SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 7
*BOOK (1)*
7️⃣
Sai wuraren la'asar tabar kitchen ta fito saidai sam ta kasa gane hanyar da zata koma 6angaren nasu gashi ita ba bakin mgn ba bare ta tambaya,hk take ta bulayi, ta yanki hanyar wata kwana kenan sukayi kici6is da yarima ayman, wasu dogarawansa biyu na take masa baya, yarima ayman shine auta ga mai martaba sarki mahmudu don hk sarki ke mutuk'ar son shi hkm mahaifiyarsa amarya jido,tsananin gata da shagwa6awa shine silar lalacewar tarbiyyar yarima ayman, komai yyi daidai ne ba tsawatarwa, sun taho kenan itama ta taho batare data ankara dasu sai dasu ba, d'aya daga cikin dogarawan dake tare dashi ya daka mata tsawa yace"ke! gafara y'ar talakawa, yarima ne tafe" batasan me yake fad'a ba
saidai ta lura ita yake kallo yana mgn, saidai bata dakata sun wuce ba sannan batayi gaisuwa ba saidai kawai sunkuyar dakanta da tayi k'asa ta taho ta k'etara ta gefensu ta wuce, abun yyi mugun basu mamaki gashi dai sun ga kayan bayi ne sanye a jikinta sun tabbata baiwa ce amma yanayin yadda tayi tamkar wata d'iyar saraki, ko gaisuwa batayi ga yarima ba take neman k'etaresu ta wuce, tsawa suka sake doka mata, d'aya dogarin ya d'aga wata bulala mai baki biyu da niyyar tsulala mata, cikin sauri
yarima ayman ya dakatar dashi, k'ura mata idanu yyi yana kallonta har ta k'etaresu ta wuce abinta, wani bak'on al'amari ne ya ziyarce shi tashi d'aya yaji duk jikinsa ya mutu murus, zuciyarsa na harbawa yana son ya juya ya sake kallonta saidai izzah irin tasu ta jinin sarauta ta hana shi ya juya, dakatawa yyi da tfy, cikin sauri dogarawan nasa suka kalleshi don sun lura tamkar yanayinshi ya sauya amma sai sukayi zaton ko ransa ne ya 6aci game da abunda wannan baiwa tayi, cikin sauri habibu yace" tabbas,hukunci ya tabbata ga wannan baiwa wacce tayi ganganci 6atawa yarima zuciya" cikin sauri ya d'ago idanunsa ya kallesu yace" ban baku wannan izinin ba" yana fad'ar hk ya wuce ya shige 6angarensa, yana shiga ya fad'a kan sofa ya zauna, d'ora hannunsa yyi akan k'irjinsa dake harbawa ya runtse idanunsa cikin sauri,ya soma girgiza kanshi alamun bai son hk ta kasance.....
Rumana kuwa tana cikin bulayinta ta hangi fitowar su bintu daga 6angaren fulanin yola, da gudu ta k'arasa wurinsu ta rik'e hannun bintu, cikin sauri duk suka juyo suna kallonta don basu lura da ita ba da fari, ganinta ne yasa duk sukayi dariya suka wuce zuwa 6angarensu, washegari, jakadiya ta sauyawa rumana wurin aiki bisa ga umarnin fulani kilishi, rumana ta dawo cikin jerin bayin dake mata hidima a cikin k'waryar sashinta, ita ke share share da goge goge, rumana aiki take da kuzarinta sosai bata da ragwanci ko kadan akan aikinta, sannan bata da shiga shirgin da ba nata bare har takaita ga tsegumi ko gulma bisa lamarun wasu, mutane dayawa suna mata kallon miskila, bata dariya saidai kawai murmushi, duk lkcin data tuna da rasuwar innaro sai tasha kuka tamkar lkcin ta rasu....
Yarima ayman kuwa kwana biyu ya rage yawon zuwa club, tunda yyi bincike ya gano rumana tana bauta ne a k'waryar sashin fulani kilishi ya maida 6angaren fulani kilishi wurin zuwansa, abunda daya soma bawa kowa mamaki kenan domin tsakanin yola da manbilah babu jituwa ko kad'an, yauma kamar kullum ya shiga da safe ya tarar fulani ko tashi batayi ba sai bayi dake kai kawon a 6angaren suna gudanar da aikinsu, suna ganinshi suka soma mik'a gaisuwa yana daga musu hannu ya wuce, yana shiga parlourn fulani ya nemi doguwar kujera ya kishingid'e, rumana kuwa shigowarta kenan rik'e da mopping machine ta soma mopping sam bata lura dashi dayake kwance a saman doguwar kujera yana kallonta har ta k'araso gefen kujerar dayake, dakatawa tayi da mopping din ta soma gyara zaman throw pillows din dake saman kowacce kujera tana karkade kujerun tana zuwa inda yake tayi saurin ja da baya a d'an firgice don batayi tsammanin ganin mutum a kwance ba don tasan duk basu tashi ba, gani tayi ya k'ureta da ido yana kallonta tamkar wani maye, sunkuyar dakanta tayi da sauri, idan ta sunkuyar
dakanta k'asa shine alamar gaisuwarta, d'ago dakanta tayi ta juya ta koma ta cigaba da mopping d'in har ta gama yana kallonta, yanzu kam yasan ita din kurma ce, bayan ta fita da mopper din ta dawo ta soma kunna turaren wuta kowacce kusurwa na parlorn tuni parlourn ya turnik'e da k'amshi, jikinta ya bata idanunsa na kanta har yanzu don hk ta waiga don ta tabbatar aikuwa karaff suka hada ido dashi tayi saurin dauke idanunta duk sai ta soma jin takura, sake curtains d'in parlourn ta somayi sbd kar turaren wutan data saka ya fice, tuni parlourn yyi duhu dayake safiya ce sosai, kunna wuta tayi ko'ina ya gauraye da haske, hayakin turaren wuta ya soma cika parlourn, cikin sauri ya mik'e yana tari don shi sam baya son turaren hayaki, kallonshi ta tabbatar hayakin ne baya so, cikin sauri ta tayi waje da kaskon wuta, tana dawowa ta tarar dashi yana shan fresh milk, yana son ya mata mgn amma besan yadda zeyi mata mgn ba don be iya mgn da kurame ba, alamar kira ya mata da hannunsa ta nufo inda yake ta tsuguna gefe guda, sai kawai ya samu kanshi da shagala da kallonta har ta tsargu, sanin bata jinsa ne yasa yace" kinsan kuwa bana cikin nutsuwata tunda na d'ora kwayar idanu na akan ki? " ita kuwa motsawa bakinsa kawai take kallo, ajiyar zuciya yyi ya mika mata ragowar fresh milk din dake hannunsa ya mata alama wai tasha, girgiza masa kai tayi alamar ta gode, shima ya girgiza mata kai tare da nok'e kafada wai sai tasha dole, yanayin yadda yyi ne tamkar wani d'an karamin yaro yasa ta murmusa, shi kuwa k'ureta yyi sosai da idanu don be ta6a ganin murmushi a fuskarta ba, bud'e bottle na fresh milk din tayi ta d'an sha kadan ta rufe, murmushi yyi ya mik'a mata hannu ta bashi fresh milk d'insa ya bude sha, batare da kyankyami ba yasa bakin daidai inda tasa nata yasa fresh milk, ita kanta tayi mamakin hkn, murmushi ya mata ya sake mik'a mata bottle d'in fresh milk d'in ta amsa, mik'ewa yyi ya kwashi wayoyinsa ya daga mata hannu ya fice, ita kuwa ta rakashi da ido......
Yana fita daga yola ya wuce manbilah wato 6angaren mahaifiyarsa, aikuwa yana shiga ya taddata ta cika tayi fam don an kawo mata rahoto kullum sai ya fara shiga yola yake shigowa 6angaren nata, yana ganinta yasan ranta a 6ace yake don hk ya rissina ya soma mata jinjina yana mata kirari, tuni ta saki ranta ta soma murmushi, k'afarta ya janyo ya soma mata tausa a hnkli, ya riga yasan halinta sarai ko laifi ya tafka ta d'auki zafi yasan yadda yake shawo kansa ko fadan ma tak'i masa, kallon tayi tace" me kk zuwa yi yola da sassafe kullum" dariya yyi yace"wanne d'an gulma da sanya idon ne ya kawo miki wannan rahoton" harararsa tayi tace" dadin abun dai ba k'arya d'an rahoton nawa yyi ba" ta6e baki yyi ya mik'e zai fice wai shi a lalle yaji haushi, cikin sauri ta rik'eshi tace" haba,son kaima kasan bawai yarda nayi ba kawai tmbyrka nakeyi' komawa yyi ya zauna yana qunquni yace" gsky ana takuramin a gdn nan na gaji wlh, mai martaba ya sanyamin takunkumin fita wai ina janyo masa abun fada, na hkr na rage fita, yanzu kuma ni da gdn ubana ana neman a takuramin, cikin gdn nan ina ne bani da ikon na shiga" murmushi tayi tace" kana da ikon shiga ko'ina babu me hanaka son tunda gidan ubanka ne" sosa k'eyarsa yyi cike da shagwa6a yace" ki fadawa masu sakamin ido su dena" dariya taja hancinsa cike da tsolaya tace" ohh, rigimar yawa gareta son, shikenan naji" girke girken dake jere a gabanta ya soma bud'ewa, dambun nama ya soma ci yana shan hot coffee, suna hira da mahaifiyarsa, gaimbiya bilkisu ce ta fito sanye take da wata gown bak'a ta tufke dogon gashin kanta da wani white band, yana ganinta ya yatsine fuska yace" mom, wai ita wannan baza tayi aure bane, nifa na gaji da ganinta" harararsa tayi
tace" bani son tsokana, so kk kuyi hayaniya koh" tsuke fuskarsa yyi ya cigaba da cin dambun namansa, gimbiya bilkisu ta kalleshi tace" mtss, mutum ya girma amma har yanzu sai besan ya girma ba sai uban sangarci" remote d'in tv ta dauka ta sauya tasha zuwa bollyhood, harararta yyi yace" wata kuma ta girma har yau tak'i aure" tasowa tayi tayo kansa ranta a 6ace, bushewa yyi da dariya ya cigaba da cin dambun namansa, cikin saurin amarya ta daka mata tsawa tace" kul, bani so shirme,ke kk fara tsokanarshi shine don ya rama sai kiji haushi" fashewa tayi da kuka tace" shine fa ya fara tsokanata tun shigowa ta" tace"tunda dai kece babba ai hkr zakiyi wataran idan kkyi auren dakanshi zeje inda kk amma kedai kin fi son kullum kiyita biye masa kuyita hayaniya sbd rashin girma irin nk" a fusace ta fita fuuuu, murmushi yyi ya girgiza kansa kawai, tissue ya zara ya goge bakinsa sannan ya mik'e shima ya fice yyi 6angarensa......
Abu kamar wasa soyayyar rumana ta yiwa zuciyarsa mummunan kamu takai duk safiyar duniya sbd ya ganta kawai yake shiga yola, sai ya ganta yake jin dad'i yyi harkokinsa idan kuwa be ganta ba gbdy hnklinsa kasa kwanciya yake, amarya kuwa ta tsani wannan shiga yola dayake saida batason masa mgn ranshi ya 6aci, har yau babu wanda ya fahimci dalilin dayasa yake yawan shiga yola, soyayyar rumana ta zamto sirrinshi tsakaninshi da zuciyarsa babu wanda ya fahimta, ita kanta wacce yake son bata gane nufinshi ba, saidai yawan kallon dayake takura mata dashi shine ya soma sanyawa take mutukar shakkar gari ya waye ta shiga yola aiki su hadu dashi don bata fashin ganin a saman doguwar kujera kullum idan ta shiga shara.....
Mai martaba sarki kuwa ya shirya tsaf wurin k'ulla dangantakar aure tsakanin masarautar zazzau da masarautar adamawa, lamid'on adamawa dakanshi ya kawo ziyara ta musammam masarautar zazzau suka kuma tattauna akan wannan batu, burinsu su had'a jininsu aure, gimbiya bilkisu da yariman adamawa......... *SHARUZZAMAN*...............
_Sharuzzamana d'an sarki abdurrahmana_
_Yariman adamawa mai duniya yariman adamawa sharuzzamani mai zamani_
_Yarima mai tarin izzah_
Muje zuwa har mu riski duniyar da wannan d'an sarki yake...........
No comments