SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 14
*BOOK ONE*(1)
Cikin qasaitaccen takunsa ya fara takawa har ya isa daidai inda take, ita kuwa tana zaune fuskarta a rufe amma sassanyan qamshin turarensa ya gbdy ya cika mata hanci, gabanta na cigaba da bugawa taji ya sunkuyo daidai fuskarta ya d'aga hannunsa wanda yake d'auke da zara zaran kwantaccen gashi ya yaye laffayar data rufe mata fuska cikin sauri tayi qasa dakanta, hannu ya kuma sanyawa ya d'ago ha6arta yana kallon fuskarta,yana wani maqetacin murmushi yace" meyesa kk amince da aureni duk kuwa da gargad'in dana miki sbd kina sona koh?" dariya yyi sosai har jerarrun fararen haqoransa suka bayyana,
rumana kallonshi take cike da tsantsar rud'ewa saidai duk da halin da take ciki hkn be hanata yabawa da kyawunsa ba musamman k'wayar idanunsa da suke blue tamkar na turawa sannan kyakykyawan sajensa baqi wuluk ya zagaye masa fuska, samun kanta tayi da zareshi da ido bata ankara ba taji yasa yatsansa ya tsole mata idanu, tuni ta dawo hayyacinta, fuskarsa taga ya had'e tamkar be ta6a dariya ba, juyawa yyi abinsa ya shige bathroom ya sakarwa kansa shower, babu jima ya fito d'aure da wani white towel hannunsa riqe da wani small white towel d'in yana goge kansa dake d'igar ruwa, gbdy jikinsa duk gashi musamman ma broad chest nasa, tana tozali da surar jikinsa ta rufe idanunta ruf, k'irji ya soma bugawa tamkar ze faso, jikin ya cigaba 6ari don ita tunda take bata ta6a ganin namiji babba babu riga ba sai yau, shi kuwa bema san tanayi ba har ya gama shiryawarsa ya sanya wasu fararen sleeping dress riga da wando ya feshe jikinsa da turare sannan ya nufo wurin tafkeken gadonsa, kallonta yyi yace" oyah sauke ki koma qasan floor" ita kuwa dayake ba jinsa take ba kuma idanunta a rufe gam suke don hk ko motsawa batayi ba bare ta amsa umarninsa wanda hkn yyi masifar qularshi, hannu yasa ya finciketa ya watsata qasa kanta ya bugu da wani qaramin stool gbdy laffyar dake saman kanta ta cire dogayen kitson kalban dake kanta suka baje a gadon bayanta, shi kuwa yana kwance abinsa yana latsa phone d'insa yana kuma kallonta ta gefen ido, kuka ta somayi mara sauti saidai kawai ruwan hawaye dake ambaliya a saman fuskarta, jan jiki tayi ta miqe ta koma gefe guda ta takure, kallonta yyi a karo na biyu yace" ba zama zakiyi ba miqe kije ki sauke wadancan littatafan ki sake jerasu sannan ki fito da kayan dake cikin drawer d'in can ki sake shiryasu,idan kin gama ki wuce ki wanke toilet, wannan shine aikinki a wannan daren" yana fadar hk ya koma ya kwanta, but to his surprise yaga ko motsawa batayi daga inda take don batasan me yake fad'i ba ita dai taga bakinsa na motsi alamun yana mgn, wata uwar tsawa ya daka mata amma sai yaga kawai ta qureshi da idanu kallonshi, saukowa yyi daga saman bed d'in ya nufo wurin da take babu wata wata ya kwasheta da lafiyayyen mari har saida shatun yatsunsa suka fito rud'u rud'u a saman fuskarta, kunsa farar fata, ja ta somayi da baya tana girgixa masa kai tare da masa alamar ban hkr da hannunta, wannan abu yyi masifar d'aure masa kai, zuba mata idanu yyi don gbdy kwakwalwarsa ta dakata da aiki na wucin gadi sbd tsananin d'aure dakansa yyi yadda yaga tana masa alamun yaren kurame da hannu, kwatanta yanayin 6acin ransa a wannan lkci bazai misaltu ba, tunanin daya zo kansa kawai shine wato shi za'a raina ma hnkli a aura masa kurma batare da saninsa ba, duk iya tunaninsa ya kasa fahimtar abunda lamid'o yake nufi da hkn, tuni fuskarsa tayi jajir ransa yakai qololuwar 6aci, dunk'ule hannunsa yyi gbdy ya rotsa tankamemen dressing mirror d'in dake d'akin ya soma wani huci tamkar mayunwacin zaki, madubin duk ya yanka masa hannu sai d'igar jini yake, hannu d'aya kawai yasa ya shak'o wuyanta, jira kawai yake yaga