Breaking News

SHARUZZAMAN 1 PAGE 3

 *BOOK (1)*

            _SHARUZZAMAN_🌟

_BINTU S££R_✍🏻

                      3️⃣

Wannan matar ce ta dazu ita da wata budurwa suka shigo  d'auke da wasu manyan jakunkuna guda biyu, innaro itama tuni ta farka tana zaune har suka shigo suka shiga d'aya daga cikin bedroom d'in dake d'akin sun jima ciki kafin suka fito, matar ta kalli innaro tace" ga kayan sawa nan  cikin wardrobe idan kuna da buk'ata" k'ada musu kai kawai tayi don itama yanzu abun ya soma bata mamaki tashi guda mutum ya tsincesu a titi ya d'aukosu yana musu

wannan hidima, anya kuwa babu abunda yake nufi dasu, abunda ya soma d'arsuwa a zuciyarta kenan, tashi guda wani azabebben tsoro ya soma shigarta ta d'aga kanta tana kuma k'arewa ko'ina na d'akin kallo, ranar zuciyarsu fal da tsoro suka kwana cikin wannan gida, washegari, wannan macen ce dai ta kuma kawo musu breakfast mai rai da motsi suka ci sukayi nak, tun suna d'ari d'ari har suka soma sakin jikinsu suka soma aminta cewa wannan alhaji yana da kyakykyawar manufa akansu, har fitowa suke compound na BQ su sha iska, babban abunda ya soma d'aure musu kai shine yau satinsu guda kenan a gidan amma basu kuma tozali da wannan alhaji ba, innaro ce tayi k'arfin halin tmbyr wannan mata dake dawainiyya dasu tun zuwansu tace"niko maigidan bashi nan ne" tace" ehh, jiya da dare ya dawo daga spain" shiru innaro tayi bata kuma cewa komai ba, ranar kuwa da dare alhaji badaru magal yasa  a shigo dasu parlorn shi, mustapha wata drivernshi ne yaje ya sanar musu alhaji yana son ganinsu, cikin sauri duk suka mik'e zura hijab yana gaba suna biye dashi har suka shiga 6angare mafi girma a gidan, kai tsaye k'ofar babban parlournshi suka nufa, suna sanya k'afa cikin wannan katafaren parlour gbdy suka soma kalle kalle, gyaran muryan alhaji badaru ne ta dawo dasu nutsuwarsu, yana zaune a d'aya daga cikin royal chairs d'in da suka k'awata parlourn, sanye yake da y'an cikin shadda fara an masa d'inki sardauna a office, zama sukayi a k'asan carpet,innaro ta d'aga murya ta gaishe shi ya amsa a tak'aice, sun fi minti goma kafin ya dawo da hnklinshi kansu yace" kamar yadda nace zan taimaka muku  tabbas bana mgn biyu saidai nima ina da abunda nakeso a wurinki" saurin d'ago dakanta tayi ta kalleshi yace" abunda nakeso wurinki shine ki bani auren d'iyarki ni kuma zan d'auki nauyin duk wata buk'atarku kuma zan fidda d'iyarki waje a dawo mata da muryarta" shiru innaro tayi tana kallon k'asa zuciyarta na bugawa da sauri sauri, rumana kuwa na zaune gefe guda  bata san me ake fad'a ba a wurin, tabbas a duniya bata da burin daya wuce ta wayi gari taga rumana na magana kamar kowa saidai babu yadda zatayi ne, kallonta alhaji badaru yyi yana murmushi yace" kije kiyi tunanin kan hkn na baki kwana uku" muryarta na rawa tace"toh alhaji" kama hannun rumana tayi suka mik'e suka nufi hanyar ficewa daga parlourn jikinta duk a sanyaye, hk suka fito suka koma 6angarensu, saidai sosai innaro ta zurfafa cikin kogin tunani kan wannan buk'ata na auren rumana da alhaji badaru ya bijiro mata dashi, gefe guda kuma tana masifar son ganin muryar rumana ta dawo, shin yaya zatayi,amincewa zatayi da aurar da d'iyarta ga mutumin da batasan waye shi ba ko kuma yaya?  wata zuciyar ta gargad'eta wata kuma saita soma ingizata, washegari, kamar kullum bintalo ta shigo musu da abinci har zata fita innaro tayi saurin tsayar da ita,dawowa tayi ciki ta zauna, kallonta innaro tayi sosai tace"don Allah ina son ki sanar dani waye maigidan nan" cike da mamaki bintalo tayi saurin kallon innaro tana zaro idanu waje tace"meyesa kkmin wannan tmby hk" tace"ki kwantar da hnklinki kuma ki kalli wannan d'iyar tamkar d'iyarki ki sanar dani abunda ya  kamata na sani" tace"bansan