Breaking News

DUDUWA 11

          _11_

""Hmmm gani nan kam Hansai ya ya akai ke kika zo nan,Ina zaune cikin rumfar baba naji wuta iska me ƙarfi ta kwashe ni tayi sama dani ban kuma sanin inda kai na yake ba sai yanzu da na gani a nan,shin nan ɗin ina ne Talatu,'Yo ni ma ina na shina, yanda aka miki haka nan aka mun ban shan ta inda aka kawo ni ba,bare hanyar futa amma bisa alama muna shikin tsaka me wuya dan aradun Allah muna hannun haka haka,talatu ta zara ido ta ƙwambare hannun ta tanaiwa Hansai nuni da halitun da suke a ƙasan inda suke da sauri hansai ta musku to gefan da talatu ke zaune ta kama hannun talatun ta riƙe gam tana faɗin"".


      ""'Ki dubi Allah talatu ki mai dani gida na san gwaggo da baba na chan suna nema na ruwa a jallo ki taimaka mun ba dan halina ba ni babu abinda na aika ta aka yanken wannan hukunci,"Ni ma aradun Allah ban aikata ko mi ba Hansai na gani anan ne kawai ki taimake ni ki mai da ni wayoo baffoji na shi ke nan na rabu dasu har abadan abidina,gaba ɗaya suka saki kuka suna riƙe da hannun junna,ko sakan ba arufa ba Hansai taji wani abu a hannun ta cikin sauri ta ɗago kanta dan ganin me ya faru,wayam taga babu talatu a inda sauke sai wani ɗan kututturan ɗan yatsa daya fara matsi cikin hannun hansai nan da nan hansai ta sake shi haɗe da ihu tana ƙoƙarin murginawa ɗaya ɓarin tana kiran sunan talatu,chan ita ma hansai ɗin aka ne meta aka rasa.




*GARIN KANWA*



""Tun da aka lura da ɓatan su Talatu da Hansai,garin Kanwa ya shiga tashin hankali,babu babba babu yaro wajan ne man ƴan matan amma shiru kake ji ba labarin su,haka aka cigaba da nema ana saka ran ganin su a ko yaushe aka bada cigiya a maƙwaftan ƙauyukan dake kusa da garin kanwa shiru kake ji lamarin daya tsorata Al'umma da dama a cikin garin gashi shi kansa mai gari sama ko ƙasa an nemeshi an rasa ga tashin hankalin Duduwa ke haddasawa ta addabi uban kowa..


    Kwanan su talatu biyu da ɓata mai gari ya fito daga maɓuyarsa sakamakwan yunwa da ƙishirwa da suka addabe shi dan ba zai iya jure rashin watu ba,ko da mai gari ya dawo tuni labari ya zagaya ko ina fada ta cika maƙil da masu yiwa mai gari barka da dawowa a cewar sa ziyara ya kai ƙauyen dambo dayake mai garin dambon abokinsa ne na ƙud da ƙud,,me unguwa na gama miƙa tashi gaisuwar ya miƙe da sauri yana sosa ƙeya""


       ""Umm ranka shi daɗi ko zan iya wucewa gona na gano dawar da zan ciraAi babu laifi mai unguwa kaje ka gabatar da uzirin ka kafin yamma akwai maganganun da zamu tattauna iya shaƙiƙan cikin fadar nan ka sanar da wanda bai sani ba.


Insha Allah zan isar da sakon ga kowa yallaɓai.


Yauwa sai kuma gargaɗi,kar a kuskura abar mara lafiyar yarinyar nan ta san da zuwa na na kwaɓi kowa dan haka akiyaye.


Ai ranka shi daɗi ni kai na abinda ke zuciya ta kenan ka rigani furtawa,suma duk zan sanar dasu zaman namu na siri ne.


to babu laifi.mai gari ya furta ya cigaba da karɓar gaisuwa,ko da me unguwa yabar ƙofar fadda kai tsaye gidan inna ya wuce da sauri ya ƙarasa ƙofar gidan cikin zumuɗi ya shiga doka sallama.


