Breaking News

JAMI'IN DAN SANDA 20

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

🅿️_20

..........wani irin hucin zafi ya fitar daga bakinshi jin furucin Momma , hannu biyu yasa ya damk'i sumar kanshi da k'arfi kamar zai cireta yana fadin "Miyasa miyasa Momma tuni zuciyarshi ta karye durk'ushewa yayi a wajan tareda fashewa da wani irin kuma mai tsuma zuciya da ban tsoro , kuka yakeyi wanda tunda uwarshi ta haifeshi bai ta'ba yin irinshi ba ,baima san yadda akeyin kukan ba don shi tun yana yaro abune mai wuya kaga hawayenshi bare kuma kukanshi ,


Jin sautin kukanshi ba k'aramun dukan zuciyar Momma yayi ba hankali tashe ta zabura ta bude d'akin ta nufi falon ,


Tana zuwa ta iske Ibrahim na lalla'bashi duk ya rikice saboda ganin irin kukan da Abokinshi keyi wanda har ya zarta hankali dukda ba ihu da kururuwa yake hawayene kawai sai sheshekar da yakeyi wanda takeyi kamar zata tafi da numfashin shi ,


Cikin sanyin jiki ta k'arasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi ,d'ayan kuma ta rink'a shafa kanshi dashi a hankali, 

Jikinshi yayi zafi sosai hakama kanshi kamar  garwashi , haka yake tun yana yaro in ranshi ya 'baci tuni zazzafan zazzaɓi zai rufeshi , 

Yadda Momma ke mashi yasa a hankali jikinshi yafara rage tawar da yakeyi ya fara samun nutsuwa yayinda zafin zuciyarshi ke raguwa a hankali ,ajiyar zuciya kawai yake saukewa , ganin hakan yasa Momma tafara mashi nasiha mai ratsa zuciya , saida ta kwashe sama da 30mnt tana mashi nasiha da kawo mashi hujjojinta na hanashi abunda yakeson aikatawa , 

Har lokacin baice komai ba sai zamewa da yayi ya kwanta akan k'afafunta tareda sake runtse idonshi , 


Ibrahim dake gefe yana kallon su yayi gyaran murya yace " duk abunda kika fad'a Momma kinada gaskiya kuma banga laifinki ba , domin taron wad'an nan mutanen kamar taron aradu da ka ne , hatsabibaine na gaske sannan komai zasu iya aikatawa ga duk wanda yace zaija dasu , to amma hakan bashi zaisa mu zuba masu ido suci bulus ba yazama doli muma muyi amfani da matsayinmu wajan ganin mun kwatowa kanmu 'yanci 

A matsayin da Hisham yake kai a yanzu a dakuma matsayina na babban *Lauya* mai zaman kansa zamuyi amfani da wannan damar don ganin cewa mun gurfanar da wadan nan azzaluman agaban koto ,Kuma zamu jajirce don ganin cewa an hukuntasu dai dai da abunda suka aikata ............." A'a Ibrahim bazaku iya ja da wadan nan mutanen ba, ina gudun abunda yafaru abaya ya sake faruwa , bakuda karfin da zaku ja da wadan nan mutanen sunfiku komai tunda suke da abunda zasu iya juya duk wanda sukaso a lokacin da suka so ,.................."a'a Momma Ina tabbatar maki da zamuyi nasara akansu , karki hanamu don wannan jahadi ne zamuyi ko ba don mu ba bakisan iyakar mutanen da suka jefa a hadari irin wannan ba bakisan iya adadin mutanen da suka cuta ba ,tabbas zama da irin wadan nan mutanen ba karamin hatsari ne ga al'umma koba komai harda k'asarmu zamuyiwa aiki, zamu shiga mu fita har sai munga cewa sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu insha Allah kuma nasan DPO ma zai mara mana baya sosai,


