JAMI'IN DAN SANDA 23
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_23
........................."idan fa bakiyi da gaske ba wallahi Abba zai baki mamaki anty ,kinga dai yayi ta baki lokaci amma har yanzu kin kasa kawo mutum daya acikin samarinki , kuma kinada su bare kice babu wanda yake sonki , "Yamutsa fuska tayi cikin matukar damuwa tace , " bazaki gane bane zee nifa wallahi gaba daya banida tsarin aure a yanzu sannan wadan nan samarin nawa Ni ba wanda nakeso acikinsu gaba daya basumun ba narasa yadda zanyi gashi ga dukkan alamu a wannan karon Abba bazai dagamun k'afa ba" tayi maganar kamar zata fashe da kuka,
Dariya zee tayi tace "kina bani mamaki anty idan har kikace babu tsarin aure a rayuwarki , shin abunda nakeson na sani shine auren ne bakiso gaba daya ko kuwa akwai lokacin da kike ganin Yakamata kiyi auren , ? Yakamata dai kisani ita rayuwar mace ƙalilan ce kinada shekara 29 bakiyi aure ba sai yaushe zakiyi ? Yakamata dai kiyiwa kanki fada dai don ita mace babu lokacin da ya dace tayi aure kamar lokacin da ake yayinta ake sonta rashin yin haka kuwa yanasa akai lokacin da zata rasa manemi duk kyauta da matsayinta kuwa sannan................"ke ya isa don Allah karki cikamun kunne da iyayinki na banza ki barni da abinda ya dameni, dariya zee tayi tace "bawani anty kawai dai bakison gaskiya ne amma dai kiyi tunani don wallahi Abba a shirye yake daya aura maki Koma wanene ,cikin damuwa tace " wannan shine abinda yake tsoratani yazama doli na fitar da daya daga cikin manema na tun kamun Abba ya fitarmun da kanshi ,"
Cikin zumud'i da jin dadi zee tace "yawwa anty don Allah ki fitar da Abdul wallahi duk yafi wad'an da suke zuwa wajanki sannan zakuyi matukar dacewa da juna wallahi ,"
"Nikuma bai mun ba zee don haka bazan za'beshi din ba mutum.sai shegen girman kan tsiya da jin shi wanine mrtsss ,daga haka ta tashi ta shige toilet
________________________
Tun bayan abunda yafaru gaba daya halayen Hisham suka canza , mutum mai fara'a wasa da dariya yanzu yakoma kamar wani dodo tsabar daurewar fuska yanzu ko Momma Bata cika ganin dariyarshi ba ,gaba daya ya mayar da kanshi busy aike yake yi da dukkan karfinshi ba dare ba rana ,baya ragawa duk wani azzalumi duk wanda yakama da wani laifi to fa sai ya tabbatar da an hukuntashi koshi waye , saboda jajircewarshi da aiki da gaskiya yasa yayita samun k'arin girma daga wannan sai wannan har inda yanzu Allah yasa aka mashi *mataimakin commissioner* na wannan yanki , yaji dadin wannan muƙamin sosai don yanzu yak'ara samun damar da zaiyi yak'i da azzalumai lokaci yayi da Yakamata su samu canji acikin wannan garin na Lagos , Alhamdulillah komai na tafiya yadda yakeso kuma cikin ikon Allah cikin kankanin lokaci ansamu canji mai yawan gaske a jahar sai sambarka , wannan jajircewar tashi ba k'aramun farinjini ya janyo mashi ba ga talakawan garin don yanzu duk wanda aka zalunta matukar ya kawo kukanshi a hukumar to kuwa Hisham zai tsaya tsayin daka wajan ganin ya kwatar mashi yancinshi, wanna yasa ya samu daukaka sosai fiye da tunani, dayawa zakaga unguwanni sun lika fotunanshi saboda tsabar yadda suke sonshi da kaunarahi,
Momma najin dadin yadda dan nata ke gudanar da aikinshi dakuma irin daukakar da yake samu amma acan k'asan zuciyarta kullum cikin tsoro da zullumi take don tasan doli ne d'an nata yayi mak'iya da yawa wad'an da basason gaskiya da ci gaban kasarsu , saidai tana mashi addu'a sosai tasan ba wanda ya isa yayi mashi wani abu sai da izinin Allah,
Abu daya ke damunta dashi shine rashin yin auren shi , tayi magana da fushi har tagaji amma har yanzu kullum maganar sa daya ce bai tashi yin aure ba sai lokacin da ya dibama kanshi, tasha hadashi da yayan k'awayenta amma yana guje masu duk wadda aka kawo mashi sai yace bata mashi ba , tarasa yadda zatayi dashi ,
Yauma kamar kullum yana zaune a dinning Yana karyawa ta fito daga dakin ta zama tayi kusa dashi tace "shalele da karfe nawa zaka dawo yau ?
