DUDUWA 17
~17~
'Haba Hauwa kulu uwar gida a gidan mai gari kowa da kika gani,da haka yake haƙuri idan za'aƙaro masa tinkiya kishin nan dole sai kajishi ko yaya yake a ranka sai dai na wani wafi nawa ni ki ajiye komai ki kauda kan ki daga kan tinkiyar ki.
"Tinkiya kuma gwaggo,wa aka aurowa tinkiya a matsayin kishiya aka kai masa gida.
"ke dallah chan sunan da ake kiran kishiya dashi kenan,daka ambaci sunan baƙar dagar gwamma ka kira ta da tinkiya a sauƙaƙe.
au haka zan dinga kiran duduwa dashi kenan gwaggo,kuma yasin sunan yayi kama da ita muguwa azaluma,umm ni da nace bazan koma ba meye na kiran ta da tinkiya su je chan su ƙarata,nima Allah zai bani wani santalelan namijin son kowa ƙin wanda ya rasa.
a gidan uban wa zaki samu san kowa ƙin wanda ya rasa kamar mai gari kulu ,ai kin tafka babbar asara idan kika rasa mai gari,na lura har yanzu bakida hankali ko ince rashin haihuwa ya fara saki hauka,ki dubi irin girman garin nan da jama'ar cikinsa duk fa a ƙarƙashin ikon mai gari yake,ga uban tarin dukiya ke kan ki shaida ce gonakin sa sun kusa ɗari banda garken shanu da akuyoyi ga safarar taki da yakeyi ga ƴan uwansa dake chan burni ke asarar da zakiyi billahillazi yawa gare ta ko dai ke haka kike babu sa'a,a rayuwarki ne iyeee.
"Haba gwaggo wannan kuma ai zagina kike yi.
yo ba gwamma na zageki ba da irin wannan rashin hankalin naki,gaba ɗaya dusa ta cika miki kai banda gidahumanci da shirme babu komai a kanki samun miji kamar mai gari ai alkhairi ne babba ga kowace macan data dace zakiyiwa kanki asara.
kuma fa haka ne gwaggo,bakiga yadda ake bani girma ba idan na shiga taro,inko kasuwa naje wallahi taf zan juyo da kayayyaki cike da buhu kuma kyauta ko sile na babu..
ai kinji kaɗan daga sa'ar auran mai gari kenan,ki lallaɓa a haka ki koma kiyi haƙuri abinda aka ce duduwar ma rabinta mutum ce rabin ta kuma mutanan meye zai dameki..
hmmmmm gwaggo kenan baki san dawar garin ba,bazan manta dakuwar da nayi a gunta ba kinga wawulan nan duk sanadin tane wai ni na ɗauki taɓarya zan raɗe ta,ashe ni za a kwashewa haƙora ban sani ba,gaskiya sai nayi tunani idan ma zan koma,haka kawai gaba ƙafa ko hannu za'a gutsiran ayi mini mai gaba ɗaya sam ni na haƙura da shi har a bada gwaggo da duk dukiyar daya tara,ai dolle a kalle ni akira ni da sunan matar mai gari ta dah kinga ai na shiga tarihi a garin nan babba.
Ai shikenan tunda kin ƙi komawa amma ban so haka ba kulu.
to yaya za'ayi faɗan dayafi ƙarfin ka ai daɗin kallo gareshi ni dai bazan iya ba wallahi ina naga ƙarfin faɗa da aljannu kai koda ita kanta duduwar aka barka aradun Allah ka shiga uku bare junnu,junnu,kulu ta miƙe ta faɗa ɗakin data sauka ciki dan kar gwaggo ta kawo wata maganar,gwaggo na ganin kulu tayi ɗaki ta yi ƙwafa ta cigaba da tankaɗan garin ta ba haka naso ba,zan chan zuci ya fito waje har aka fara huɗuba a babban masallacin dake bakin kasuwa kulu na ɗaki ta juyo da sauri ta miƙe ta fara safa da marwa a ɗakin hankalin ta duk ya dugun zuma ya tashi lokacin auran mai gari da duduwa na ƙaratowa sai faman magana take ita kaɗai tana"""
"Na shiga uku,ina zan saka rai na, ni Hauwa kulu da gaske fa ɗaura auran nan za'ayi kuma wallahi ina son miji na mai gari,tsintar hawaye kulu tayi shaɓe-shaɓe,a fuskar ta ta gaza samun nutsuwa dolle ta fito daga ɗakin ta koma gun gwaggo tana kuka wiwi.
