Breaking News

DUK NISAN JIFA 8

                          8

Bata san wani irin farin ciki ta samu kanta a ciki ba a lokacin da ta fito daga dakinta rai bace dan dauke fuskar Bilkiss da mari sakamakon ihun da ta hannata yi haka kawai kasancewarta mace , sai dai abinda take fada ne ya sakata ja ta tsaya, sannan ta wara idannuwanta tana mai jin wani irin farin ciki da zumudi da son gannin ta inda zata billo


KADER ne a gaba , tana biye da shi a baya har suka shigo


Baki daya hankalinta ya fi tafia kan kallon tanfatsetsen fallon dake dauke da kalar ruwan zeba da fari gini tamkar na gidan saraki, gini kamar na wani kusa a gwamnati ga uban sanyi da kanshin turaran wutar da ya mamaye dakin kamar wata duniya daban ba cikin niger ba 



*ZEINAB* Mama ta ambaci sunnanta a sanyaye cike da kaunar yar kanwarta kwalin kwal wace suka fito ciki daya


Da sauri ta juya wajen da take jin sunnan nata


Wannan karron kam mamaki ya gama dameta ya shanye tassss


Shekara da shekaru basu saka junna a ido ba, zata iya rantsewa a lokacin da ta barta ta fi yanzu tsufa, domin a yanzun Mama ta zama wata kamilaliyar yar gayu wace ta san kanta, bata da wani mugun jiki, jikinta madaidaici ne gata da tsafta ga hutu, kai idan aka barta zata iya cewa a yanzun Asma'u ta fita zama gangariyar mace mai aji da tsari


Sai da ta hadiyi wani abu a makogwaronta sannan ta lumshe idannuwanta dan ta samu damar controling din du wani abin dake taso mata


A sanyaye ta karasa ta mika hannunta kamar yanda ta saba ta kamo na Mama tana kallonta idannuwanta cike da hawaye aman ta kasa magana


Da sauri mama ta janyota jikinta ta rungumeta sosai sai kuma ta fashe da kuka mai dan sauti tana kara riketa a jikinta


Da a da ne, ba zata taba yarda ta shiga jikin Asma'u ba ko dan rashin kanshin turaren jiki da kuma wadatacen wankan da zai cire dati da kayan da suka sha rana, sai dai a yanzun wani irin kanshi ta ringa shaka a jikin yar uwar tata wanda idan dai ba mantawa ta yi ba, ko rudewa ta yi ba kamshin turaran ruwan sandal roz ne mai tsadar nan


"INA kika shiga? Ina kika je kika manta da ni? Kika manta da amanarki? Shin kin san girman hakkinmu dake kanki kuwa? Kin san girman darajar zumunci kuwa? Kina raye dama? Kina Niger ko zuwa kika yi? Aure kika yi kika manta da mu? 


Sai kuma mama ta kara dago da habar Zainab ya kasance wannan maganar da zata yi daga cen kasan zuciyarta zata fitar da ita ta raunana muryarta sosai ta ce "Koda kin san zan rike shi tamkar dan da na haifa kin manta uwa uwa ce? Kin manta ke Allah ya sakawa kwan haihuwarsa ke zai tambaya amanar da ya baki? Zeinab shekara nawa rabona da ke tun HISHAM na tatata ga shi har kaina ya fara cika da furfura? Ina kika yarda layin naki har nake kira bana samu? "


Zainab ta ce" Aunty"


Mama ta katseta da sauri tana fadin " A ranar kin ce na barki ki ji da kanki zaki tabo ni kin san cewar karya na yi masa dan na kare ki kar ya gane abinda kika fada min? Sai dai kash ina fada ya tsatsare ni da kallon da bana iya tanka masa sai sada kai na ringa yi a gaban yarona?  ? Haba Zeinaba , haba kanwata" .......Mama ta karashe tana mai fashewa da kukan da bashida sauti


Itama muryarta na rawa ta raba rukunkumar da mama ta yi ma hannayenta  a hankali ta kai kasa saman lalausan cafet din fallon ta zauna tana mai cire mayafin jikinta da dan kwalin baki daya, sai a lokacin ta kula babu Kader da Bilkissu watau sun basu waje su gana da junna