     Tiƙis tiƙis duduwa ta fito tana mai amsawa ta dubi me unguwa asheƙe ta ce.


"Yau kuma da wace gulmar aka zo.


Me unguwa ya dashe baki ya ce."""


Ran amaryar mai gari ya daɗi,habawa nan da nan haƙoran duduwa suka haska tsayuwar ma ta gagara sai zamewa tayi kan bulon ƙasa dake ƙofar gidan ta zauna tana sauraran abinda me unguwa zai furta mata,gyaran murya me unguwa yaja ya gyara rawanin kansa ya ɗora da"""".


""Ai ina faɗa miki ɗazun nan da doshin la'asar ina zaune cikin gida Rabi ta baje mun shasshaka da yaji nasaka hannu kenan da zumar zan..........."kaga me unguwa ni duk ka cikan kunne da zanchan da bai shafe ni ba yo in ma gaba da shasshaka ka kwasa ina ruwa na ko a gidan ka nake yau naji abu ko dan kaga ina ɗaga maka ƙafa duk ka cika mutane da surutu kufa bil adama nan akwai ku da ɓaɓatun baki shiya sa jinsin chan haka haka suka saku a gaba ga ƙaryar tsiya....,duduwa ta kuma ƙasa da murya.


""Ko dai Masoyi mai gari ne ya dawo me unguwa?.


Allah ya taimaki me babban ɗaki ƙwarai da gaske masoyi ya diro ɗazu ɗazun nan yanzu haka yana fada yana kwasar gaisuwa shine nace ba'ayi ba ke ba,bari nazo na sanarwa me babban ɗaki,me unguwa ya kuma washe haƙora,daga daga duduwa ta shiga buga ƙafa da rera waka.......



""Dawo dawo.........


""Dawo maza masoyi......


""Kazo ka dube ni dawo maza masoyi.....


In rausaya in jujjuya dawo maza masoyi......


Muyo rowa muyo shillo dawo maza masoyi........


    Me unguwa dai baki yasaki yana kallon rawa da waƙar duduwa har ta gama ta  dubi me unguwa ta ce."""


Kajira ni naje na shiryo sai mu wuce tare.


Aa ranki shi daɗi,gani na ɗin nan da kikayi yasin hanya na sato nace gona zani dan kawai nazo na faɗa miki masoyi ya iso kuma ma yanzu bai kamata ki jeba ki bari bayan magariba duhu ya shigo ki taho warki abinki babu wanda zai ganki bare yaje yayi tsurku mai gari ya gudu zamu zauna tattaunawa bayan magariba kinga yayi dai dai da zuwan naki Hamshaƙiya.


Haka ne kuma kaje sai anjima ɗin idan nazo me unguwa aikin ka yana kyau yasin yau sai kaci balangon baƙo me zafi zafi.


Wai dako nayi yadda nayi kinyi wuf da mai gari.


Hahahahhahahahahh,duduwa ta kwashe da dariya ta faɗa gida da murna fall cikin ranta me unguwa ya juya ya koma fada,koda ya koma fada ya tarar da an soke wannan zaman sirin da za'agabatar sai zuwa gobe idan rai ya kai mu mai gari ya ƙara da sanar da kowa yau gida zai shiga da wuri dan yana da wuridin da zai gabatar kowa ya amsa da to,ya tashi.

    Bayan kowa ya watse ne me unguwa ya runtuma da sauri zuwa gidan su duduwa dan ya guntsa mata hukuncin da mai gari ya yanke,yafi awa ɗaya a ƙofar gidan yana kwara sallam ba atanka shi ba har me unguwa ya gaji da kira ya tafi yana saƙe saƙe a ransa.



    "A yau talata ne aka tashi da rana me zafi a garin kanwa gaba ɗaya ya ɗau zafi hatta mata dake gida ƙauracewa riga suka yi ko wace ka gani da ɗaurin ƙirji da mafici a hannu tsabar zafin da ake,haka ma maza da yawa ƴar shara suka suka suka fito ƙofar gida suna shan iska wanda wasu ke faɗin a waje zasu kwana idan ka kwana bisa ɗaki kam san ƙarewa kawai zakayi.







_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments