Breaking News

TSANGAYAR MALAM 19-20

            1️⃣9️⃣-2️⃣0️⃣

A guje Malam ƙasimu cinnaka ya ibi ƙafafunsa ya arta a na kare,buhari dake tsaye tsabar dariya sai da ya dur ƙushe ƙassa ya dinga ɓaɓɓaka dariya yana"yo hauka na ke zan yarda na kwan da kaka rakiya a cikin dare nan haka kurum ta wafci ƙafata mu tafi tare danƙari dako an wawashi jamma' a da yawwa

yasin dan wa ƴanda zan wawura su baba ne sahun farko sauran su biyo baya,ku da ya zamar muku dole sai kun zauna da ita kuje chan ku taya ta zama amma ban da buhari cikin almajirai zani na kwana har bayan bakwai bazan dawo ba zan dai zo in ci wara da sadakar waina da gumba na ware tana zaman zamanta a ƙauye da iyayin ka kaje ka kwaso ta ka kawo ashe ita tasan me ta haɗa maka su baba da kwanan keso wayyo Allah na zan so naga wannan ranar umm ba dani ba gaɗa a lahira,buhari ya ɗauki hanyar makarantar malam me awaki da zuwa ya shiga cikin jerin almajiran sa ya kwanta bacci ɓarawo yai awon gaba da shi.

    Malam ƙasimu cinnaka bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan sa da kukan jamma'ah ya tuna masa ashe fa gidan ya nufo ya jima a soron gidan kafin ya tusa kan sa ciki ya shiga,yana shiga matansa da yaran gidan suka kuma rushewa da kuka sai shima ya fashe da kukan ya kasa matsawa daga inda ya coge,uwar gidan sa ce ta dube shi cikin kuka ta ce""


"ka ƙaraso mana malam ga kaka dai lokaci yayi kafin ta cika sunanka ne raɗau a bakin ta idan ban manta ba ta kiraye ka yafi sau dubu ko da tazo gangar sai da ta ambace ka.


"innalillahi wa inna ilaihirraju'una,Sarai kuma ni ka ɗai ta dinga ambata su sauran ƴan uwan namu fa.


  babu wanda ta faɗa sai dai data ambaci sunan naka a ƙarshe ta ce Amadu shi zai biyo bayan ka.


la'ilaha'illallahu,bayana kuma kenan ni zan bita daga baya sai amadu,cikin zuciyar malam ƙasimu ke ayyana masa haka gaba ɗaya hankalin sa ya tashi zuciyarsa sai dam dam take yana salati a fili da ba fitowa filin yake ba sai motsi da bakin sa yake,hangawa yayi yaga daga matansa sai ƙananun yaransa duk garadan basa wajan ya ce da matarsa ta biyu.


"Ladiyo ina su ayuba da yautai suka tafi kuma ma ina maƙofta ko baku sanar da jamma'ah mutuwar bane.


   Duk mun sanar kuma sun shigo sun daɗe anan tun lokacin da kaka ta mutu tafiya gidajen su sukayi zuwa safiya su dawo,yara kuma wai tsoro suke ji duk sun fuce ka ƙaraso mana malam bari na buɗe maka fuskar kaka rakiyan kuyi sallama,ladiyo ta kai hannun ta kan gawar kaka rakiya zata yaye zanin da suka rufe ta dashi kenan malam ya dakatar da ladiyo sai dai ta riga da ta buɗe fuskar kaka rakiya malam ƙasimu cinnaka ya fara karkarwa yana faɗin.


"Summa Inna Alaina Baiyanaaaa...............


malam bafa ɓata kaka rakiya tayi ba mutuwa tayi kayi rafkuwa ne.



To to to sarai wallahi ji nake ɓata tayi ke ladiyo maza rufe ta ku riƙa yi mata addu'ah karku sake kuyi bacci dan ba a bacci da mamaci kunji ƴan aljanna.


Malam.


