YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 30-31
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
*PAGE 30-31*
___ Abakin gate d'in gidansu ta tsayar da motar ta tana danna hon kamar zata tashi sama, aguje maigadi ya bud'e mata get d'in gidan tashige da motar ta. Parking d'in motar tayi a parking space dake cikin gidan sanan tafata da d'an sauri-sauri da gudu-gudu tana kwalla qiran sunan
"Mum! Mum!!
Harta shige babban parlour d'in gidan bako sallama, Mum d'inta kuwa dake zauna akan kujera tana kallo da remote ahanunta da sauri tatashi tana cewa " lafiya FINAH kike min wanan qiran?"
Aguje tafad'a jikin Mum d'in nata ta fashe da kuka.
Haba FINAH kifad'amin mana menene kinfasan bama son damuwarki fad'amin me kikeso my only one daughter?"
"Mum ABUDULJABBAR ne?
"ABUDULJABBAR kuma me yasa meshi?"
"Mum yau kwana biyu bansa mijina a idona ba kuma bai sanar mana yayi tafiya ba"
"To shi ABUDULJABBAR yaro ne da za' a nemeshi a rasa qilade yatafi wani wajenne" inji Abban FINAHdake sauqowa daga beni, da gudu FINAH ta nufi Abban nata ta rungumeshi bubuga bayan ta yayi yace cool down my lovely daughter meme kefaruwa?"
"Abbah ABUDULJABBAR ne baifa sanarmana zashi wani guriba ni da Mum d'insa yau kwana biyu kenan bamu ganshiba shine nake tsoron karshima aure yayi tare da daddynsa ya 'boyemin"
"Murmushi Abban FINAH yayi sanan yace " FINAH rigima ki kwantar da hankalinki mijinki baiyi aure ba domin da yayi zamu samu labari amma karki damu zansa a bincikamin inda yatafi haka ba sallama"
"Yauwa Abbana nasan zaka iya"
Sallama yayi musu ita da Mum d'inta yafice a gidan.
FINAH kuwa ita da Mum d'inta zama sukayi suna tazancen auren daddy ya qara inda sukai tayiwa MUM dariya, nan MUM d'in FINAH tace zata takar'bowa FINAH maganin mallaka ta mallake ABUDULJABBAR Ya zama na baison ko wata 'ya mace sai ita kad'ai, haka de sukayi ta qulle-qullensu abunsu har yamma tayi FINAH takoma gida.
Tana komawa ta iske MUM a zaune a parlour ita d'aya tayi tagumi, kallon Mum FINAH tayi tace " lafiya Mum menene?
"Hhmm FINAH ba dole nayi tagumi fa ki dubafa tin jiya da daddare da daddynku yashiga gurin tsinaniyar amaryarcan dangin bariki har yanzu bai fito ba, nama tambayi maigadi yace min yau Alhaji ko sallar Asuba bai jeba shi da Sallah bata wuceshi, Sanan ni IKIRAM ma bansan inda yakaita ba, ga ABUDULJABBAR shima kwana biyu ban sashi a idona ba"
Mum taqare maganar tana kwalla.
Ita ko FINAH dariyarta ta 'boye sanan tace " to yanzu Mum haka zaki sa ido kina kallansu bazakiyi maganin suba? Nifa Mum dama na dad'e da gano daddy ba sonki yakeyi ba kawai de zaman haquri yakeyi dake sbd yaranki"
"To yanzu FINAH ni yazanyi ni nasan mijina yana sona saide inshiga tsakaninmu akayi"
Juyawa FINAH tayi tayi, dariyarta sanan tajuyo ta kalli Mum tace " Mum kisande ina sonki tamkar uwar da ta haifeni?"
"Haka FINAH 'yata"
"Yauwa"
"Sbd haka tashi zakiyi muje muci uwarta muyi waje da ita tunkafin lokaci ya quremana, sanan shi kuma Daddy ki titsiyeshi akan sai ya dawo miki da yaranki domin yasan inda suke ai.
"A'a FINAH bazan iyaba matuqar daddynku yanan amma de zuwa gobe idan yafita maje mu sameta"
"To Shikenan Mum amma de wlh karde ki yarda ki zauna da kishiya abunda ba amiki ba tun yarinta sai yanzu da girma yazo ai sai qawayenki su Mum surainaki suma cireki a group d'in su na manyan mata"
"Shikenan FINAH 'yata 'yar Albarka nagode kuma inde inaraye ABUDULJABBAR bai isa yamiki kishiya ba"
Rungume Mum FINAH tayi tace " yauwa mumsay kin biyani"
Koda dare yayi Mum taita qiran wayar daddy akan tatambeyeshi ina 'ya'yanta, amma wayar taqaraci ringing d'inta ba a d'aga ba, adaranan kwana Mum tayi tana kukan kishin mijinta da kuma rashin yaranta akusa da ita dad'inta d'aya ma ga FINAH, akusa da ita.
Washe gari kuwa da safe misalin qarfe goma Mum da FINAH suka fito harabar gidan, Suka tambayi maigadi ko Daddy yafita, nan maigadi yace musu Eh amma da alamu ba nisa zaiyi ba dan da qafa ma yafita bai d'au motaba, ai kuwa da sauri suka nufi 'bangaren Amaryar suka qwanqwasa qofa, ita kuwa Amarya daga ciki tace " honey Ina zuwa"
Tana zuwa tana bud'e qofar Mum da FINAH suka danno ciki inda Mum ta d'aga hanunta ta shararawa Amaryar daddy mari tace " wanan na hana mijina shiga gurina ne" ta sake sharara mata wani tace wanan narabani da Mijina da yarana ne"
Itako FINAH me zatayi inba dariya ba sanan tadaka tsalle tace " Yauwa Mumsay aikinki yana kyau"
Sake d'aga hanun Mum tayi daniyar zata qara marin Amaryar daddy, sai Amaryar daddy tariqe hanun, itako Mum kallon Amaryar tayi daga sama harqasa sai taga kaya 'yan kantine ajikinta riga top mai bud'ad'en qirji an rubuta my Sweet agaban rigar da jan rubutu da sket na jins wanda ya matseta sosai kuma iya cinya siket d'in ya tsaya, ga Amaryar ba wata babba bace sosai dan Mum tafita nesa ba kusa ba amma de zata iya aurar da 'ya ashekarunta, wani ihu Mum tafasa tace "zangani ni Murjanatu bariki tsagwaro a gidana?
Itama FINAH kallon amaryar daddy tayi sama da qasa gaskiya abun yabata mamaki dan ko ita da yarintarta bata ta'ba yiwa mijinta irin wanan kwaliyar ba.
Itako Amaryar daddy cewa tayi "ai bariki tukkanama bakiga komai ba Hajiya kuma wlh marin nan da kikayimin kinci mitincin mijinki bazan rama ba domin dama ya lallasheni sbd yasan yana tare da karya mai haushi abunda nakeso dake kitattari tsiman qafarki kibar min shashina"
Cikin masifa Mum tace " ai wlh sai kinbar gidan nan yau d'inan tinda ba na ubanki bane tsinaniya karuwa dangin Arna kawai"
Haba FINAH ko me takeci inba Dariya ba sanan tace " ai wlh Mum karki yadda dan wanan daga ganinta ta gogu abarikinma"
Ai wani wawan duka Amaryar daddy tayiwa bakin FINAH sai ga bakin FINAH yana zubar da jinin azaba.
Haba Mum kuwa tace da wa zatayi tinda anta'ba mata 'Yar lelenta FINAH.
MUM ce ta kama Amaryar daddy da kukuwa sai ga Daddy yayi sallama ya shigo hanunsa d'auke da manyan ledodi.
