SHINE SILAH 41-45
PAGE 41-45
📖Yana gama fad'in haka ya fice daga d'akin ya barta a zaune agurin
Gaba 'daya Najma ta fita hayacinta dan bata gane me meyake faruwa da ita hawaye ne kawai suke anba liya a fuskarta a hankali ta futa "inalilahi wa'ina ilaihirraji'un wai sakina kayi Najib menai maka da zafi haka wane laifin nai maka a rayuwa ka tsane ni why" sai yanzu tasaki kuka me sauki ta kifa kanta a kan bad tana kuka me tsuma zuciya gani take kamar mafarki take amma wai da gaske ne Najib ya sake ta zuciyar ta tadafe wadda take bugawa d'a k'arfi tana cewa "tukucin soyayya ta a gareka kabani Najib shine saki ka cutar da rayuwa ta baka yiwa zuciyar da take sonka a dalci ba"
Haka takoma kamar zararriya ta ringa sunba tu ita kad'ai duk wadda ya ganta a lokacin saiya tausa ya mata
Shi kuwa Najib a parlour Khairat ya zauna yana jin zuciyar sa ba dad'i laifin da Najma ta mai bekai na saki ba amma meyasa ya sake ta in ma haihuwa yake so tayi SHINE SILAH da bata haihu ba shiya ringa bata maganin planing a 'boye bayan in plan da ya kaita aka sa mata yasan son da take masa ne yasa ta yarda dashi a lokacin yanzu shi meya ai kata bayan yasan har yanzu yana sonta amma ya sake ta yana cikin wannan tunane-tunanen bacci yai awan gaba dashi mafarki yayi wai Najma tayi aure harta haifi 'ya'ya a firgice ya farka ya mik'e a gigice yashiga part dinta amma me bakowa a ciki Najma ta d'ebi kayanta na sawa dana anfani ta tafi
Komawa yayi parlour ya zauna yarasa meya ke masa dad'i yabita gida ko ya rabu da ita Khairat ce ta shigo tana kalonsa tace "wai meyake faruwa ne" hannu ta ya kamo ta zauna kusa dashi yace "nasaki Najma" tab'e baki tayi tace "garin yaya?" "Amanata suke ci da Ahmad shiyasa na yake shawarar rabuwa da ita" "wannan yayi daidai mene anfanin zama da mazinata a gida yanzu kawai ka tashi muje kafi abinci" hannuta ya saki yace "bazan ciba" lallab'a shi ta ringayi har ya yarda yakoma part 'dinta tana ta mishi murmushin keta dan yau burinta ya cika ta rabasu ko yau ya saketa taci riba"
Najma tana shiga gida da Yaya Nura taci karo kasa mashi magana tayi ta huce shi yabita da kalo cike da mamaki kafin ya mik'e yabi bayanta a parlour ya tadda ita Ummi na tanba yarta tayi shiru zama Yaya Nura yayi yace "idan baza kiyi wa mutane magana ba bari na kira Najib 'din shi saiya fad'a mun meya had'aku kika kwaso kaya kika taho" da sauri Najma tace "Aa Yaya karka kirashi ina rokon ma dan Allah ka goge number sa a wayarka" wayarsa ya dako yana cewa idan kinga na fasa kiran sa to kin sanar da mu abunda ya faru" ganin da gaske yake kiran Najib zaiyi tace "karka kirashi Yaya ya sakeni kuma yace ya tsani ya tsani kuwa nawa har Baba yace wa 'dan ......" sai lokacin tasaki kuka salati Ummi da Yaya Nura suka saka Ummi tai karfin halin cewa "meya had'aku ya sakeki?" Kwashe komai tayi ta sanar dasu sun san Najma baza tayi musu 'karya ba shiyasa jikin su duk yayi sanyi Yaya Nura yace "yanzu duk Soyayyar dake tsaka ninku ko shekara biyu baku rufa ba ace anyi auren angama" "tashi ki shiga ciki" Ummi tace da ita mik'ewa tayi tana kuka tashiga d'aki
Ummi ta kali Yaya Nura take "Dan Allah Nura idan kunyi aure kuyi hakuri narasa meyasa auren yaran zamani baya 'karko ace aure wata biyu ko uku yake mutuwa wadda ya jima shine yake shekara bayan anyi soyayya kamar a cinye juna a waje meyake kawo haka? ni jikar mutum hud'u" ajiyar zuciya Yaya Nura yayi yace "k'aryar da muka 'dorawa kanmu ce tun farko ya kamata kowa yafito da ainayin halinsa da kaman ninsa maza zaka samu suna k'aryar kayan sawa abun hawa da cewa su masu kud'ine abun da ke damun matan mu kuma da yawan su wata bak'ace ta koma fara sai anyi aure mijin ya gano bak'a ce bayan ara'a yinsa farar mace yake so dayawa 'yayan mu na Hausa wa basa fito da ai nihin surarsu zakaga hips brez gashi da haske duk na bogini bayan shikuma Namiji ga dan abunda ya aureki ba gaskiya bane kinga dole asamu matsa" "hakane kuma yaran yanzu sun 'dauka aure jin dadi ne kawai ba kalo bale a ciki kiji yarinya za'ayi auren ta tace za'a kaita gidan dad'i gidan dad'i ne amma gidan ibada da hakuri ne kalu balen dake cikin aure yafi dad'in sa yawa Allah yasa mu ringa kai zuciyo yonmu nesa muyi hakuri da abokan zaman mu" "ameen Ummi Allah ya kawo k'ashen mace-macen aure da muke fama da su" "ameen ya Allah" nan suka cigaba da jajan tawa juna ita dai Najma tana 'daki tana aikin kuka.
Ahmad yana zaune a kan bad ya tunanin butul ci rin na abokin nashi shi gowar message yagani ya 'dauka yaga Number Najib bud'ewa yayi ya fara karan tawa kamar haka
BAN TAB'A TUNANIN ZAKA CI AMANA TA DA KAI DA NAJMA BA AMMA ALLAH YA TONA MUKU ASIRI DAN HAKA NA SAKAR MAKA ITA KUJE KU CIGA BA DA FASIKAN CIN A WAJE.
Ran Ahmad in yai dubu ya b'aci kiran Najib ya farayi amma wayarsa a kashe huci ya ringa yi kafin ya miki ya 'dauki mukulin mota ya fice daga gidan.
Kai tsaye gidan Najib ya nufa a kofar gidan yayi parking yace da me gadi yaki rawo masa Najib bazai shiga gidan ba,
Me gadi ne yaje ya sanar da Najib Ahmad na waje na jiransa da kamar ba zai jeba sai kuma ya mik'e ya fita.
Kalo d'aya Ahmad yai wa Najib ya 'dauke kai kafin ya amsa salamar da Najib din yayi yace "da gaske ne abunda katuro min yanzu a message?" cikin rashin fahimta Najib yace "waye yai maka message kuma?" "Ya zan tan bayeka ka dawo min da tab baya, cewa nayi kaine kamun wannan message d'in" amsar wayar da yake mik'o masa yayi ya karanta message d'in yace "gaskiya basan waye yama wannan message d'in ba amma kuma naga number tace" murmushin ta kaici Ahmad yayi yace "to ina wayar taka?" "Tana d'akin Khairat nasa caji" "hmm kasaki Najma ko?" fuska Najib ya had'e ya zaro pepper a alji hunsa ya jefawa Ahmad
D'auka yayi ya karanta yayi murmushi yace "Najib ya kamata ka far ka daga baccin da kake kamar yadda baka da alak'a da sakon wayata haka nima bani da alak'a da wannan takar dar amma ka zauna kayi tunani meyake faruwa da kai suwaye a zagaye da kai ni bazan cema komai ba kai zaka nemowa kanka solution"
Yana gama fad'in haka ya juya ya shiga motarsa yabar gurin
Shiru Najib yayi yana nazarin magan ganun Ahmad to wana irin tunani Ahmad ya keso yayi akan sakin Najma ko yaya? To suwaye na zagaye dashi? shiru yayi tuna d'azu yaji Khairat tana. waya da Mami tana cewa "Aikin ki ya kamala Hajiya ta amma duk da nima aikin nawa ne gaskiya saikin salame ni" ta kama dariya kuma tajin motsin sa ta kashe wayar, wane irin aiki take magana? Ya 'kara tan bayar kansa ganin bashi da amsa ya juya cikin gidan yana...........!
COMMENTS
AND
SHARE
by
*XAHRA*
No comments