Breaking News

YAR AMANA 15-16

 *NUSUIBA*

         *'YAR AMANA☘️☘️*

*page 15-16*

______ Acikin kurkuku kuwa tsorone ya cika 'YAR AMANA saboda duhu da baqin gurin can jikin gini ta samu ta raku'be tamkar zata shige cikin ginin, rufe idanuwanta tayi gam tana karanta duk wata addu'a da ta iya arayuwata, a haka kuwa barci 'barawo ya fara gaba da ita.


Shi kuwa ABUDULJABBAR  can cikin dare ya farko ya bud'e idonsa ji yayi kansa ya masa nauyi ga uban duhu da zafi dukka ga sauro, gigicewa ABUDULJABBAR yayi domin ba yason sauro da kuma duhu,  dan haka ya fara lalube agurin ji yayi ya ta'ba mutum, lalubawa ya qara yi ai kuwa hanunsa ya sauqa kan laulausan Abu, ita kuwa 'YAR AMANA da bacci ya fara gaba da ita jin anta'ba qirjinta kawai sai tafarka tare da riqe hanun mutum caraf, cikin sanyin muryarta tace " hanun wa na kama"?

Shi kuwa ABUDULJABBAR daskarewa yayi agurin sbd dajin dadd'ar miryarta tini ya saddaqar da tabas shi kam gamo yayi da aljana wanda har ta d'auke shi ta kawoshi gidan ta me duhu, shima cikin nitsatsiyar miyarsa yace " waye ke mutum ce ko aljanna"? 

'YAR AMANA kuwa cikin tsoro tace " nice wacce ka taimaka daga hanun 'yan iskan rugarnan" 

"To meya kawoni nan gurin mai duhu"

Cikin kuka 'YAR AMANA ta zaiyana mar duk abun da ke faruwa, shi kuwa ABUDULJABBAR tinani yatafi can kuma ya tuno wayarsa na jikinsa dan haka da sauri ya miqe ya shiga laluba aljihun wandonsa ya ciro wayartasa, kunnata yayi domin tama mutu, tini hasken wayar ya mamaye gurin, itama 'YAR AMANA da taga kamar alamun haske sai tad'ago kai nan suka had'a ido ita da ABUDULJABBAR da yake qoqarin haska fuskarta, shi kuwa ABUDULJABBAR tsateta da idanu yayi fuskarsa ba alamun wasa ko kad'an yace " ke wacece ke kuma ma yakaiki hanun wa 'yanan mazan har sukeso sulalataki?"

'YAR AMANA kuwa sosai jikinta yake tsuma dan kuwa yanzu ta qara tabbatarwa gamo da aljani tayi sbd tsantsar kyawunsa da tagani acikin haske, shi ko ABUDULJABBAR cewa "yayi dake fa nake baby"

Cikin kuka 'YAR AMANA tabashi labarin rayuwar ta, da kuma irin al'adarsu ta 'yan mata, basa tallar nono sai de matan aure ko bazawara,  sosai lamarin ya d'aurewa ABUDULJABBAR kai sanan yace haka yana nufin Gwaggo da Baffa basu bane iyayenki kenan"?

"A'a Baffa na shine mahaifina amma Gwaggo ba ita bace ta haifeni sbd tana min gorin bani da asali, kuma ma mutanen rugarmu suma sunsan Gwaggo ba ita bace ta haifeni". 

"To idan haka ne me ya sa shi Baffa shima ya fara nuna miki halaiya irin ta Gwaggo?"

"Eh to qila yabi zugar Gwaggo ne, amma wata rana naji Gwaggo da qawarta Asabe suna cewa wai bokansu ya iya aiki tinda gashi yanzu duk abun da tace shi Baffa na keyi, wai har ma da rashin sona da yadena duk sunji dad'i" shiru ABUDULJABBAR yayi sanan yace " to wani hukunci kenan za'ama na gobe da safe sbd sharin da aka mana?"

"Ni ma bansaniba amma me zai hana ka 'bace 'bat katafi abunka can duniyarku tinda dama Baffana yace min ku aljanu 'bacewa kukeyi"

Shi kuwa ABUDULJABBAR waro ido yayi ya kalleta sosai yace "aljannu kuma ni d'in?"

"Eh mana ko kai ba aljanni bane?"

"A'a sai de in kece aljana amma ni mutum ne bil adama"

"To ai nima mutum ce, kawai de naga kaid'in kyawunka yayi yawa shi yasa nazata ko aljani ne kai"

ABUDULJABBAR kuwa ji yayi ya gaji domin shi sam baima fiye surutu ba, amma Gashi yanzu ya biyewa yarinya qarama yana magana, 

Cemata yayi "Shikenan yanzu ki kwanta sai da safe zansan abunyi"

"Nide gaskiya bana son acutar da kai domin kuwa ka taimakeni da badan kaiba qila yanzu da tsintsaye suncinye nama na"

ABUDULJABBAR kuwa fitilar wayarsa ya bari akunne sanan yace jacket d'in dake saman rigarsa ya tsinfad'a agurin sanan yace " to kwanta akan wanan abun kiyi bacci sai da safe" har zata musa amma ya tsareta da ido dan haka ba musu tayi bismillah ta kwanta akan jacket wanda sai qamshi mai dad'i takeyi.


