MATAN HAFIZ 12
12.
K'arar kukan tane yasa mahaifinta saurin dawowa daga qofar fita da ya nufa.
"Subhanalla ke zainabu lfy kike wnn uban ihun mimakon kiyi salati inma firgici ko razani kikayi abin zaizo miki da sauqi"
tashi zaune zainab tayi daga burgimar ihun kukan nata hawaye nata shatato mata masu tsananin zafi da qunan a zuciya,
ta dubi mahaifin ta tace
"Baba Hafiz ya sakeni kaga ynxun ya fadamun kiran da akayimn a waya ynx baba ka agaji rayuwata wlh inna rasa Hafiz mutuwa zata aboceni koma na kashe kaina da kaina dan rayuwa ta babu tabbacin amfani matuqar babu Hafiz a cikin ta"!! taqarashe mgnr cikin sake rushewa da kuka har tana dukan kanta da garo nan danan kuwa gefen goshinta ya fashe, salati mahaifinta keyi daqyar yasamu ya dafa garo ya zuqunna jikin bango a saman qafafun sa.
"innalillahe'wa'inna'ilaihirraji'un....daga Allah muka fito kuma garesa zamu koma!".
abunda mlm usman mahaifin zee knn yake furtawa kansa a Sama, cikin dauriya ya dubi zee yace "zainabu miya faru tsakaninku da hafizun haka da zafi har saki ya ratso ciki?"!
bud'e baki tai zatayi mgn Yy saurin dakatar da ita da furta
"wnn karon gskian lamari nakesonji daga gareki dan a ynx na tabbatar da mgnr da kika zomun da ita kika fadamun qanzon kurege ce dan muddin abinda kika fad'amun gski@ ne to babu ynda za'ayi ace shine silar shikan nan dan haka maza2 ki kiramun Hafiz din a waya".
cikin sabon kuka zainab keta faman girgizawa babanta Kai danta kasa ma mgn gaba 1,
"kiyi abinda nace mutuniyaz kawai ay nasan halinki bakkida nutsuwa zainabu lokutta da dama, lallaikam na tabbatar ba qaramin abu kikaiwa Hafiz ba dahar kika iya fusatasa lkc 1 haka ya iya furta miki saki dudda kuwa da yawan haqurinsa,
tabbas bani kadai ke shedar kyawawan halayen Hafiz ba mutanen dasuke tareda shi ma sunfini sanin hkn Dan HK wallahil azim bana raba d'aya biyu zainab da babban laifin da kikai masa, dn haka ina mai sake umartarki dakiyi hanzarin kiramun shi kmr ynda na umarceki, kiran da zainab taiwa Hafiz yafi a qilga amman ya shareta gaba 1.
dan a lkcn ma shiri yk yana saurin den zuwa Barrack dinsu koda ma ya gama shirinsa yasuri key din motarsa yafito falo yasamu heema kishingid'e da tumtum iriyar na gidan sarakai tana shan had'in ta datayi da kanta ynx na garin rogo da murjajjiyan gyad'a da kwakwa wnda yasha madara saisha take tana lumshe ido dan kuwa had'in ba qaramin dad'i yayi mata ba,
dan kamin ma ta had'asa d la ta tunosa yawunta har tsinkewa yk,
mutum taji ta bayanta an rungumota sosai,sansanyar dadaddden qamsasasshen qamshinsa daya kama jikinsa shine ya tabbatar mata da heron sojan ta ne a manne da ita, tare suks sauke wani sansanyen numfshi sanda taji yana goga tausasan red lips dinsa a gefen wuyanta tareda juyota suka fuskanci Juna yana mai binta da hayataccen kallonsa mai kashe mata illahirin sansar jiki, bin cup din hannunta yayi da fararen qal din kyawawan idanunsa masu yalwar bak'in gashi , yayinda ita kuma tabi ga baki dayan azabbbiyar kyakkyawar fuskarsa da kallo, tabbss dud wacce Allah ya azurtata da samun kyakkywan namiji kmr Hafiz baqaramin dace tayi a rayuwar ta na tarayya dashi ba, koda kuwa a misali ace babu wani abunda yake giftawa a tsakaninku na aurataya dashi baqaramin alfari baneba gareka bare shidin ma cikakken mutum ne nutsattse kamili mai son tsananin son addinin sa dan shedar hakanma gata a goshinsa wato d'igon baqin shedar sallayan sa, hakan kuwa baqaramin sake fiddo masa da sihirtaccen kyaunsa ya kumayi ba na usulin larabawa jinin mahaifiyarsa uwa uba gashi matashin saurayi ingarman namijin zaki dan 32,yrs ga masu gida rana kai Allah na gode ma gskia dolema nazo na canza taku nima kodan sake cusa qauna ta a cikin zuciyars...
hure mata idanuwa taji yayi hakanne yasata sauke ajiyar xuciya tareda dubansa.
kanne mata ido 1 yai gamida furta "yadai mom twins kada kiciyeni da kallon nan fa" dariya heema ta qyalqake dashi tasa hannu tana shafa gefen fuskarsa tace
"Yes my man inma na cinye ka nawa ne ay ko my soja?".
sake zuba mata idanu yai yace "yes amman miye haka kike sha my heema a cup?" Yy mgnr idanunsa nabin cup din hannunta da ido yana sake leqawa, murmushi tai tace
"abbun sultana had'in abin shan kwadayin masu cikine ko zaka sha kaima?"
waro idanuwa yai yace
"to aini bnd@ ciki fa, kuma yaza'ay nasha madam inba cikin zaki mun ba nima em?" Yy mgnr yana mata wani kallo mai kashe lakkan jikin wnda ake jifarsa dashi. Murmushi tai tace
"basai masu ciki ba kowa ma zai iya sha ay"
sake kanne mata ido yai yace "to na yarda zansha amman innayi cikin snn OK?"
dariya sosai mgnrsa ta bata tama kasa mgn sbd kunyar mgnrsa.
miqewa tsaye yai yana sakin murmushi bayan duqowa dayai yayi kissing babyn cikinta, dagowa tai tabisa da kallo tana yaba ynda uniform din sojojin yamasa kyau sosai ajikin farar fatar sa uwa yau ta fara ganinsa, yamutsa fuskarsa yayi bayan yaduba agogon diamond din hannunsa, sam baison late, sunkuyowa yai ya bata Peck a lips din ta gamida zuqo kwakwr datasa a bakinta yayi murmushi ya nufi dakin fateema.
yasamu tana wanka bakin toilet din ya qarasa ya mata mgn snn yawuce compound din gidan inda motocinsa suke.
yana fitows waje yaji sautin wayarsa ta dauki Ringing. tabe baki yai dan yasan bai wuce zainab bace, sam baida wani burin sake zama da dud macen dabata dauki iyayensa da Kima ba da daraja ba. saida ya shiga direbnsa wani kurtun soja ya iso gun da sauri ya bude masa motar ya shiga shima ya shiga yaja suka fiita,
sun hau hanya sosai yaji wani kiran ya kuma shigowa a wayar tasa, cikin kufula ya zare Bluetooth din kunnuwan sa daya sa ya na kai dubansa ga wayan da shirin d'agawa ya yarfa mata rashin mutuncin da ya qudur tama zuciyar sa kota shafa masa lfy ammsn saiyaga sa6anin hkn wato sunan surikinsa mlm usman maihaifin zee din ne yaga yake shawagi a kan wayar tasa..
lumshe idanunsa yai gamida sakin wani iriyar huci mai zafi daya furzo daga bakinsa dan idanunsa har sun fara sakin kalar ja....
"Ya salam"
abinda ya furta knn biyo bayan bud'e idanunsa dayai....
*From 4 writer's fasaha*😍
No comments