WAYAR MIJI 5
*📱😱WAYAR MIJI😱📱*
*PAGE 5️⃣*
Sosai take kuka shiko bai saurareta ba duk da har cikin ransa ya ke jin kukan nata amma haka ya danne zuciyarsa. Faɗawa ya yi kan gado yana mai sauke ajiyar zuciya. Ƙanshi na kallon sama ya rintsa idanunsa nan hawayen dake maƙale cikin idonsa suka zuraro masa gefen idonsa. Sosai abin da Hafsat ta masa a yau ya yi matuƙar kona masa rai, duk da yasan shine da laifi amma ya bata hakuri, sai dai ta gaza hakurin domin wannan abin da ta aikata ya tabbatar masa da Hafsat bata hakura ba. Jan dogon numfashi ya yi, tare da dafe goshin sa, ji yake zuciyarsa na ƙuna. To Wai ma in banda bincike irin na
Hafsat duk yadda yake ɓoye wayarsa saboda gudun faruwa wannan abu amma sanda ta binkico, gashi ta janyo musu rashin zaman lafiya cikin gidansu. Shiru ya yi yana nazi, shi dai har zuwa yanzu bai ji zai iya daina chart da mace a wayarsa ba domin suna matuƙar ɗebe masa kewa, duk da yasan Hafsat ita ma gwanace wanjen bashi kulawa, sai dai duk da hakan ba zai iya dainawa ba. Sauke ajiyar zuciya ya yi yana mai furaz da iska mai zafi daga bakinsa. Shika ɗai yasan kunan da zuciyarsa take masa.Can ɓangaren Hafsat kuwa kuka ta ke sosai da sosai wanda daga ƙarshe ta bawa kanta hakuri ta mike da kyar idanunta sun mata nauyi, da kyar ta iya jan jikinta ta shige bedroom nata. Nan ma gado ta faɗa tare da fashewa da wani irin kuka. Hannunta na ɗaure wajen daya mareta cikin kuka ta ke faɗin "Wai ni yau Mus'ab zai ɗaga hannu ya maren akan waya? Mus'ab ya mare ni, bayan tunda mukai aure bai taɓa ɗaga hannu ya bugeni ba, sai yau? Tabbas Mus'ab bashi ka ɗauka don bazan taɓa lamunta ba, sai ka yi nadama da dana sanin marin da kai mini". Wasu hawayen suka shiga sakko mata, mikewa tai da kyar ta shige toilet ta je ta yi wanka, sannan ta fito doguwar bacci ta sa batare da ta shafa ko mai ba, ta haye gado sai dai kwanciya a yau gagararta ta yi, dole ta tashi ta zauna tare da jingina da jikin gado, filo ta jawo ta rungume, ta zuba uban tagumi kwalla na gudu kan fuskarta. Babu abunda ya fi kona mata rai irin marin da Mus'ab ya mata a kan waya. Kenan ya nuna waya ta fita muhimmanci da daraja wajen sa, zai iya yi mata komai akan waya. Idan ko hakane to tabbas zaman lafiya da jin daɗi ya ƙauracewa gidan, don bazata lamunta daga rana mai kamar ta yau ta ɗau ɗamaran yin yaki da Mus'ab akan waya idan har bazai daina ba, to itama ba zata daina ba. Dogon ajiyar zuciyata ta sauke tare da sa hannu ta share kwallan da suke zubo mata. Zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗi sosai take jin takaici abin da Mus'ab ya mata a yau. Tana cikin wannan tunaninne, sai taga an turo kofa Mus'ab ta gani tsaye sanye da kayan bacci ruwan ƙasa duk da yana yinsa ya nuna yana cikin damuwa bai hana kyawun kayan suka fito a jikinsa ba. Tana dubansa a zuciyarta ta ce "Lalle Mus'ab ya kai maƙura wajen rashin kunya, me ya kawo sa inda nake?" Tambayar da ta jefowa kanta tana mai binsa da wani irin kallo. Ganin ƙara tunkaro ta ya ke ne yasa ta yi saurin mikewa tare da gyara wuyar rigar ta cike da masifa ta ce "Malam mai ya ƙawo ka ɗaki na? kai da ka zaɓi waya akai na, to mai ya kawo ka inda nake?".
Mus'ab tsayuwa ya yi kamar gunki ba tare da ya ce da ita ƙalaba ba yana ji ta ci gaba da faɗin. "Bana bukatar ka wuce ka fita mini a ɗaki, domin wayar ka ta fini amfani a wajen ka don haka ka fice mini daga ɗaki". Kare maganar ta yi tana mai fashewa da kuka mai kunan zuciya. Mus'ab ta kawa ya yi ya ƙarasa inda take ja da baya ta dinga yi tana cewa ya "Kar yadda kataɓa......". Bata ƙarara abin da take faɗi ba Mus'ab ya janyota jikinka tare da mannata bisa kirjinta. Duk wani abinda Hafsat za ta masa zai iya jurewa don bazai iya gujen rashin taba ko da sunyi faɗa baya iya kaurace mata, domin ya riga da ya saba da kansancewa da ita a ko wani lokaci musamman a wannan lokaci daya fi kaunar ta kasance da shi. Cikin tattausan murya ya furata "Tabbas nasan na miki laifi, amma don Allah kimin afwa!". Murya a sanyaye ya kare maganar.
