Breaking News

JAMI'IN DAN SANDA 15

 .a👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

🅿️_15

................wata irin k'ara Ibrahim ya fasa tareda kiran Hishammm sakin Momma yayi ya dawo wajan shi yana bubbugashi duk ya firgice  yama rasa abunda zaiyi ,ganin hakan yasa wani daga cikin yan sandan yin azamar fita daga gidan motar da suka zo da ita ya bude ya dauko ruwa a gora yakoma ciki da sauri , nan yashiga yayyafawa  Hisham ruwan ba'a dau lokaci ba ya farfado a razane yana kiran sunan Momma , hangota da yayi a kwance a wajan data fadi ne yasa ya zabura da karfi ya nufi wajen da take , d'ago kanta yayi ya d'ora bisa k'afafunshi yafara kiran sunanta da k'arfi ,

 

"Momma Momma ki tashi ki tashi nace muje mu gano halin da Abba yake ciki , ki tashi Momma Abbana Abbana kazo kace ta tashi arikice  yake maganar daga nan kuma sai yafara sambatu wanda sun kasa fahimtar abunda yake cewa , ganin Momma bata farfado ba kuma suna k'ara 'bata lokaci da Hisham ma baya hayyacinshi yasa d'aya daga cikinsu kallon Ibrahim yace ku kamata musata amota muje asibiti zaifi , haka kuwa akayi Ibrahim shi kadai ya dauketa ya sanyata amota sannan ya kamo hannun Hisham suka shiga , direc suka nufi asibitin da aka kai Abba. Suna zuwa likitoci suka rufu akan Momma cikin ikon Allah bata dauki lokaci ba ta farfaɗo , sai dai tana farfadowa da kuka ta farka sai kiran Hisham takeyi, likitan ne yafara kwantar mata da hankali akan ta tsaya za'a kira mata shi amma ina sam tak'i k'arin ruwan da aka sanya mata ma tuni ta fisge hannunta ta mike tsaye ,ganin hakan yasa yabada umurnin a je a kira Hisham , 


Banda Safa da marwa ba abinda yakeyi har wannan lokacin yakasa tambayar halin da mahaifinshi yake ciki saboda yana fargaban abunda za'a gayamashi wani irin zufa ne mai zafin gaske ke keto mashi ta ko ina kamar an masa wanka da ruwan zafi , ahaka wannan ma'aikacin jinyar ya taddashi , nan ya gayamashi likita na nemanshi , tun bai k'arasaba ya juya da sauri ya nufi inda aka shiga da Momma,


Tana ganinshi ta k'arasa wajanshi da sauri tace " Hisham ya jikin Abbanka mi yasameshi ka ganshi kuwa yanadai lafiya ko ?? 

Tunda tafara jero mashi tambayoyin ido kawai ya zuba mata yana kallonta , a wannan lokacin sam bazaice ga abinda yake tunawa ba gaba daya komai ya tsaya mashi tunda yaga irin yadda asibitin yacika da jami'an tsaro sai shige da fice sukeyi yasan tabbas sai Allah idan Abba yana raye ,

Jan hannu Momma kawai yayi batare da ya bi takan likitan ba suka fita daga dakin , direct wajan mutanen da sukazo dasu ya nufa yana zuwa cikin sark'ewar murya yace masu "a ina Abba yake"?


Duk diriricewa sukayi kamun daya daga cikinsu yayi masu jagora zuwa dakin da gawar Abba take, 


Tunda suka nufi wajan gabansu ke wani irin bugu kamar zai fashe a haka har suka shiga dakin, 

Dukkansu cak suka tsaya a inda suke suna k'arewa farin k'yallen da aka rufa mashi kallo wanda gaba daya ya 'baci da jini , 

Jiri ne yafara d'iban Momma a haka tarink'a tafiya har ta k'arasa inda gawar take a hankali ta sanya hannunta wanda yake rawa sosai tafara janye farin k'yallen, runtse idonta tayi da k'arfi kamun kuma a hankali takoma budesu ta zuba mashisu ko k'yaftawa batayi yayinda a lokacin komai tsaya mata yayi tana kallon abun kamar a mafarki sai fatan take Allah ya tayar da ita daga wannan mummunan mafarkin da takeyi , 

Shafa fuskarshi tayi a hankali tare da furta " "Abban shalele" Abban shalele da gaske mutuwa zakayi kabarmu , ? Kar ka mana haka Yaya ka tashi Sam bazamu iya rayuwa ba in babu kai ganin har yanzu bai motsaba yasa tafara magana da karfi tana Kiran sunanshi tareda jijjigashi tana kiran karya mutu ya tashi ,


Matsawa dan sandan yayi kusa da ita sannan yasa hannu ya janyo farin kyallen yakoma rufe Abba dashi ,cikin matukar tausayawa yace " Hajiya saidai muyi hakuri Allahn da yabamu shi ya karbi abunsa , sai dai mubishi da addu'a kawai , 


