JAMI'IN DAN SANDA 26
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_26
.......................kallon ido cikin ido Duke yiwa juna , kamun cikin had'e fuska tare da watsa mashi wani irin kallon kai mugu ne taci gaba da cewa , malam ka rabu dashi haka nan komai yai maka ai bai cancanci irin wannan dukan ba ko don bakasan darajar da jini yake da ita ga d'an Adam ba zakazo kana zubar mashi da jininshi a banza ,
Wani dan adai daita ne cikin fushi yafara magana yana cewa " Ke Dan Allah rufewa mutane baki daga zuwanki bakisan abunda yake faruwaba zaki hau masifa to wannan da kike tarewa yanzu yanzu nan yakusa kashe wata tsohuwa wajan shegen tuk'insu na ganganci yanzu haka ma sai Allah idan zata rayu kuma a haka baidamu ba saima k'ok'arin guduwa da yakeyi ni wallahi wannan bawan Allah yamun dai dai gara yaci uban d'an iska tunda baisan darajar mutane ba,
Jin wannan bayanin yasa jikin laurat yin sanyi saikuma duk kunya ta kamata a hankali ta saci kallon Hisham Wanda har lokacin akwai fushi mai tsanani tattare dashi wannan yasa yakasa yin wata magana saidai yaji haushinta sosai don shi ya tsani rainin wayo ,ganin hakan yasa laurat kamo hannun zee da nufin subar wajan , Wanda haka yayi daidai da zuwa motar yan sanda wajan, yan sanda ne sunkai su shida suka fito daga motar cikin sauri suka nufi wajan da Hisham yake suka k'ame waje d'aya tare da Sara mashi , hakan da mutane suka gani ne ya sasu fahimtar lallai wannan Dan sanda ne kuma acikin yan sandan ma shi babba ne duba da yanayin muk'amin wad'an da suka Sara mashi din,
Zee kuwa idanu ta zaro waje cike da tsoro don Allah yayita da shegen tsoron yan sanda , cikin sauri ta rik'o hannun Lauratu cikin k'asa k'asa da murya tace "anty munshiga ukku kin janyo mana masifa don Allah kizo muje tun kamun yasa a kamamu kinji, "
Wata harara laurat ta zabga mata don itakam ko a jikinta saima tsaki da tayi sannan ta fisge hannunta daga cikin na zee tayi wucewarta inda motarsu take, da sassarfa itama zee tabi bayanta , koda taje har kauratu ta shiga ta zauna a mazaunin direba tafara kiciniyar Tayar da motar , da sauri itama ta bude gaba ta zauna ta ja sukabar wajan aguje tana maijin haushin tsayar dasu da zee tayi wajan shegen shashancinta,
Duk abunda sukeyi Hisham na kallonsu ta k'asan ido kuma yana jinsu don Allah yayi mashi ji kamar maciji , maida hankalinshi yayi kan yan sandan inda yabasu umurnin su tafi da yaron station kuma duk Wanda yazo kar su bada shi har sai yazo gobe, inda shikuma ya juya yanufi motar shi Wanda sai yanzu yake mamakin rashin ganin Momma a wajan,
Wayam haka ya tadda motar bakowa a ciki , da sauri ya zaro wayarshi daga aljihu yafara kiran layinta, ringing biyu ta d'auka ,ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa momma kina ina ne nazo baki cikin mortar, dariya momma tayi tace nikam na tsufa a gida yaushe zan tsaya jiranka kaida bansan lokacin da zaka bar wajanba tunda nasan doli zaku kai matar asibiti wannan yasa na fita na tare nafef na tahowata , "
"Wallahi momma kin kayarmun da gaba , amma alhamdulillah tunda kina lafiya ganinan zuwa gashi har wani wajan anfara sallah"
"To ai shalele kai d'inne sai a hankaki akan wannan aikin naka ,nasan tunda ka kama wannan mai lafin sai inda mai ya k'are kuma , fatan dai jikin tsohuwar da sauk'i ,"
