JAMI'IN DAN SANDA 30
👨🏻✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻✈️
🅿️_30
..........."innalillahi wa inna ilaihin rajiun, wai Hisham mi yake damunka ne ? Kayi magana mana tun d'azu Ina maka magana Amma ka kasa cewa komai," juyo kanshi yayi ya d'aura akan kafafunta Yana sakin ajiyar zuciya Mai k'arfi, shikad'ai yasan irin zafin da yakeji a zuciyarshi musamman in ya tuno fuskar safiya da Babanta , yanzu wane irin kallo zasuyi mashi tabbas zasuyi zargin an saye shi ne da sa hannunshi,
cikin huci da tsananin takaicin da yake ciki yafara magana Yana cewa " har yaushe sai yaushe k'asarmu zata gyaru sai yaushe za'a daina kashin dankali a k'asar nan , kullum manya su suke danne na k'asa dasu, zalunci yayi yawa sosai a k'asarmu Kuma ba Wanda zai iya daukar wani mataki kullum tsoro da zullumi da mutuwar zuciya su suke k'ara jefamu a halin da muke ciki ,kowa Yana tsoron yayi magana wani abu ya sameshi to shikenan mu a haka zamuyi ta rayuwa kenan talaka bashida wani 'yanci na kansa duk sharar da aka kwasa a zuba mashi , 'a'a bazai yiwu ba bazan zuba ido suci bulus ba doli sai na k'watowa yarinyar nan hak'inta kota halin Yaya wannan alk'awari"............"dakata Hisham" Momma ta katseci cikin sauri don tunda yafara magana jikinta ke rawa duk da Bata fahimci abunda yake magana akai ba , Amma ta fuskanci inda yasa gaba ,cikin rawar harshe tace "Hisham ka nutsu ka gayamun abunda ke faruwa ko na baka shawarar da ta dace inason ka rink'a sarrafa fushinka kar watarana ka aikata aikin Dana sani Wanda bana fata ,Amma wannan fushin naka yayi yawa in Abu ya dameka karinka maimaita innalillahi wa inna ilaihin rajiun zakaji sauki a zuciyarka kaji"
Daga kanshi yayi alamar amsawa kamar k'aramin yaro , cikin hikima da dabara momma ta samu ya gaya mata abunda yake faruwa , ai kamun ma ya k'arasa tuni momma tafara zubar da hawaye jikinta har rawa yakeyi cikin wata irin murya Mai cike da tashin hankali da bayyanar da zallan tsoron da take.ciki tafara cewa " Hisham ka duba girman Allah ka janye wannan case din , don Allah ka fidda hannuka daga ciki, banason. Kana shiga irin wad'an nan case din Hisham sunfi k'arfinka ,bazaka iya komai akai ba kabarsu duk Wanda yayi na gari kansa , Amma don Allah karka je ka janyomin abunda bazan iya dauka ba kasani Kai kad'ai gareni Kai nake kallo naji sanyi ba uwa ba uba ba miji ba marik'ana ba wa ba k'ani ka tausayamun bazan iya jurar wani abu ya sameka ba tunda kasani ba Imani ne da mutanen nan ba, ba abunda bazasu iya aikatawa ba indai akan take gaskiya ne Kai shaida ne akan mahaifinka ,a irin hakane aka kashe shi idan suka cutar dakai a wannan karon bazan iya jurewa ba don Allah Hisham ,ta k'arasa maganar tana had'a hannayenta da nashi cikin kuka,
Tuni zuciyarshi tak'ara hasala ga kukan mahaifiyarshi da yakejin kamar Ana zuba mashi darma a azuciya cikin sanyi da raunin da zuciyarshi tayi akan mahaifiyar tashi yace " Momma ya zanyi ? Zaluntarsu fa akayi Kuma zalunci Mai matukar girma yanzu shikenan a haka zasu zauna cikin bak'in cikin zaluncin Da akayi masu ..............katseshi tayi da cewa Hisham na k'are magana inason ka janye hannunka a wannan case din , insha Allah Allah zai bi masu hakkinsu Allah ba azzalumin bawansa bane saidai bawa ya zalunci kanshi , da sannu Allah zaiyi Mana maganinsu da sannu zasu girbi abunda suka shuka da hannunsu, "
