SHINE SILAH 46-50
*PAGE* 46-50
.........................📖Tunani mata kin da ya kamata ya d'auka d'akin sa yaje ya kwanta yana jin zuciyar sa ba dad'i to yanzu shike nan ya rabo da Najma yana son zuwa gurinta amma besan meyasa ya kasa zuwa ba ido ya rintse cike da tashin hankali yarasa me yake masa dad'i a duniya,
Tunda ya shiga dakin nasa ya zauna yaki fitowa ko ina saida safe, ba irin neman da Khairat bata mishi ba amma bata ganshi ba, tana zaune gaban madubi tana kwali ya yashigo ko salama babu tana kalonsa ya bud'e sif ya zaro kayan sa yashiga toilet yayi wanka duk tana zaune ya fito yazo har gaban madubin ya shafa mai da turaruka ya dau kayansa yasa,
Yazo fita Khairat tace "jimana" tsaya wa yayi ba tare da ya juyoba ta mik'e ta taka har gaban sa tana gyara masa hula tace "to hakimu sai ina?" Harara ya watsa mata yace "sunana Najib karki kuskura ki k'ara kirana hakimu kuma bake kika haifa ni ba bare na zauna na sanar dace ida zani" ya keb'e ta ya huce.
Da kalo Khairat ta bishi tace lalai d'an zaki ya girma yaushe nayi wannan saken har kake iya maida mun da marta ni to wallahi da ga kai har tsohuwar taka saina koya muku hankali bakusan wace Khairat ba,
Haka taita sak'a da mugun zare harta tsaida matsayar meya kamata tayi.
Shikuwa Najib yana fita gidan Ahmad ya nufa cikin sa'a ya tadda shi be fita office ba ya same shi a d'akin sa.
Sama-sama suka gaisa kafin Najib ya k'arfin halin cewa "kayi hakuri abokina nayi kuskure na yanke hukunci a cikin fushi amma kaya femun" murmushi me ciwo Ahmad yayi yace "ni baka mun laifi ba Najib matar da ka saki ita kayiwa laifi ita zaka bawa hakuri" shiru yayi kafin yace "harga Allah lokacin dana auri Najma auran sha'awa ne shiyasa tun farko banyi gagancin barinta ta haihu da wuri ta tsufa ba daga baya dana aureta halinta na kirki yasa na fara sonta amma wallahi basan ina son Najma ba saida na sake ta yanzu na sani ko komawa nayi gareta bazata saurare niba" dafashi Ahmad yayi yace "tabbas Najib ka tabka babban kuskure kuma a cutar da 'yar mutane amma koda Najma bazata saurare kaba kaje ka nemi yafiyarta sabuda ka cutar da ita" "a'a Ahmad bazan iya zuwa in bata hakuri ba amma kai kaje pls" murmushin mugunta Ahmad yayi yace "is okay hakan ma yayi zanje na sameta" "okay nagode" nan suka sha hirarsu kamar ba abunda ya tab'a shiga tsaka ninsu.
Ummi ce tasa Najma a gaba tai mata nasiha kan ta kwantar da hankalinta ta mik'awa Allah lamarinta shine zai mata sakayya da canjin mafi alkairi,
Nasihar Ummi ta ratsata ta daina kukan da takeyi ta dage da addu'a kan Allah yai mata canjin alkairi duk da 'kasan zuciyar ta akwai so da k'aunar Najib amma tana rokon Allah ya yaye mata son sa a zuciyar ta ko ta samu salama.
2weeks da sakinta Ahmad yazo gidan da farko Najma kin harda tayi ta fito saida Ummi ta mata magana sannan ta mik'e tasa hijab tafita,
Har k'asa ta gaida shi ya amsa fuskar sa cike da annuri yace "ya mutan gidan su Annur da Noor" murmushi tayi tace "duk lafiyar su k'alau" "to masha Allah, da farko nazo na baki hakuri da neman yafiya akan abunda ya faru nasan sakin da Najib ya miki nine SILAH da ban aika miki sako ba da duk haka bata faruba" hawaye ta share tace "ayyah ba haka bane dama can Allah ya k'adara aure na da Najib ba mai tsayi bane kuma in ma kan sakone kome nema ai SHINE SILAH da ya juya mun baya amma Allah ya na nan kuma baya bacci shi zai saka mun abunda suka mun shida matarsa" cikin tsananin tausayinta Ahmad yace "hakane amma duk da haka kiya femun" "na yafe maka amma kaima ka yafe mun shiga tsaka ninka da abokin ka da nayi" murmushi yayi yace "ai mun shirya shine ma ya aikoni biki" annurin kan fuskar ta ne ya b'ace Ahmad yasa dariya yaringa tsokanarta harta saki jiki suka sha hirarsu.
Gidan Najib kuwa
Komai ya koma sai abunda Khairat tace shi Najib ma ya koma d'an kalo komai Khairat ce keyi a gidan shi damura sa d'aya yanzu kawai ya samu haihu Allah ya d'ora masa son yara yanzu kamar me da Khairat ta fahimci haka shine fa ta fara laulayin k'arya nan ya rikice sai abunda tace shi za'ayi,
Yau ma kamar kulum suna zaune a parlour Khairat tayi ma tashin kai da cinyar sa sai kwar kwasa take masa salamar Mami sukaji Najib ya amsa amma ita hakimar ko d'agowa batayi ta kaleta ba, zama Mami tayi tace "Khairat baki ji shigowa ta bane ko bacci take?" Ta tanbayi Najib "A'a Mami hutawa take bata son takura ne"
Baki Mami ta saki tace "ke dan uban ki baki san nashi goba?" Fuska Khairat ta yamutsa tace "Dear wai wace take mun ihu akaina?" "Mami ce fa taz......!" Muryar Mami da yaji ne yasa shi kama bakin sa "uwarki Maryam ita tazo dan ubanki" mik'ewa zaune Khairat tayi tace "gaskiya Hajiya karki k'ara zagar mun uwa wallahi sabuda aka uwa ta zan iya keta rigar mutun cin koma waye wallahi" "Khairat ni kike fad'a wan nan maganar?" Tsaki Khairat taja tace "mtsss Dear muje kitchen baby yana son cin dan kali soyaye" mik'ewa yayi yace "to jeki bara mu gaisa da Mami" harara ta watsa masa tace "saika zab'a 'dan cikin nawa kake so ko ita" bita yayi suka shiga kitchen sun jima Mami tana zaune a gurin ta kasa tashi sai tafa hannu takeyi.
Najib ne ya fito yaganta k'ara sawa yayi yace "A Mami baki tafi ba?" Kasa magana Mami tayi dan ta kaici yace "kiyi hakuri Mami kinsan masu ciki da fad'a itama bayin kanta bane cike ne yake sata fad'a amma kiyi hakuri" mik'ewa Mami tayi tace muje waje ina son magana da kai" carab sukaji Khairat tace "Dear baby bacci yakeji muje kamun wanka mu kwanta" ko Mami bata kala ba taja han nun Najib suka shige bedroom harda b'amo kofa,
Mami dake tsaye kamar gunki tana huci ta fice a matu k'ar zuciye ta tafi gida Amina da Aysha ta samu a gida ko mayafi bata ajiye ba tace "umar ni nake baku ba sawara ba ku tashi yanzu kuje gidan Hajiya Maryam Maman su Khairat ku zage mun ita ta uwa ta uba idan baku jeba ban yafe muku ba" kalon juna sukayi kafin Aysha tai k'arfin halin cewa "Mami Hajiya fa............!
COMMENTS
AND
SHARE
by
*XAHRA*
No comments