Muryarta a sanyaye ta ce" Haba Asma'u ashe har yanzun baki daina saurin kuka ba? Ke da zaki yi ta farin cikin na dawo sai kuma ki yi ta kuka? Dan Allah ki daina haka ya isa kar kanki ya zo yana ciwo, Asma'u yanzun gani na dawo gare ku, kuma ba inda zan koma"


Mama ta zauna kusa da ita tana daria hakan ya baiwa hakoran makkar dake bakinta kwaya biyu damar bayana a kan idannuwan Zeinab wanda ke shaida mata cewar Mamar har makkah ta je, Mama ta ce" Ba zaki gane bane, ban san yaya aka yi kika kasance mai karfin zuciya da kokarin rayuwa cikin duban jama'ar dake baki a gare ki, ni na sha wahala, Zeinab iyayenmu sun fadi sun rasu haka mijina da naki, bayan iyayen marigayi da ke wa na sani? Dole na ji wuyar rayuwa ni kadai kin sanni da sarkafa"


Zeinab ta yi murmushi tana kamo hannunta cikin nata biyu ta ce" Yanzun ba ganni a kusa da ke ba, yanzun ba ganni  na zo inda kike ba? Ba zan kuma barinki ba, ki fada min yaya bayan gamo? Me ya faru da ku? Yaya kuka yi kuke cikin wannan gidan? Gidan waye"


Mama ta yi murmushi ta kara rike hannunta da kyau ta ce" Zeinab abubuwa na alkhairi su muka yi ta haduwa da su, HISHAM da kike ganni shine mamalakin wannan daula, ke bama wannan ba maganar da nake maki HISHAM a yanzun ya zama wani kwaron da nake bi da adu'a dan Allah ya shiga tsakaninsa da magauta, Zeinaba a ranar da na yi kiranki dan na sanar maki dadadan labarin dacen da aka yi na samun fitarsa karatu, Zeinab bayansa na yi ta kiranki a ranar da ya fara yi min aike......na takaice maki sai dai na cire na anfanina na ajiye maki naki dan na kiyaye masa fita hakkin uwa, ina kika shiga kika bar yaronki har haka? Ina kika shiga ke? Me kike yi yanzun a rayuwarki? "


Murmushi mai ciwon gaske Zeinab ta yi, sai take gannin rayuwa batai mata adalci ba, tana cen tana wahala? Wahala mana karatun nan ita kadai ta san irin wahalar da ta sha a kansa, ta gama ta samu aikin a matsayinta na mai aikin sai gashi ta zo ta tardo wace ta bari cikin tsuma ta dameta ta shanye a gata? Yaron da ta dire a bayanta yana ihun kuka yana rarumar hannu yana neman nono shine yanzun ta je ganninsa ya gagara? Ashe su a nan din da take yiwa kallon kauye ta tafiyarta baban birni dan ta zama wata sai gashi su dake kauyen sun fita da komai ciki harda wayewa? 

A hankali ta ce da Mama" karatu na yi mai Zurfi Asma'u, na sha wahalar rayuwa dan neman na kaina, wani tudu wani gangare a shekarun nan nakan iya wuni ban ci ba, da kyar na samu takardar da nake nema sannan na shiga fafutukar neman aiki, kin san garinmu, kin san me yake cikinsa, da kyar Allah ya tsaya min na samu, layina da wayar bacewa suka yi Asma'u a lokacin bani da halin tasowa na zo gareku dan amsar numberku kuma bani da wanda zan turo hakan ya sa na ci gaba da karatuna da ku a zuciyata, bayan na gama kuma na samu aikin nan sam oganmu baya bari mu matsa, adu'ata Allah ya nunan ranar da zan samu damar zuwa inda kuke, to a wajen aikin namu baban namu ne mahaifiyarsa ba lafia, idan kin ga irin wahalar da take sha gaskiya sai kin tausaya mata, tana fama ne da matsala a kanta, mayar zata summe na lokaci kafin ta farfado, jikinta bai taba daina zafin jiki ba, idan kin ganta tana fama da jiki hakan ya tayarwa da oganmu hankali

