YAR AMANA 13-14
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA☘️☘️*
*Page 13&14*
___Shi kuwa ABUDULJABBAR gudu yake zubawa sosai akan titi dake tsakanin Abuja da kaduna, domin yau ba su fita a meeting da wuri ba, har sai yamma sosai kuma ji yakeyi bazai iya kwana Abuja ba, dan haka ya kamo hanyar Kaduna domin so yakeyi komin dare yau ya kwana a gidan su dan shi sam bai iya kwana a wani gurin ba mudin kuwa in kusa da gida yake, wanan dalilin yasa ABUDULJABBAR ya kamo hanya daga Abuja zuwa Kaduna.
Yayi tafiya sosai dan yabar Abuja sosai ya kusa kaduna, yazo daf da wani qauyen fulani wanda qauyen ke can cikin dajin dake bakin titin, kawai sai yaga anzagaye kan hanyar da itace anyi get alamun ba hanya kuma ga gurin shiru ba kowa titinma yayi shiru ba motoci masu wucewa jefi-jefi, dan haka ABUDULJABBAR ya tsayar da motarsa ya fita acikin ta bakinsa d'auke da addu'a, kai tsaye wajen ita cuwan ya nufa yafara d'aukesu yana miyarwa gefe, abunda da ABUDULJABBAR bai sani ba shine Akwai wasu maza abayansa acan gefen titi sun 'buya cikin ciyayi suna kallonsa, ai kuwa ya kusa gama kwashe itacuwan nan yaji sauqar duka da icce agadon bayan sa, a gigice ya d'ago sbd azaba amma me sai yaga wasu matasa majiya qarfi su 5 atsaye akansa hanuwansu riqe da mungayen makamai babban cikin sune ya d'aga wata adda zai sarawa ABUDULJABBAR, ai kuwa ABUDULJABBAR yayi ta maza ya riqe addar tini tafinhanunsa ya yanke ya dare ya shiga zubar da jini, wawan duka Oganasu ya kaiwa ABUDULJABBAR afuska yana cewa " kai dan ubanka ai yo saide uwarka ta haifi wani domin kuwa kud'ad'e masu yawa aka bamu domin kwangilar kasheka sbd haka dolene mu cika aikinmu, sake d'aga
Addar yayi da niyar zai sarawa ABUDULJABBAR, shi kuwa ABUDULJABBAR ya tureshi da qarfinsa ai kuwa Oganasu ya fad'i qasa warwas, dan haka ABUDULJABBAR ya ibi gudu yayi cikin wanan dajin da qauyen fulanin ke ciki, suma kuwa suka rufa masa baya, suka bishi da gudu.
Ita kuwa 'YAR AMANA ihu sosai takeyi da addu'o,i amma haka mazan nan suka jata cikin duhuwar nan shi kuma babban nasu yabi bayansu yana qoqarin zame wandonsa, 'YAR AMANA kuwa sai ihu takeyi tana cewa " dan Allah ataimakamin zasu cutar dani dan Allah kuyi haquri wlh ni ba karuwa bace banma san abunda kuke nufiba"
ABUDULJABBAR kuwa yayi gudu har yagaji dan kuwa 'bat ya 'bacewa mutanen dake binsa, can yana gudu yana haqi ya jiyo kamar ihun mace tana neman taimako dan haka kawai ya nufi gurin, adai - dai lokacin kuma wanan qaton yafad'o kan 'YAR AMANA, ABUDULJABBAR kuwa da gudu da zafin nama ya qaraso gurin ya ture wanan ba fulatanin yabishi da wani mugun naushi atake hancinsa da bakinsa suka fashe hatta ganin sama saida ya daukemar na wasu sakonni, shi kuwa ABUDULJABBAR yama manta yana rungume da mutum, juyowar da zaiyi kawai sai suka fad'i suka shiga mirginawa akan juna acikin ciyayin dake gurin, qarshede har suka fad'a cikin wani rami da ruwa ke taruwa in anyi ruwan sama, gashi kuwa ramin cike yake da ruwa taf kasancewar lokacin damuna ne, haka suka suka fad'a cikin ramin 'YAR AMANA na qasa shi kuma ABUDULJABBAR ya fad'a bisa kanta ya danneta, ita kuwa 'YAR AMANA