SHARUZZAMAN 1 PAGE 2
*BOOK (1)*
_SHARUZZAMAN_
_BINTU S££R_
2️⃣
Suna tafe cikin kasuwa suna bara amma mafi yawan mutane wucesu suke batare da sun basu ko asi ba, wata mace ce daga rumfarta ta kwala musu kira da *Sadaka yallah* juyawa sukayi da sauri suka nufi wurin rumfar nata, suna k'arasawa ta kallesu galala tace"wannan y'arki ce?" tambayar data yiwa innaro kenan kan rumana, tace"ehh" murmushi matar tayi tace"tun dazu nake kallonku amma
fisabilillahi baki san yadda garin nan yake bane zaki sako wannan zuk'ek'iyar yarinya a gaba kuna yawon bara kodai daman neman me tayata kkyi tunda daman yawancin sadaka yallah hk suke, y'ayansu sune jarinsu" shiru innaro tayi kawai tana kallon matar nan, sai daga k'arshe ta ciro naira dari ta mik'a musu, cikin sauri innaro da sunkuya ta amshi kudin tana mata gdy da hausarta irinta fulanin nijar, rumana kawai kallo take da idanu bata jin komai, lkcin da suka bar wurin matar ne rumana take yiwa innaro alama da hannu kan me wannan mata take fad'a, murmushi innaro tayi ta mata alama da hannu cikin yaren kurame kan matar tace tana dakyau, murmushi tayi har wishiryarta ta fito, sun d'anyi gaba kenan sun kira wata mai abinci zasu siya sai kawai ganin wata dank'areriyar mota sukayi ta tsaya gabansu, basu ta6a tsammanin motar su ta tsayawa ba sai da suka ga drivern motar ya tsuge glass din motar ya lek'o dakansa yana kiransu aikuwa da rawar jiki innaro ta rik'o hannun rumana suka nufi wurin motar tunaninsu ya basu mai motar sadaka ze basu, suna k'arasawa wurin motar drivern motar ya fito da sauri ya bud'e musu bayan motar yace"bismillah, ku shiga maigidana yana da burin taimakawa irinku" cike da tsoro suka ja da baya, innaro tace"kayi hkr bawan Allah bamu shiga" murmushi yyi yace"alamu sun nuna kamar tsoro kkji koh, toh ku kwantar da hnklinku niyyarmu mai kyau ce akanku domin taimaka muku zamuyi amma idan baku buk'ata ai shikenan" rufe motar yyi ya juya ze koma driving seat yaja ya tafi, cikin innaro ta tsaidashi tace"shikenan zamu shiga" murmushi yyi ya dawo ya bud'e musu gidan baya, innaro ta kamo hannun rumana zasu shiga ta tirje tana girgiza mata kai alamar kar su shiga, murmushi tayi mata mgn cikin yaren buzanci sai tabi bayanta suka shiga motar, suna shiga sanyi Ac ya soma shigarsu, sai lkcin suka lura ashe mutum biyu ne a gaban motar, gefe guda wani hamshak'in alhajin birni ne,jibgege dashi sai kayan tumbi amma ido da ganinsa had'i da sutturar dake sanye jikinsa ansan yyi matashi da daloli,cikin sauri innaro ta gaishe shi ya amsa a tak'aice, drivern dake jan motar wato wanda ya bud'e musu suka shigo kenan, yace"baiwar Allah ita wannan d'iyar taki bata iya gaisuwa bane" tace"kurma ce bata mgn" daga shi har alhajin nan saida suka juyo suka kuma kallon rumana, yarinya tamkar ita tayi kanta don kyau amma gata kurma, tun daga nan babu wanda ya kuma mgn suka cigaba da tfy kan kwalta har lkcin da suka sha kwanar wata unguwa mai k'arancin hayaniya da yalwar manyan gine gine, innaro da rumana kuwa sai kalle kalle suke tamkar wasu k'auyawa, suna zuwa daidai wani tafkeken gidan hutu mai d'auke da wata jibgegiyar gate drivern ya danna horn, wani tsohon baba maigadi ya lek'o yana ganin motar yyi saurin tsuge musu wannan k'atuwar gate suka shige ciki, innaro da rumana kuwa gabansu ne ya soma bugawa da k'arfi musamman da suka ga girman wannan gida, tsakiyar gidan akwai round about mai d'auke da shuke shuken furanni, daidai wurin parking d'in motoci ya tsaida motar ya fito da sauri ya bud'ewa wannan alhaji murfin mota ya fita, suma suka bud'e motar suka fita, kai tsaye wannan alhajin wucewa yyi can wani 6angare wanda yake shine mafi girma a gidan, su kuma drivern y kira wani babban mutum d'aya daga cikin masu aikin gidan yace ya kaisu boys quaters inji alhaji, batare da wani 6ata lkci ba ya shige gaba suka bishi a baya dukkanin jikinsu a sanyaye, rumana kuwa rik'e take k'am da hannun mahaifiyarta har suka k'arasa BQ na gidan, bud'e musu yyi suka shiga, maidaidaicin parlour ne d'auke da bak'ak'en leather seats sai wani madaidacin plasma, gefe da gefe d'akuna ne guda biyu, kallonsu mutumin yyi yace"anan zaku zauna kafin alhaji yyi mgn akanku, zaku iya amfani da ko'ina da kuma komai kk buk'ata " yana gama mgn ya juya ya fita, su kuma suka cigaba da kalle kalle, lek'a