Ai da gudu Amaryar daddy tafad'a jikin daddy tana kuka, shi kuwa Daddy rudewa yayi yana cewa "menene Rahama wa ya ta'bamin farin cikina cikin shagwa'ba ta nuna su Mum tace "ai matarkace ta qaremin zagi ita da matar d'anta sanan tamareni"
Mari kuma? my Rahama wlh bazan yarda da haka ba maza jeki rama kayanki ko na ramamiki ne da kaina?"
"A'a My Sweet kawai abarta ba dan komai ba saidan tana tare da wawiwar surukarta kaga idan d'anmu yaji labarin anyiwa mahaifyarsa haka agaban matarsa bazeji dad'iba sbd haka sufitarmin a d'aki kawai"
"Shikenan angama my Rahama"
Bubuga qafa Amaryar daddy tayi sanan tace cikin shagwa'ba "amma nace kadena kirana da sunanko"?
Shiko Daddy cewa yayi "angama my Sweet wife"
Da sauri Mum ta fice ad'akin tana kuka, itama FINAH tabi bayan ta.
Ayya MUM harkinban tausayi domin kishi da wayaiyar mace sai kinshirya😃
Haka yauma daddy da amaryarsa suka yini suna shan amarci domin kuwa yau girkinta zai qare ya koma 'bangaren Mum daddy kuwa duk yadamu domin kuwa amaryar tasa ta shayar dashi zuma mai dad'i.
Dan haka daddy da yamma yasa aka dawo da 'YAR AMANA da IKIRAM gida inda Mus'ab yakawo su amotarsa yaita tsokanar IKIRAM akan sai yadawo zance.
Daddy kuwa da yamman yasa IKIRAM takwaso kayan amfaninsu suka dawo 'bangaren Anti Amarya inda suke ta murna itama Amaryar daddy tana murna domin ta samu abokan hira tinda daddy 'bangaren MUM zai kwana yau.
*Italy*
ABUDULJABBAR kuwa yana isa qasar Italy, kai tsaye wani hotel yaje ya kama ya yada zango anan kwanansa biyu a hotel d'in baije ko inaba, yana cikin qunci Mum da FINAH amma ta 'bangare d'aya inya tuno 'YAR AMANA sai yajishi cikin nishad'i sbd shirmen yarinyar ba yanda inyatuno inda yabata soyayyen kwai take tambayarshi abincin aljanune ko na 'Yan aljanna? Maganar nasa shi nishad'i dan haka yarinyar tashiga ransa ta zauna daram duk harbawar da zuciyarsa zatayi sai ya Tina da ita, hakan yana bashi mamaki akan me zai damu da ita haka yakan tambayar kanshi kodan tana da haqqi akansane shiyasa?
Wata zuciyar takance dashi kawai idan kakoma Nigeria kasaketa kahutawa ranka da wanan shawarar zuciyar tashi ya aminta, sai wani tashin hankalin idan ya tuno da surorin jikin yarinyar sai yaji hankalinsa ya tashi sha'awarsa ta motsa dan haka kawai yau munday sai ya tashi da azumi domin rage sha'awa datake addabarsa, sanan ya takurawa zuciyarsa akan dole tadena tinanin 'YAR AMANA dan wani zubin har gizau take masa.
Yaude shiryawa yayi ya nufi school d'in da zai farayi ko da yaje ya gama komai da komai, akabashi class, kuma a computer suke karatun dan haka kasa yin komai ma yayi domin tinanin NUSAIBA ya hana shi sakat, da qar yasamu ya yakice ta kad'an arnsa yayi aikin dake gaban sa ya gama yadawo hotel d'in da yake ya watsa ruwa yaci abinci, ya fito harabar hotel d'in nan yaga yaran turawa 'yan mata - mata sa'anun su 'YAR AMANA suna wasaninsu acikin su wata tamasa kama da 'YAR AMANA sosai dan haka ya shagala da kallon ta........
Hhmm muje zuwa dan yanzu aka fara
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH WA ATUBU ILAIKA*🤲
No comments