YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 32-33
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA ☘️☘️*
*PAGE 32-33*
------- Sosai ya shagala da kallon yarinyar nan har yaji wani abu na jansa dan haka baisan sanda yatafi gurin yaranba gaban yarinyar yaje yaduqa ya kama hanunta ya riqe yana kallon ta yana murmushi, itako yarinya kasacwar bata sanshiba saita sa ihu, iyayen yaranne da suke nasu sha'anin a gefe, suka taho gurin yaran aguje, cikin harshen turanci uban yarinyar ya tambayi ABUDULJABBAR dame yake
faruwa shiko ABUDULJABBAR sosai ya shagala da kallonta yana murmushi shi d'aya bai sanma ancika akansa ba, dan haka cikin zafin nama uban yarinyar ya ture ABUDULJABBAR ya wuntsila qasa agurin nan kowa dake gurin yasa dariya alokacin ne ABUDULJABBAR ya dawo haiyacinsa sai shima yake tambayarsu me yake faruwa? Uwar yarinyar ne ta yarfa masa mari cikin masifa take tambayarsa mai yayiwa 'yarta da har yarinyar ta take kuka wato irin sune masubi hotel-hotel suna 'bata qanan yara.Nan fa qaramar magana ta zama babba inda har ake batun qiran police dan kuwa basu yarda da ABUDULJABBAR ba, sai da ma aikatan hotel d'in suka tabbatar da shima aciki yake, sanan iyayen yaran suka qaleshi tare da masa kashedi akan 'ya'yansu domin sun lura shi ba yarensu bane, shima ABUDULJABBAR da yasan bai da gaskiya haquri ya basu yace yaga yarinyar tayi kama da qanwarsa ne shi yasa yazo gurin ta.
Haka de yasamu ya koma ciki yana mamakin kansa da kansa dan haka tin daga ranar bai kuma leqa harabar hotel d'in ba sai de infita zaiyi.
Yaukam ko da daddy ya koma 'bangaren Mum bai ma nemeta ba da yaga ma abunda zaiyi sai yayi kwanciyarsa abunsa a d'akinsa, itama MUM fita aharkarsa tayi sbd tana fishi dashi sosai amma da ta tuno da ABUDULJABBAR sai tatashi ta nufi d'akin daddy sallama tayi tashiga ta zauna a bakin gadon shiko daddy yana ganinta ya juya baya abunsa.
Cikin 'bacin rai Mum tace " eh ai dole kajuya baya tinda kaga dodo, ai duk wanda yaci moriyar ganga dole ya yada korenta sbd haka ba wanan bace ta kawoni ina so ne insan ina d'ana ABUDULJABBAR yatafi batare da yayimin sallama ba, domin baya haka"?
Da daddy kamar bazai kula taba sai kuma yace " shi yaronaki kindamu da shine bare kisan ina yatafi to bara kiji kamar yanda bakisan inda yake ba haka nima kema baki sani ba, bare ni kuma bare"
"Wlh Alhaji qarya ne kasan inda ABUDULJABBAR yake sbd haka ka fad'amin ina d'ana ABUDULJABBAR?
Domin naga sbd ka auri karuwa hatta 'ya'yana sokakeyi karabani dasu tinda kamayar da IKIRAM 'bangaren karuw.....
"Ki iya bakinki Murjanatu karki kuskura kisake qiran matata da karuwa inba haka ba tabbas ranki zai 'baci.
"Cikin masifa Mum tatashi tace " nafad'a karuwa danko wanan daga gani agidan karuwai ka aurota dan kuwa ni Murjanatu banga alamun tana da usuli ba kuma wlh kadowomin da 'ya'yana domin basuyi gadon karuwanci ba dan haka baza akoyar dasu ba"
"Cikin masifa Daddy yace " Rahama Amaryata 'yar asali ce kije tudun wada kibincika anan asalinsu yake amma rayuwarsu sunyita ne a Lagos, rasuwar mijinta yasa tadawo nan tare da 'ya'yanta uku, maza biyu mace d'aya, kuma duk zasu dawo nan da zama dan kuwa marayune kuma riqon maraya Akwai lada"
"Qarya kake Alhaji baka isaba ba wani shegen agola da za akawo gidan nan wlh domin kuwa gida nawa ne daga ni sai 'ya'ya na"
"To ai sai kihana Murjanatu tinda ke kika ginamin gidan to bara kiji wlh ko sunfi su uku sai na riqesu domin ina son mahaifiyarsu dan kuwa tasani farin cikin da ke kika kasa sani, kinbiyewa surukarki marar mutunci sbd haka kuje can ku qare qalau nidai nawa ido domin wanan yarinyar ba matar arziqi bace, kuma wlh ABUDULJABBAR very soon aure zaiyi dan bazan sa ido rayuwar d'ana ya tagaiyara ba"
"Ai kuwa kamakaro domin in ni na haifi ABUDULJABBAR bai isa yaqara aure ba, inkuwa yaqi tabbas sai yabiyani nono na da yasha domin kuwa FINAH itace za'bina itace suruka mafi soyuwa araina sbd haka ita ta dace da d'ana ABUDULJABBAR"
Hanyar fita daddy ya nuna mata yace " maza kifita kafin inuna miki nawa rashin hankalin kuma sai naga qarshen rashin hankalin ki, zanga wa kika fi so ABUDULJABBAR ko mahaukaciyar surukarki irinki?" Sanan Daddy ya kora Mum waje ya sawa d'akinsa key aranar de bawanda ya runtsa daga MUM har daddy.
Washe gari kuwa FINAH tatashi da rigimar sai anfad'a mata inda mijinta ya tafi, ita de Mum kitchen ta shiga ta had'a musu abun kari ita da FINAH inda FINAH ta botsare taqi cin komai wai ita mijinta takeson gani.
Nan Mum tahau lalashinta akan ta kwantar da hankalinta ai koma ina yaje dolensa yadawo, aikuwa FINAH ta hau zage-zage tana cewa " ai ni nagane sbd ba ason zama na dashi shi yasa aka zigashi yabar garin kuma wlh ni da ABUDULJABBAR mutu karaba" itama Mum sai tayata takeyi suna ta habaice-habaice, ana cikin haka daddy ya sauqo zaifita MUM tasha gaban sa ta tada masifar sai ya gaya mata ina d'anta ko kuma yabata number d'insa da yasanja domin ainihin layinsa bai zuwa.
Daddy kuwa cewa " yayi ni bansan inda yake ba kuma bani da Number sa amma idan matarsa taga baza ta iyaba to tayi magana domin araba auren"
Haba wa ina wuta Mum ta tsindima daddy nanfa tahau jaraba tana cewa "to inma abunda kuka qulla kenan ka fad'a masa shi da FINAH sunzama auren zobe ba rabuwa ko bayan raina ya saki FINAH banyafe masa ba domin itace za'bina"
Shiko Daddy ko takansu bai sake biba ya fice abunsa ya nufi 'bangaren Anti Amarya inda takawo masa girki ya kwasa yai wucewarsa kasuwa yana zuwa kasuwa ya qira ABUDULJABBAR awaya ya zaiya ne masa komai yanda sukayi da MUM, nan hankalin ABUDULJABBAR ya tashi domin shi kam yayi alqawari ya gama had'a jiki da FINAH tinda bata son jininsa dan haka yasan me zaiyi tabbas FINAH sai tagaji dan karan kanta tanemi saki da kanta domin aurenta bai qareshi da komai ba sai had'ashi fad'a da mahaifiyarsa. Shi kad'ai ABUDULJABBAR ya raya hakan azuciyarsa, shi de daddy haquri ya bashi tare da yimasa nasiha ya kashe wayarsa.
Haka daddy ya gama kwana biyunsa a 'bangaren MUM kullum cikin fad'a tamkar qananan yara, harya tatara ya dawo 'bangaren amaryarsa inda suka ci gaba da amarcinsu, su ma su 'YAR AMANA ya sa mamusu wani driver yana kaisu school ya dawo dasu tare da yaran Amaryarsa domin ya sata ta kwaso yaranta, in da yasa su wata school da bata kai da bata kai ta su 'YAR AMANA kud'i ba.
MUM kuwa dan baqin ciki tamkar ta mutu inda FINAH ke qara zugata kullum idan daddy ya fita su IKIRAM suka tafi makaranta sai sunje sunciwa amaryar daddy mutunci itako bata kulasu kuma bata ta'ba fad'awa daddy ba.