"Cikin muryarshi mai cike da jarumta ya amsa da cewa " sai dare zan dawo Momma yau inada ayukka sosai a office, "
"To koma dai minene inason ka dawo da karfe hudu akwai inda zaka rakani kuma saura kak'i zuwa kaga abunda zan maka,
Dafe kanshi yayi cike da damuwa yace ohhhh Momma rakiya fa nikuwa ina zan rakaki sai kace wani mace , nasan dai bazai wuce gidajen k'awayenki ba kiyi hkr zan turo direba ya kaiki kinji,"
"Karma ka fara kai nakeson ka kaini kuma doli ne kazo kaji na gaya maka, "
Kamar zaiyi kuka ya amsa mata da "to" don yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i kila takoma nema mashi wata yarinyar ne shiyasa takeso tajashi suje ,shi kam yaga ta kansa kullum Momma cikin talansa take sai kace yarasa masoya gashi sai ja mashi raini takeyi wajan yara ƙanana , 'bata fuska yayi cikin shagwabar da shi kanshi baisan yayita ba yace "amma Momma saboda Allah haka zakiyi ta talla ta sai kace narasa mai sona kuma ............."kai rufamun baki kullum maganarka daya ce baka rasa masoya ba nikuma banga alamar hakan ba don haka bazan gaji da nema maka ba kuma wannan karon in har kawatsamun k'asa a ido nikadai nasan abunda zanmaka kaji na gaya maka tunda har yanzu kai bakasan cewa ka girma ba a matsayinka ai bai kamata ace bakada mata ba don aure shine cikar mutuncin kowane mutum , baice komai ba haka ya ajiye abincin da yakeci ya tashi yabar gidan,
Momma kuwa bata damuba don tasha alwashin komai zaiyi a wannan karon bazata daga mashi k'afa ba bakomai ne yasa takeson yayi aure ba saidon wannan bakin halin da ya daukama kanshi mutum kullum fuska a hade kamar hadari ba wanda yake ganin damanshi ita kuma tafison ya dawo ainahin Hisham dinshi mai sakin fuska da dariya da tsokana sam ta tsani wannan sabon halin nashi wanda take ganin idan har yayi aure matar zata taimaka mashi wajan canza shi ya dawo kamar da,
_________________________
Gaba dayansu a buge suke yau sunsha sunyi tatil sai raye raye sukeyi mata da maza kuma abun takaici abun tausayi dukkansu yara ne sosai da bazasu wuce 22 to 25yrs ba abin karin bak'inciki da takaici mafi yawansu 'ya'yan mu na hausa Fulani ne ,mafi yawansu ya'yan manya ne masu kudi da masu mulki , iskanci suke kala kala acikin gidan rawa wanda ya kasance mallakin Zayyan ne,
Shikuma shaid'anin yana gefe akan wata kyakkyawar kujera irin ta sarakai ya hakimce , mata biyu ne a gefenshi sai faman shafashi sukeyi suna sumbutarshi tako ina ba kunya ba tsoron Allah yayinda yan korenshi ke gefenshi suna k'ara zugashi da yi mashi kirari irin wanda yakeso ,
Sun shagala sosai ba zato ba tsammani yan matan nan sukaga Zayyan ya hankadesu da k'arfi har saida suka fad'i , daga yan matan har abokanshi da sukaga abunda ya faru ido suka zuba mashi da mamakin ko lafiya,
Yamutsa fuska yayi cike da shak'iyanci yace "abokai nifa yau ranar ta mussaman ce agareni ina bukatar abunda zai sanyani nishadi sosai , wani daga cikinsu yace " wane irin nishadi kake nema da ya wuce wanan ne babban yaro , ai babu wani nishadi da yafi wadan nan kayan da ka ture kawai kabada kai ka kwashi rabonka Baba,
Tsaki Zayyan yayi yace " kai nifa yau wallahi babbar harka nakeso kota wane hali ,wad'an nan duk tsaffin hannu ne yau sabuwa dal aleda nakeso gaskiya......wani irin ihu suka sanya suna dariyar shak'iyanci da yi mashi kirarin da suka saba idan ya tafka wata ta'asar ,
Yan matan kuwa wani irin haushine ya kamasu musamman ma surayya wadda ake kira da sury yar minister ce Allah ya jarabeta da mugun son Zayyan Wanda ba komai ke rudarta akan shi ba irin tsananin kyaun da yake dashi , kuma a sanadin soyayyarshi ne ta samu kanta a wannan halin shine mutum na farko daya fara saninta 'ya mace kuma bayanshi bata kula kowa amma ta kula tuni ya jefata kwandon shara tunda yasamu abunda yakeso yakewulakanta ta ,cikin jin haushi kamar zatayi kuka tace "haba dear abunda kakemun ka kyauta kenan miyasa kake wulakanta Ni ne bayan kasan irin son da nake maka, abunda kakemun yayi yawa dear yakamata karinka tausayamun , Ina tsananin sonka da kishin ka amma nakula kai sam bakama san inayi ba , kasan bakincikin da nakeji aduk lokacin Dana ganka da wata mace , wannan kaskar ma don narasa yadda zanyi da ita ne na barta tana ra'barka amma daga yau zan fara daukar mataki akan duk shegiyar da na koma ganinka tare da ita wallahi "tayi maganar a haukace tana nuna d'ayar budurwar dake kwance har yanzu tun da Zayyan ya tureta , ita kam sama sama ma take jinsu don gaba daya Zayyan ya daga mata hankali wanda batajin zata iya hakura dashi , tashi tayi tana layi takoma nufo inda yake , cikin fitar hayyaci kamar wata zakanya ta far mashi da salon wasanninta ,tsabar rashin kunya sam bata damu da mutanen dake wajan ba sai kokari take tasamu abunda takeso gaba daya tsabar jaraba yasa takasa control din kanta , ba zato ba tsammani sai gani akayi sury ta nufota da kwalba gadan gadan kamun suyi wani yunkuri tuni ta kwada mata kwalbar akai , wata gigitacciyar k'ara yarinyar tafasa ,take kanta yafara fitar da jini sosai , banda ihu ba abunda takeyi ,
Duk mutanen wajan tsai akayi ana kallonsu amma ankasa samun wanda zasu taimaki yarinyar ,shi wanda akayi domin shi ma dariya abun yabashi haka yarinka sakin murmushin shi mai kyau wanda ba k'aramin k'ara fito da ainahin kyaushi yake ba, cikin rashin damuwa sury ta dauki jakanta tayi tafiyarta,
Wata yarinya ce ta k'araso a guje tana tambayar yarinyar da aka fasama kai tana cewa " ke taly mi yake faruwa ne waya maki wannan aiki , arikice take magana da yake batasan abunda yafaru ba fitowar ta kenan daga d'aya daga cikin d'akunan dake wajan ita da saurayinta ta hango k'awar tata a wannan halin kuma kowa ya zuba mata ido anrasa wanda zai taimaka mata,
Kamata tayi tayi hanyar waje da ita , sanyata tayi a mota taja aguje tabar gidan rawar ta nufi asibiti da ita don ganin yadda tafara layi alamar jinin yafara bugeta,
Zayyan da abokanshi kuwa ko a jikinsu saima dariya da sukeyi ,tashi Zayyan yayi ya dube su yace kunga kuzo muje yau zamu fita farauta don wallahi sai na samo sabuwa dal a leda , ihu sukayi tareda fadin "yau zamu ga mai tsautsayin da zata shigo hanyarmu,hhhhhhhhh,
Fita sukayi suka shiga ƙatuwar motarsu suka fice daga gidan ,
***************************
Da kyar ya ajiye ayukkan dake gabanshi ya baro office din ya nufi gida, tafe yake a motarshi sai faman gungini yakeyi gaba daya Momma ta takura mashi akan sai yayi aure shikuma sam baida ra'ayin aure a yanzu shi matan ne ma bala'in haushi suke bashi wallahi ,
Da sallama ya shiga falon ,Momma na zaune cikin shirinta tsaf shi kadai take jira ,ta amsa sallamarshi , gaisheta yayi ta amsa zai zauna kenan tace "a'a karka zauna maza kaje kayi wanka ka ciremun wadan nan bak'ak'en kayan ka nemi manyan kaya kasa kazo mu tafi kuma karka kuskura ka batamun lokaci ,
Baice komai sai yamutsa fuska da yayi ya tashi ya nufi dakinshi,
Wanka yayi ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda ruwan k'asa ya daura hularshi kalar aikin shaddar sai tsadadden takalminshi suma dai kalar aikin shaddar ne yayi kyau sosai daukar agogonshi da farin glass dinshi yayi ya fito daga dakin ,
Hannu ya mik'awa Momma ta Sanya mashi agogo sannan ta tashi suka fita , sai faman washe baki takeyi tanajin dadi , azuciyarta kuwa sai addu'a take akan Allah yasa yarinyar tayi mashi don tasan hali ba yau yasaba bata kunya ba,
*************************
Tafe suke kamar kullum akan titin sai faman shek'a gudu sukeyi kamar zasu tashi sama yayinda music da iface ifacensu ya cika motar , a haka har suka zo wata unguwar talakawa nan suka rage yawan gudun da sukeyi a hankali suka fara bin kowane lungu da sako na cikin unguwar , cikin ikon Allah kuwa Allah ya hadasu da wasu yan mata biyu 'yan makarantar secondry sun taso daga school suna tafiya a hankali suna dan ta'ba fira,
Tundaga nesa suke k'are masu kallo , tuni Zayyan ya k'uresu da ido yana nazarin wadda zai za'ba aciki,
Cak ya tsaida idonshi ga d'ayar wadda ta kasance fara tass kuma doguwar mace ga kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta tara abubuwan da duk namiji zai so a wajan mace , cikin wani shu'umin murmushi ya nuna masu ita ,
A take suka kunna motar suka bi bayansu don har sun Dan gotasu k'ad'an, suna zuwa dai dai inda 'yan matan suke suka tsayar da motar , cikin matukar zafin nama da kwarewa suka cafko yarinyar suka turata mota suka shiga Zayyan yaja motar aguje inda sukabar dayar yarinyar na zunduma ihu da kiran a taimaka mata 'barayi ne , kasancewar wajan ba mutane sosai da kyar mutane suka fara taruwa akanta wanda zuwa lokacin ko k'urar motar su Zayyan babu a wajan,....................
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
*SHAHARARRA KUMA K'ASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA _MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TA SAKE ZO MAKU DA KAYATATTUN KAYAN MATA ZAFAFA MASU KYAU DA INGANCI SAYEN DAYA KO SARI INA SOKOTO INA AIKAWA KOWANE GARI A NIGERIA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH KUDAI KU MATSO KAR AYI BABU KU KAYANMU NA MUSAMMAN NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
09035027743
*KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA MUKE DASU*
maganin sanyi
Maganin KIBA
Maganin rage tunbi da kiba
Maganin sanyi na maza
Maganin gashi - Yana Sanya tsawon gashi Hana karyewar gashi bakin gashi yana maganin sali kurajen Kai da sauran matsalolin Kai
*Akwai zafafan kayan Mata Kamar jaka*
Gumar Madara
Gumbar gero
Gumbar Jan icce
Gumbar Sha ki matse
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar ridi
Gumbar shinkafa
Gumbar Aya
Gumbar ukku bala'i
Sarauniyar gumba
Da dai sauran kalolin gumbunan da muke dasu
*Kalolin gari*
Dakan jaraba
Kinfi budurwa
Jita salaf
Garin mallaka
Dakan Ni'ima
Bita zai-zai
Sabon budurci
Mai kwamson gyada
Dakan tabaje
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Dakan Amare
Emergency
Dakan sa buzu kuwa
Dakan sha yanzu magani yanzu
Da sauran kalolin da ban fada ba
09035027743 mmn yusuf skt
*Munada kalolin matsi da basuda illah Kuma masu matukar aiki da Kara lafiya ga HQ*
Matsin mallaka
Matsin a Daren farko
Matsin sabon budurci
Danba gigita
Matsin kishiya in bakiyi bani waje
Matsin Dan la'asar
Gam-gam
Matsin kinfi budurwa
Matsin rantse bakida kishiya
Matsin Dan mannau
Matsin k'yallen al'ajabu babban sirri kenan
Da sauransu
*AKWAI*
original Dan goshi ba bugi ba tare da Mahadi shi
Original man ayu
Original man damo da kitsensa
dan goshi sabon salo wanda ake amfani dashi ga mara
*Muna dahuwa Kamar haka*
Dahuwar kaza
Kazar yar gata
Kazar Amarya
Kazar maijego
Ciccibi
Yan shila
Nama
dambun nama Wanda yake jimawa ajiki
Kifi
Da dai sauransu
*Daga gefe Kuma akwai*
1,Maganin kiba maisa cikowa da laushin fata,
2,maganin gyaran nono 3in1
3 na hips mai ingaci dake aiki a cikin sati daya
Kalolin sabulun wanka masu gyara fata da Sanya hasken fata mai kyau
Sabulun tsarki Yana maganin duk wata matsala ta HQ Yana matsi ciki da waje Yana saukar da Ni'ima
Turaren jiki
Turaren daki
Turaren tsugunno
Tsarkin jaraba
Dan la'asar na Sha
Kayan gyaran jiki na Amare irin su dilka halwa sabulun Amare turarrukan Amare masu gyara fata da Sanya k'amshi ajiki
Hatsabibin turarene
Hatsabibiyar humara
Kalolin humara
Colecca
Sirrin mallaka na tafin kafa hmmm yar uwa jaraba kiga abun mamaki
Dama sauran abubuwan Dana manta ban fada ba duk zaku samesu a wajan yar mutan sokoto mmn yusuf skt
*A'bangaren girki ma muna bada namu tallafi akwai curry kala kala Masu kamshi da bada launin abinci nai kyau da jan raayi yara da oga ga abinci ki hjy* 09035027743
*A'bangaren tsumi ma ba'a barmu a baya ba akawai*
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin madarar Ni'ima tsumin tabaje💃🏻
Shayin Amare
Tsumin nono rakumi
Zumar Mata mai ridi & zumar. Icce xallah tamasu jego
Tsumin ruwa lumtsum
Tsumin Sabon budurci
Tsimin bita xaixai
Tsimin makalemata
Tsimin sa sambatun oga
Da dai sauransu
09035027743
*Muna hada kayan Mai jego abubuwan da zasu dawo Mata da martabanta a wajan maigida kasancewar duk wadda ta haihu to ni'imar jikinta na tafiya sosai hakama HQ dinta zai bude to muna hada kayanda zasu dawo Mata da martabanta zata matse sosai ciki da waje Kamar bata haihu ba da Wanda zasu dawo Mata da martabanta akan kudi kalilan*💃🏻💃🏻
Hakama zawara Mai Shirin yin aure muna hada Mata kaya masu taken ubanka sabon budurci💃🏻
Hakama budare muna hada kayan gyaran Amarya ciki da wajenta zatayi das abunta gwanin sha'awa sauran bayani Kuma ango ne zai yi maki😉
Karku manta da sunan maman yusuf yar mutan sokoto
Address _unguwar Makerar Assada area sokoto
Phone number _09035027743 do neman Karin bayani 👍🏽
*Don Allah don annabi duk wadda Bata shirya siyaba kar tamun magana tabari sai ta shirya tukunna kar mu batawa juna lokaci* 🤗🤗🤗🤗
No comments