JAMI'IN DAN SANDA 14
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_14
.................har k'arfe biyu bai dawoba ,gaba d'aya Momma tashiga damuwa gashi sai kiran wayarshi takeyi amma a kashe ,tunani takeyi to mi ya tsayar dashi har wannan lokacin bayan yace mata bazai jima ba ,sannan ga al'adanshi ma baya fita ko ina in weekend ne wuni yakeyi a gida idan kuwa har wani uzuri ya fitar dashi tofa bazai jima ba zai dawo, Tunda ya fita daga gidan bai zame a ko'ina ba sai gidansu Ibrahim , yana zuwa ko cikin gidan baishigaba ya wuce dakin Ibrahim ciki ciki yayi sallama ya shiga dakin,
Ibrahim na zaune Yana aiki a laptop dinshi yaji sallamar abokin nashi , kamun ma yayi wata magana har Hisham ya haye kan katifarshi yayi ruf da ciki batare da ya ko kalli inda Ibrahim yake ba ,
Ganin hakan yasa Ibrahim ya kyaleshi don yasan ko yayi mashi magana bazai kullashi ba juyawa yayi yacigaba da aikinshi ,
Yana nan kwance tsawon wani lokaci kamun bacci 'barawo yayi awon gaba dashi, fiye da awa biyu yana bacci kamun ya tashi a firgice yana nanata kalmar innalillahi wa inna ilaihin raji'un, cikin kankanin lokaci ya hada wani uban zufa, sai fama sauke ajiyar zuciya yake , duk sakamakon mummunan mafarkin da yayi akan Abbansa, mafarkin yayi Abbanshi na cikin wani surkullen daji mai matukar ban tsoro sai faman gudu yakeyi kamar ba gobe yayinda wasu mutane suke biye dashi da muggan makamai suna neman su kasheshi , shikuwa Abba banda gudu da kiran sunan Hisham ba abunda yakeyi har yakai ga ya k'ure hanyar ba sauran inda zai gadu ganin hakan yasa ya runtse idonshi yafara maimaita kalmar shahada , yayinda mutanen suka tsaya akanshi sai faman babbaka dariya sukeyi wanda dariyarsu ke amsa kuwa acikin dajin , daya daga cikinsu ne ya daga takobinshi ya sarewa Abba kai wanda hakan yayi daidai da k'arasowar Hisham a wajan , wani irin ihu yayi kamun yayin kan mutanen nan amma kamun yak'arasa sun 'bace 'bat babu su babu alamarsu , haka ya karasa wajan Abba aguje saidai kamun ya k'arasa ne ya farka a razane,
"Lafiya dai Hisham "? Cewar Ibrahim da shigowar shi kenan ya fito daga cikin gida,
Girgiza kai kawai Hisham yayi don yama kasa magana gaba daya jikinshi da harshen shi sunyi mashi nauyi ga wani bugu da zuciyarshi keyi , a hankali ya mike tsaye ya sanya takalminshi batare da yacewa Ibrahim komai ba yakama hanyar fita daga dakin,
Ganin hakan yasa Ibrahim ajiye abincin da ya karbo masu wajan mamanshi ,janyo kofar dakin yayi ya rufe da sauri yabi baya Hisham don sam bai gamsu da yanayin da yagani a tattare da abokin nashi ba , ƙarara yake hango tsananin tashin hankali a cikin kwayar idonsa,
Jiki a sanyaye yayi sallama akofar falon kamun ma Momma ta amsa mashi ya d'age labulen ya shiga,
Zaune take akan kujera ta buga uban tagumi ,gaba daya jin yanayinta takeyi ba dadi saidai tarasa abinda yake damunta , shiyasa ta alamk'anta hakan da rashin dawowar mijin nata,
Zama yayi ya gaisheta kamun yace " Momma Abba fa"?
"Abbanka ya fita tun d'azu tun bayan fitarka amma har yanzu bai dawoba sannan nayita kiran wayarshi amma bata shiga ," tafad'a cikin matukar damuwa ,
Dum dum dum gabanshi yayi wani irin bugu da karfi , amma tuni ya daidaita nutsuwarshi ya zaro wayarshi yafara kiran Abban , shima dai bata shiga ba ,suna haka Ibrahim yayi sallama ya shigo , bayan ya gaida Momma ne ya nemi waje ya zauna , ganin damuwa ƙarara akan fuskokinsu ne yasa ya dubi Momma yace
"Momma lafiya dai naga kamar kuna cikin damuwa?"
Murmushin karfin hali tayi tace ba komai Ibrahim kawai muna jiran Abbanku ne ya fita tun d'azu amma har yanzu baidawoba , "
"Ayya Momma kila wani abun ne ya tsareshi amma insha Allah zai dawo bada jimawa ba "
"To Allah yasa , ku tashi kuje kuyi sallah sai kuzo ga abinci can kuci kamun yazo",
"To Momma" cewar Ibrahim,
Shikam gogan ko bakin magana baisamu ba don sosai ya tsorata da mafarkin da yayi,
A hankali ya furta " amma Momma Ina yace maki zaije ne?"