"Bansani ba momma sai sai nazo daga haka ya kashe wayar tare da Jan motar yabar wajan , yanajin zuciyarshi na bugawa da sauri da sauri wanda yarasa dalilin hakan,
_________________________
Gudu suke sosai kamar zasu tashi sama , sunzo daidai inda suka dauke yarinyar da yake dama can hanyar batada mutane don ba gidaje a wajan sai filaye saikuma wani mai tireda daga can nesa da inda suka dauketa , inda shagonshi yake kallon wajan , zaune mai shagon yake shida wasu abokanshi su biyu akan benci da yake baijima da bud'e shagon ba don lokacin da suka dauketa shagonshi a rufe yake shiyasa da tabbas zai gansu alokacin,
Kamar k'yaftawar ido sukaga abund'e mota an cillota waje sannan aka koma Jan motar a 360 aka bar wajan kamun kace mi sai k'urar motar kawai,
Cikin zaro ido da tsananin tsoro suka kalli junansu kamun suka koma maida dubansu ga yarinyar Wanda basa iya fahimtar halin da take ciki ko kuma wacece saboda d'an tazarar dake tsakaninsu da inda take ,
" innalillahi Iro mike shirin faruwa ne " d'aya daga cikinsu ya fad'a ,
"Ina zan sani Abba kawai kuzo muje muyi shahada muga abunda Ke faruwa zaifi,
😳zaro ido d'ayan yayi yace "mii bakuda hankaline to wallahi badani ba wai ganganci haihuwa ga damana kunga ma tafiyata wallahi yanzu wani Abu na faruwa mu yan sanda zasu fara tuhuma , kuma ina Baku shawara da kubar wajan nan zaifi maku , ka rufe shagonka ka k'ara gaba ni nayi nan, yafada cike da tsoron abunda zai iya faruwa suna kallo yayi tafiyarshi,
Suna haka sukaga wata yarinya sanye da kayan makaranta irin Wanda yake jikin wannan dake kwance bayanta kuma mazane sunfi su shida saikuma yan sanda su biyu sai faman zuba sauri sukeyi kamar zasu tashi sama ,
Aikuwa suna hango yarinyar kwance suka kwasa aguje suka nufeta , iyayenta ne su biyu sai yayyunta su hudu sai kuma wannan yarinyar da suke tare lokacin da su zayyan suka saceta itace taje ta fada agidansu tana kuka nanfa suka fito suna nemanta sunyi zagaye har sungaji kamun suka yanke shawarar sanarma da yan sanda to shine aka nemi yarinyar da ta kawo su daidai inda abun yafaru shine suna zuwa suka taddata awajan a yashe,
Cikin tsananin tashin hankali ganin halin da yarinyar Ke ciki yasa gaba dayansu suka rikice yayyunta har sunfara kuka musamman da sukaji Baffansu yana cewa ai bata Numfashi , d'aya daga cikin yan sandan ne cikin tausayamasu yace Baba bari mutafi asibiti zaifi kila suma tayi insha Allah bata mutu ba ,d'ayan d'an sandan kuma wajan yake k'arema kallo inda idonshi ya hango mashi su iro sun zuba masu ido, da hannu yamasu alamar suzo ,jiki a sanyaye iro ya rufe shagon suka nufi inda suke , suna zuwa aka kwashi yarinyar suka Sanya a motar yan sandan , nan Dan sanda daya yashiga yaja motar suka nufi asibiti inda d'ayan ya sanya. Su iro da yayan yarinyar d'aya suka nufi station don yimasu wasu yan tambayoyi,
__________________________
Saida yayi sallar isha sannan ya dawo gida , wanka kawai yayi ya fito daga dakin nashi yanufi falon Momma , zaune ya sameta tana kallon labarai a tashar Al'jazira ,gaisheta yayi ta amsa tareda cewa "shalele sai yanzu aka dawo "
"Eh Momma na tsaya masallaci ne,"
"To da kyau akawo maka abinci ne ?"
