Breaking News

DUDUWA 21

~21~

             Baki mai gari ya saki yana kallon yadda kulu ke zabga ihu ita kaɗai a kan gado har dasu majina mai gari ya gaza jure kukan da kulu keyi gaba ɗaya tausayin ta ya kamashi shi bai son yaga mace duk ƙanƙantar ta tana kuka idan baka girmama mace ka tausaya mata ba to wazaka girmama wa a cewar mai garin ya shiga rarrashi da bawa kulu baki duk da abinda tayi masa sam bai hana shi rarrashin taba yana""


    ""Haba uwar gidan mai gari, me yayi zafi haka zaki saka kuka kamar wata ƴar ƙanƙanuwar yarinya shin dawowar ce baki buƙata ko kuma ni ne dana shigo miki ɗaki?


cukin kukan kulu ta kwaɓe baki ta ce"""


Wallahi ina son dawowa jikina ne dukka ke mun ciwo musamman gadon bayana kamar zaya karye....


    ,"Subhanallahi garin yaya kikaji wannan ciwukan a bayan ki kulu wannan dai da gani ba ciwo bane dukka ne, jibi yanda shatin bulala suka kwanta dara-dara a  bayan ki faɗa mun gaskiya uban waye a cikin garin nan kaf ya duke ki yanzu ya gatanki,mai gari ya miƙe a fusace yana jiran abinda kulu zata furta, sake narkar da murya kulu tayi, tayi rau rau da ido ta ce.


""Ni dai kabar maganar nan kawai ka gasa mun dukka jikina ko zan samu saukin abinda nake ji.


,"to to yanzu kuwa da ruwan zafi kike so ko dana sanyi?


Ya za'ayi ka gasan jiki da ruwan sanyi ka ƙaran azabar danake ji kenan.


haba ya ya za'ai na ƙarawa kuluwa ta azaba bacin ni danake nema miki sauki bara na kira ƴar uwarki Duduwa ta taimaka mun mu gasaki gashi me kyawu hauwa kulu ta.


Ni kar kasake ka kira mun wata Duduwa ɗaki,kai kaɗai nake so kayi mun bayan ita tajanyo mini duk masifar dana shiga muguwa a zaluma ai tunda nashigo gidan ban sakata a ƙwayar ido na ba data kwashi kashin ta a hannu wallahi.


To...... yausha kuma hakan ta faru kulu.


ɗazu nan taje har gida ta same ni da tsimagiya har guda goma wallahi gaba ɗaya sai da suka kakkarye a kai na wai dolle sai na dawo gidan ka bayan na amsa mata zan dawo ɗin ta cigaba da jibga ta kamar wace aka aiko.


Ya salam...In dai kuwa haka ne,to Duduwa bata kyauta ba auwo ashe shi yasa tace na kwantar da hankali na zaki dawo gidan da ƙafarki.


to kaji fa yasin kuwa da ƙafafuwa na nashigo kamar yanda ta faɗa maka ni wallahi dama tsoran zama da ita ne yasa nayi tafiya ta gashi a gidan uban nawa ma ban tsira ba sai da ta bi ni,kulu ta sake fashewa da matsanancin kuka,rikicewa mai gari yayi yace""


yi shiru mana kulu zan yiwa tufkar hanci bazata daki banza a barta haka sakayau ba dani take zancen daure ki sauko muje bayin na gaggasa miki jiki kafin ta dawo kinji kuluwa kuluwan mai gari.


Ni bazan iya ɗaga ko ɗan yatsa na ba kazo ka ɗauke ni kawai ka kai ni,mai gari ya matso daf da kulu ya miƙa hannu ba kunya babu tsoron Allah ya sunƙumi kulu zai fito da ita daga ɗakin kenan Duduwa ta faɗo ɗakin kamar an jefota, riƙe ƙugu tayi tana binsu da kallo chan kuma ta fara gyatsina hanci da hurashi kamar zai dare ta ce.


""Kan uban chan ni za'aciwa amana ina duniyar da rai ban mutu ba, na rantse da gemun kaka na yau kulu sai na ci ubanki da gaske na kirɓaki a turmi na haɗa na dake da daddawa da tsidigu idan ance gobe ki kuma bazaki sake ba.......tini kulu ta ƙanƙame mai gari ta saki wani irin gunji mai ban tausayi mai gari ya juya da sauri zai mai da kulu inda ya kwasota Duduwa ta daka masa tsawa ta ce""


""Kar ka kuskura ka mai da ta mai gari ba kai ka kwaso ta ba.


wallahi bani bane cewa tayi na ɗauko ta.


sai kuma ka yayimo ta ko,to duk zaku faɗawa ƴan garin ku.


wallahi amarya ita tace na yayimo ta na kai ta bayi.


iyeeee har bayi ma zaka kwasheta ka kai ta,to ma shin me zakayi mata a cikin bayin?


jiki na rawa mai gari yace.