Tunda Ibrahim yafara magana Hisham ya kafeshi da ido bayako k'yaftawa tuni k'wak'walwarshi tafara aiki lokaci daya wani tunani ya fado mashi a rai , tabbas da wannan hanyar zaiyi amfani wajan ganin sunyi mutuwar walakanci , duk da ba haka yaso ba amma zaiyi amfani da wannan damar don ganin  bayan azzalumai ,duk acikin ranshi yake wannan tunanin don har wannan lokacin yakasa bude bakinshi ma bare yayi magana ,



Momma da ta jima shiru batace komai ba , sai can ta sauke ajiyar zuciya tace "to shikenan Ibrahim Allah yamaku albarka Allah ya shige maku gaba , tabbas Allah yana bayan mai gaskiya don haka nabaku goyon baya dari bisa dari ",


Daga haka sukaci gaba da tattaunawa da Ibrahim , Hisham kam baice masu kala ba saima idonshi da ya rufe kamar mai bacci azahiri kuwa tuni ya lula duniyar tunanin yadda zai gudanar da shirinshi cikin kankanin lokaci don bazai iya jure tsawo lokaci batare da ya kawar da wadan da suka shiga tsakaninshi da farincikinshi ba ,


Bayan tafiyar Ibrahim magani Momma tabashi kasancewar har lokacin jikinshi da zafi sosai alamar zazzaɓi ,baijima da shan maganin ba bacci yayi awon gaba dashi don kaso mafi yawa na daga cikin damuwarshi ya sauka kasancewar ya samo bakin zaren,


________________________


Washe gari

Da wuri Hisham ya tashi yayi wanka tareda shirin shi na fita aiki , a falo ya tadda Momma zaune ta buga uban tagumi tana tunanin da ya zame mata jiki , ba abunda yake damunta irin kad'aici ,sosai takeson d'an nata yayi aure kodon ta huta da zaman kad'aicin nan amma taga alamar shi babu ma wannan a gabanshi , ko maganar aure bayaso ayi mashi gashi kuma yanzu yanason sa kanshi a wata sabuwar rigimar itakam da zai yarda da ya rabu dasu da sannu Allah zaiyi maganinsu don zalunci baya taba d'orewa,


A hankali taji hannunshi akan nata , juyowa tayi ta zuba mashi ido ,murmushin karfin hali yayi mata kamun cikin shak'ak'k'iyar muryarshi da bata fita sosai tun jiya yace "kiyi hkr Momma kiyi mana addu'a ba abunda zai faru insha Allah, daga haka ya mik'e yanufi hanyar fita cikin takunshi  na cikakken namiji maiji da karfi da k'urciya,


Bin bayanshi kawai tayi da kallo har ya kai bakin k'ofa tace "haka zaka fita bazaka karya ba,"?


Batare da ya juyo ba yace " na koshi Momma," yasa kai yayi ficewarshi , 


Office dinshi yafara zuwa saida ya rage wasu ayukkan sannan ya fito ya nufi office din DPO Huzaifa Umar ,

Da sallama yashiga office din , bayan ya sara mashi ne yabashi izinin zama , gayar dashi Hisham yayi kamun yace "sir wajanka nazo da wata muhimmiyar magana ina fatan zaka goya mana baya ta yadda zamu samu abunda mukeso ,"


Ajiye biron dake hannunshi sir Huzaifa yayi ya zubama Hisham idanunshi yana nazarin shi kamun yace " ok Hisham ina saurarenka ,mi ya faru ??