me kkson sani ba game da alhaji amma koma meye gsky kiyi hkr bana sanya kaina cikin fitina"    cikin sauri innaro ta soma sanar da ita taimakon da alhaji badaru ya musu duk kuwa dabai sansu ba da kuma buk'atar daya bijiro mata dashi yanzu nason auren d'iyarta, shiru tayi tana wani nazari can kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da yin k'asa da murya tace" alhaji badaru cikakken bazazzagi ne kuma cikakken d'an kasuwa kowa yasan shi cikin garin zazzau saidai Allah yyi masa muguwar jarabta wad'anda dayasa dayawan mutane suka soma zarginsa, jarabta da Allah yyi masa kuwa itace, aurensa hud'u matan suna mutuwa dalilin kenan dayasa ya dakata da aure ko nace dayawan mutane suka dena bashi aure sbd wasu na ganin kamar kudi yake da matan nasa, wannan zargi da mutane ke masa shine babban dalilin dayasa auren ya fita daga ransa har kawo yanzu, wannan shine iyakar abunda nima na sani game dashi"  innaro tuni jikinta ya d'auki rawa ta kasa koda k'wakwkwaran motsi,bakinta kuwa ya kasa furta koda kalma d'aya har bintalo ta mik'e ta fice bata ankara ba, tirk'ashi! fitowar rumana daga wanka ne yasa ta dawo daidai gudun kar ta fahimci matsala a tare da ita amma duk da hk saida ta fahimta, hkn yasa ta k'araso kusa da ita ta zauna ta rik'o hannunta tana mata alama irinta kurame kan ta fad'a mata abunda ke faruwa, girgiza mata kai tayi ta shafa kanta tana murmushi ta mata alama da cewa babu komai, innaro kuwa tunanin hanyar daya kamata tabi ta gudu da y'arta kawai take don bazata ta6a yarda alhaji badaru ya auri rumana ba, wato don ya gansu marasa gata shine ze 6ullo musu da wannan babban al'amari, mik'ewa rumana tayi tana hamma da alamun bacci a idonta ta shige cikin d'aki ta haye gado ta kwanta, innaro kuma tana parlour tayi nitso cikin tunani, ihun rumana data jiyo ne daga cikin d'aki yasa ta mik'e zumbur a mutuk'ar razane ta afka bedroom d'in, ganinta tayi a takure a k'arshen gado duk ta jik'e da gumi jikinta sai makyarkyarwa yake, rik'eta tayi da sauri tana tmbyr da yaren kurame kan mene ya sameta ta fad'ata, shiru tayi bata mata wata alama ba kuma jikinta ya d'auki zafi tamkar garwashi wuta, zazza6i sosai ya kamata tashi d'aya, ranar innaro kasa runtsawa tayi sbd tashin hnkli data shiga, hk suka kwana rumana ba lfy har safe, mustapha ne yazo yaga halin da rumana take ciki tuni suka d'auketa sukayi asibiti da ita bisa umarnin alhaji badaru, kwanansu uku a asibiti amma jikin nata ba sauk'i don yanzu ko zama bata iya yi, hnkli innaro yakai k'ololuwar tashi,  likitoci sun sanar dasu kan cewa tana d'auke da appendix ne yyi mata girma a ciki dole tana buk'atar surgery cikin gaggawa, lkcin da alhaji badaru yaji wannan batu sai ya kalli innaro yace" jiya ne ranar dana d'ibar miki kan ki sanar dani abunda kk yanke game da bani auren d'iyarki"  shiru innaro tayi ta kasa mgn yace"bazan iya cigaba da daukar nauyin biyan kudin asibitin d'iyarki ba har sai naji abunda kk yanke game da buk'ata ta kan auren d'iyarki" jikin innaro ya soma 6ari, idan har alhaji yak'i biyan kudinsa a yiwa rumana aiki toh kuwa ina zata samu wannan anan kusa koda kuwa sata zatayi, alhaji badaru kuwa karon farko kenan daya samu zuwa asibitin, juyawa yyi ya fice ya nufi wurin motarshi, da gudu innnaro ta biyoshi tace"na amince na bk auren rumana don Allah ka taimakani ka biyasu suyi mata aikin nan" juyowa yyi ya kalleta yace"shikenan, gobe zasu mata aikin" gdy ta shiga zabga masa har da rissinawa, shi kuwa ya shige mota mustapha yaja suka fice daga asibitin, innaro kuwa abunda ta shirya shine ana yiwa rumana aiki ta samu sauk'i zasu gudu baza ma su koma gdn alhaji badaru ba bare ya aurar mata d'iya, washegari, kuwa likitoci suka shige da rumana operation room, zasu mata aiki.....




