TSANGAYAR MALAM 17-18
1️⃣7️⃣-1️⃣8️⃣
Malam ya dubi ɗan malam samma da ƙassa yai gyaran murya ya ce"kai ya sunan ka na yanka daga wacce nahiya kake meye dalilin da ya sa aka kawo ka?duk waɗannan tambayoyin malam ya jefawa ɗan malam da ya yi sakatau yana kallon ƙwayar idon malam,'kai ba da kai nake magana bane ka tsare ni da
ido kamar na mujiya,ɗan malam dai bai tankawa malam ba,bai kuma ɗauke idon sa daga kan malam ɗin ba sai ma baki da ya wangale ya fara dalalar yawu haɗe da matsowa inda malam ke zaune akan buzunsa dake tsakankanin samma da ƙasa da gaske ɗan malam ke nufo malam,malam dake zaune akan buzun ya ƙara yin samma har kan sa na taɓo rufin bukar yayi saurin miƙa kansa samman jin zafin buguwar da yayi.Miƙewa ɗan malam yayi a sukwane ya daka tsale ya kaiwa buzun malam chafka Allah cikin ikon sa ɗan malam ya chafe buzun sai ga ɗan malam na reto a sama ƙafafuwansa na ƙasa nan da nan nauyin ɗan malam ya rinjiyi malam ya sauko da kansa ƙasa cike da mamaki malam ya nuna ɗan malam da ɗan yatsan sa take ɗan malam ya sulale ƙasa ya soma bacci kashirɓan kamar gawa a kwance, malam yaja gyaran murya garada biyu suka faɗo bukar.
"ku ɗauke shi ku mai da shi inda kuka ɗauko shi sannan ku tabbata an bashi taimako ya sha na tsawon mako guda dan kan yaron nan da ƙwari daga gani bashi kaɗai bane amma gidan ya zo duk tantirancin mutum sai yayi laushe kamar niƙan dawa ku hanzarta kai shi.
"Allah gafarta malam naga ya tafi dogon bacci ya za'abashi taimakon ya shanye a wannan yanayin.
zai farka da zaran kun fita da shi daga nan ku lura kusa ido akan motsinsa sannan a cire mai marin muga iya gudun ruwan sa.
an gama Allah gafarta malam,garadan suka kwashi ɗan malam a hannn suka yo waje dashi,da fitowar su ɗan malam ya dawo hayyacin sa sai raba ido yake yana ƙarewa wajan kallo"Allah ɗaya gari bam-bam,duniya da faɗi take, cikin zuciyar sa ya ke furta kalaman har aka shiga bukar dashi aka dire shi a wajan da aka yi masa shimfiɗa ɗaya gardin ya miƙawa ɗan malam rubutu a ƙoƙo cike da zafin nama ɗan malam yai hanzarim wafce ƙoƙon haɗe da kai ƙoƙon bakinsa garadan suka juya suka fita daga bukar,,sauke ƙoƙon ɗan malam yayi haɗe da juyawa ya dubi sani ƙolo dake rarrafowa wajan sa,yana zuwa ya ɗan leƙa yaga babu kowa a wajen maida hankalin sa ga ɗan malam yayi ya ce"
"Ya ya me ya wakana a bukkar malam?
ɗan malam ya zayyanewa ƙolo komai har da nuna shi da yatsan da malam yayi nan ƙolo ya zaro ido waje ya soma faɗin""
""Taɓ ai karka kuskura ka kuma yadda malam ya nuna ka da yatsa wallahi duk wani ƙarfin malam da shirin sa a wannan ɗan yatsan yake duk yanda zakayi karka bari yasake nuna ka dashi nasan za a kuma zuwa akwasheka a kai masa dan Allah Attahiru,ƙolo ya dafa kafaɗar ɗan malam kana ya ɗora""
Idan da halli ka gutsire ɗan yatsan ko kasan yadda zaka nakasa ɗan yatsan kowa ya huta dayawa na cikin matsi da takura a gidan nan kowa tunanin ranar da zai bar gidan ka zama silar taimakon jama'ar gurin nan dan Allah Attahiru.
