Breaking News

ZAN FASA KWAI 20

 *ZAN FASA KWAI*

                *Page 20*

Yara suka taso cikin kulawa inda ummita iyaye da Yan uwan uwa da na uba ke nuna Mata so da kauna da Kuma kokarin dorata bisa bigiren tarbiya me kyau inda tayi matukar sabo da ubanta eng AK Wanda ko yaushe tana hannun shi Yana Mata wasa har tayi sabo me yawa dashi don in har Yana gida to Bata Rabuwa da shi tafi like mishi fiye da Uwar ta shima Kuma Yana janta jiki don wani irin so yake Mata jinta yake tamkar Ruhin shi lokacin da ta Kara wayo ma dakin shi take kwana in kaga sun Rabu to baya gari shima sai da hikima in ko ta na farke ya tafi ya barta to zata wuni kuka sai da kyar zata hakura in Kuma ya dawo kaf abinda ya Riko natane ba kuma zata yarda ya kubce Mata ba 


Lokacin da ta Kai shekara biyu sabon ya Kara karfi da ta kula zai yi Mata wayo ya gudu sai tayi ca cumi rigar shi ta rike Taki saki sai anyi da gaske kafin akwace shi hannun ta


Sai da ta shekara biyar kafin lubabatu ta Kuma haihuwa inda ta haifo Mubarak bayan Mubarak sai Ahmed sai Fatima daga kansu haihuwa ta tsaya inda yaran ke samun kulawa Amma duk tsananin so da kulawar da ake Basu Bai Hana atarbiyan ce su bisa tsari ba don gaskiya lubabatu tana da kokarin tarbiya Bata kuma yarda da sakarci ba ko don ta tashi da tata tarbiyar ne? Sai yaran suka tashi cikin tarbiya da girmama mutane duk inda suka SHIGA sai sun zamo abin so da Sha awa 


Sai dai soyayyar ummita da ban take azuciyar mahaifin su sai dai Yana kokarin saita Kan yaranshi ba tare da nuna wariya ba Amma duk da haka ummita na karbar girmama wa irin ta babban wa sai lamarin gidan eng AK ya zamo abin Sha awa akasin na gidan Kabir mashi


Daular da ake tanadawa humaira fulani ta zarce afadeta don akullum shaharar Kabir karuwa take kwagiloli Kai da Kai suke zuwa inda izzatu tace haihuwar fulani ne tazo da goshi Wai da ma ummul khairi aka samata inda kuma Kabir ya yarda da maganar ta


Kullum Kara shahara yake inda izzatu ke matukar kulawa da humaira wadda ta taso ba kwaba ba harara ko da ko zata yaga kudi


Yan magana sukace nono alkalin Da ai kuwa hakan ta na Shirin tabbata domin kuwa nonon da humaira ta tsotso ajikin uwar goyon ta na Shirin tabbata domin kuwa ta taso da wata irin sangarta da tabara bama wannan ne abin ji ba tun tana Yar shekara biyar ta iya tijara da wulakanci  hakama idan ta na kuka Bata Jin rarrashi inda Kabir ke matukar so da kaunar ta Amma batayi sabo da shi ba sosai kamar izzatu Amma duk wani gata tana samun shi  


Makaranta ma pravet aka saka ta me shegen tsada aka Kuma yi sa a tana da fahimta sai dai kullum sai tayi fada da yara Yan uwanta inda Kuma kaf din yaran da take fadan dasu Suma ya'yan wasu ne da yawan su ma sun fita matsayi da daraja shiyasa ake Zama lafiya Amma Wanda izzatu ta Raina ajawalin su yanzu ne zata fito ta wanke mutum soso da sabulu in ma taga Kai ba kowa bane to yanzu zata sa akulle ka


Lokacin da fulani ta shekara goma izzar ta ta fito fili duk wani wulakanci na izzatu fulani ta kwashe shi kaf har ma tacewa izzatu Bata iya ba inda Kuma tace waje take so akaita tayi karatu ai kuwa izzatu tasa Kabir ya sama Mata makaranta a America ta Kuma dage ta tafi inda acan ne Kuma ta Kara koyo izza da dagawa har da jijji da Kai har Allah da ikon shi ta kammala karatun ta dawo gida


Inda Kuma can ummita eng AK ya so fiddata waje tayo karatu Amma ita ummita tace Bata son abinda zai rabata da abban ta tafi son kullum ta ganshi 

Yayi murmushi "to sai kinyi min alkawari Zakiyi karatu sosai don so nake kiyi karatu me zurfi......

"Nayi maka alkawari Abba in Sha Allah ba Zan baka kunya ba kuma sai kayi alfahari Dani",


Hakan kuwa akayi itama tayi nata karatun anan cikin garin Abuja har ta Kare inda ita Kuma ta taso cikin nuna irin nata alkalin da ta tsotso 

Babu hayaniya sai tsantsar irin tarbiyar da ta samu ita da kowa sai mutunci  da mutuntawa da Kuma sanyin hali inda shima eng ya soma shahara akan kwagiloli Kan na kamfuna da Kuma na gwamnati komai dai cikin rufin asiri Rayuwa Kuma na tafiya cikin godiya da Kuma wadata.....................

No comments