------A ɓangaran mai gari kuwa sati guda ya cika yana shirye-shirye yanda biki zai zo,hatta gidanna sa sai da ya fidda kuɗi aka kuma gyara taɓon ɗakunan aka zuba suminti tun daga ɗakunan har tsakar gidan da soro da ƙofar gida gida dai ya ɗau harama aka yaɓa farin fenti da sababbun ƙauraye abun sai wanda ya gani,ta fuskar cima tini mai gari ya bada umarni a fito da shinkafa da ƙaton sa a yanka sadaka saboda baƙin da zasu zo ɗaurin aure da mutanan burni duk aka hattama komai a aka aje,me unguwa da liman sai magatakarda su suka kasa zaune suka kasa tsaye wajan shirya duk abinda mai gari ya bada umarnin ayi,tini aka yanaka zakaru guda goma aka figesu aka gasa aka ajiye da dakakken yaje me ɗan karan daɗi,me unguwa ya bawa Rabi aikin lamurje nan da nan ta hattama komai akan lokaci malam mamuda shi kuma ya bawa matarsa aikin zobo lemuka suka tashi kala biyu ga lamurje ga zoɓo ga shinkafa da miya da tuwon masara yasha miyar taushe da nama zuƙu zuƙu a ciki kamar dunƙulan hannu,ta sifar kaya kam Abubakari ƙani ga mai gari ya antayo masa kusan kala goma harda na amarya duduwa,sai dai a wan da akayi aka ɗinka kayan anyi rashin sa'a gaba ɗaya sunyi mata kaɗan a haka Abubakari yaje yasake sayo wasu ya dawo shi kansa da yayi tozali da duduwa sai da ya dara ganin kwaliyar data ɗuma kamar wata filfiwa ga uban gwagwaro data naɗa akanta yayi zani biyu ba shiri inna ta hauta da faɗa,tana tuno mutanan nata ta dashe baki tana""Na tuba na bi Allah.
Gari ya cika ya batse dam da baƙi musamman a masallaci,mutane har waje suka zazzauna tsabar cikowa abinda ya fara baiwa jama'ar garin kanwa tsoro kenan suka fara tunanin ko suma mutanan sunwa uwar ɗakin nasu kara sun halarci ɗaurin auran,bakin kowa ka duba Addu'a yakeyi sunyi tsiru tsiru,babu damar gulma,daga wannan ya dubi wannan sai dai kaga haƙora na sallama.
bayan an idar da Sallar juma'a aka ɗaura auran *MALAM IBRAHIMU DA AMARYARSA MALAMA ASAMA'U,AKAN SADAKI NERA NA DUKAN NERA HAR DUBU ASHIRIN LAKADAN BA AJALAN BA* jama'aka suka shiga gaggaisawa da junna musamman me gayya me aikin Ango mai gari,bakin gaba ɗaya yaƙi rufuwa sai darawa yake yana gaisawa da jama'a,me unguwa na take masa baya.
Abinda na manta ban sanar da kuba tun lokacin dasu inna da duduwa suka bar gidan mai gari,ko gida basu ƙarasa ba ya nemi gashin gemunsa ya rasa,tsabar murna a wannan rana sai da mai gari yayi sadakar kuɗi yayi dubo goma ya ƙara ƙaimi wa zuciyarsa da ƙudirin auran duduwa ko zai rasa karagarsa, shauƙi na ƙara shiga jikinsa idan ya tuna amaryar sa har wani murmushi yake saki wanda bai san yana yi ba😂😂😂.
""Nan da nan aka shiga fito da abinci da abun sha ana miƙashi ga mazaunin baƙi daban na ƴan gari da sauran jama'a daban hatta almajirai sai da suka ci sukayi haniƙan a ranar biki yayi biki sai dai ba makaɗa mai gari ya ce ba dashi ba wannan safgar albarka yake biɗa ba tarin kalangu ba,haka a gidan inna mata sun ciki gidan dam da abokan arziƙi kai wasu ma gayyar soɗi suka kwaso ƙafa suka zo dan kawai su shaida zanchan da ake,dayawan mata sun duma hannu anata kwasar wara amarya tayi kyau dan wannan kwaliyar daban take da ta farko waya sani ko,"ummmmm,su sukayi mata,duk inda duduwa ta gifta wani hamshaƙin ƙamshi ne yake tashi sai washe baki take tana gaida jama'a ko baka amsa ba.
Gefe na waiga na hangi Saudat da baby sayyada,sai afa wara ake ana gyara zama su Khadyabdul da Zeesha kuwa an duƙufa sai zuƙe lamurje suke suna jefa ledar cikin jaka dan kar a lissafa wanda suka sha,su zee kam ana cikin tsakiyar ƴan kiɗin ƙwarya sai sabada ake ana chashewa ita a dole sai ta burge duduwa ita ko duduwa sai washe bakin take datayi buguzun zata shige filin rawa sai inna ta damƙota......😆😆😆😆😆😆😆
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments