DUDUWA 1
🧟♀️DÛDÛWÂ🧟♀️*_
_1_
'Aaa ruwa ruwa na malale.........
Ai ruwan bana yaci samari,Amma baici saurayin ba.......
Ruwa na malale.......
Inna ta ki zo ki dudduba.......
Ruwa na malale.........
'Amalala Mai futsarin kwance...
Ya tsula,ya Kuma tsulawa.....
Daya tsula har gidansu laurrrrrrrrrrrrrrre........
"Laure fara fara tamai gari..........
Laure fara fara Uwar abashe,abashen wa,abashan Mai gari,maigarin wa,Mai garin rugarsu laurrrrrrrre............
Tafe take tana buga hannayenta biyu da Dan botikinta saqale a hammatar ta har ta iso bakin rijiyar,da isowarta gurin yayi tsit kamar ruwa ya shanye 'yan matan dake Kan layin iban ruwan,wace gugan ke hannunta tayi saurin ajiyeshi ta matsa inda sauran matan suke suna bin jibgegiyar matashiyar da ido duban kowa 'yar kulullu6ar tayi farrrr da Ido alamar ba wasa da qar ta duqa tsabar qibba tadauki gugar ta jefa cikin rijiyar tana Nishi da kyar kamar wace tayi gudun shekara.
Guga daya tayi nasarar janyowa ta juye cikin botikin ta Bata Kai ga ibo na biyun ba takoma gefe Dan hutawa tana maida nufarfashi ahankali duk idanuwansu ya koma Kan gugar gashi dai aqasa Amma ba damar dauka bare akai ga iban ruwa sai dai su kalla su bari idan Mai gayya Mai aikin ta kammala tukunna kowa ya koma Kan layinsa ya ibi nashi ruwan ya wuce,,talatu wace ayanzu tacika tayi 6am da haushin anzo an hanasu iban ruwa gashi zataje cin kasuwa gabas sai qunquni take aciki Wanda Baya fitowa fili har 'yar kulullu6ar tayi nasarar cika botikinta taf da ruwa ta dagashi charaf ta Dora bisa kanta tajuya danyin nata waje cikin rashin sa'a ta taka farar leda jikake.......tikkkkkk jibgegiyar yarinyar tayi flt aqasa sakamakon ledar data taka Bata luraba dame Allah ya hada sauran matan suka kwashe da dariya da shewa suna nunata Dan mugunta TANI dake kusa da ABULIYA tini ta kaiwa bakinta chafka gudan Kar itama ta dara nata yai zafi Dan tasan karo da Duduwa ba wasa bane🤣 gabanta harya fara dukan 9_9.
Sai da tadauki daqiqa kusan goma abaje aqasa tana hakki kafin numfashinta ya dai daita chan ta muskuta mazaunanta gefe ta dafe qasan taja goran numfashi ta miqe da qyar tana karkade qasar data kwaso cikin tafun hannunta tafara hangen inda botikinta ya Lula.
A chan gefe tayi Ido 2 dashi Babu komai cikinsa ruwan ya zube qasa ta6ar ta6ar taja lukutayen sahunta Wanda taku 4 tayi batakai ga na 5 dinba tasaka Hannu ta dauka hawaye suka fara kwaranya daga kuncinta tasoma shafa inda botikin ya dare 2 tana........
"Ina yake,Ina yake...Dan Amana inna.
Yatafi ya barni...Dan Amana inna.
A wajan inane...Dan Amana inna
Wajan dibo ruwa ne... Dan Amana inna.
Yadare ruwan ya zube... Dan Amana inna.
Har wai su kemun dariya akan Dan Amana inna......
Tana waqa hawaye na kwaranya a kuncinta 'yan matan naqara 6a66aka dariyarsu kamar sababbun kamu TANI da haryanzu hannunta na chakume da bakinta gam gudun yin dariya ga hawayen dataga na bulala daga idon Duduwa ba qaramun rikicewa tayi ba har wata ajiyar zuciya take saki jifa jifa,,"yau Kam garin *KANWA* sai ta Allah ba dai mutum ba, Tani ta furta tana mai shirin barin wajan,,,,cikin kuka ta kalli 'yan matan 1 bayan 1 ta dauke kanta ta nufi hanyar dazata kaita gida, da zuwanta ta iske ba kowa a tsakar gidan hakan ba qaramin dadi ranta yayi ba lokon data san Inna ke ajiye turmin ta Mai Kama da ita ta nufa takoci sa'a ba adadi da jingine shiba duk kayan Miya ajiki, 'yar Duma dumar ta6arya ta sa6a awuya tayi hanyar zaure da sauri sauri tana shar6e hawaye hade da Jan majina a dai dai lokacin Inna ta fito daga makewayi ta hangota ko butar Bata ajiyeba tabiyo bayanta tana salati da doka mata Kira.
_*DUDUWA!!!*_
_*DUDUWA!!!*_
_*DUDUWA!!!*_
Ai tini Duduwa tayi nisan kiwo kafin inna ta juya neman mayafin da zata rufa har Duduwa ta 6ace daga layin ba shiri Inna ta bazama ne manta dauke da butar ta a hannu qafarta ko takalmi babu tsabar tashin hankali da firgicin abinda Duduwa zata dako mata.
_*By*_
_*Mâmâñ Dr @ff@ñ*_
No comments