Breaking News

DUDUWA 2

🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_

           _2_

Bakin rijiyar Duduwa ta nufa cikin rashin sa'a Bata iske kowa a wajan ba sai guga a gefe hakan yaqar tunzura ta ta nuf gidansu ABULIYA Kai tsaye Dan shi ne kusa da rijiyar,gadan² gadan ta fada gidan da ta6aryar ta a hannu malam baqo na zaune Yana tura lomar tuwon da ya kwaso har wani lumshe Ido yake dan dadi Yana zuba surutun da ba atambayeshi ba Uwani na daka tana bashi amsa har da Yar tsokanar shi Santi ya abeshi,jin saukar duka aqeyarsa yai lomar da Bai ka bakinsa ba kenan ya kwar ma uban ihu Yana...


"Uwani gini,gini ya rufto mini a kai na ya rufto mini Uwaniiiii......


A sittin Uwani ta fito daga dakin tana Sallati Dan kai wa malam baqo dauki,tana fitowa Duduwa na sauke ta6aryar a kwi6inta shi malam baqo yasamu damar magana ita kuwa Uwani ihun ma kasawa tayi sai wani fari da Ido take tana gurnani kamar Dan Akuya Dame Allah ya hada Duduwa ta shiga jibgawa Uwani ta6arya da malam baqo dake kwance cikin tuwo da miya baje baje Yana runtuma ihu da majina sha6e sha6e afuska.


Tuni maqota suka cika bakin katangar gidan suna leqe ganin wace ke surfe da daka dasu malam baqo yasa duk Wanda ya shigo burki yake da baya sai dai kaga Ido na leqe Amma anrasa Wanda zai kawo wa su Uwani taimakon gaggawa ya kar6e su daga hanun Duduwa har tayi musu lilis ta koma Kan botukai da randunan gidan ta fashe su gaba daya har kwanuka Bata barsu ba a haka akaje aka sanarwa da Mai gari abinda ke wakana.

 Gun gun tawagar Mai gari ce gaba daya suka rufo Masa baya zuwa gidan malam baqo,da qyar da sidin goshi aka lalla6a Duduwa tabar Rotsa kayan gidan da sharadin sai an biya ta botikinta sak irin wanda ya fashe abakin rijiya mai gari yace yaji ya gani tabiyoshi FADA ta amsa.

    "Duduwa ta amsa da, to suka fito jama'a kowa yafara kokawar rufe fuskarsa Dan kar Duduwa ta ganoshi kashinsa ya bushe data fito din kuwa sai raba Ido take tana kalle kalle har suka dauki hanyar FADA,Mai gari yace awuce da Uwani da malam baqo wajan liman ya dubasu ko sun Sami karaya da targade.🤣🤣



""Tun a Tasha ABULIYA ta samu labarin Danyan hukuncin da DUDUWA tayiwa iyayenta,da gudu ta nufi fadar Mai gari sai rusa kuka take jama'a na Bata haquri wasu na jajanta mata don labari yazaga ko Ina na cikin qauyen Inna ma a hanya aka jefeta da habaici wanda yai mata nuni da Duduwa na fada, Inna ta nufi fadar Mai gari a rude tana runtuma Sallati tini cikin Tani ya Karta Jin labarin da ya dauki garin gaba daya ta kewaya bayi yafi a qirga wani lokacin ma ba zawon ke kai ta ba ita dai ta fada ban dakin kotaji Dan sanyi aranta idan Allah ya kawo Duduwa Bata kanta zata fara ba ta fara takan uban kowa a gidan tunda Ni na 6uya yo Ni nagama banyi dariyar ba,kut su iyayen ABULIYA dariyar sukayi ta qare a kan su naji ance karaya tafi Sittin ajikinsu targadi kuwa yai dari da hamsin Banda gocewar qashi tamanin wayyo Allah Ni Tani wallahi kashina yagama bushewa Ni idan ta jibgeni Yasin ko doruwa bazan ba Ni Tani na shiga uku wayyo baba da iya ta muna cikin tsaka Mai wuya,sai kuka a ciki Ta na toshe Bakin ta Kar ajiyo......





_*By*_

_*Mâmâñ Dr @ff@ñ*_

No comments