Na'am ladiyo ki rage ambatar sunan nan da tsohun daran nan dan Allah gabana faɗuwa yake ni bari na wuce.


wai malam me kake nufi da kar muyi bacci anan ne kana tunanin anan zamu kwana,taɓ wallahi bada ni ba in zaka zo ka kwan da kakar ka kazo ku kwana ai kai da ita kuka fi kusan ci ba damu ba,sale lantana bashiru ku tashi mu tafi ɗaki ke yaya sai ku kwana lafiya Allah jiƙan ki kaka Rakiya.


   ba shiri sarai ta miƙe ita ma tayiwa malam ƙasimu cinnaka gaisuwa ta tattara ƴan guni gunin yaranta a gaba suka shige ɗaki har da garƙame ƙofar ta idon malam ƙasimu cinnaka yai tulu tulu daya zubawa kaka rakiya ido sai ya ɗauke ya waiwaya bayan sa ya sake waiwayo wa tsakar gidan yayi tsit sai iska da kukan tsintsaye kaɗai ke tashi a daran,charbin sa ya laluba ya chafko ya fara jan sa yana tofe gabas yamma kudu da arewa iska ta busa ƙyauren ɗakin kaka rakiya ya motsa ihu malam ƙasimu ya saka haɗe da sakin kuka me tsuma zuciya ya rufe idonsa gam da hannayen sa ladiyo dake tager ta tana kallon ikon Allah sai da tayi dariya dan ita ma tsoron ya hanata kataɓus musamman data saka hannu ta yaye zanin kaka rakiya gani take kamar tana kalonta ita ko sarai dama kasa ce wajan bacci tini ta ɓingire ta soma minshari da yaranta ya rage malam da ladiyo ne kaɗai idan su biyu a gidan,cikin duhun idanun malam ƙasimu cinnaka ya hangi fuskar kaka rakiya sai murmushi take masa tana" taho taho ƙasimu, ba shiri ya sauke hannuwan biyu ya fara wani sabon kukan haɗe da zama a chan gefan gawar ladiyo da ta ga malam a zaune a hankali ta buɗe ƙofar ta har malam zai zura da gudu yaga kuma ladiyo ce bai san sanda ya soma murmushin ƙarfin hali ba chan kuma ya saka kuka haɗe da hamdallah na ganin ladiyo ta nufo wajan da yake,rarrashin sa ladiyo tayi ta je ta ɗauro alwala ta ɗauki charbi tazo inda malam ƙasimu cinnaka yake ta zauna tana ta jan charbin shima ya fara jan nasa hannun sa na karkarwa yana hangen baya da gefan da ya zauna har dare ya raba.





………………





            Godu suke yi a cikin jejen kamar baza su kai ba iya dauriya da ƙoƙari sunyi sun jigata dan ba ƙaramin nisa sukayi wa inda suka baro ba ɗan malam ya duƙa yana haki da nishi da ƙyar kamar zai tuntsira ya kifa shi ko ƙolo da wasu matasa su uku suka ja burki suka tsaya suna mai da numfashin wahala da ƙyar haɗe da sauke ajiyar zuciya ba wanda ya tanka wa wani sai duban gabansu da sukayi a lokaci ɗaya ƙolo ya ce"


  "Kamar motsi nake jiyo wa ko dai kunnuwa nane?


tabbas motsi ne da ƙarar wucewar abun hawa ko dai mun ƙaraso babban titin,ɗaya daga cikin matasan ya furta yana me kalon su,dukkan su murmushi sukayiwa junnan su da hanzari suka miƙe atare suka nufo inda mitsin yake har suka fito kan titi dai dai wajan wata babbar mota dake danƙare da buhun huna maƙil sun kai kusan ɗari ko sufi haka,mutumin dake ɗaura taya yayi sauren tashi tsaye haɗe da zaro sukundire ba ya nuna su ɗan malam da ita, ɗan malam yayi saurin cewa.


"Bawan Allah mu ba macu ta bane muma taimako muke nema dan Allah ka taimake mu wallahi mutanan ƙwarai ne mu.


Mutumin bai tankawa ɗan malam ba sai ma cewa da yayi"Habu"habu,na amma yallaɓai ka gama ɗaura tayar?



zo nan ka ga,wanda mutumin ya kira da sunan habu ya zagayo wajan da mutumin yake yana zagayowa da ya ga su ɗan malam ya funciko ice ƙato daga jikin motar ya buɗa,su ɗan malam suka durƙushe gwiwoyin su ƙasa haɗe da cewa.


""Wallahi tallahi mu ba ma cuta bane asali ma bamu san'a inda muke ba sato mu akayi dan girman Allah ku saurare mu bamu da nufin cutar da kowa ku taimaka mana saboda Allah.


Waya satoku ya kawo ku nan wajan,kuma ta yaya ma kuka san nan titin?


da ƙafarmu muka gudu  daga inda aka sato mu,muka yanki daji kawai mu ka fito ta nan,ƙolo ya maidawa da habu amsar daya tambaye su,ɗan nazari habun yayi kana ya maida icen saman motar haɗe da duban ogan nasa ya ce"


yallaɓai waɗannan mutanan ba mugaye bane a nazarin da nayi lura da gaba ɗaya ajigace suke.