Yana ta neman likitan da ya kware ne aka ce masa ya zo damagaram

Baki ga irin farin cikin da na yi jin yana maganar cewa damagaram, ai ban san lokacin da na dira na ce garinmu ne, zan yi masu jagora, yanzu haka maganar da anake maki cen na baro su na gudo na zo dan na ganku "


Mama da wani farin cikin da ya rufe mata dukan fahimta a zancen yar uwarta, da murnar ganninta ta ce" aa, likitan kai? To HISHAM ne fa in dai baban likitan kai ake fada na niger din baki daya "


Kamar bata san da zancen ba ta zarro ido da mamaki ta ce" kika nufin HISHAM din ne ya zama likita? Likitanma baba? "


Mama ta yi murmushi ta ce" Shine, likitan kwakwaluwa, likitan mata kuma soja a cikin gidan sojoji "


Wani irin girma ta ringa ji kanta na yi mata da wani irin abu da ta rasa ko na meye, a zumudance ta ce" Auntu na barsu a cen, muna cen mun kama layi ko zamu samu ganninsa ashe Hisham ne? Sai dai ina cike da tsoron ta yadda zaya kale mu, shin zai iya dubana kuwa? "


Mama ta dan yi tsam na wani dan lokaci, ba dan komai ba sai dan irin yanda tun yaron na zumudi a da idan aka ce mahaifiyarsa ce a waya, har ya dawo ya ringa rage zumudin amsarta a waya, tun idan ya ce da ita Mama? Tana kwabarsa cewa ni ba mamanka bace, wannan ta kusanka ira ce mamanka ni tatinka ce, har ya dawo ya daina kiranta da mama sai dai ya ce da ita tati, kai sannu a hankali amsar wayartama sai ya zamana sai maman ta yi masa jan ido kan cewa mahaifiya ba abin wasa bace, sai ya ce Mama ki yi hakuri a kulun idan muna magana da ita a gagauce take, takan ce min karma na yi gigin cewa zan ringa tambayarta kudi domin itana ta kanta take, bata san kina siya min komai ba? Wai mama yaya aka yi wata ta haife ni ba ke ba? Da zan iya kwace a duniya da zan yiwa BILKISSUNA kwace ne, zan kwace mata tsaftataciyar uwa ne, zan hanna mata mamana ne na rike abina ni kadai, ita kuwa mama sai ta yi kici kicin da rai dan ya baiwa maganarta mahinmanci domin irin kalaman nan nasa sukan bata tsoro ainun


Ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta ce" Bara na saka hijab dina mu tafi "


BILKISU kam hade haden kayan ciye ciye da shaye shaye ta baje ta yiwa Tatinsu


Cike da katon faranti ta shigo ta dire mata komai a gabanta tana ta murmushi tana kallon matar, irin feeling din nan mai girman gaske na yau kaima gaka ga wani naka na danginka bayan ka cire rai da gannin hakan


Zeinab cike da jin kaunar yarinyar ya mika hannunta ta kamota ta tsayar da ita kusa da ita sosai, a sanyaye ta ce" U'r cut babyna masha Allah"


Bilkisu ta ringa murmushi ta tsiyaya mata jus na kankana da peak sansanya ta mika mata tana kallonta ta ce" Tati, ina yini, yaya hanya? "


Zeinab ta sha tana lumshe idannuwanta hakan ya saka Bilkisu kallonta da mamakin irin yanda take lumshe ido, a hankali ta sauke ajiyar zuciya ba na komai ba sai na gannin yannayin yayanta , irin yanda yake da sarar lumshe ido a dukan motsinsa


Fitowar mama sanye da dogon hijab dinta har kasa rike da yar pos dinta ya saka Bilkisu dan dakatawa da harhadawa Zeinab abinci a plat


Mama ta ce" Bilkisu zamu je asibitin wajen yayanki, ki dora sabon girki kafin mu dawo "


Bilkisu ta ce" Ayah mama zan bi ku, na gama girkina fa tun da safe "


Mama ta yi murmushi ta girgiza kai ta ce" Ba guduwa ba zata yi tatinku, zamu dawo tare in sha Allah "


Ita dai Zeinab yannayin innocent face din yarinyar, da fatar jikinta, da tsarin halitarta uwa uba irin tarbiyarta ta birge ta, hakan ya sa ta yi ta janta a jikinta sosai tana jinta har cikin ranta, dan haka ta kamo hannayenta a hankali ta sakata cikin jikinta ta rungumeta sosai, muryarta sanyaye wace dukan abubuwan da ta tarar suka sanyayar mata da ita ta ce" zan dawo, ko da ke babyna "


'Kai wani dadi take ji gide idan tana ce mata babyna din nan iyeah, yau ga sha'ani sabo a gidansu da ganni tatin nan tata zata daure mata a Damagaram' Bilkissu ke ayannawa a kasan zuciyarta sai kuma ta saki murmushi ta masu rakiya har kusan motar kader


Kwarai ta yarda cewa ta bar waje, waje ya barta..........................   


A matsayinsu na masu takardu da aikin yi sun zo asibitin nan duda babar kalmar da ta fada cewa a je a ce masa *mahaifiyarsa ce* sai kawai a bita da kallo aman ba wani rawar jiki ko wani bada girma kamar yanda a yanzun da suka zo da Mama take gannin ikon Allah


Jin cewa ya shiga tiyata mai tsayin lokaci sai kawai mama ta nemi da gannin doctor din da baya cikin tiyatar tare da shi


Nan da nan ya zo cike da girmamawa ya gaishe da mama, 


Mama ta shaida masa cewa marar lafia ne suke tafe da shi, 

Ta yi nuni da Zeinab dake tsaye ta dora da fadin" Mahaifiyar Hisham ce a garin Niamey take aiki "


Da mamaki ya bi mama da kallo, dama ba ita ta haifi Boss ba?  Sai ya kasa jin wani farin cikin gannin maman Boss, sai kawai ya tsinci bakinsa da fadin " Aya, ina yini yaya aiki "


Daga haka sai ya maida dubansa wajen mama ya ce" Mama, ku je ku zauna ku huta zamu kula da marar lafiar har ya samu ganninta"


Godiya mama ta yi ta ja hannun Zeinab suka nufi office din HISHAM


Ba'a dakatar da su ba, saima bude masu da sekatariarsa ta yi suka shiga


A hankali take bin office din da kallo, kwarai ta so ta ga hotonsa a wannan tankamemen office din, sai dai babu, shin wace kama yake da ita a yanzu?


A hankali ta zauna saman kujera tana bin office din da kallo, so take ta tinano a cikin manya manyan da ta shiga offishinsu na wa ya kai na D'Anta kyau?


Hira suka ringa yi da Mama, duda yawancin hirar mama ke bata labarin irin abubuwan da suka faru bayan bata nan, sai tambayoyin da take yiwa maman wa'inda du yawanci a kan HISHAM ne


A kadan sun kwashe awani shida a office din nan domin har magariba ta kawo kai, sallah kadai ke tashinsu sai su koma su dora daga inda suka tsaya


Karar bude kofar shigowa ya saka su waigawa a tare


Da yannayin tafiar nan tasa kamar ya gaji yana jefa kafafunsa a hankali, da farar rigar likitoci, wuyansa dauke da abin tsinkayo numfashi, hannunsa sanye da safar likitoci, kafarsa sanye da farin takalmin likitoci, fuskarsa dauke da face mask manyan idannuwansa a fili yana lumshe su yana karrawa


Da dan sauri ya cire idannuwansa a kan fuskarta, irin kallon da ta kafe shi da shi da mikewar da ta yi tsaye da sauri ya saka masa bugawar zuciya

Ya kasa yarda da abinda yake ganni a gabansa


*MAHAIFIYA* Kalma mai girma da daraja, kalmar da ba kowa zai amsa idan aka kire shi da hakan ba, abinda duban jama'a ke kai goshinsu kasa su roki Allah ya sa zasu ga ranar da zasu kasance *MAHAIFIYA* Girma, daraja, daukaka, irin na Mahaifiya, yau shima gashi tsaye a wajen da wace aka ce ita ce ta yi nakudarsa ta kawo shi duniya 

*ASHE TANA RAYE?*

*ME YA YI MATA DA ZAFI?*

*KO ZAFIN NEMA NE YA SAKATA YIN FATALI DA SHI?*

*SHIN IDAN YA KALETA YA KIRETA DA MAHAIFIYA BAI TAFKA KUSKURE BA KUWA?*

*UMANSA ASMA'UL HUSNAH CE, UMANSA NURIYAH CE, WACE YA JI DUMIN JIKINTA ASMA'U CE MAMANSA ITA CE ASMA'U*


A hankali ya karasa kusa da mama sosai har kamar zai zauna jikinta irin kusancin da ya hadasa a tsakaninsu


Dukawa ya yi kamar yanda ya saba a hankali ya dora kansa saman cinyarta, muryarsa sanyaye ya ce" To yanzu da kika fito tun dazun wa zai tirsasata ta ci abinci bayan kin san bata ci Mamana?"


Mama ta yi wani iri, du sai ta daburce ta kasa bashi amsa, hannayenta ta saka ta dago fuskarsa a tafin hannayen nata ta sauke dubanta a saman fuskarsa, nan take ta karanci irin bacin ran dake tatare da shi bayan tarin gajiya, haka kuma ta karanci wani yannayi mai nuni da tsoro da fargaba da tashin hankali a tatare da yaron nata


Muryarta ta sanyaya sosai ta kara rike Fuskarsa a tafin hannayenta duda nauyin da ta masa kuwa ta ce" Ban horeka da haka ba, kai ka san me ya kawo ni , ko kamaninmu zai shaida maka , ka kiyaye kar bacin rai ya saka ka aikata aikin da Allah zai kona ka HISHAM!"


ZEINAB dake tsaye baki daya abubuwa ne suka dagule mata, tambayar kanta take hala fushi yake da ita? Mamakin girman yaronta take, mamakin irin nutsuwa da tarin lafia dake tatare da shi take, a kamanin mahaifinsa lebe ne da manyan idannuwa kawai suka bambanta


Baki daya hannunta ne ya dauki rawa a hankali ta karasa ta dora hannun nata gefen kafadarsa muryarta na rawa rawa ta ce" HISHAM, baka gane ni ba ? Ni ce Mamanka fa? "


Da mamaki matuka ya buda jajayen idannuwansa ya sauke a saman fuskarta, mamansa? Yanzun ita ne ta budi baki a gaban Mama ta furta cewa ita ce mamansa? Ita dake kwabarsa ta ce da shi kar ta ji kar ta gani ya kireta da mama ne yau take fadin ita ce mamansa? Sai kawai ya yi tunanin yanzun da a wani mumunan Hali ta same shi anya zata so a rabata da shi a matsayin d'a? Waima me ya mata ne? 


Nan take ya ji duniyar ta yi masa zafi, a hankali ya kai dubansa wajen Mama, ya kuma mayar kan Zainab, sai abu daya ya shiga cikin kwakwaluwarsa, kasancewarsa mutun mai saurin fadin abinda ya tsaye masa a kasan zuciya sai ya kara gyara tsugunnonsa sannan ya dan zame hannunta dake gefen kafadarsa a sanyaye ya ce" Ina yini? Ya hanya? Yaya aiki? "


Dubansa ya mayar wajen mama ya kara sanyaya muryarsa ya ce" Ki tashi Kader ya maida ku gida dan ALLAH mamana ko zaki matsa mata ta ci abinci, ina ji a jikina tana cen tana gadin zuwanku, zan je na kula da marar lafiar da ta kawo domin na san tati bata son wasa da aikinta, na yi maza na gama masu komai su juya "


Yana gama fada ya mike tsaye ya juya da sauri hakan ya saka Mama wangalar baki cike da mamaki


Da sauri ta mike tsaye da niyar binsa dan kuwa ita bata ga wani damuwa dan Zainab ta kire shi da D'Anta ba, ai danta ne, kuma uwa ta fi gaban haka, bata kai ga fita ba Zainab ta saka hannayenta ta rikota


Da sauri mama ta juyo tana kallonta, tana shirin yin  magana Zainab ta ce"


   

No comments