Shima matsawa gefe kad'an yayi sanan ya kwanta acikin qasar dake gurin ya juya mata baya kamar yanda itama taju ya  abunta, yabar musu fitilar wayar akunne sbd yaga yarinyar duk atsorace take, 

Can kuma juyowa yayi kawai sai yaga itama ta juyo ashe tana kallon bayan sa,  da sauri tajuya bayan ta tana rufe idonta alamun kunya shi ko murmushi yayi yajuya abunsa tare da rufe idonsa.

Can cikin bacci yaji hayaniyar mutane akan sa bud'e ido yayi yaga matasa akan sa sanan ga 'YAR AMANA atsaye agefe,  tashi yayi ya d'au jacket d'insa tare da wayarsa sanan yace " lafiya?" Nan matasan suka fara cewa " shege kad'o zaka ci uwariyonka maza muje hard'o na son ganinku 'yan iskan banza"

Ba musu ABUDULJABBAR yabisu suka fito inda sukayo fadar hard'o, gurin da kowa da kowa ya taru yara da manya, Hard'o ne yayi gyara murya sanan yace " kowa de ya sani agarina ba amana iskanci amma wanan yarinya 'YAR AMANA ta juma tana abubuwa masu yawa amma muka qaleta sbd itad'in AMANA ce ahanunmu ashe har kad'd'o take shigo mana dashi rugarmu ba wanda yasani har sai jiya asirinsu ya tonu, sbd haka za'a musu hukunci dai dai da laifinsu sanan mokori 'YAR AMANA agarinan"

Nan kowa yace " tabbas hukuncin yayi domin kuwa inba haka ba 'YAR AMANA zata 'bata mana tarbiyar yaranmu"

Nan hard'o yace "za ayi musu bulali sanan akoresu agarin akuma sa yara suna jifarsu har su fita arugar"

Shi kuwa ABUDULJABBAR ko ajikinsa sai neman Number wayar wani a bikinsa d.p.o yakeyi amma sam wayar taqi tafiya sbd ba service agurin, ita ko 'YAR AMANA inbanda kuka ba abunda takeyi harda fitsari awando sbd tsoro sai dudubawa takeyi ko zata ga Baffanta amma bata ganshi ba.

Shiko ABUDULJABBAR cikin daga murya yace " ban yarda da wanan hukuncin ba domin kuwa ni ba mazinaci bane mezan samu ajikin wanan yarinyar, asalima taimakonta nayi daga hanun wasu shashasun samarin 'ya'yanku da sukeso su lalatata, shine sukazo suka qulla wanan qaryar"


"Cikin tsawa hard'o yace " kai kad'do ahir d'inka domin mu bamu da yara malalata anya ma wanan kad'd'one kuwa ba ya hudu bane"?

"Shima ABUDULJABBAR cikin tsawa yace " kai tsoho karkaga ina cikin rugarku kanemi kaci zarafina yanzu nan ina iya sawa aturomin motar 'yan sanda duk akaiku kurkukun birni wanda yafi naka horo mai tsanani"

Samarin garinne suka yiwa ABUDULJABBAR ca aka suna cewa kai " Nasara qarya kake mu munfi qarfin jami'an tsaro, domin kuwa ba mayin aiki dasu arugarnan sbd ba gaskiya garesu ba, amma yau zakasan hukunci irin ta rigarmu"

"Ni S.S ABUDULJABBAR ASHIRU MAINA tabbas zan nuna muku ni wanene matsalar ma d'aya baku da Service amma tabbas da yanzu an gama kwasheku an kaiku kurkukun birnin kaduna"

Mallamin su 'YAR AMANA nane ya matso kusa da hard'o yama sa rad'a sanan hard'o yace " hukuncin ku biyu ne koma kai wanene kai tabbas bai damemuba amma acikin hukuncin ka dolene kaza'bi d'aya ko ayimuku bulali akoreku tare da duwatsu, ko ka auri yarinyar katafi da ita munyafeta har abada" 

ABUDULJABBAR kuwa cewa yayi "duk cikin hukuncin ku ba wanda yayi min kuma ba wanda zanbi nifa baqone wucewa nazo yi 'yan fashi suka tareni............ Nan yabasu labarin komai da yafaru, amma suka ce qaryane domin su ayankinsu ba afashi, 