Kai me ya hanaka aikata hakan?
tun farko na faɗa maka ni na ɓata shirin da kaina nayi yunƙurin guduwa,tun daga wannan lokacin ban kuma ido da ido da malam ba sai dai mabiyansa,motsi suka jiyo da sauri ƙolo ya ja ƙafafunsa ya koma tashi shinfiɗar garadan suka faɗo bukkar ɗauke da ƙoƙo a hannun ɗayan,miƙawa ɗan malam ƙoƙon gardin yayi ɗan malam ya karɓa ya kafa bakin sa akai garadan suka fita sani ƙolo yayi masa inkiya da inda zai zuba rubutun ai kuwa ɗan malam ya juye cikin saharar dake gefan sa ya juye haɗe da ajiye ƙoƙon a gefe, bayan wasu ƴan daƙiƙu garadan suka dawo suka kwance ɗan malam daga mari haɗe da ɗauƙar ƙoƙon su.
Sai da aka kwashi mako bakwai ana ɗirkawa ɗan malam rubutu shi kuma yana juyewa a inda ƙolo ya masa inkiya da ya zuba a kwana bakwan aka cire shi daga mari ya fara fita yana taya sauran almajiran malam aiki idon garadan nan nakan ɗan malam shi kuwa ko kallon hanyar fita baya yi,da murna suka garzaya suka sanar da malam abinda ake ciki amma fa ba ummm ba ummmm yaron daga gani bebe ne,malam ya ce""
"Maza aje a taho mun dashi,garadan suka je suka sake ɗauko ɗan malam aka suka zo suka aje a gaban malam suka koma bakin bukkar, yau malam zaune yake a ƙasa ba buzun ba tarin charbin sa malam ya sake jefawa ɗan malam tambayoyi"""
"meye sunnan yankan ka kuma saboda wani dalili aka kawo ka tsangayar nan,karka kuskura kayi mun ƙarya yanzu sai na faɗa maka inda gyatumarka da gyatumin ka su ke.
Galau ɗan malam ya yiwa malam ya sake zubawa masa manyan idanuwansa.
kai kuna ina?.
ran malam ya daɗe gamu nan kusa.
ku shigo da tsimagiyar nan ku gyara mun bakin ɗan nan,ai ko rufe baki malam bai yi ba garadan suka shigo da ƙatuwar bulala,malam ya umarci ɗaya daga cikin su ai ko gardin ya dage ya sambaɗawa ɗan malam a ƙeya.
Tini ɗan malam ya buntsure haɗe da fusata ya wawuro gemun malam ya ƙanƙame shi gam yana janyo shi.
Innalillahi,malam azaba tayi azaba ya ɗaga ɗanya tsansa zai nuna ɗan malam charaf ɗan malam ya lunƙume shi abaki ya gartsawa ɗanyatsan cizo haɗe da riƙe shi gam malam najan ɗan yatsan sa shima yana jansa da haƙora har da kukan akuya su malam da shure shure tsabar azaba haƙora talatin kai ko ɗan yatsan malam garadan suka fara ƙoƙarin janye ɗan malam kamar kwaɗo suna jan ɗan malam yana ƙara kaiwa malam cizo da janyo gemun har wani fusga ɗan malam yakewa gemun malam ya rasa duniyar da yake futsari da guntun kashin da malam ya riƙe suka ƙwace ba shiri ya saki abunsa.
Duk irin taron dangin da akayi akan ɗan malam abu yaƙi kamar ƙara masa ƙaimi ake wajan riƙe malam ihun malam ya karaɗe gaba ɗaya tsangayar kamar da lasifaƙa yake sambatun har da su asshariya da kiran matayen sa daga cikin matan *Bushira* ce tafi kowa shan kira ɗan malam ya jigata malam ya tabbatar ba zai moru ba ko da ya sake shi chan ya saki yatsan da gemun ya ɗafe yaron malam dake ƙoƙarin ƙwatar malam.
gefan wuyan yaron malam ɗan malam ya wawura Allah ya bashi sa'a ya chafki naman wajan haɗe da riƙo kunnuwa yaron malam najin shi a duniyar azaba yayo waje da gudu yana ataimaka masa riiii sauran garadan sukayi kan malam😆😆😆.
