DUDUWA 3
_*🧟♀️DÛDÛWÂ🧟♀️*_
_3_
Fadar cike take taf da mutane wasu a zaune wasu ko suna tsaye kowa ya baje kunnuwa Yana jiran Mai zai faru,chan na hangi DUDUWA zaune a tsakiyar tabarma sai raba Ido take tana hange²hange ko me take hangowa oho,hakan ba qaramin razana 'yan zuwa Jin kwakkwafi yai ba, ganin dube duben na Duduwa ba qarau bane sai gaba yake Yana dad`a ha66aka Mai gari yaja gyaran murya yace.
"Ke yanzu Duduwa bazakiyi hankali ba ko da yaushe Ana Kan kawo qararki a gari ko tsoran bakin mutane bakiyi kullum Duduwa, Duduwa Wai bakya gajiya da masifa ne kamar karya...
Yo tsoran me zan ji Mai gari duk wanda ya ta6o Ni na rantse da gemun kakana d`an kande sai na jibgi shi Kamar Allah ya Aiko Ni, da kace Kuma bana Jin magana Kai Jin maganar ka ke da zaka zageni,Naga kullum sai ka tura kasuwa da gidaje amsar kudin jangali shi ba cuta da takurawa jama'a kake ba duk garin Nan zaginka suke har da Inna Dan Allah ya isanta ma ya kusa kai cikin rafun kuka idan so kake ka ji sunayen wasu daga ciki yanzu na lissafa maka su dalla dalla.................""La'illaha ilallahu, jama'a kowa ya dauka Kar Duduwa ta ambaci sunan sa musamman magatakarda dake gefan Mai gari a zaune.
Jikin Mai gari ne yayi sanyi Jin kato6arar da Duduwa ta gwa6a Masa Nan take Mai gari ya shiga daya sanin sauraran qarar Amma gashi ta sanar dani abinda Ban sani ba,kauda zanchan yayi da.
Me ya hadaki da malam baqo da Uwani?.
Ko quda Basu ta6an ba 'yar su ABULIYA ce ta janyo musu.
Subhannallah,yanzu akan 'yarsu kadai kika sassa6awa bayin Allah kamani da ta6arya Duduwa.
Yo me za'afasa idan kuma Rama musu zakayi to ga te6a matso liman nace ka matso gani ka rama musu,, Duduwa ta shiga muskutowa inda liman ke zaune tana Mai nuna Masa te6ar cinyar ta.
'A'uzubillah!!,A'uzubillahi.....Liman ya furta Yana Mai kauda kansa gefe a dai dai lokacin ABULIYA ta ratso wajan tana rasga kuka Kamar wace iyayen ta suka mutu,zambur Duduwa ta miqe jama'a suka fara darewa suna bata hanya Kan kace me har Duduwa ta qarasa inda ABULIYA ta ke Nan da nan takai mata wa wura a fusace ta chakumi wuyanta sai Kan mai gari da tini ya miqe yana Jan babbar rigarsa yai cikin mutane da gudu.
Duka tashiga Kai Mata da cizo ta ko ina ABULIYA na ihu da kururuwar ne man taimako da qyar aka kwaci ABULIYA daga hannun Duduwa aka shiga gidan Mai gari da ita mutane sai mahawara suke kowa na tofa Albarkacin bakinsa akan Duduwa daga qarshe Mai gari yace adakata asaurareshi kowa yaja bakinsa yai shiru.
''Alal haqiqa abinda yarinyar Nan Duduwa take a cikin garin Nan ya ta'azzara daga ta karya wannan sai ta targada wanchan yanzu duk abinda yafaru kowa ya gani da idonsa Bata bar Kan babba da yaro ba har mu masu rawanin to bazamu dauki hakan ba dolle sai an hukunta ta hukuncin da agaba idan ance ta maki wani bazata qara ba.
Wannan gaskiya ne yalla6ai yarinyar Nan ba qaramar taqaddiri bace kawai Dan ta ganta da auki Kamar buhun masara take wannan Doke doken,liman yaqare 6atun Yana duban inda Duduwa ke zaune tana Mai da nufashi,charaf Mai unguwa ya kar6i zanchan da.
Yo ta ganta ne shirmmm abinka da kitse yai yawa Na rantse da Allah Dani ta buga bazata sake bugun wani ba wargima waje ya samu 'yar jakar uba Ido quri akan mutane sai iya shege kala kala,Mai unguwa ya zarowa Duduwa Ido Yana kallon ta.
Ku barni da ita hukunci zamu kaita ayi mata dai dai da ita a chan wajan 'yan sanda ashata mata layi akan jibgar mutanan da take gaba bazata sake ba idan ma qulleta zasiyi duk za'aji kowa ya huta,ai yalla6ai Bata Kai ga wajan 'yan sanda ba mu Nan kadai mun isheta a hukunta ta da bulala kamar yanda akewa kowa idan yai laifi,waje ya kaure da.
Wannan gaskiya ne Wanda ya daka adakeshi........................ Duduwa dai Ido kadai ta zuba musu daya bayan daya.
"Kayiwa Allah da Manzonsa ka yafe mata yalla6ai Kar akai ga 'yan doka.
Tsohuwa dolle a hukunta jikarki ai kina gani ta addabi kowa Baki tsawatar mata ba.
Haba Mai unguwa yarinyar Nan kasan marainiya ce ga yarinta wallahi girman jikin ne kadai ba shekarun ba duka duka agabanku Duduwa ta tashi kasan da ba haka take ba.
Ba wani da ba haka take ba kina daurewa qarya gindi kawai Amma dolle hukunci ya hau kanta ko kina so ko bakya so.........kuka Inna tasaka daga inda Duduwa ke zaune ita ma ta rushe da kuka ganin innarta nayi kallo sai ya koma kanta.
Dariya Mai unguwa yasaka yace.
Oh Kaji munafunci duk Dan atausaya arabu dasu ne wallahi sai anyi daya acikin biyu ko adaketa ko akai ta wajan 'yan doka siyi maganin shegiya..........,haba Mai unguwa kamar ba wakilin jama'a ba, yalla6ai sanin halin wadannan mutanan yasa kaga Ina tankawa,duk da haka ka gyara kalamanka babba babba ne ko ya zubda girmansa.
Tuba nake yalla6ai Amma aduba ayi hukunci dai dai da abinda ta aikata.
Naji baza akai ga 'yan sanda ba za'ayi mata bulala goma yayi Miki.
A sassauta yalla6ai marainiya ce,Inna ta furta cikin kuka .
Wannan shine adalcin mu Inna haquri zakiyi..................
_*By*_
_*Mâmâñ Dr @ff@ñ*_
No comments