"Aa sai anjima zanci"
"To shikenan ya labarin 'yata kuma , tund'azu nake jiranka kazo naji yadda ake ciki, "
Kallon rashin fahimta yamata yace " wane labari kuma ? Wace 'yar taki ? "
Tsuke fuska Momma tayi jin zai fara mata rainin wayo ,cikin tsuke fuska tace 'yata Samra nake.nufi mana , "
"Samra ? Wacece haka kuma ? don shi harga Allah ya manta da wata Samra kuma dama can bawai yasan sunanta bane ,
Cikin fusata Momma tace kaga banson lalata yarinyar da mukaje dazu dazu dakai wajanta shine har zakace ka manta tsabar kai rainani , to inason inji inda aka kwana ne don da wuri zamusa lokacin bikin nagaji da ganinka haka ba sure,
Wani makirin murmushi yayi cikin sigar lallashi yace au ai bangane wadda kike nufi bane , dama sunanta Samra masha Allah suna mai dad'i ai da yake ban tambayeta sunanta bane shiyasa bangane ita kike nufi ba, "
Kallon tuhuma momma tayi mashi tana tunanin taya har zai kira yarinya suyi fira amma yakasa tambayarta sunanta anya kuwa kodai .......kauda tunanin tayi sannan tace " to yanzu dai ya ake ciki ? Tayi maka ko ? don bamuson aja lokaci, "
"Eh Momma tayimun masha Allah ai kin iya za'be kam masha Allah yarinya kamar Zar'be saboda azabar tsawo , aikam tacika mace gaskiya , gata fara Tass ," " Sam murna bata bari Momma ta fahimci sukar yarinyar yayi ba cikin farinciki tace to alhamdulillah masha Allah zankira hajiya Sarah tagayawa mahaifin yarinyar zamu aiko anjima zan kira kawunka da abokan Abbanka sai Susa rana suje Neman auren,
Cikin fad'uwar gaba da tsoro kar yayiwa kanshi salalar tsiya fa yace "Aa momma afara tuntu'bar yarinyar Aji ta bakinta karku yanke hukunci batareda da anbata damarta ba , atambayeta aji in ta amunce kinga shikenan , "
"Kaga karka damu indan ta Samra ne dama can Kaine abunji amma ita kam tuni ta amince ,cikin tsoro ya zaro ido waje tare da cewa "nashiga ukku Allah gani gareka,"
Cikin mamaki tace "kashiga ukku kuma ? Ancema ka kwantar da hankalinka tuni ta amince to wane ukku ka shiga ,ada kamun muje kanata bak'in rai yanzu kuwa gani d'aya har ka zauce haka algungumi anaso ana munafurci ni bari kaga naje na kira hajiya Sara tayi maganar tana mikewa tsaye tayi shigewarta dakinta ta barshi nan yana rabon idanu kamar Wanda yayiwa sarki k'arya,
Hannu bibbiyu ya dora akai kamar wani mace yace yau nashiga Tara bama ukku ba Allah ka dubeni wannan yarinyar ko a lahira akabani ita ai nasan banyi abun kirki ba wallahi🙊😹tashi yayi yakoma d'aki cike da zullumin ko barazanarsa zatayi aiki akan yarinyar kuwa , ya zaiyi in yarinyar bataji gargad'inshi ba , ! Wata zuciyar tace mashi kai kwantar da hankalinka ai da ganin yadda ta tsorata bazatayi gigin cewa tana sonka ba da wannan tunanin yasamu nutsuwa,
Laptop d'inshi ya janyo yafara late latse tsawon awa biyu yayi yana wani aiki aciki kamun ya rufe , wanka ya sake tareda yin alwala yayi shafa'i da wuturi sannan yayi shirin kwanciya don baccine sosai a idonshi , sai dai kwanciyar shi keda wuya ya nemi baccin ya rasa sakamakon fuskar kyakyawar yarinyar dake mashi gizo, gaba d'aya yanayinta yake gani lokacin da take masa masifa da Dan bakinta mai kama dana yara yayinda dimple d'inta na gefen dama Ke lo'bawa sosai Wanda yake k'ara ma fuskarta kyau , gaba daya ya shagala da tunanin wannan yarinyar da baimasan a duniyar da take ba , sai faman murmushi yakeyi Wanda shi kanshi baisan yanayinshi ba , sai samun kanshi yayi da ayyana inama itace Momma ta za'ba mashi ba wannan tinkiyar ba yarinya Sam ba fasali ba aji irin na mata gatanan dai sakakaka kamar ansako shanuwa tsaki yayi a fili yace " kai miye hakane ina ruwana da ita akanmi zan tsaya tunanin wata mace har ta hanani bacci yazama doli na yak'iceki koda Ke mayya ce to ni nafi karfinki banza masifaffafiya kawai ,mrtsss yak'ara jan tsaki a haka ya gyara kwanciyarshi yafara salatin annabi a hankali kamun kace mi bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,
_______________________
Washe gari da wuri ya shirya ya nufi office ,yana zuwa ya nemi ganin Wanda ya wakilta don kula da tsohuwar da aka bige jiya, inspector Sale , yana shigowa ya Sara mashi tare da cewa good morning sir , "morning " yace mashi yaci gaba da tattara wasu takardu saida yagama ya dubeshi da kyau yace "ya jikin matar nan kuwa da sauk'i ? sannan ansamu wani Dan uwanta ne ? "
"Jikinta da sauki sir Allah ya taimaka bata wani ji ciyo sosai ba yar kurkurjewa CE kawai sai buguwa da bayanta yayi sosai amma da sauk'i , ansamu yan uwanta yanzu haka kuma likitan yabada tabbacin nan da kwana ukku zasu sallameta tunda jikin da sauk'i ,
Ajiyar zuciya yayi yace "to Alhamdulillah anjima zanje naduba jikin nata , Allah yakara tsare gaba , Sale ya amsa da amin , bashi takardun yayi yace zaka iya tafiya ga wannan ka kaiwa sajen Abubakar shi yasan inda zai kai ," "OK Sir yes sir ya Sara mashi ,maimakon ya juya ya tafi sai kuma ya tsaya yana yan soshe soshe , kallonshi Hisham yayi tare da d'age mashi girarshi d'aya yace da matsala ne ??"