Girgiza kai Momma tafarayi tana ja da baya har takai da bango durk'ushewa tayi a wajan  tana wani irin jan numfashi zuciyarta kuwa kamar zata fasa kirjinta ta fito tsabar bugun da takeyi , kamun bugun zuciyarta ya tsaya cak ta koma sulalewa ta fadi a wajan a some ,


Dan sandan ne yayi saurin fita kiran likita yayinda akabar Hisham nan tsaye ba um ba um um shi baiyi gaba ba kuma baiyi bayaba yayinda idonshi ke kafe akan gawar mahaifinshi duk da faduwar da Momma tayi hakan baisa ya juya ya kalleta ba ,kalaman wannan ma'aikacin kawai yakeji yana mashi amsa kuwa acikin kunne *_Allahn da ya bamushi ya k'arbi abunshi_*


Ahaka wasu likitoci biyu suka shigo suka shiga bawa Momma taimakon gaggawa yayinda wannan dan sandan yaja hannun Hisham suka fita haka yarinka bin shi kamar wani wawa sam yakasa gane komai yakasa fahimtar komai yakasa aikata komai sai zuciyarshi dake mashi wani irin lugude mai tafe da tsantsar fargaba, 


Office din babba likita suka nufa don yin duk wani cike cike don karbar gawar , haka akasa Hisham ya rattaba hannu  aka gama duk wani cikwu-cikwu aka basu gawar , 

Haka suka dauko gawar a motar asibiti suka nufi gida ,


Lokacin da suka zo har kofar gidan tafara cika da mutane nan aka shiga dashi aka mashi wanka aka shiryashi cikin likkafani , har wannan lokacin Hisham yakasa furta koda kalma d'aya ne yayinda idanunshi da zuciyarshi suka soye sam ba alamar hawaye a idonshi , 


Acan asibiti kuwa Momma tana farfadowa bata sauke  idonta a ko ina ba sai akan gadon da taga gawar mijinta a kwance ,dubawa tayi da kyau tare da sake murza idonta amma har lokacin bataga komai ba a zabure ta tashi tana fadin "ina mijina ina kuka kaimun mijina , ?

"Kiyi hkr Hajiya sun tafi da gawar gida kizo muje akwai wad'an da aka bari idan kin farka sai su tafi dake cewar likita, 


Gawa gawa gawa fa yace kenan da gaske ne tarasa mijinta uban danta majinginarta kuma majibincin lamarinta , a hankali cikin wata irin murya ta furta " *Innalillahi wa inna ilaihin raji'un Alhamdulillah ala kulli halin*  a hankali taji wata irin natsuwa da tawakalli ya ziyarceta , tunawa da tayi ai tanada Allah kuma shine gatan kowane bawa , sannan Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i daga nan taci gaba da ambaton sunan Allah yayinda a hankali wata irin nutsuwa ke k'ara shigarta , ahaka har suka isa gida , 


Lokacin da tayi arba da taron jama'a k'iris yarage bata koma faduwa ba haka dai ta daure tana tafe tana dafa bango har ta shige cikin gidan , 


A falo ta tarar da mata dank'am matan abokanshi ne da makota sai k'awayenta nan ta ra'basu ta shige cikin bedroom dinta ta mayar da kofar ta rufe kamun ta zame anan wajan ta saki wani irin kuka mai ban tausayi,



Bayan an shirya shi ne aka nemi Momma da Hisham da suje suyi mashi addu'a , 


Addu'a sosai Momma tayi mashi tanayi tana kuka mai tsuma zuciya yayinda Hisham yakasa koda motsa bakinshi ne bare yayi magana sai dai idanunshi da suka kad'a sukayi jajir ga wani girma da suka k'ara abun tsoro , ganin yakasa yin komai ne aka dauke gawar akayi waje da ita inda za'ayi mashi sallah,


Bayan angama sallah ne aka nufi mak'abarta , sai a lokacin Hisham yafara dawowa hayyacinshi , lokacin da aka bashi gawar ne don ya sanya mahaifinshi da kanshi wani irin sanyi mai haɗe da makyarkyata suka kamashi gada daya jikinshi rawa yakeyi sam yakasa rike gawar sai da aka taimaka mashi bayan an sakashi ne aka rufe kamar yadda akema kowane mahaluk'i alokacin ne wani marayan kuka ya kwace mashi mai tafe da wani irin sauti mai taba zuciya lokaci daya wani tari mai karfi ya sark'eshi kamun kace mi yazube a wajan a some , 

Nan aka daukeshi wasu suka nufi wajan amsar gaisuwa abokanshi kuma suka nufi asibiti dashi ,