Duk abunda ya faru tun daga farko har karshe Hisham ya sanar dashi zuwa lokacin idanunshi sun sake rinewa sosai da tsabar fitina da burin daukar fansa,


Tunda yafara maganar DPO ke kallonshi shima idonshi har ya kada yayi jajir tsabar yadda labarin ya ta'bashi , ranshi ya sosu sosai don ba abunda ya tsana kamar irin yadda ake raina *Jami'in dan sanda* abun yana mashi ciyo sosai yadda duk wani abunda zai faru yan sanda sune farkon wad'an da ake nema Don kawo d'auki a wajan , haka zasu shiga duk hadarin waje don ganin sun Bama al'umma kariya amma sukuma mutane basuda abun wulakantawa sai *dan sanda* bashida wata k'ima ko wata daraja a idanun jama'a saboda kawai 'bata garin cikinsu wanda kuma ba duka aka taru aka zama daya ba ,


Yayinda gefe d'aya masu mulki da masu kudi kecin dudduniyar yan sanda masu gaskiya da rikon amana saboda kawai takamar sunada kudi da mulki wanda suke ganin sunfi k'arfin hukunci duk abunda zasuyi shiyasa duk Jamiin da yace zai ja dasu to kuwa zasuga bayansa ne ta hanyar amfani da karfin mulki da kudi wajan saukeshi daga kan aikinshi yayinda wasu ma zasu kaudasu daga doron kasa kamar yadda sukayi akan mahaifin Hisham  wannan ba sabon abu bane amma tabbas a wannan karon shima zai tauna tsakuwa don aya taji tsoro indai yana kan wannan kujerar tasa to tabbas sai yaga abunda ya turewa buzu nadi lokaci yayi da zasu tashi tsaye don memawa kasarsu da jami'ansu 'yanci bazasu sake yarda da wani tozarci ko cin zarafin *yan sanda* ba insha Allah,


"Wannan babban al'amari ne wanda doli sai yaje sama zanyi iyakar kokarina na ganin munsamu goyon baya daga sama kuma daga wannan lokacin bazamu sake saurarawa ire-iren su Alhaji Manu ba a garin nan zamuyi fito na fito dasu ai ba wanda yafi karfin hukuma dama can k'yalesu akeyi amma yanzu kam ya isa haka ,"



Cikin tsananin farinciki Hisham yafara mashi gdy duk da har wannan lokacin ba fara'a a fuskarshi amma a maganarshi kawai za'a fahimci yaji dadi sosai ,


File din da ya shigo dashi ya mikawa DPO yana cewa " wannan file din akan cases din yaran da muka kama ne da hodar ibilis to bincike ya nuna mana cewa yaran su Alhaji Manu ne , inaga da wannan damar zamuyi amfani wajan gurfanar dasu agaban alkali , sanna daga baya zan shigo da wannan case din , "


Duba file din DPO yayi da kyau kamun ya jinjina kai yace "eh tabbas kayi tunani kuma cikin ruwan sanyi zasu shigo hannu , amma kamun nan kana buk'atar kwararre lauya wanda yasan aikinsa don hatsabibancinsu yanada yawa inhar bakada kwararan hojjoji to abune mai sauki su juya case din zuwa kanka , sannan Yakamata kasan halin da Inspector Haruna yake ciki kayi kokari kayi control din fushinka akansa don zai mana amfani, "



Ok sir zanyi duk yadda kace , amma maganar lauya inada lauya yanzu haka , Haruna kuma anijima zamuje wajanshi ,"


"To shikenan Allah ya shige mana gaba" 


"Amin sir ngd sosai"


Daga haka yabar office din dama station din gaba daya ,


_______________________


Direct office din ibrahim ya nufa inda ya gayamashi duk yadda sukayi da DPO , Ibrahim yaji dadi sosai inda sukaci gaba da tsara yadda zasu gudanar da bincikensu,


______________________


Hisham, Jafar, Asmy, gaba daya sun duk'ufa akan binciken da sukeyi a boye saboda munafukan cikinsu wadan da son abun duniya ya rufewa ido suka sayarda yan cinsu ga azzalumai ,

Cikin ikon Allah komai yana zuwa masu cikin sauki don sam basuyi zaton zasu samu sauk'in bincikensu irin haka ba , yaran su Alhaji Musa sun taimaka masu k'warai wajan basu hadin kai kasancewar ba karamar azaba Hisham ke gana masu ba cikin kankanin lokaci suka fita daga hayyacinsu da sun gashi take jikinsu ke fara rawa,,  duk tambayar da zai masu kuwa take zasu bashi amsa har rigegen fada mashi sukeyi , (hhhhhhhhhhh su Goga anji maza) 