Sbd haka dolene ya za'bi hukunci d'aya, haka de su kai tayi da ABUDULJABBAR amma yaqi yarda, sai da yaga de tabbas da gaske sukeyi har antanado manyan bulali 'YAR AMANA Kuwa sai kuka take tayi jikinta na ta tsuma, sanan ya tuno labarin da yarinyar tabashi na rayuwarta,  dan haka kawai yaji yana tausayin yarinyar ko ba komai zai iya taimakonta yasamu lada masu yawa, dan haka yace " Na amince zan aureta amma gaskiya bani da kud'i ajikina wanda zanbada amatsayin sadakinta domin kuwa komai nawa na bari amotata" nanfa wani saurayi da yake zuwa birni acikin rugar yace " to ni ka fansarmin da Wayar hanunka inyaso sai na baka kud'i kabiya sadakinka dashi" bayanda ABUDULJABBAR ya iya dan haka ya amince, nan saurayin yaje ya kawo kud'i dubu goma yabawa ABUDULJABBAR, ya bashi waya bayan ya cire layinsa dake cikin wayar kuma yacire komai da yake kanta, ABUDULJABBAR kuwa hard'o ne yasa aka kar 'bo kud'in daga hanunsa aka miqawa 'YAR AMANA A matsayin sadakinta, shiko ABUDULJABBAR baqin ciki kamar yayi yaya wai shi za'a aurawa wanan ta tsitsiyar yarinyar, da ya tabbata ya kusa haifarta sanan ma anrabashi da wayarsa da yafi so acikin wayoyinsa wanda ko miliyan daya bazai iya siyar da ita ba bare dubu 10, amma de yasan ba yanda ya iya domin ba shida wata manufa, haka kuwa aka daura auren ABUDULJABBAR da 'YAR AMANA inda akatambayi Baffa sunan 'YAR AMANA nagaskiya sai yace NUSAIBA, bayan angama d'aurin aure hard'o yace 'YAR AMANA da Nasara subarmar qasarsa kar suqara yin koda rabin sa'a ne acikin ta, haka Baffa yana kuka da baisan na miye ba yazo gaban 'YAR AMANA ya miqa mata wani tsohon buhu yace " gashi NUSAIBA wanan kayanki ne aciki, ki bari sai kin isa inda zaki sanan ki bud'e, domin mahaifiyar kine tabani kafin tarasu dan kuwa Gwaggo ba ita bace asalin mahaifiyar kiba" 'YAR AMANA tana kuka ta kar'ba sanan tace " dama Baffa sunana NUSUIBA?"

"Eh yace mata tare da barin gurin sanan tace " to Baffa ina 'yan uwan mahaifiyata suke? Amma shiko baima jiba, gashi hard'o yasa akoresu dan haka ABUDULJABBAR yayi gaba itama tabi bayan sa tana tafiya tana waige, ahaka har  aka fitar dasu daga rugar sanan matasan garin suka koma, tafiya mai nisa sosai sukayi sanan suka fita titi, itakam ma 'YAR AMANA tinda take bata ta'ba zuwa bakin titinba domin kuwa sai masu zuwa birni suke biyowa ta wajen, sosai tagaji lilis ga yunwa da qishi dake damunta, shiko ABUDULJABBAR atunaninsa zai ga motarsa awajen amma abun mamaki shine ba motar ga kuma shatin tayoyinta alamun antafi da ita, dan haka suka ci gaba da tafiyar qafa, hatta shima ya gaji liqis dan bai saba ba, itakam 'YAR AMANA fad'uwa ma tayi agurin, har ABUDULJABBAR yayi nisa sanan ya juyo yaganta jefe aqasa kamar yayi tafiyarsa abunsa sai me kuma ya tuna oho yadawo baya ya tsaya akanta yace " ke wlh ki tashi ko nayi tafiya ta nide kan taimakonki bai zamemin alkairiba yanzu me zanje infadawa iyayena da matata?"

Itako 'YAR AMANA tana jinsa tayi banza da shi, azuciyarta kuwa cewa takeyi au ashema yana da mata ko itama aljanarce oho? Wata tsawa ABUDULJABBAR ya mata dan haka ba shiri tamiqe Suka ci gaba da dingisawa domin gwanda itama tasaba dabin rugage sai de yunwa dake d'a wainiya da ita. Gashi kuma ABUDULJABBAR babban ta kaicinsa yaga ma motoci ko wullawa ba sayi atitin shiru kakeji sai da sukayi nisa sanan motoci suka fara wucewa d'ad'd'aya kuma ko ya tsayar  dasu basa tsayuwa.

Haka de sukaci gaba da tafiya cikin qunci. Ga zafin rana.



Shi ko Baffa da zaza'bi jikinsa ya koma gida, Gwaggo naganinsa tataso tana  dariya tana cewa " kai naji dad'i munrabu da mugun iri domin kuwa naji labarin komai da yafaru, qilama mijinata yaje yasiyar da ita, tinda tace ta iya bin maza"

Shiko Baffa wani mugun kallo yayi mata yayi shigewarsa d'aki abunsa ya lulu'ba da bargo domin sanyi yakeji

Gwaggo ko sai tiqa rawa takeyi atsakar gidan domin kuwa burinta ya cika na rabuwa da 'YAR AMANA dan kuwa inda abunda ta tsana to shine ta riqe d'an wani ba nata ba....





Hhmm muje zuwa dan yanzu aka fara wasan





Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups please




*ASSTAGAFIRILLAH, WA ATUBU ILAIKA*🤲

No comments