Ayanzukam sai de muce Alhamdulillah domin 'YAR AMANA ta kwantar da hankalinta sosai tana karatunta kuma tana ganewa dan kuwa IKIRAM na sake ko ya mata haka ma Amaryar daddy, dan kuwa Daddy yace mata yanaso ta wayar masa da kan 'YAR AMANA sosai ta zama mace mai class da sanin abunda takeyi duk da daddy ya 'boyewa Amaryar tasa matsayin 'YAR AMANA agidan, Amma Amaryar daddy ta gano da wata a qasa dan haka ta tsaya tsayin daka akan NUSAIBA ganin ta wayar mata dakai dan kuwa yanzu NUSAIBA har turanci ta fara iyawa, gashi akullum jikinta qara murjewa ya keyi, Mum da FINAH kuwa harma sun manta da wata 'YAR AMANA agidan, domin kuwa IKIRAM tana shiga gunsu amma ita 'YAR AMANA sam-sam bata yarda ta shiga, sai wata rana adole, IKIRAM tajata suka shiga 'bangaren su Mum tare ai kuwa Mum da FINAH suna parlour dan haka suka ce da wa zasuyi inba da 'YAR AMANA ba domin sun tsorata da kyawunta da kuma nutsuwarta uwa uba wayewa cikin watanni da basu fi biyu ba amma tawaye ta sanja kamar ba wanan aljanar yarinyar ba, dan haka FINAH taita zaginta tana cewa" banza maiya marar zuciya ankoreki amma kinqi komawa qauyenku andeyi asara wlh dangin maita kawai" itako 'YAR AMANA ko ajikinta, IKIRAM ce ta kalleta tace " haba Anti ya kike zagin NUSAIBA haka karfa kimanta ita d'infa dangin daddy ce kenan shima daddy mayene?
Mum ce ta doki bakinta cikin masifa tace "to sai me qarya akayimusu dangin ubanaki ba mayunbane ai wanan yarinyar daga ganin idonta itama maiyarce kuma wlh jikokina sunfi qarfinku saide kilashe wa 'yanda kike tare dasu munafukai kawai"
Ita kuwa FINAH cewa tayi Mum dubi jikin mayarnan Inda ya nuna alamun hutu, ai ni wlh wankin kayana zanbata tinda dama ankorar mana mai wanki sunan natarasu da yawa danni ban iya wahalar sa kaya a machine sanan in matse in shanya"
"Eh mana bata miye amfaninta ai yanzu munsami 'YAR AIKI maiya kawai nan fa FINAH tai ta fito da tilin kayanta takai gurin da suke wanki, AI kuwa MUM tasa 'YAR AMANA agaba harda dukka tafara wanke kayanan, koda IKIRAM tazo zata tayata nan itama Mum tarufeta da dukka ta koreta kuma tace ta yafeta amunafukar amaryar daddy tinda itama ta zama muna fuka, nan IKIRAM taje da kuka tafad'awa Amaryar daddy komai, habawa dama itama Amaryar daddy tagaji da iskancinsu dan haka tabiyo IKIRAM suka taho nanfa tatsaya akan Mum tace " maza kuban 'YAR AMANA ta mutafi 'bangarena domin kuwa AMANAR ta mijina ya bani dan haka banyarda wani yasata aiki ba"
Nanfa mum ta shiga zagin Anti Amarya harda gori iri-iri, itako Anti Amarya bangaje Mum tayi tawuce ta ruqo hanun 'YAR AMANA zasu fice FINAH tazo da sauri ta make hanun Anti Amarya ta cika 'YAR AMANA, ai kuwa Anti Amarya na juyowa ta yarfe FINAH da mari, nanfa FINAH ta shiga zagin Amaryar daddy wai karuwa ce harda 'ya'yan shegu ta kwaso ta kawo.
Itako Amaryar daddy tace "eh gwanda ni ina da shegun ke ina naki shegun shegiya juya annoba baki haifaba amma kin addabi mutane kin hanasu zaman lafiya dan haka kiyi zuciya ki haifa kema.
Nan Mum itama taringa zagin Amaryar daddy, itako IKIRAM hanun 'YAR AMANA takama Suka fice agurin domin sunsan Anti Amarya zata iya dasu.
FINAH kuwa kuka tasa wiwi wai Amaryar daddy ta mata gorin haihuwa Inda Mum ta rud'e tace saita kashe 'YAR AMANA domin itace silar komai........
Hhmm muje de zuwa domin kuwa da sauran rina akaba.
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups nagode
No comments
No Typing
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*
No comments