________________________



A yau sukayi gagarumin shiri na zuwa kamo su Alhaji Musa inda dama can duk wani motsinsu akan idon jami'an tsaro ne don tuni aka sanya masu ido sosai , shiri sukayi sosai sanin cewa su Alhaji Manu da muggan yan daba sosai wadan da suke amfani da muggan makamai wanda suke fatan har su sukama shiyasa tun farko basu kama kowa ba sunason ne su hada masu tarkon da zasu kamasu gaba daya, 



______________________


Zaune suke sunyi jugum jugum ,ba k'aramar damuwa suke ciki ba ganin k'aramun abu yana nema yafi karfinsu , sun rasa dalilin da wasu abubuwan ke faruwa dasu , yanzu duk yadda zasuyi wani sirri ko a waya ne to sai sunji maganar ta fita sun rasa wake masu zagon kasa ne , waya shirya ganin bayansu ne ,?? bayan duk wasu kadarorinsu a hankali iftila'i ke fada masu d'ai bayan d'ai ,  sosai suka fara zargin junasu da cin dudduniyar juna inda suka fara tada jijiyar wuya , sai daga bayane Alhaji Buba ya ankarar dasu akan Yakamata koma minene to subar k'asar kawai har komai ya lafa sai su dawo kuma zasu samu damar da zasuyi nazarin inda aka samu wannan 'barakar, gaba d'ayansu sun yarda da wannan shawarar wannan yasa sukayi shirin barin kasar zuwa Dubai,


Abunda suka tarar ne yayi bala'in daga masu hankali don sun nemi paspo dinsu sama ko k'asa sun rasa , wannan yasa suka hadu gidan shak'atawarsu don neman mafita,


Suna haka suka fara jiyo jiniyar motocin yan sanda tacika wajan , mamaki ne da tsoro suka kamasu lokaci daya ganin inda suke sam ba'a cikin gari bane dajine sosai wanda ba wanda ya san da gidan dagasu sai yaransu , to mi hakan ke nufi kenan ????


Kamun suyi wani yunk'uri har yan sanda sun cika gidan inda suka fara yin gaba da yaransu kamun suma su fito dasu , kallo kallon sunakayi tsakaninsu da Hisham inda suke mashi kallon zamu hadu da kai yayinda shikuma yake masu kallon na gama daku, ahaka aka sanya su a mota akayi gaba dasu ,su Hisham saida suka shiga gidan sukayi bincike kamun suka fito suma suka bi bayansu,


_____________________________


Kotun tacika makil ba masak'ar tsinke , kowa so yake yaga yadda wannan shari'ar zata kaya da mutanen da kowa kema kallon mutanen kirki ashe su din sun kasance azzalumai masu ha'intar kasarsu ta hanyar shigowa da muggan makamai kayan maye da lalatattun magunguna wadan da Allah ne kadai yasan iya adadin rayukkan da suka salwanta a sanadiyar su, jamaar gari sai Allah tsine suke masu ,


Bayan gabatar da shaidu da kwararan hojjoji kotu ta gamsu da cewa Alhaji Buba da Alhaji Musa da Alhaji Manu suna aikata laifukan da ake zargin su akai sannan tabbas hukunci zai tabbata akansu kamar yadda kundin mulkin k'asar ya tanada ,

 ana shirin yanke masu hukunci ne Bariste Ibrahim Umar ya mike tsaye ya shigar da k'ara akan kisan Da su Alhaji manu sukama Jami'in dan sanda Inspector Abdurahaman ,


Jin wannan bayanin yasa kotun harmutsewa da hayaniya jin wata sabuwa kuma inji yan caca , 

Yayinda cikinsu Alhaji Musa yayi wata irin murdewa tuni suka fara zare idanu alamar rashin gaskiya gashi dama a tsorace suke da hukuncin da za'a yanke masu sai ga kuma wannan tashin hankalin,


Da kyar aka samu mutane suka nutsu inda aka shiga gabatar da Shari'a yadda Yakamata , su Hisham sun tanadi duk wasu shaidu da zasu bukata don basa son ko kad'an ad'aga shari'ar sunfi son yau yau ayita ta k'are kawai,


Acikin shaidun sun gabatar da record din da shi marigayi inspector Abdulrahaman yayi a wayarshi lokacin da suke mashi barazana ,wanda tuni wayar na hannun Momma sai a wannan lokacin ya tabawa Hisham wayar ,dama kuma tana sane da wannan daukar don a kanta ne ma ta boye wayar,

Sannan sun gabatar da direban babbar motar wanda aka biyashi don ya haddasa hadarin , 


Saikuma yaran da suka taimaka wajan ganin shirinsu ya tafi dai dai ,


Shaidar su ta karshe shine Inspector Haruna wanda aka shigo dashi a keken guragu saboda sam bazai iya tashi ba bare har yy tafiya,


Shi yayiwa kotun cikakken bayani akan yadda suka shirya komai har zuwa lokacin da suka samu nasarar aikata shirinsu yakuma gabatar ma da kotun dun wani recording da ya rink'ayi dasu Alhaji Musa a duk lokacin da suke magana batare da sun sani ba , 


Nan aka bawa magatakarda ya jona ga tv yadda kowa zaiji , aikuwa sai ga muryarsu Alhaji Musa radau lokacin da suke kulle kulle su, da wannan kwararan hojjoji da shaidu kotu ta yanke masu hukuncin Daurin rai da rai agidan kaso tareda horo mai tsanani hade da tarar kudi masu yawan gaske ,haka aka kada keyar su Alhaji Musa tareda direban da wadan nan yaran nasu da Inspector Haruna zuwa gidan maza ,yayinda mutane keta Allah wadai dasu suna tsine masu ,



____________________


A wannan rana Momma tayi kuka mai yawa kukan farinciki Allah ya nuna mata ranar da ta jima tana jira an hukunta wadan da sukayi sanadiyar rabata da farinkinta , sai yanzu tasamu wani abu da yayi mata tsaye a mak'oshi tun lokacin da ta fuskanci kashe mata miji akayi ya fada , 


Hisham da Ibrahim kuwa cike suke da farinki suma duk da ba haka sukaso ba sun so ne a yanke masu hukuncin kisa nan take to amma yanzu ma Alhamdulillah, DPO ma yaji Dadi sosai koba komai sun rage mugun iri,


*BAYAN SHEKARA DAYA*.............✍🏼





*Mun kada labarin su Alhaji Musa ne a gurguje don suna bata mana lkc inason mushiga gundarin labarin ne ,tabbas cakwakiya na gaba wannan sharar fage ne*


*YAKAMATA MUSAM WADAN NAN TAMBAYOYIN*👇👇


Miyafaru da Hisham yabar gida 

Ina Momma take da Abokinshi ibrahim

Wacce Mariya da ahalinta suwa sukayi mata fyade har tarasa ranta ,

wanene zayyan wacece Amna su waye iyayensu 

Wanene Amna keso sannan waya kashe zayyan 

Wanene Baffah da ahalinshi

Ya makomar Hisham da Muneeba  idan su Baffa suka tafi suka barsu

*_tambaya mai muhimmanci shin ina mahaifiyar Muneeba*?????

Miyafaru da ita sannan wace fansa ce Hisham yake cewa zai dauka 

Shin zai dauki fansar ne kokuwa zai hakura ???

 


*Hmmmmmmm akwai rigima sosai a gaba yanzu book ya fara ku taimaka kubani hadin kai wajan yin comment ta yadda zakuci gaba da samun typing akai akai*


Pls ku tayani share🥰

No comments