d'akunan dake parlourn suka somayi, kowanne d'aki d'auke yake da double bed da k'atuwar sip da dressing mirrow, kuma akwai toilet a kowanne room,innaro tayi murmushi tana kallon rumana tace"lalle mu muka shigo nigeria da k'afar dama" duk da cewa rumana batasan abunda take fad'a ba amma yanayin fuskarta ya tabbatar mata tana cikin farin ciki, fitowa parlour suka kumayi suka zazzauna bisa wad'annan leather seats, daidai lkcin wata dattijuwar mace ta turo k'ofar parlourn ta shigo da sallama hannunta d'auke da kulolin abinci, fuskarta d'auke da yalwatacciyar fara'a suka gaisa ta ajiye musu kulolin abincin ta juya ta fita, innaro ta bud'e kulolin nan inda ta hango ferfesun kaza ne a d'ayar kular dayar kuma hadaddiyar jellop rice wacce taji kayan hadi sai tashi k'amshi take, matar nan ce ta sake shigowa ta nuna musu fridge din dake k'uryar parlourn tace"akwai ruwan sha ciki" gdy innaro ta mata ta fita, rumana kam har yanzu hnklinta yakasa kwanciya da wannan gida, ita kuwa innaro har tayi k'asa ta tank'washe k'afafu ta fara zuzzuba musu abinci a plates din da aka had'o musu dashi, da ferfesun kaza ta fara tuni ta soma yagar cinyar kaza hnklinta kwance, rumana kuwa duk a d'arare take amma ganin mahaifiyarta tana cin abincin hnkli kwance yasa itama ta sakko ta soma cin abincin a hnkli, sai suka k'oshi sukayi nak, innaro ta kwanta a lallausan center carpet din dake tsakiyar parlourn sanyin Ac na ratsata ta soma bacci, rumana kuwa tashi tayi ta shige toilet ta d'auro alwala tazo ta tayar da sallah, tana iddarwa innaro ta farka itama taje tayi alwalan tazo ta fara sauke farali, innaro sake komawa tayi ta kwanta abinta ta cigaba da baccinta, itama rumana saita kwanta gefen mahaifiyarta kawai ta soma tunanin yar'uwarta khadi da kyallu addu'a ta soma musu Allah yasa suma sun tsira, hawaye ne ya soma cika mata idanu tana tsananin k'aunar yar'uwarta su biyu ne kawai a wurin mahaifiyarsu, su y'an asalin janhuriyyar nijar ne cikin garin yemen, k'auyen jinto, mahaifinsu sunanshi barde, buzu ne gaba da baya amma Allah ya had'ashi da mahaifiyarsu innaro wacce take bafulatana sukayi aure duk kuwa da kasancewar danginsa da mahaifiyarshi basu son auren amma Allah ya k'addara dole suka rumguma, innaro tare suke da mahaifiyar mijinta kyallu a gida d'aya hkn ya kawo tsana da tsangwama tsakaninta da ita, tana masifar tsoron kyallu don shi kansa barde yana shakkar uwar tasa, zaman doya da manja suke sosai kwatsam suka wayi gari Allah ya yiwa barde rasuwa, innaro tayi kuka kamar ranta ze fita, bayan rasuwar mijinta da wata shida ta fara shirin tfy garinsu ita da y'ayanta amma kyallu tace Allah ya kasheta innaro bata isa ta tafi mata nan da can da jikokinta ba, ita kadai tazo ita kadai zata tafi, hkn yasa innaro ta rok'i kyallu alfarma kan toh tabarta ta zauna tare da y'ayanta don batason tayi nisa dasu, dakyar kyallu ta amince innaro ta cigaba da zama da yayanta saidai komai na aikin gidan ita takeyi ko yaran nata hanasj kyallu take su tayata, hk dai innaro ke hkrn zama albarkacin yayanta, kwatam, wata k'awar kyallu shatu ta dawo daga nigeria tazo ta kawo mata ziyara, lkcin data hada idanu da rumana da khadi sai ta tambayi kyallu wadannan jikokinki ne, kyallu tace"ehh" murmushi tayi tace"yanzu kina da wannan jarin kk rayuwa hk" kyallu ta kalleta cike da rashin fahimta, tace"me kk nufi shatu"dariya tayi tace"kawai gani nayi meze hana ki kwashi wadannan jikokin naki ku tafi nigeria don alhazawansu suna masifar son kyawawa mata tabbas zaki samu kudi dasu" shiru innaro tayi amma a zahiri gsky tayi na'am da wannan shawara ta shatu, kyallu akwaita da jarabben son abun duniya, washegari kuwa ta kira innaro tace ta shirya ta koma kauyansu ita zata kwashi yaran su wuce nigeria, innaro ta din ga hada kyallu da Allah kan itama zata bisu nigeria, kyallu tace"ta yiwa kanta ya'yanta kudin mota" hk innaro ta fara aikatau na kudi tana tara musu kudin motar zuwa nigeria, shatu itama ta taimaka musu suka taho nigeria ta basu nambar waya da zasu kira idan suka je kano, zasu basu masauki, motsin bud'e k'ofar parlorn ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data afka tayi zumbur ta mik'e ta jawo dankwalinta ta soma d'aurawa.....*Littafi na farko kyauta ne na biyu kuwa saida abokan tfy wato kudi*.......
No comments