Kamar yaya kake da tabbacin haka habu jeka chaje dukkan su kafin mu amunta da su,kai tsaye habu ya matsa kusa da su ɗan malam ya shiga chaje jikin su a talitalin daran habu ya chaje kaf jikinsu bai samu koda finsir ba ogan ya sauke ajiyar zuciya ya kalle su.


ina zakuyi to?


Ɗan malam ne ya fara magantuwa ya ce"



Ni a *NAGERIA* nake amma a garin *LAMBU.*


tab amma Allah ya taimake ku muma nageria mukayi ku kuma ina ne garuruwan ku muji wanda zamu ɗauka mu bari.



ƙolo ya kada baki ya ce"duk ƴan nageria ne sai dai garuruwan mu da ya banbanta dan ni a gumel nake waɗannan ukun kuma ƴan bauci ne.


Tirƙashi yanzu ya za'ayi mu da tafiyar mu a iya kano ta tsaya zamu ibe ku, amma bari kai da kake a gumel zamu maka alfarma ɗaya mu yanka ta *ME GATARI* sai mu shiga *GUMEL* ɗin sai mu wuto *KANO* kai tsaye zan taimake ku kowa zan bashi kuɗin motar garin su ya ƙarasa Allah ya tsare gaba ya kiyaye.


kusan atare suka haɗa baki suka ce"""



Amin amin,sai murmushi fuskar kowa take da murna fall a ransu,kayan habu ya hau motar ya gyaggyara zaman su yanda kowa zai samu waje suka haye saman motar, suka zauna shima me motar ya tada motar sa sai tafiya a hanyar ya siyawa kowane lemon roba da burodi ya basu suka hau ci hannu baka hannu ƙwarya an jima ba a haɗu ba ga uwar yunwa da ta addabe su a haka aka ɗauki hanyar me gatari.


Wajejan uku na dare motar ta isa gumel dan ma sun tsaya guraran da ma'aikatan tsaro suke chakin inda aka sauke ƙolo a tasha sukayi bankwana da sauran ƴan uwa da ɗan malam kamar karsu rabu ƙolo ya ce insha Allahu zai je lambu tunda ɗan malam ya kwatanta masa kuma ba ɓoyayye ne gidan su ba,da haka suka rabu me motar ya bawa ƙolo dubu ɗaya ya ƙarasa gidan su,su kuma suka ɗauki hanyar kano,ƙarfe (7:00am),a garin kano tayi musu bayan kano line,gaba ɗaya su ɗan malam suka sauka mutumin ma ya sako da kansa yaje ya bibiya musu kuɗin motar garuruwan su haɗe da basu dubu dubu a hannu su riƙe sukai tayi masa godiya da fatan alkhairi ya juya motar sa ya ɗauki hanya su kuma suka ware kowane motar garin su ta,tashi aka ɗauki hanya.







………………Ko da gari ya waye nan da nan gidan malam ƙasimu ya cika da jamma'ah ƴan uwa da abokan arziƙi idon malam ƙasimu da yayi jajir saboda rashin bacci na kan Sarai sai hararar ta yake yana kumbure kumbure da yaga ladiyo kuma sai kaji ya fara"ƴar aljanna maca ta gari jamma'ah har kallon sa suke ko ajikinsa ita ko ladiyo bakin nan a buɗe kanta ya ɗau ɗumi sai zurga zurga take tana iyayi sarai duk ta dubur burce ta rasa me hakan ke nufi har aka kira me wankan gawa ta shiga tayiwa kaka rakiya wanka haɗe da shirya ta maza suka kai ta makwancin ta na gaskiya a maƙabartar ma sai da akayi da malam ƙasimu cinnaka aka ce ƴan uwan mamaciyar su ɗauke ta su saka ta,shi kuma ya ce sam ai ga ƙannen sa nan su su saka ta shi da ya kwan da ita jiya akwai wanda ya kaishi jarumta,tofa ƙannen malam ƙasimu cinnaka suka saka kaka rakiya a gidan ta na gaskiya aka rufe ta bayan anyi addu'a anyi nasiha da tunatar da jamma'ah kowa gidan sa ne kuma yana nan tafe duk sa'in da kwanan sa ya ƙare aka ɗungumo aka yo gidan malam ƙasimu cinnaka da zuwa yaga an shimfiɗa tabarmi manya manya ana fito da tuwo masu sha'awar ci na ci.