Batare da ya sake cewa komai ba ya mik'e ya nufi d'akinshi zuciyarshi kamar wuta yanajin in Bai hukunta wadan nan shegun yaran ba bazai taba samun nutsuwa ba Amma doli zai zare hannunshi akan case din saboda Momma , shi ya sani basu isa suyi mashi komai ba saidai zai barsu ne saboda kwanciyar hankalin mahaifiyarshi, alwala yayi ya gabatar da sallar magrib da Isha alk'ur'ani ya dauko yafara karantawa a fili cikin zazzak'ar muryarshi yajima sosai Yana karatun kamun ya rufe littafin ya ajiyeshi inda yake ,yakoma bisa gadonshi ya kwanta , sai a lokacin yaji zuciyarshi tayi mashi sanyi sosai lumshe idonshi yayi da son yayi bacci ko zaiji saukin ciyon da kanshi keyi mashi , a hankali kyakyawar fuskarta tafara yi mashi gizo kamar dai jiya babu shiri ya bud'e idanunshi tare da dafe kanshi hannunshi Yana mamakin yadda ya manta da zancan zuwa wajan yarinyar nan, da sauri ya dauko wayarshi ya lalubo number ta wadda yayi serving da *Likita* bugu biyu ta dauka cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa tace "assalamu alaikum "
Saida ya lumshe idonshi ya bud'e kamun ya amsa mata sallamar tata cikin Jan aji, take ta had'e fuskarta don ta shaida muryarshi shine ya kirata jiya Yana mata rainin wayo,
Cikin wata irin murya da shi kanshi baisan yanada itaba yace " Matar kinga yau Baki ganni ba ko nasan kinyi ta jirana wallahi Sam na manta ne Amma insha Allah gobe Zaki ganni kiyi bacci lafiya "ya k'arashe maganar da hura mata wani sanyayyen kiss Wanda taji iskanshi har a kunnenta Wanda take tsikar jikinta ta shi da sauri ta cire wayar a kunnenta kamun tayi wani yunk'uri ma har ya kashe wayar tashi, tajima tana kallon wayar cike da wani irin yanayi Amma takasayin tunanin komai sai can Kuma tayi tsaki tana mamakin rainin hankalinshi , wai ya manta Kuma a hakan wai sonta yakeyi tsaki tayi tana jifa da wayar tare da k'ara gyara kwanciyarta ,
Hisham kamnan take bacci yayi awon gaba dashi cike da annashuwa Kai kace bashine.yake cikin matsanancin fushi ba a d'azun'
___________________________
WASHE GARI
Sosai ake bawa zayyan kulawa wanda alhamdulillah ya fara jin sauk'i ,kumburin fuskar ma yafara sacewa , Momy sosai take kula dashi Amma Amna ko sau d'aya bataje ta gaidashi ba saima haushin yadda duk Daddyn da momy suka damu akanshi takeji,
Yanzu ma Daddyn ne zaune agefen makeken gadon da Zayyan yake kwance Yana shafa kanshi a hankali tare da k'ara kwantar mashi da hankali akan zai daukar mashi fansa akan duk wani Wanda yake da hannu da ta'ba lafiyarshi , Yana jirane yasamu sauki ta yadda zaiga yadda zaiyi da wannan banzan Mataimakin commissioner din,
____________________________
Tunda yazo office yau yakasa ta'buka komai har na tsawon awa biyu , gajiya yayi da zaman kamun ya tashi yabar office din , direct asibiti ya nufa inda aka kwantar da Safiya ,da sallama ya shiga d'akin , mamanta ce zaune kusa da ita tana rik'e da hannunta sai fisge fisge takeyi tanason cire k'arin ruwan da aka samata , ga wani kuka da takeyi wanda komai rashin imaninka sai ka tausaya mata ,itama mamar kuka takeyi tana rirrik'eta da Bata Baki,tashinta kenan daga alluran baccin da akayi mata d'azu da safe , zuba masu jajayen idanunshi yayi da suka canza nan take a hankali fushinsa na jiya ke dawowa , daurewa yayi ya matsa inda suke kallon maman yayi yace " "saketa Mama, "
"Yalla'bai zata jima kanta ciyo ne"
"Saketa zata daina "
Jin hakan yasa batayi musu ba ta saketa zama yayi kusa da ita yafara mata magana a hankali Wanda ko maman bataji abunda yake ce mata ba , nan take ta nutsu tare da zuba mashi kumburarrun idanunta don gasgata maganar da yake fad'a mata , jinjina mata kanshi yayi alamar hakane , lumshe idonta tayi a hankali wasu hawaye masu zafi suna zubo mata , kamun tayi baya ta kwanta ,mamaki ne ya rufe maman ganin duk irin lallashin da sukeyiwa Safiya Bata ko daga ido ta kallesu Amma gashi cikin yan seconni Hisham ya bi da ita cikin ruwan sanyi , wani girmanshi ne da kaunarshi suka k'ara kama maman sai addua take zuba mashi Yana amsawa da Amin cikin tausayinsu ,lokaci. Da zai wuce ne yake barmata sakon Yana neman Baban safiya a office in ya zo ,to Mama tace mashi kamun suyi sallama ya tafi,