Cikin in ina yace "am dama maganar yaron nan ne tun jiya mahaifinshi Ke zarya anan Ashe wai d'an alhaji Kabir naira ne to shine suketa zarya anan , " ya k'arashe maganar a sanyaye ganin wani mugun kallo da ogan nashi yayi mashi cikin kaukausar murya yace "to sai akayi Yaya ? Karka sake zomun da. Wannan maganar banshirya ganinsu ba zaka iya tafiya , cikin jin haushin ogan nashi ya juya tareda cewa sorry sir yafita daga office din yana mai tsinewa Hisham don yaso samun kudin da alhaji kabir yamashi alkawarin zai bashi inhar yayi masu kokarin da aka basu Berlin yaron.
Sai misalin k'arfe 4 na yamma yabar office din yanufi asibitin da aka kwantar. Da matar nan tareda insfector sale ,
A hankali suka murd'a hannun gambun suka shiga ciki ,
tsaye take tana wasu rubuce rubuce akan file. Din matar , k'amshin turarenshi ne yafara yi masu sallama a d'akin , kamun ya shigo bakinshi dauke da sallama, d'ago kan da laurat zatayi ne idonta yafad'a cikin nashi , gaba dayansu saida zuciyoyinsu suka buga kamun suyiwa junansu kallon ido cikin ido ......................kai nagaji don Allah sai kuma gobe🙄🙄🙄
JAMIIN DAN SANDA FANS 2 BAKU COMMENT YAKAMATA KU GYARA DON WALLAHI ZANKAI INDA ZAKU BUKACE LITTAFIN NAN AMMA BAZAKU SAMU BA HAKAMA GRP DIN *MMN YUSUF FANS* ZAN CINCI MASU COMMENT MUKOMA GEFE MUYI ABUNMU TAU KUMA BA YANZU BA SAI LOKACIN DA BAZAKU IYA JURAR RASHINSHI BA NIKUMA ALOKACIN ZAN RAMA💃🏻💃🏻💃🏻
*masuyimun comment ngd sosai Allah ya biyaku ya faranta maku kamar yadda kuke farantamun duk wadda tamun comment ina gani kuma inajin dadi saida bazan zamu damar binku dai bayan dai ina gdy ba saboda idona sake ciyo saboda hasken wayar amma ina ganinku kuma inajin dadi ngd sosai*
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*💃🏻💃🏻💃🏻
*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji✋🏻✋🏻✋🏻
Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,💃🏻💃🏻
*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips
Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar,
Maganin gashi
Maganin hawan jini
Maganin sugar
Sabulun wanka na gyaran jiki
Sabulun dilka na amare
Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai)
Maltinar mata
Bobintan mata
Set na lalata gindin kiahiya
Set na ukku bala'i
Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba
Kalolin gari
Kalolin matsi
Kalolin sabulan tsarki
Zumar mata
Zumar ridi
Zumar goron tula
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin sabon budurci
Tsumin kankana
Tsumin tabaje
Tsumin makalemata
Shayin mata
Sirrikan mallaka
Dan goshi da mahadinshi
Dan goshi na Mara
Kyallen al'ajabu
Rakumi da akala
Bita zai zai
Dahuwar kalolin kaza zabo zakara
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar zuciya
Dambun nama
Dahuwar yan shila
Yajin mata
Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani ,
Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah ,
Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 07069711327
No comments