Breaking News

DUDUWA 6

          _6_

"Tsawon awa daya Inna ta shere dunqule a daka ko ta abinda za ta kai bakin salati ba tayi ba sai du'a'i take daga wannan Addu'ar ta kama wannan har cikinta ya fara kiran ciroma taga zaman ba me yuwa bane a daddafe ta fito,tana fitowa tayi waje da gudu gudun kar qawayen na duduwa su riqo ta,ta Dade tsaye a waje tana nazarin me zatayi wata zuciyar ta ayyana mata.

""Ki tafi nemo Duduwa kawai idan tana kusa dake to babu abinda zasiyi Miki,""wannan shawarar tayi inna ta furta tana mai bazama neman Duduwa layi da saqo ba Duduwa babu labarin ta har a zahar ta gabato Inna na neman Duduwa Bata ganta ba ta gaji da bulayi ta koma gida dan sarrafa abinda zata ci dayawan mutane har wasu sun fara murna suna fadin" ko abinda Duduwa ta aikata yasa ta gudu ta bar garin gaba daya labari yazagaya ko Ina aka shiga jajantawa junna Ana hamdala.


  Kwatsam bayan magariba sai ga duduwa ta shigo gidan kamar an jefota daga sama Inna ta zabura zata ruga da gudu Duduwa ta riqota Gam tanai mata dariya sai ga fitsari na biyo qafar Inna tana.


Natuba nabi Allah da Manzonsa kuyi mini aikin gafara........


""Inna kin gama tuwon ne?


Inna ta zaro Ido tana duban Duduwa dake barka dariya.


Duduwa.


Na am Inna,Ina zaki tashi da wannan uban gudu haka.


Sakar ni karki karyan sangalalan hannu tunda ke ce ai shikenan.


Lah su Inna har da fitsari a zani.


Wai Daga Ina kike tun sahe Duduwa baki dawo gida ba.


Ina chan duniyar qawayena yanzu ma haka jirana suke mu koma.


Na shiga Tara ba uku ba Ni Suwaibatu jikar na dudu,akai Inna ta dora hannayenta dukka biyun,Duduwa na dariya tace.


To kinji sunce nayi zamana suje su dawo zubo min tuwon da zafi zafinsa naci Inna.


Too too Mara nawa zan sako miki?


Sako daya Allah yasa incinye cikina duk ya cushe da baqara kashi Inna,duduwa ta qare batun tana dariya inna ko cewa tayi.


Ummmm ummmm gashi Nan ki dauka,Duduwa tasaka Hannu ta dauki tuwon tana.



""Hmmmm yau su Tani za'aci Uba kan ajuya kansu Hansai da Asabe, Duduwa ta Kama waqa tana rawa ta6ar ta6ar...... ...


""Allah Kai mu kai mu......


""Kai mu Madina Misha zam zam da dabino.....


""Muci dandamal Hamid har dasu baqara Kashi........


Inna dake tsaye da jiqaqan zaninta tace.....


Aa aa Duduwa adinga haquri Ana kai zuciya nesa Dan Allah.


To fada musu ai suna jinki yasin aka nane bakin ki Inna ko haquri bazan basu na kwabo su bude Miki shiba.........


Wallahi na Dena kar ma suyi haqurin duk wanda ya ta6osu suci malafar ubatai.


Duduwa ta kuma kwashewa da dariya har da kaiwa te6ar cinyar ta duka,""kaga su Inna akwai Dan Karan tsoro sai shegen surutu ungo tuwonki Yama ishe Ni,ta miqe tabar Inna da zani a hannu tana tofa KURSIYU ta ko Ina ta kasa shiga makewayi ga fitila a hannun ta.




 ...........Tani ce zaune a daka a takure taga kamar an gefta daga qofar dakin da take ciki,basarwa tayi ta Kuma duqulewa hankalinta gaba daya ya koma kan qofar da aka Kuma geftawa akaro na biyu da sauri ta miqe tana.


"""Gwaggo!!,gwaggo!!,kizo Dan Allah gwaggo,shiru kake ji ba Wanda ya amsa mata bare yazo inda take gashi tana jiyo hayaniyar 'yan gidanna su gaba daya a tsakar gida.

  Wuff taga an sake wucewa da gudu sai dai yanzu kofato idonta ya hango cikin razana ta miqe tsaye da sauri ta hade tafukan hannunta biyun zuwa fuskarta ta rufe tana kuka da qarfi dan ajiyo ta akawo mata dauki a dai dai kunnanta aka furta.


       ““Tani muta nan mu,,,.


Haba wa Tani najin haka Sai ihu da kiraye kirayen mutanan gidan babu wanda sunansa Bai fito ba Amma shiru kake ji kamar ba ihu da kiransu Tani keyi ba aka sake tintsirewa da dariya chan Kuma a Ka ce““


””Dama kin rufawa kanki asiri kinyi shiru da bakin ki daya fi miki alkhairi don babu wanda zai jiyo ihun ki idan ba mu ba.


Qarfin Hali tusa da usur Tani da ke ihu ta iya cire hannayenta daga fuskarta Dan ganini wake magana.

      Wata tsuhuwa ce da girmanta Bai fi na qaramin turmi ba duk gashi jikinta sai washe zaqo zaqon haqoranta take a gaban Tani da tini numfashi ta ya kusa daukewa sai shassheqa take tana ja da baya.


Tsohuwar matar ce ta hade fuska kamar ba ita ke dariya ba tace da Tani.......


  “““Ziiyara na kawo miki don ki tayani cinye tuwon gidanku gaba daya idan kika yi taurin kai sai na Mai da idonki goshi na dawo da goshinki idon ki Dan haka ki tayani ci babu abinda zan yi miki.

   Nana da Nan Tani ta saki fitsari da zawon daya saura a cikinta a hankali ta soma kuka tana rufe ido ta bude,matar sai dariya take tana tsalli tsalle kamar guntun kashi a gun chan kuma ta ce.


Ga tsarabar mu Nan maza ki dau haramar ci kina gamawa zanyi tafiya ta idan kin qi ci to Nan fa zamu kwana mu yinni ba Wanda ya Isa ya yaganmu idan Kuma ta Raya min daukar ki San mu tafi chan duniyar mu ki qarasa rayuwar ki achan.


Ta ajiye qatuwar qwarya da aka hada tuwo da miya aciki fal ta koma gefe tana kallon Tani,idon tani na rufe ta sanqamo qwaryar gabanta nan da nan tashiga Kai tuwon cikinta hawaye na bin fuskarta jikinta sai karkarwa yake data nemi qwarewa zataji ruwa dai dai bakinta sai ta wani fashe da kuka tana hadiyar ruwan da tuwon a hade,a hankali ta cinye tuwon cikin qarya ga ruwan da aketa tuttula mata atake cikin tani yacika yai 6am nishi ma da qyar take tana hawaye,bayan'yan daqiqu jin an Dena kai ruwa bakin ta tayi saurin bude Ido,wayam taga babu kowa a gun da matar ta zauna Nan Tani ta taqarqare ta kwarma ihu daya fargar da 'yan gidan nasu gaba daya suka dungumo sukayo dakin da suka ji ihun ya fito kusan kowa toshe hancinsa yai Yana duban Tani da kukan ma ta kasa sai qoqarin tashi take Amma ta kasa miqewa gwaggo ta matsu daf da ita.


Tani me zan gani haka.


Gwaggo Duduwa...........kafin tani ta qarasa gaba daya yayun tani da qannanta an nemi kowa agun an rasa dayawansu ma gidan suka bari daga gwaggo sai tani sai malam Qasimu a gidan su kansu sun kasa daga Tani ta miqe bare ita da take ji ajikinta,ruwa gwaggo ta dako botiki biyu ta riqa zubawa Tani ajiki kashin datayi yana biyo ruwan daya ke zawo ne ga amai da Tani ta dinga sheqawa kamar zatayi sallama da duniya a ranar Tani taji abinda Bata ta6a jiba har su gwaggo da sukayi aikin da fargaba fall cikin ransu Dan dai da da ne Amma da guduwa Suma zasuyi...




★★★★



     Washe gari babu wanda yasan Duduwa ta dawo gari ban da Inna da Kuma Tani dake kwance ba lfy, jama'a kowa ya shiga safgarsa har gidan mai gari a ranar duk ya zagaya ya duba 'yan tawagarsa da suka sami raunuka irinsu mai unguwa da mlm jatau wa'yanda basu samu ba Kuma aka hallara a fada Ana tattauna yanda Duduwa ta wargaza kowa a wajan,Ana cikin hira kulu ta aiko da fate fatan tsaki yasha yakuwa da attaruhu aka baje a faffadar dadduma kowa yasaka hannu yana kaiwa bakin salati Ana zuba surutu da dariya kwatsam Duduwar ka ta danno kai bakinta yasha KANTA KILE,wato jan janbaki girar Tasha zanan kwali da digo a saman goshinta da hancin kwaliya dai sosai ta shawo tazo ta zauna daga chan gefen da mai gari yake a zaune yayi mutuwar tsaye.


""Mai gari Ina wuni.


"Aa ni ya kamata na gaida ki Duduwa Inna yinni,mai gari ya furta Yana mai durqusowa qasan daddumar gaba daya Duduwa ta amsa cikin salon soyayya da fari tace.


Qalau qalau nake ya jama'a kuma.


Gasu nan suna zaune mai gari ya dubesu,ku bazaku gaida ta bane.


Yaranki shi dade Ina kwana... Duduwa ta dubi su.


Qalau qalau,yanaga kun Dena Shan fate fatan to Idan kun qoshi akwai masu ci,"Qawaye ku kwashi rabanku,cikin abinda Bai fi qiftawar ido da budewa ba aka nemi fate fatan aka rasa ba mai gari ba 'yan tawagar ma gaba daya  take qafarsu sukai sai gudu Duduwa tabi mai gari cikin gidan da gudu Yana gudu Yana kiran"""

     """""""...........😜😜


_*By*_

_*Mâmâñ Dr @ff@ñ*_

No comments