____________________________
Hisham ne zaune tare da Baban safiya da kanenshi office dinshi , da k'yar ya daure yayi masu bayanin halin da ake ciki tare da sanar dasu an kar'be case din a hannunshi yanzu case din Yana hannun manyanshi Wanda shi bashida wani abu da zai iyayi akansu sai yadda sukayi sai dai yayi masu alkawarin abunda akayiwa safiya bazai taba tafiya a banza ba inaha Allah zaisan matakin da zai dauka haka dai yayi ta kwantar masu da hankali ,saidai hankalin nasu yakasa kwanciya sunga samu sunga Rashi tabbas wanna. K'asar tamu abun tausayi ce yanzu shikenan. Talakan Nigeria bashida wani yan cin Kai ??? Kullum sukenan zasu zauna a mulkin mallaka ? Sosai Baban safiya ke kuka da idanunshi tare da adduar Allah yasakama 'yashi yasan in sunfi karfin hukuma ai bazasufi k'arfi. Allah ba, da k'yar Hisham ya lallabasu suka tafi ,cikin rashin jin dadin zuciya yabar office din shima yanufi gida,
_________________
Misalin k'arfe 4 ya isa gida a massalaci yafara tsayawa yayi sallar la'sar kamun ya k'arasa gida , koda yazo ya tarar da momma Bata nan dama ta gaya mashi zataje gidan k'awarta hajiya Hadiza , wanka yayi ya canza kayan aikinshi , cikin wani tsadadden bak'in yadi Mai shara shara ya shirya Wanda ya k'ara haska farar fatarshi yayi mashi kyau sosai bak'in takalmi yasa sai agigonshi fari Mai azabar tsada da kyau , farin glass dinshi ya dauka ya Sanya ,Masha Allah yayi kyau sosai kamar ka saceshi ka 'boye🤪 a gurguje yagama Shirin ya fita ya dauki wata bak'ar motarshi wadda Tasha wanki da guga sai daukar ido takeyi direct unguwar su laurat ya nufa kasancewar tun kwanaki yayi bincike akanta sosai yasan komai akanta sai abunda ba'a rasa ba wannan yakara bashi k'warin gwuiwa akanta don tasamu yabo ita da iyayenta sosai ,
A bakin get din ya tsaya ya dauko wayarshi ya Danna mata Kira , sai wani farinciki yakeji daga can k'asan zuciyarshi ,Yana jin kanshi wani daban don Bai taba zuwa zance ba baimasan yadda akeyin zancan ba ,daga kafadunshi yayi afili Yana cewa ai sai ta koyamun don da alama ita tasan yadda akeyin zancan, har wayar ta tsinke Bata d'aga ba , tsaki yayi ya sake Kira ringing biyu ta dauka tare da yin sallama, cikin lumshe idonshi ya amsa mata sallamar ya Dora da fadin "da bakiyi niyar dauka bane ko kuwa Jan aji ne ? Bai bata damar magana ba yace kifito ki shigo Dani Ina k'ofar gida,
Dam dam zuciyarta ta buga tana mamakin wai wannan wane irin karfin hali yake dashi, kallonta zee tayi tace "lafiya anty, ?"
"Hmm inafa lafiya wani dan rainin hankali ya sakoni agaba gashi Abba Yana nan bansan ya zanyi ba , wai gashi a k'ofar gida ,"
"To Kuma anty bake kikace yazo ba ?"
"Taya zance yazo bayan banko sanshi ba Ni banma San inda yasamu number ta ba wallahi, don Allah ki taimaka kije ki koreshi tun kamun Abba ya ganshi kinsan dai kiris yake jira Dani wallahi ,dariya zee tayi tace "okay to Bari naje Naga ko waye "
"Yawwa my swt.sis don Allah taimaka"
Gyalenta ta dauka ta yafa tafita a hankali ta nufi bakin get din tana dariyar Shirmen lauratu na korar samari ita kam in taga yayi mata wallahi bazata koreshi ba shigo dashi zatayi sai dai duk abunda za'ayi ayi,da wannan tunanin ta k'arasa get din ,bude karamar k'ofar tayi ta fita ,motar ta nufa tana k'wank'awasawa a hankali kasancewar motar Mai duhun glass ce Bata ganin Wanda ke ciki ,
A hankali ya bude motar yafara fito da k'afarshi ,gaba daya zee ta k'ara waro idonta don ganin Wanda zai fito daga motar, fitowarshi gaba daya yasa ta kusan fasa ihun murna ,da k'yar ta danne murnar ta cikin rawar jiki tafara gaisheshi bakin nan kamar gonar auduga don ba karamun ganin dacewarshi da antyn nata tayi ba ,cikin farin ciki tace "sannu da zuwa Yaya anzo lafiya yagida anty tana ciki tace nayi maka iso ,
Murmushi yayi don lokaci d'aya zee ta shiga ranshi rawar kanta na kara bashi dariya , rufe motar yayi Yana amsa mata gaisuwarta kamun yabi bayanta suka nufi cikin gidan ...............nagaji sai gobe🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
No comments