"Wallahi bai gayamun ba yadai ce mun zasu fita ne shida inspector Haruna"
Jinjina kanshi kawai yayi sannan ya tashi ya koma dakinshi , alwala yayi yayi Sallah shida Ibrahim sannan suka koma falon Momma alokacin itama ta idar da salla kenan. Zamansu kenan sukaji ana buga get din gidan
******************
Acan 'bangaren su Abba kuwa lokacin da abun ya faru akan idon wasu bayin Allah su ukku aikuwa a firgice suka rafka salati tareda juyawa aguje suka nufi motar da Abba ke ciki , zuwa lokacin kuwa tuni mutanen dake wucewa sun fara tsayawa kamun kace mi wajan yacika da jama'a haka aka taru da kyar aka 'ban'baro Abba daga karkashin motar , gaba daya fuskarshi tayi dameji ga kafafuwanshi da hannayenshi duk sun karairaye jini kuwa yace ina bakayi bani waje tuni wajan ya jike da jini , ahakan kuwa cikin ikon Allah yana numfashi saidai in yaja numfashi sai yayi kusan minti biyu kamun numfashin ya dawo , gaba daya mutanen dake wajan suncika da tausayinshi masu raguwar zuciyar tuni sun fara kuka , ganin har lokacin yana numfashi yasa wani saurayi ciccibarshi ya sanya mota suka nufi hospital mafi kusa dasu ,
Sai bayan tafiyarsu ne sannan wasu suka lura da inspector Haruna yashe a kasa cikin halin suma shima nan suka kwasheshi sukabi bayansu
Suna zuwa basuyi wata wata ba suka karbeshi ganin kakin 'yan sanda ajikinshi , emergency aka nufa dashi ,likitoci biyar ne akanshi suna faman ceton rayuwarsa , duk da kuwa su kansu sunsan ba lallai ne ya rayu ba ganin irin halin da yake ciki ,
Haka suka share sama da 30mnt kamun Allah yayi ikonsa , Allahu Akbar Allah mai yin yadda yaso alokacin da yaso duk da Abba yana cikin mawuyacin hali kuma baisan inda kansa yake ba amma Allah yabashi ikon yin kalmar shahada yayin fitar rayuwarsa wanda su kansu likitocin sunyi mamakin jin magana a bakinshi, bayan sun cire mashi kowace na'ura da suka sa mashi ne sukaja farin kyalle suka rufeshi, sannan suka fara fitowa dai bayan dai,
Nan suka sanar da mutanen da suka kawo shi Allah yamashi rasuwa ,
Duk da basu sanshiba amma sunji mutuwarshi sosai wannan saurayin kuwa harda hawayenshi , ganin kayan yan sanda ne ajikin Abba yasa ya fito yanufi babbar HQ ta yan sanda , nan ya zayyanemasu duk abunda ke faruwa , haka aka hadashi da wasu yan sanda suka nufi asibitin,
Lokacin da sukayi arba da gawar ba karamin firgita sukayi ba ganin fuskar inspector Abdulrahaman nan suka kira HQ suka fadin abinda yake faruwa , ai kamun kace mi asibitin yacika da jami'an yan sanda kota ina , masu jin dadi naji masu jin ciyon tashin nagartaccen Jami'i nayi , a haka aka tura wasu daga cikin yan sandan akan suje su sanar a gidansa , shine fa suka zo suna buga get din gidan,
Jiki a sanyaye Ibrahim yaje ya bude get din, ganin yan sanda abakin k'ofar ba karamin kayar mashi da gaba yayi ba wanda baisan dalili ba,
Gaisawa sukayi kamun suka ce mashi suna sallama da matar gidan ne ,
Jin haka yak'ara hautsina ma Ibrahim hanji , amma haka nan ya daure yace "to shikenan kushigo daga nan zanje in gayamata , " suka amsa da "to"
"Momma Wai wasune keson magana dake" ............. Kamun yak'ara magana Hisham yayi zubur yace " su waye"?
"Bansansu ba amma dai nagansu da kayan yan sanda" cewar Ibrahim
Ai kamun ma su farga har Hisham yakai waje inda Momma da Ibrahim suka rufa mashi baya,
Daga Momma har Hisham saida gabansu yayi mugun faduwa lokacin da sukayi arba da wadan nan yan sandan , cikin sark'ewar murya Hisham yafara jefo masu tambayoyi batareda ya tsaya gaisawa dasu ba,
"Lafiya mi yake faruwa mi kukazoyi nan ina Abbana yake yanadai lafiya ko" ?? Haka yayita jera masu tambayoyi ,
D'aya daga cikinsu ne yayi karfin halin cewa "ka kwantar da hankalinka dama munzo tafiya daku ne saboda sir yasamu had'ari a hanyarsa ta zuwa gwangulori yanzu haka yana hospital shiyasa mukazo tafiya daku,
Wani irin sarawa kan Hisham yayi da k'arfi kamar an buga mashi guduma da sauri ya sanya duka hannayenshi ya tallabe kanshi da yakeji kamar ba'a jikinshi yake ba sai maganar wanna mutumin kemasa amsa kuwwa a kunne tabbas wani mummunan abu yafaru da Abbanshi koda ganin yadda mutumin ke magana yana sunne kai ,kamun kace mi juwa tafara daukarshi taga-taga yayi zai fad'i da sauri Ibrahim ya rikeshi , basu ankaraba sai jin faduwar Momma sukayi timmm ak'asa ta fadi babu numfashi,
Da sauri Ibrahim ya sakeshi ya nufi Momma yana kwala kiran sunanta a firgice , Hisham kam tuni yayi mutuwar tsaye kwakwalwar shi ta tsaya cak yakasa tuna komai a hankali idonshi yafara rufewa sai gashi shima a kasa a some..............✍🏼
*Littafina yakoma na kud'i 200 Kuma kowane lokaci zan iya dakatar da post dinshi har sai a paid grp Wanda rashin comment ne ya janyo hakan , kuma ko yanzu kuka canza ton zan canza Nima nabarshi a free dinshi kamar yadda nayi niya daga farko*😎😎
*Sannan na rokeku ku taimaka ku tayani share*👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼
No comments