bata numfashi kafin ya saketa saidai suna hada idanu da ita yaga yadda take kallonsa tuni k'wayar idonta tayi tasirin hanashi aiwatar da abunda yyi niyya yyi watsi da ita gefe, idan ransa ya 6aci babu uban wanda yake gani da gashi hk yake komawa tamkar mahaukaci don rasa control yake kuma ba mahalukin daya isa ya tunkareshi bare ya hanashi aiwatar da nufinsa shiyasa wasu suke yad'awa cewa yariman adamawa na da ta6in hnkli, saida yyi watsi da komai na d'akin sannan ya koma gefe ya zauna a bakin gado ya dafe kansa dake sara masa kamar ze ra6e biyu, rumana kam mutuwar zaune tayi don ta gama sadak'arwa yana gama fashe fashensa kanta de dawo ya kasheta sai taga ya koma ya zauna, kallonshi take cike da tausayi sbd hannunsa dake zubar da jini, tashi guda taji tsoro ya fita daga ranta ta miqe riqe da wuyanta data sha shak'a ta nufi inda bathroom ta fito da qaramin towel ta nufi inda yake a zaune ta nemi gefensa a qasa ta zauna tasa hannu ta riqo hannunsa, d'ago dakansa yyi yana kallonta da rinannun idanunsa sai kawai gani yyi tasa wannan qaramin towel din tana d'aure masa hannu sbd jinin dake fita ya dakata, kasa janye hannun nasa yyi ya tsareta da idanu yana kallonta, batare data gama ba ya janye hannunsa ya miqe ya fice daga d'akin, gbdy ma ya fice daga sashin ya wuce wurin motoci, dogaran dake tsaron wurin suna ganinsa su kansu suka sha jinin jikinsu babu wanda ya sake koda kyakykyawan tari don sun san ifiritan kansa ne suka motsa, suna ganin shi ta fada mota yaja ta da wani mugun speed ya fice a million duk kuwa da dare yyi sosai, kai tsaye wani five star hotel ya wuce.......6angaren rumana kuwa saida ta gyara duk 6arnan da yyi sannan itama ta fice saidai bulayi ta somayi cikin 6angaren nasa don batasan hanya ba ga 6angaren nada girma sosai, wata zuciyar ta sanar da ita toh yanzu ina zaki idan kin fita da tsakar daren nan gashi ba sanin wannan masarauta kkyi ba, kar fa kije asirinku keda gimbiya ya tonu idan wani ya ganki cikin daren nan, wannan tunanin ne yasa ta koma d'akin ta takure gbdy hanklinta a tashe, fitar yarima kuwa tuni yakai ga mai martaba, hnklin ya tashi yasa aje a duba lfyr yar mutane kar yaje ya illata musu d'iya, cikin daren yayyinsa mata suka shiga 6angaren nasa, suna bud'e bedroom d'insa suka hangota a takure a can quryan d'akin, duk da kasancewar ta gyara wasu abubuwan daya 6ata amma hkn be 6oye musu hango 6arnar daya tafka ba, cikin sauri fulani habiba da adda shatu suka d'ago da ita tana d'ingishi don k'afarta ta gurd'e sannan gefen goshinta jini ne ke fita, saidai me zai faru?? idanunsu na sauka kan fuskarta duk sukayi turus, suna kallonta cike da tarin mamaki don wata suka gani daban ba gimbiya bilkisu amaryar yarima ba, kallon kallo aka soma duk sun kasa mgn sbd tsantsar mamaki, sai can fulani hindatu tayi karfin hali ta bude baki tana kallonta tace" wace ce ke? meye ya kawo ki 6angaren nan har cikin dakin magaji??" duk a lkci guda ta mata wannan tmby, ita kuwa 6ari kawai jikinta keyi gumi ya soma keto mata don ta tabbatar yau asirin gimbiya ya gama tonuwa, ja ta somayi da baya tana musu alamar yaren kurame da hannu, wani kyakykyawan mari fulani habiba ta sauke mata a fuska tace" dan ubanki wace ce ke daga ina kk kuma ina amaryar yarima take??" gbdy mgn suke a mugun fusace da hausarsu iirinta fulani, chafko hannunta fulani hindatu tayi suka fice da ita kai tsaye 6angaren gimbiya bilkisu suka nufa, suna tura kofar bedroom dinta suka hangota tayi dai dai a saman tafkeken gadonta tana baccinta mai cike da jin dadi, cike da tarin mamaki suka soma kallon juna da al'ajabi, toh meke faruwa??...........wace ce amaryar wannan ko waccan..........akwai chakwakiya jama'a, hhhh, muje zuwa....
*Littafi na Biyu na kudi ne*
Alkalamin Bintu ne.....
No comments