Kwana sambatu Hisham yayi kamar wani mahaukaci sabon kamu , Ibrahim da wani abokinsu Aliyu ne a wajanshi , Momma kam tuni k'arfin imani ya shigeta ta fawwalawa Allah komai sai addu'a take ma mijinta saidai duk da hakan takasa tsayar da hawayenta musamman in ta tuna da Hisham ,


*Washegari*


K'arfe 10am na safe a Lagos tayi masu , Abdullahi ne da Inna Asabe sai matarshi da yaranshi , suma tunda labari ya riskesu jiya suke cikin tashin hankali musamman ma Abdullahi yayi kuka kamar ba gobe yayi dana sani tafi cikin kwando haka kawai akan mace ya dauki tsanar duniya ya  daurawa tilon d'an uwanshi akan *mace* yafita sabgarshi baya shiga duk wani abinda ya shafeshi yayi watsi da zumunci duk akan mace yanzu wa gari ya waya gashi nan yarasa tilon d'an uwanshi da bashida kamarshi duk duniya , mahaifinsu har ya mutu yana masu nasiha akan su kula da  zumunci Amma duk da haka baisa ya gyara tsakaninshi da dan uwanshi ba to ga irin ta nan yarasashi a lokacin da yafi buk'atarshi    


Kuka yake sosai yana neman yafiyarsu lokacin da yakewa Momma da Hisham gaisuwa da yake tun da sassafe Hisham ya baro asibitin batare da an sallame shi ba , duk da har wannan lokacin bai gama dawowa daidai ba ,


Nan Alhaji Abdullahi da iyalanshi suka zauna har aka gama amsar gaisuwa , saida akayi kwana bakwai sannan yayi shirin komawa tareda matarshi bayan ya ajiye masu duk wani abunda yasan zasu buk'ata tareda gaya masu duk abunda sukeso su kira su gayamashi , anan aka bar inna Asabe don tace anan zata zauna tarink'a debewa Momma kewa har ta saki jikinta , don ta kula daga Momma har Hisham basu gama dawowa hayyacinsu ba barinsu su kadai zai iya haifar masu da wata matsalar saboda yawan tunani da damuwar da suke ciki,



Agurguje pls🙄🙄🙄🙄🙄Zan baku agurguje saboda inason mushiga gundarin labarin ne don wannan sharar fage ne kawai kuma sam ba wannan matsalar ce ta rabo Hisham da gida ba cakwakiyar tana gaba😍😍



*Bayan wata shida*


Zuwa yanzu komai yazama tarihi Alhamdulillah daga Momma har Hisham sun mik'a lamarinsu ga Allah suna rayuwa cikin farin ciki , saidai yanzu gaba daya Hisham ya canza yakoma shiru shiru sam bayason abunda zaisa yayi magana yakoma miskilin karfi da yaji Momma ma yanzu saidai taga murmushinshi amma badai dariya ba ga wani fad'a da ya taso mashi abu kadan zai kama masifa a haka dai sukaci gaba da rayuwa kuma har wannan lokacin inna Asabe tana tare dasu duk lokacin da tace zata tafi yanzu Momma zata fara koke koke shiyasa yanzu har ta daina cewa zata tafi ,



 Dayan bangaren kuwa kkowanne da damuwa dankare acikin zuciyarshi saidai suna kokarin nunawa juna basa tare da wata damuwa , 

Momma tana zargin  kashe mata miji akayi saboda wasu dalilai  amma takasa gaya kowa batasan yadda Hisham zai dauki al'amarin ba shiyasa taja bakinta tayi shiru , 


Yayinda a 'bangaren Hisham yake ta tunanin ta yadda zaiyi ya shawo kan Momma ta barshi  *ya cikawa mahaifinshi burinshi na zama _Jami'in dan sanda_*


Yau ma kamar kullum suna zaune a dining suna karyawa ya d'ago kanshi yace "Momma akwai maganar da nakeson muyi amma don Allah inason ki tsaya kiyiwa abun kyakkyawar fahimta Kuma pls momma karki ce Zaki hanani don Allah ,"


"Ina jinka Hisham gayamun mi kake so , "?


Cikin inda inda yace Momma dama shekaranjiya ne naje na cike Form na aikin *dan sanda* to inatason namaki bayani amma...............baisamu damar k'arasawa ba sakamakon wani irin tari da ya sark'e Momma , a rikice ya debo ruwa zai bata amma ga mamakinshi sai gani yayi tasa hannu ta ture ruwan tareda wurga mashi wani irin kallo wanda tunda yake da ita bai taba ganin tayi mashi koda makamancin shi bane ga wani tsantsar tashin hankali da fushi hade da masifa da ya hango acikin kwayar idanunta , 


Pls momma .............hannu ta daga mashi kamun ta tashi tabar wajan batare da ta ko kalli inda yake ba,.................✍🏼




*Zanyi aike Kano da Zamfara gobe kuma kudin motar kyauta ne maiso ingantattun kayan mata tayimun magana ta pc ngd* 09035027743

No comments