiti sakamakon buguwar da kanshi yayi wanda har gashi hakan ya zame mashi matsala don in ciyon kan ya tashi haka zai koma kamar mahaukaci yana ihu da buge buge tsabar azabar da yakeji , dama shirinshi shine suna bashi kudin zai fita kasar waje amashi aikin sauran sai ya ja jari kawai , don a niyarshi ma zai ajiye aikinshi ne yafara kasuwanci tunda banza ta samu, to sai gashi cikin kankanin lokaci sun rusa mashi komai Kuma bazai iyayin komai ba!!!!
" Inaaaa wallahi bazai taba yiwuwa ba suna nufin sunci moriyar ganga kenan bayan duk irin kokarin dana masu , sannan ga kasadar da nayi wanda gashi nan na hadu da ciyo mai matukar had'ari ga cin amanar abokina da aikina da nayi sannan ace duk wannan ya tashi a banza to wallahi bazai taba yiwuwa ba wallahi koni ko su sai dai ayi mutuwar kasko, " sambatun da ya rink'a yi kenan bayan ya dawo gida ya kulle kanshi a daki , daga baya ma tsabar bacin rai bai san sanda yayi zaune dirshan ba yafara kuka wiwi kamar wani karamin yaro,........
__________________________
"Assalamu alaikum , " yayi sallama tareda d'age labulen falon , Momma ce da Inna Indo zaune suna karyawa , Inna Indo ce kawai ta amsa mashi amma Momma ko kallon inda yake batayi ba , tadai amsa sallamar acikin ranta, sati Daya kenan da yayi mata maganar son shiga aikin d'an sanda ,tun daga lokacin ta dauke mashi wuta , ta daina shiga sabgarshi gaba daya , fushi takeyi dashi sosai , ta yadda zai dauki abun da muhimmanci , tasan Hisham bayason fushinta ko kad'an duk yadda yakai ga son abu data nuna bataso to zaibar abun duk yadda yakeson shi kuwa , amma abunda yake bata mamaki shine yanzu k'iri-k'iri ya kafe akan ra'ayinshi , duk kuwa da irin fushin da takeyi dashi,
Kusa da Inna Indo ya zauna yana gayar da ita kamun ya juya wajan Momma yace "Momma Ina kwana,"
Shiru bata amsa mashi ba , har cikin ranshi yanajin ciyon yadda mahaifiyar tashi ke fushi da dashi amma ya zaiyi tunda ya dauki alk'awarin sai ya cikawa mahaifinshi burinshi,
"Momma izuwa yanzu Yakamata ki fahimceni sam bana kafe akan ra'ayina bane don na 'bata maki , a'a kawai dai inason na cikawa Abbana burinshi ne , kema kin sani Momma sam wannan aikin baya raina amma a haka na ajiye nawa ra'ayin don ganin nayi abunda mahaifina yakeso , ki tuna Momma ko a ranar da zai bar duniya saida yayimun magana akan wannan buri nashi , ai Yakamata ki bani goyon baya , insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi Momma ,
"Runtse idonta tayi yayinda wasu hawaye Masu zafi suka zubo mata cikin Muryar kuka tace " kai yaro ne Hisham har yanzu da k'urciya a tare dakai , sam bazaka iya hangowa kanka abinda Ni nake hango maka ba , sannan indai har Ni na haifeka to inason kabar wannan maganar don sam bazan ta'ba yarda kayi wannan aikin ba , nasanka nasan halinka shigarka wannan aikin zai iya ...................." Haba Maryamu karki yiwa d'anki baki mana miye aibun wannan aikin ne da kike k'iyayya dashi haka , Ni banga abun tashin hankali ba anan , tunda har ya nuna ga abunda yakeso kibarshi yayi aikinshi mana , tunda kinaji yace saboda mahaifinshi zaiyi, shin ke bazaki iya goya mashi baya ba don ganin kin tabbatar da burin mijinki ya tabbata ba akanshi , na tabbatar da in kece kika mutu da irin wannan burin to duk yadda Abdulrahaman zaiyi sai yayi don ganin yacika maki burinki koda baki a duniya haba Maryam kiyi hkr ki bishi da addu'a kawai shi zaifi,
Batare da Momma tace komai ba ta tashi tayi shigewarta d'aki tabarsu anan , tana shiga ta fad'a saman gado tare da sakin wani marayan kuka yayinda kewar mijinta ta dawo mata sabuwa ,
Batason Hisham yayi wannan aikin ne don tana gudun watarana ya binciko gaskiyar abunda ya faru da Abbanshi ta tabbatar da sai ya dauki fansa bazai taba yin shiru ba , in hakan ta kasance tayaya zai iya ja da wadan nan hamshak'an mutane , karshenta shima su samu sharrin da zasuyi mashi , taya zata juri wani abu yasamu Hisham a yanzu shikadai take kalla taji dadi batada kowa sai Allah sai Hisham taya zata bari tanaji tana gani ya jefa rayuwarshi a hadari irin wannan,......
Dukkansu da kallo kawai suka bita lokacin da take shigewa dakin , ajiyar zuciya suka sauke yayinda gaba daya Hisham yaji duniyar na juya mashi kwata kwata ya tsani ganin 'bacin ran mahaifiyarshi ,tunani yakeyi ko ya hakura da aikin ne kawai kamar yadda takeso,!
Wata zuciyar tace zaka iya hakura da burin mahaifinka kuwa wanda ka dauki alk'awarin sai ka cika mashi shi , kawai kaci gaba da lallaba Momma insha Allah zata sauko ta amince , haka yayi ta sake sake a zuciyarshi,
Dafashi Inna tayi tace " karka damu Hisham zata sauko ne kuma nakama alk'awari. Zan shawo maka kanta insha Allah,"
Yawwa Inna Indo dakuwa kin kyautamun sosai wallahi,
Acikin satin kuwa Inna Indo ta samu ta shawo kan Momma da lallashi da wa'azi , a wannan ranar Hisham yayi farinciki sosai , bai zame ko ina ba sai inda ya ajiye form din da yasiya , ya dauko shi ya ciccike komai sannan. Ya dauka ya fita dashi ,
Bayan wata daya komai ya kammala aka tura su makarantar koyon aikin dan sanda inda daga wannan zuwan bazasu dawo ba sai sun zama cikakkun *jami'an tsaron na police*
Wata d'aya kenan da yaje wajansu Alhaji Manu , tun daga lokacin yake shirya masu tuggu kala kala amma yakasa samun nasara akansu saima barazana da suke masa don shekaranjiya har gidanshi suka turo mashi yan daba inda suka kama matarshi da yaranshi suka rufesu a cikin daki shikuma suka tu'beshi suka zaneshi tass saida jikinshi ya farfashe sannan suka mashi barazana da cewa idan har bai dauke idonshi daga kan su Alhaji Musa ba to zasu rabashi da duniyar baki daya ,
Aikuwa ya tsorata da lamarinmu sosai don yasan Daga su har uwayen gidan nasu basu da k'warar imani zasu iyayin komai don ba abunda aka isa ayi masu ,gashi tun daga lokacin ciyon kanshi keson tashi kullum baya bacci yarasa abinda ke masa dadi duniya , sai yanzu yafara nadamar abunda ya aikata ma Abokinshi dakuma cin amanar kasar shi.....................kai nagaji sai jibi kuma...🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
*Kuyi hkr rashin jina kwana biyu nayi rashin waya ne*
*Please comment and share*🥰🥰🥰🥰
*ZANYI AIKE KANO DA KATSINA ABUJA KADUNA DA ZARIYA MAISON INGANTATTUN KAYAN MATAN MASU KYAU DA INGANCI TAYI MAGANA TA PC KO TA KIRA WAYA NGD 09035027743* 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
No comments