nauyin taji ya mata yawa aqirjinta dan haka ta shiga ture abunda ke kanta, dan ita batasan ma waye ya taimake taba domin ko fuskarsa bata gani ba, balle gangar jikinsa kawai de taga ya zone tamkar walqiya, shi ma ABUDULJABBAR acikin ruwan idonsa arufe yake kirif, tureshin da yaji anayi yasa shi, bud'e idonsa ahankali ya zubasu akan ta fuskar mace yagani tana ta ture qirjinsa ga ruwa sai shigarmata baki yakeyi sbd ramin babban tafkine, da sauri ya d'aga ta ya d'agota daga cikin ruwan suka tsaya, kallon juna suka shigayi acikin duhun da ya fara mamaye gurin, kasa magana ABUDULJABBAR yayi sbd kyawun yarinyar ya rud'ashi domin aganinsa ma gamo yayi da 'yar aljanu, dan haka tini ya fara addu'a azuciyarsa domin shide tinda yake baita'ba ganin yarinya mai kyau irin wanan ba, koda kuwa a India ne, mussaman ma gashinta da yaji ruwa ya ware aikuwa gashin ya kusa ta'bowa qasa domin tsawonsa har qafafunta, dan haka tini jikin ABUDULJABBAR yayi sanyi, ita kuwa 'YAR AMANA lura tayi da jinin dake 'barara ahanunsa duk ya 'bata kalar ruwan da suke ciki, kuma tagane shi ne mutumin da ya taimaketa dan haka sai ta cire siririn mayafinta dake d'aure akunkuminta haqorinta tasa ta ya gi kad'an sanan ta kamo hanun ABUDULJABBAR dake zubar da jini, jikinta na tarawa domin itama ta tsorata da ABUDULJABBAR dan azatonta gamo tayi da aljani, sbd kyawu da qirar ABUDULJABBAR, dan haka gaban ta na fad'uwa ta kamo hanun ABUDULJABBAR ta shiga d'aure mar domin kuwa Baffanta ya sanar mata ko acikin aljannu Akwai na qarai masu temako dan Allah, dan haka 'YAR AMANA tazaci ABUDULJABBAR shima aljaninne dan ita bata ta'ba taganin kyakyawar sura irin wanan ba, ga kuma qira irin qirar na mijin da ya cika namiji, haka de take d'aure masa hanun kowa da tinanin da yake saqawa aransa shikam ABUDULJABBAR jira yakeyi yaga ta 'bace kawai domin kuwa yasan ba tantama aljanace tinda gashi ma kayan fulani ne ajikinta, azuciyarsa kuwa cewa yayi kenan ma ba fulatanar aljana nayi gamo da ita".
__________________________
A'bangaren matasan nan kuwa da suka tare 'YAR AMANA har ABUDULJABBAR yazo ya taimaka mata, dan haka sai babban nasu yayi fushi yace " duk suzo suji abunda ya kama ta suyi domin kuwa intasan wata bata san wata ba, ce musa yayi "dole ne mukayo qarshen iskanci yarinyar nan yau domin kuwa karuwanci nata ya isa haka agarinan, ba kwa ganin wanda yazo ya kwace ta ahanuna shima d'an iskanne irinta?"
"Sosai ma kuwa kawai muje mu fad'awa hard'o inyaso azo aka masu ayi musu hukuncin da yadace dasu" d'aya daga cikin su yace, haka kuwa suka ruga zuwa cikin rigar Suka nufi gidan hard'on rigar tasu, inda suka sanar dashi qarya da gaskiya, tini ran hard'o ya 'baci ya tura aka qira masa Baffa, Gwaggo kuwa dan gulma harda biyo Baffa gidan hard'on, koda Baffa yaji bayanin da hard'o yayi masa, shide kasa cewa komai yayi, ka yasa qarya tawa kuma ya kasa gasgatawa, itako Gwaggo sai qara tinzira abun takeyi tana kuka WIWI da face majina wai 'YAR AMANA taci Amanarsu, ita tsoroma takeji kar takwaso musu abun kunya, nan hard'o yasa aka tatara matasa sama da goma yaba da Umarnin aje akamo 'YAR AMANA ita da kwartonata.