 Da ƙyar malam ƙasimu ya bawa zuciyarsa haƙurin barin jamma'a cin abinci kai tsaye ya shiga gidan ya faɗa ɗakin ladiyo ƴan uwanta suka fito suka bar mishi ɗakin ladiyi ta kawo masa tuwansa ya kwasa sai da yaji cikin sa ya ɗauka yayi gyatsa tukunna ya fito tsakar gidan mata duk sun cika ana cin tuwa.



       Icen dake cikin murhu ya zaro ko ƙarasa mutuwa bai yi ba ya tsaya a tsakar gida ya ce""""




"Ko wacce ƙatuwa ta tashi ta kwashi ƙafafunta ta bar mun gida ko yanzu na ragargazawa ƴar banza baki eh an silalo an taho za acinyen hatsi jiya daya kamata ku zo mu taro mu taya gawa kwana ko wacce shegiya ta maƙale a gidan ta wato ci ya kawo ku to atashi atafi ba zaman makoki, wai ba magana nake yi ba sai na fara saukewa ɗaya kafaɗa,ya ɗaga icen zai rafkawa wata mata ai da gudu mata suka fara kokowar fita wannan na bin takan wannan wachan nabin takan wachan haka suka fara gudu suna fitowa daga gidan,mazan dake waje wasu sun tashi zasu gudu ƴan uwan malam ƙasimu suka ce su zauna su shiga suga me yake faruwa ko rufe baki basu yi ba,malam ƙasimu ya fito wajan da ƙaton itacen sa a hannu ya fara kaiwa jamma'ah duka ta ko'ina har da ƴan uwansa sai da suka watse nan ya shiga sababi babu zaman makokin da za'ayi masa""



 kaka dai ta riga ta mutu kuma ni da ladiyo muka kwan da ita to babu wani sheggen da zai zauna ya cinyen hatsi kowa ya ware gidan sa achan ayi mata addu'ar,nan da nan labari ya zagaya ko ina na abunda babban limami kuma malami malam ƙasimu cinnaka ya aikata,wasu kam dama sun shedeshi sam bai da mutunci ga faɗan tsiya da shiga shirgin da ba ruwansa sunan malam ƙasimu ya ɗaga burni da ƙauyu a garin *LAMBU.*



Zaune uwaila take tana jimamin abinda malam ƙasimi cinnaka ya aikata da maƙofciyar ta ta gama labarta mata suwaiba,kawai taji musukur musukur a ɗakin ɗan malam kamar ta basar ta dai tashi jin motsin ya ƙara yawa uwaila ta miƙe da sauri dan ganin me ke motsi a ɗakin wata zuciyar ta ayyana mata ko akuyar ta ce ta shiga zatayi kashi a ciki ta bata wajan,,,uwaila na tura kai cikin ɗakin su kayi ido huɗu da ɗan malam a guje uwaila ta fito tana kwarawa malam kira da salati tayi gamo da fatalwar ɗan malam,ɗan malam ya fito a hankali yana duban uwaila,uwaila na sallati da tofa tofan du'a'in da duk ya faɗo mata baki,ɗan malam ya kada baki ya ce"



"Nine fa ba wata fatalwa ba ce.


Ido a waje uwaila ta shiga mutsuke mutsuken ido ta buɗe su tarau dai ɗan malam ɗin ne a gabanta bakin ta na karkarwa ta furta.




"Attahiru da gaske kai ne?


"Ni ne inna gudowa nayi.



"Alhamdulillah,Allah na gode maka ya Allah godiya nake a gareka daka dawo mana da Attahiru cikin ƙoshin lafiya,durƙushewa uwaila tayi tayiwa Allah sujjada tayi Addu'ah ta shafa,ƙassa ƙassa da murya ta ce"



Babu dai wanda ya ganka ko?



ɗan malam yayi murmushi haɗe da cewa"babu wanda na haɗu da shi yo ma idan sun gani ya zasuyi dani Allah inna sai na rama duk iskancin da hakimi ya aikata akai na sai sun ɗanɗana kuɗar su a hannu wallahi.



A'a Attahiru tun da dai ka dawo mun godewa Allah ka bar su kawai Allah zai bi maka kadinka dan ma bakaji abunda sukayiwa malam ba bayan barin ka gida.



"Me sukayi masa yi sauri ki sanar dani inna zuciya ta kar ta buga.




Ai…………………………………………






_*Wash hannuna🤣😛,Comments/Share*_

No comments