         6angaren alhaji badaru magal kuwa kai tsaye yasa aka kira limamin unguwar yazo ya gabatar masa da sadaki, shaidu suka had'u, wani shehin malami shine ya zama waliyyin amarya inda aka d'aura auren rumana da angonta alhaji badaru magal kan sadaki naira dubu dari, washegari, alhaji badaru dakansa ya koma asibitin bayan an fito da rumana daga tiyata, dubu dari chas ya fito dashi ya mik'awa innaro tasa hannu biyu ta amsa tana jinjina yawan kudin cike da tsoro amma a zahiri sai tace" alhaji wannan kudi hk ai sun yi yawa" murmushi yyi yace" ki ajiyewa rumana sadakinta ne!" cike da rashin fahimta ta d'ago idanunta a razane tace" ban fahimta ba,me kace alhaji?" murmushi ya kumayi a karo na biyu yace" jiya aka d'aura aure na da rumana wannan shine sadakin nata" kasa motsawa innaro tayi tuni ta saki dumin kudin suka watse a kasa jikinta ya soma rawa, muryarta na rawa tace" badai auren diyata ba sai ko wata" kallonta yyi cike da mamaki yace" da amincewarki da yarjewarki aka daura auren nan me ya kawo hk kuma" fashewa tayi da kuka tace" wlh ban amince ba,kawai ka sakarmin d'iya" kuka sosai take, bece mata komai ba ya juya ya fice daga dakin, saidai yana fita yyi waya commissioner of police ya turo masa da mota guda na police sukayi surrounding room d'in dama asibitin gbdy suna ganin rumana, innaro kuwa alhaji badaru na fita ta sakko da rumana duk kuwa da rashin karfin jikinta ta kama hannunta suka fito da niyyar gudu saidai tana fita tayi ido hudu da motar yan sanda hkn yasa dole ta dawo, rumana dai ta rasa gane abunda yake faruwa da innaro sai kuka take ta kasa denawa, kwanansu biyu a asibitin jikin rumana yyi daidai alhaji dakansa yazo ya daukesu suka dawo gida, saidai wannan karon an sauya musu 6angare, innaro 6angarenta daban aka bata na wanda yasha kayan alatu na more rayuwa ga kuma masu mata hidima, rumana kuwa innaro naji na gani aka wuce da ita 6angaren alhaji badaru, 6angare mafi girma a gidan, sai lkcin rumana ta soma fahimtar abunda ke faruwa duk kuwa da bata gama fuskata cewa da igiyoyi uku akanta ba.........tirk'ashi! meke shirin faruwa cikin faifan rayuwar rumana?........kudai kawai ku cigaba da bibiyar alk'alamina,zan warware muku zare da abawa insha'Allah....


*Littafi na farko kyauta ne na biyu kuwa saida y'an chanjiki*.

No comments