'YAR AMANA kuwa da ABUDULJABBAR suna tsaye suna kallon kallo wa junansu amma ko wanensu ya kasa furta komai kawai sai taji aljaninata yasa ihu yafad'i qasa, d'ago kanda zatayi taga kusan dukka matasan rugarsu agurin nan Suka cici'bi ABUDULJABBAR suka tafi dashi, itama 'YAR AMANA rufa musu baya tayi tana kuka tana cewa " ina zaku kaishi dan Allah kudawo da shi bafa mutumba ne irinku aljanine baku gani bane yafi ku kyau?"
Ba wanda ya kula ta ahaka har suka isa qofar gidan hard'o inda kowa da kowa yake jiran ganin kwarton 'YAR AMANA suna zuwa suka jefa ABUDULJABBAR aqasa shi kuwa yama sume sbd da iccen da suka kwad'a masa akansa, hard'o kuwa cewa yayi ad'auki Saurayin da kuma 'YAR AMANA akaisu kurkukun dake bayan gidansa inda yake tsare masu laifi, haka kuwa suka qara ya yu'bar ABUDULJABBAR suka tasa qeyar 'YAR AMANA tana kuka tana qiran "Baffa Baffa na kace karsu tafi dani ni banyi komai ba wlh" shi kuwa Baffa tamkar mutum mutumi haka ya koma bakinsa ma ya kasa bud'eshi balle yace wani abu, Gwaggo kuwa cewa tayi "qarya kikeyi muna fuka dolene kitafi kurkuku waye baisanki ba agarinan?" Haka kuwa hadiman hard'o suka je suka jefa ABUDULJABBAR da 'YAR AMANA awani tsohon d'aki mai duhu da ban tsoro, wanda ko tafin hanunka baka iya gani sbd duhu, haka aka kullesu aka tafi akabarsu acikin d'akin.
Inda Hard'o ya sallami kowa yace " kowa yatafi sai gobe za a yanke musu hukunci"
Nan kuwa kowa ya watse ya tafi makwancinsa.
✴✴✴ ✴✴✴ ✴✴✴
A'bangaren FINAH kuwa sbd abunda ABUDULJABBAR yayi mata yau da zai tafi Abuja duk sai taji kwad'ayin mijinata ya dawo mata sabo domin ita tana mutuwar son ABUDULJABBAR sbd ya iya soyayya amma sai jan aji kamar mace, dan haka tashirya kanta tsaf tad'irki magungunan mata na turawa domin intafita shopping harda su take siyowa dan tarikita shi dan haka yauma ta shasu masu uban yawa da qarfi domin tana so yau ta qure ABUDULJABBAR dole ne yau taga qarshen iya soyayyarsa da baya son nuna mata ko azahiri ko abad'ini, amma me tun 10 take sa ran shigowarsa amma shiru har 12:am dan haka fa abunda ta sha yafara damunta cikin dare zuwa 1:am ciwon mara ya fara adabarta afirgice tafarka abarcin da ya fara d'aukarta, kuma a dai - dai lokacin ne qiran Abbanta ya shigo wayarta cikin sauri da dauriya ta d'aga wayar, shiko daga can cewa yayi "mijinki ya shigo?"
"A'a daddy haryanzu bai dawo ba ko lafiya?" Tace dashi, ajiyar zuciya yayi sanan yace " ba komai ki kwanta kawai sai da safe" kafin tayi magana d'if ya kashe wayar, wani wawan murd'a taji mararta ya mata dan haka batasan sanda tasa ihun da sai da gidan ya amsa ba, afirgice Mum dake dakin Abba, suka fito ita dashi domin kuwa lokacin shirin bacci sukeyi Mum ce tashigo d'akin aguje amma me FINAH tagani yashe atsakar d'aki alamun babu rai agereta dan haka itama Mum ihun tasa wanda daidai lokacin Abba ya budewa megadi qofar parlour d'in yashigo sbd ihun FINAH da yaji, aguje Abba da megadi sukayi d'akin sukatar da abunda ke faruwa nan Mum da Abba suka sa FINAH amota sukayi asibiti da ita.....
Hhmm muje zuwa dan yanzu aka fara wasan.
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups
*ASSTAGAFIRILLAH, WA A TUBU ILAIKA*🤲
No comments