"Gasa ta tace nayi.


lalalalalala,kace yau akwai shan romo ai ban sani ba ranka shi daɗe da ban tsayar da kai ba,amma duk da haka babu komai ajiye ta a hankali kafin naje na haɗo itacan na hura wutar kasan ni akwai iya gashi har babbaka nake yi bari kulu da ko tsokar kirki babu ajikinna ta...............,kafin mai gari ya dire kulu ƙasa tani kulu ta dire ta tsallaka ta haye chan ƙarshen gadon ta tana.


"la'illaha'illallahu,mai gari kana gani kuwa kana jin abinda take faɗi,,Duduwa bata tsaya bin ta kansu ba ta juya ta kamo ƙauren ɗakin ta janyo ta rufe su ruf da kubar hannun ta data ciro daga jikin tagar tayi madafa kanta tsaye,manyan itace taje ta kwaso a madafa irin wanda ake  safgar biki dasu ta sake ɗauko ƙaton murhu tazo filin tsakar gidan ta kime,kaskon suyar kulu ta ɗauko ƙato na sallar layya shima ta kime taje ta kandami gishiri da farin maggi har da ƴar daddawa da ɗan tsidigunta tazo ta dangwarar a bakin murhun karaf suka haɗa ido da kulu da mai gari a windo sun leko,suna haɗa idon gaba ɗaya sukayi ƙasa Duduwa ta kece da dariya ta miƙe tayi windon tana""""


""Haba saurin meye kukeyi haka,kayan gashin nake tattarowa kafin na ɗora uwar gida kulu banga albasa ba kin san ita ke ƙarawa abinci armashi kiji ko ina ya ɗume da ƙamshi uwa ranar sallah,banda kuka babu abinda kulu keyi shiko mai gari hankalin sa gaba ɗaya ya tashi tsoron sa ɗaya kar tace dashi zata haɗa dan ɗazu a batun ta har jam'u tayi musu,yana cikin zanchan zuci yaji an daki ƙofar ƙauren a razane ya kife ya kwanta yana""


Ya hayyu ya ƙayyumu,ka kawo mana agajin gaggawa.


murmushi Duduwa ta saki ta ce,"""daɗina da kai ranka shi daɗe ɗan banzan tsoro sai kace kai nace zan gasa,ai kai naka na nan zuwa tukunna,yauwa tunda ita uwar gidan ta gaza faɗan inda albasa gidan ƙamshin take to kai maza ka sanar dani inda take kaga gwamma nayi sauri na gama haɗa komai kar yunwa ta illatani,faɗa mun inda take mijin hauwa kulu wa Duduwa.


umm ummm tana tana tana makewayi,au madafa nake nufi aradun Allah....


baki Duduwa ta rike tayi zuru tana duban mai gari da gaba ɗaya ya rasa gaba ya rasa bayan sa sai jeka ka dawo yake yi yana fitsari a jikin wandonsa,ƙala Duduwa bata kuma cewa ba ta juya ta koma madafa,bata jima da shiga ba ta fito da uwar albasa robar Ok guda ta ajiye a gabanta.


     Nan da nan ta shiga haɗa itace da makamashi ta buɗe ledar maggi ta haɗe da gishiri waje guda ta daka daddawa da tsidigunta a tare ta ajiye su a gefe,wuka ta ɗako ta janyo robar ok ɗin ta shiga yanka albasa babu ji babu gani ga albasar da ɗan karan yaji Duduwa na yankawa tana hawaye data ɗauki ɗan lokaci kaɗan sai ta tashi da sauri kamar an tsikare ta,ta leƙa windo tace.


""makewaye ko ranka shi daɗe......wuka na hannun ta na dama.


kulu da mai gari na ƙyalla ido akan wuƙar hannun Duduwa sai dai kaji ɗaki ya ɓarke da salat da kuka kulu sai kiran sunaye take da wanda ta sani dama wanɗan da bata sani ba..............


*Dan Allah muyiwa Annabi (S'A',W),Salati guda goma,Allah ya bamu ladan baki ɗaya*


_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments