Breaking News

DUDUWA 5

          _5_


_*Dubun godiya tare da miqa gaisuwar ban girma ga Fan's na DUDUWA, musamman musu comments da masu bina fc,na gode da nuna soyayya da kulawa a garene,ina fatan Alkhairi da farin ciki ya tabbata agarku da masoya baki daya, Duduwa na miqo gwagwabar gaisuwa🤣*_


 """"Mai gari na shiga gida, dakinsa ya nufa kai tsaye kulu na ciki tana aunar dawa zata bayar akai mata surfe da nuqa.

Garam garam taji an saka sakatar sama da ta qasa,da sauri ta matso Inda mai gari yake kokawa da qofa daga shi sai Dan kamfen daya saura ajikinsa,ta dubeshi ta qara zuba Masa Ido tace.""


Anya kuwa Mai Gari ne?.


Wallahi na ne nan kulu ko baki ganeni bane,jikinsa sai makyar,kyata yake Yana qara danne qofar da qarfi duk da yasaka sakatar gaba daya.

   

Ina fa zan waye ka haka ai sai da kayi maganar nan tukuna na shaida ka, lfy ina tufafin naka yake??.......kanya tanka suka jiyo garammmm da ihu daga waje ai kan kace me mai gari ya tsalake gadon qarfan sa ta baya ya shige qasan gadon dayake achan gefa guda yake sai Sallati yake kulu na dubansa da mamaki fal aranta,jin qara da doke doke na qaruwa kulu tayi bakin qofar zata bude taga Wai meyake faruwa ne mai gari ya dan leqo dakansa sama Jin anta6a qofar da sauri ya furta.


Kinci kutumar ubanki na rantse da Allah kina budewa Ina zabga miki Allah ya isa malala gashin tunkiya daga baya kuma kiyi gidan gyatuminki,turus kulu tayi tasake zubawa mai gari Ido tana kallon ikon Allah daga waje kuma sai dukan qofa da garu ake ana ihu da koke koke kamar gidan mutuwa.        



  "Chan na hango me unguwa a baje shi ba azaune ba ba kuma a akwance ba sai farfadiya yake da Ido daya abude daya amanne dayaga Duduwa ta sa6i qafafuwan wani zatayi wurgi dashi sai dai Kaji me unguwa na karatun Dan akuya.........""


""Meee,meee,meee.


Da qarfi Bulalar sa na hannu ariqe,daga gefansa magatakarda ne manne a jikin garun mai gari kukan ma ya kasayi gashi babu halin miqewa ya gudu Duduwa na tsaye tana Zara ido da fusge fusge kamar sabuwar kamu Inna na gefe tana tofa mata Addu'o'in dasuka fado mata a Baki ta rasa yanda zatayi da Duduwa su koma gida.


   Duk yawan mutanan da sukazo ganin kwakkwaf gasu Nan baje a qasa cikin kowa ya duru ruwa wasu har zawo sukeyi Dan tsoro sha'anin Duduwa Kam ba qarami bane kamar'yar tsana take daukar mutum da zaran ya miqe tsayetai wargi dashi hakan yasa kowa ya koma yai lamo aqasa banda me gari daya sha da qyar Dan kansa tayi gadan gadan tayi tuntube ta fada kan mlm jatau da atake ya karye cinya

  Shi ko me unguwa daya zuba mata bulalar wani jifa tayi dashi yai sama ya dawo ya baje a duqe yana kukan Akuya.

     Cikin Ikon Allah Duduwa ta dawo hankalin ta lokaci daya kamar Bata aikata komai ba sim sim Inna ta kama hannunta sukayi hanyar gidan su,da zuwa Inna ta shiga hada kayansu cikin sauri Dan barin qauyen gaba daya kar jama'a su far musu.



............Mudi ne ya Dan qyalla ido Dan ganin a ina Duduwa take,wayam yaga babu ita ya qarasa bude idan nasa gaba daya haba qafa me naci ban Baki ba a sittin ya take har da tuntsurawa ya miqe yana.


""" Kowa ya fece Duduwa ta wuce............


Innanillahi,wannan na taka wannan na doke wanchan gudu kamar wa'yanda suka ci qafar kare,masu rauni kuwa jan gindi suka fara suna kuka kowa dai so yake ya tsere kar Duduwa ta dawo a ranar garin KANWA,yai tsit kamar babu dan adam idan kaga mutum a waje to fa da gudu ake fitowa adawo da gudu acewar wasu Duduwa ba iya gudun zatayi ba tunda te6a tayi mata yawa.



--------------Ki tashi mu fuce daga garin nan sahun mu alika fa Duduwa kar jama'a su far Mana.


Ni wallahi babu inda zani na bar mahaifata ke dai idan kin gaji kiyi tafiyarki tunda ni ban hanaki ba.


   Kin san ko abinda kika aikata.


Qwarai kuwa Inna tafiya ce nace banyi ko ana dole ne aa,kamanin Duduwa suka fara chanjawa.


Aa ban miki dole ba Kisha zamanki jikar Inna Amma ki tausaya mun kar jama'a su zo su nakasa mun ke kinji jikalena.


Ko sun zo babu wanda ya isa yamiki komai nifa Inna da kika gani aradu me gari zan aura............


Ruwa Inna ta kai bakinta jin furucin na Duduwa yasa ta dawo dashi gaba daya.


Mai gari kuma Duduwa.


Eh mana Inna yasin shi nake so,dama bakin ce ni matar manya bace.


Ummmm ehhhhhh fa Amma da kamar wuya.


Ni dai mai gari nake so kuma shi zan aura a duniyar qawayena.


Duduwa ina kuma kika samu qawaye.


Ta6 ai Inna duk sanda kika ga bana nan ina chan duniyar su gsky suna da kayan kwaliya da kayan ciye ciye da yawa Inna har Sarauniya ce dasu mu kinga bamu da ita gashi tashi suke da fuka fuki sama kamar wasu tsuntsaye.



Ummmm tooooo yanzu dai ba inda zakiji ko?


Wlhy sunce babu inda zani Inna kuma yasin sunce duk Wanda yata6o Ni sai sunci durun uwatar,yanzu haka suna gidan su tani suna matsata dan ma batayi mun dariya a bakin rijiya ba.


Na am, to gani Nan zuwa qawaye.,ita kadai take surutun ta ta muskuta ta miqe ta6ar ta6ar ta fuce daga gidan Inna ta rushe da kuka tana.""


Na shiga uku Ni Suwaibatu wallahi tallahi Ni nasan ba banza ba abinda Duduwa takeyi wayyo Allah TANI........."Ya ke Suwaibatu kiyi hattara da kalamanka ko ke dakike jaririyar Dudu baki wuce hukunci dai dai da abinda kika aikata ba........


Quttttt,wani abu yatafi cikin Inna ta runtuma daki da gudu ta banko qofa tana tofa KURSIYU.........





_*By*_

_*Mâmâñ Dr @ff@n*_

No comments