Ai kusan almajiran malam gaba ɗaya sun cika bukkar malam kowa na son ganin yanda abun ya wakana,dayawa du'a'i suka fara na'Allah yasa malam ya wula kowa ya kama hanya fitowar yaron malam wajan sukayi kansa da ɗan malam mene a jikinsa suna ihu da dariya.
------------
Ko da malam balarabe ya isa fadda maƙil yagan ta da jama'ah da zuwansa ya nemi waje ya duƙa ya gaishe da hakimi ya amsa a ciki ciki,hakimi bai jira abinda malam balarabe zai faɗa ba yayi karaf ya karɓe zan chan haɗe da miƙawa malam balarabe takardu ya ce"
"Duba da kyau ka gani.
"ranka ya daɗe takardun meye ni ai ban iya karatun zamani ba.
sanin hakan yasa rubutun yazo da *AJAMI*, ka duba da kyau cikin nutsuwa.
malam balarabe ya fara karanta takardun tiryen tiryen kowa najin sa daga ƙarshe ya dubi hakimi ya ce"
naji bayanan dake ciki kuma kowa ma yaji tunda afili na karanta,sai dai ban fahimci inda maganar ta dosa ba.
dama waya ce zaka fahimta bari in maka gwari-gwari yanda zaka fi ganewa,ita dai gonar da kake noma ta chan bakace to asalin ta,ta kakana ce ashe bamu farga ba sai da garin neman takardun margayi lado ƙanina aka fiddo da wannan takarda daka karance ta yanzu,na tsaya nayi nazari haɗe da saka jami'an bincike daga cikin manyan fadar nan suka ƙara tabbatar mun da gaskiyar magana malam balarabe gona dai tamu ce ta gado tun iyaye da kakani.
malam balarabe yayi murmushin takaici ya ce.
"Kaji tsoran Allah ka dubi lahirar ka da girman da Allah ya baka ka rantse wannan gonar ta gado ce ranka shi daɗe.
Hattara dai malam balarabe a fada kake ba awajan wasa ba,mai girma hakimi da kansa zaka ce ya rantse maka lallai abun naka ashe daga tsatso ya taso,rai a ɓace malam balarabe ya dubi malam ɗan tala ya ce.
"Maganar ka kenan akan rashin gaskiya da ƙarya da munafurci da shedar zir zaka mutu ka koma ga Allah malam Tala ƙarya ƙure take bata ƴaƴa duk inda gaskiya take zatayi halin ta kayi ƙoƙarin gyara mu'amular ka tayi kyau da duk wanda kuke tare dashi ku rinƙa tuna masa idan ya manta,haka zalika ku dinga gyara masa idan ya ɓata ku sanar dashi duniya da abinda ke cikin ta ba komai bane face ƙyalƙyali da ruɗani kuma anan zaka bar duk abinda ka mallaka ta hanyar dai dai da akasin haka ni bazanyi jayayya da ku ba na barku da Allah shi zai saka mun duniya ba agabana take ba ilah lahira ta nake duba.
Tsam malam balarabe ya tashi haɗe da direwa hakimi takardun a gaban sa ya saka silifas ɗin sa ya bar wajan jama'ah kowa na tofa albarkacin bakin sa,malam ado haƙiƙancewa yayi akan ai malam balarabe ya kawo raini yazo da wasa,wa hakimi dolle a hukun tashi hakimi ya kada baki ya ce"
"ai tunda kwalliya tabiya kuɗin sabulu munci riba a ƙyaleshi yaji da abinda ya dame shi kuma ta kura masa yanzu muka fara indai a LAMBU yake, ko ruwa sai malam balarabe ya gagara sha ba shi me gaskiya ba.
Mabiya hakimi suka dinga ɓaɓɓaka dariya suna ƙara fanfawa hakimi kai daga baya aka shiga tattauna yanda za'ake raba albarkar gonar kaso ɗaya abawa hakimi kasu ɗaya kuma su chanchanashi tsakanin su kowa ya dangwli arziƙin dake ttattare da gonar.
Ko da malam ya koma gida ya sanarwa uwaila kuka ta saka masa da ƙyar ya iya rarrashinta atake ta ɗauki takardun gonakin ta guda uku tabawa malam balaraɓe kyauta,malam balarabe ya ce"
"A'a uwaila ni namiji ne da nema aka sani insha Allah ko hayar gonar na yi musamu na cin hatsi ki bar abinki ko dan gaba"ni wallahi har ga Allah na baka badan wani abu ba malam idan baka amsa ba kana tunanin zan iya bacci yau dan Allah dan Annabi ka amsa har zuciyata na barmaka idan kana tunanin ƴan uwana na daɗe da sanar musu nabaka gonakina gaba ɗaya kasan babu ruwansu hakan ne kawai banyi ba dan nasan zaka ƙi amsa a lokacin amma ka daure ka amsa dan Allah malam ba dan ni ba.
Uwaila ni........"dan Allah malam kar kace komai ka bar wata magana abuna ai abunka ne haka abunka nawa ne malam.
shikenan zan karɓa amma hayya na noma idan na sayar sai mu dinga raba kuɗin kina ajiyewa kema yayi miki amfani gaba.
Ni wallahi kyauta nabaka su malam badan naci ko kwabo a ciki ba.
to ki bashi tunda baki yadda da hakan ba.
na amince indai zaka amsa.
na amsa Allah yasa mana albarka uwaila ya baki aljanna da masu miki addu'a.
Amin amin malam komai nufine na Ubangiji idan yabamu muna godiya agareshi haka idan bai bamu ba yasan tanadin daya yi mana ni kam ga Attahiru ko shi na duba ina jin daɗi a raina dan a matsayin ɗan da na haifa nake kallonsa.
Allahu Akhubar,uwaila irin ku kaɗan ne a duniya.
Haba malam har kabani dariya da kunya,anan dai uwaila da malam suka cigaba da hirarsu ta soyayya da ƙarawa junna ƙaimi akan nomar da zasu fara..........
"""""""""Tafe malam ƙasimu cinnaka yake zai nufi gida wajejan sha ɗaya na dare, sukayi karo da wani yaro da ganinsa a firgice yake,bugun da yaron yayiwa malam ƙasimu cinnaka yasa shi riƙo yaron zai wanka masa mari yaron da sauri ya ce"
"baba nine Buhari,inna ce tace nazo na kira ka kaka Rakiya ta rasu yanzu a ɗaki...
Wacce kaka rakiyan kake nufi buhari?
taka mana baba sai kuka ake a gidan ana ta nemanka.
",Innalillahi wa inna ilaihirraju'un,yanzu dan Allah kaka rakiya ki rasa yaushe zaki mutu sai da daddare na shiga uku kwanan keso kenan zakiyi a cikin gidan kuma nasan har dani cikin masu kwana a ɗakin gaskiya kaka rakiya bakiyi mun adalci ba.
kaiii Baba ta riga ta mutu fa kake bata kyauta maka ba.
Au wai dama baka tafi gidan ba buhari uwar meye kake yi anan wajan to,baka riga ka faɗan ba ka wuce ka kama hanyar gida ko naci uwarka yanzu wallahi.
ni wallahi bazan koma gidan ba cikin almajirai zani na kwana tsoro nake ji baba.
Mu kuma mu kwana gidan uwarka,zaka wuce muje ko sai na karya maka ƙafar dama,kai Allah ma yau da kai zamu kwana a ɗakin tunda ka iya zuwa kawo tsegumi.
Wayyo Allah baba ga kaka rakiyan ma ta biyo ka.
Na shiga uku ta wani ɓarin ta biyo...............
_*A nan zan gimtse in da Comments/Share*_
No comments