"Wallahi Mus'ab baka da kunya ko kaɗan, yanzu kai kake furta kalamar yafiya bayan abin da ka mini mari akan waya, ka kusan karya mini hannu akan waya, kuma a hakan har kake tunani zaka zo naiman yafiya na yafe maka, Ni Hafsat bayan ka nuna waya ta fini muhimmanci. To idan kana tunanin yafiya da ga gareni, kai gaggawar dai nawa, don haka ka sake ni kai tafiyarka bana bukatar ka". Tana faɗa haka tai kokarin kwace wa, ƙara rikota zaiyi kawai sai ta tsinci kanta da gasa masa cizo bisa hannunsa. Tsabar azaba ya sanya wani kara tare da sake ta.
"Kafita mini a ɗaki na ce, domin bana bukatarka".
"Hafsat ni kika ciza?".
"An ciza kuma idan ka kuma taɓa jiki kina sai na abin da ya fi haka. Don d duk mutumin da bai ragar min ba, to wallahi bazan ragar masa ba don haka ka fice mini a ɗaki tun wuri". Cikin zafin rai take faɗi inda numfashi na sarkewa kamar wanda zai ɗauke, hawaye na ziraro mata.
"Ka fita na ce". Cikin tsawa ta yi maganar tana mai fashe wa da wani sabon kuka.
Mus'ab cike da tsanani takaici ya ce "Ina ni kike kora?".
"Na kora ɗin, kafita ka barmini ɗakina, ka tafi can wajan wayarka wacce ta fini muhimmaci".
Girgiza kai ya yi cikin bacin rai idanunsa sunyi ja ya ce "Ok, tunda kin ce haka shikenam. Ai waya a wannan zamani ba abunda za kane ma ka rasa a cikinta, sai da safen ki". Yana faɗar haka ya fice a ɗakin tare da bugo kofar. Yana fita Hafsat ta fashe da wani kukan, ranta na mata kuna da raɗaɗi "Wato zai je ya yi bincike cikin wayarsa har ya sami biyan buƙatar shi". Abin da zuciyarta ta raya mata kawai saita sake fashewa da wani kuka. "Wallahi baka isa ba Mus'ab, baka isa ba yau sai na fasa wayar nan". Tana faɗar haka ta ja jiki cikin sauri ta fice a ɗakinta ta nufi ɗakinsa sai ko ta tadda kofar ya sanya mata key, bugun kofar ta shiga yi tana kiran sunanshi. Shiko yana kwance bisa gado ya yi kwanciyar rubda ciki, zuciyarshi na masa kuna yana jin bugun kofarta ya yi banza da ita. Tun tana yi da karfi har ta gaji, ya zamana sai shasshekar kukanta ya ke jiyo wa. Tabbas har cikin zuciyarsa ya ke jin kukan Hafsat don a rayuwar ya tsani jin kukanta, domin yana ɗaga masa hankali matuƙa. To amma ya zaiyi? Ya je ɗakinta akan ya bata hakuri ta gaya masa maganganu marar daɗi, ta kuma korosa to mai ya ƙawota inda ya ke? Bayan ita ta korosa, mai zai mata bayan ta ce bata fukatarsa?. Furzar da iska mai zafi ya yi a bakinsa tare da tashi ya zauna, ya ma rasa yadda zaiyi. Tabbas dole ya sanya wannan daren cikin kundun tarihin RAYUWAR shi, domin wannan daren ya zama dare da yafi bakin ciki tun daga auren su zuwa yau. Daren ya fita daban cikin dare don ko jiyama bai shiga cikin tashin hankalin irin na yau ba. "To wai Hafsat mai take nufi da shi ne?" Tambayar daya jefowa kansa kenan wanda ya rasa samun amsarta.
Hafsat kuwa ganin bai buɗe kofar mata zaiyi ba ya sa ta ja jiki tamkar zata faɗi ta koma ɗakinta ta kwanta bisa gado tana sharan kwalla. A wannan daren dai gaba ɗaya bacci ƙaurace musu ya yi sai kusan daf da asuba ya kwashe su batare da sun sani ba. Jin kiran sallar asuba ne ya ratsa kunnuwan su wanda ya sanya su tashi dole, cikin sauri Mus'ab ya yi alwala ya fice masallaci dake jikin gidan shi. Ita kuma Hafsat da kyar ta iya mikewa sakamakon azababben ciwon kai da ya risketa da kyar ta iya zuwa ta ɗauro alwala, a daddafe ta yi sallar domin zuwa yanzu ciwon kan ya fara haifar mata da zazzaɓi. Jikinta na barin ta idar da sallar da kyar ta iya yin addu'oin ta shafa, a wajen ta kwanta tare da dukunkune jikinta cikin hijabi. Sosai take barin sanyi domin ciwon kaman wanda ake ƙara mata shi.
Shiko Mus'ab ko da ya dawo bai kula harkar ta ya ci gaba da hidimar shi da kansa. Misalin ƙarfe takwas na safe ya kammala shirinsa na fita kasuwa domin yau asbar ce ranar lissafi ce don duk karshen sati sukan lissafi tare da ma'aikatan shi. Ruwan tea kawai ya sha ya ɗauki Briefcase ɗin sa tare da key ɗin motar shi ya yi ficewar shi ba tare da ya duba Ya Hafsat ta kwana ba. Bayan sun gaisa da maigadi ne ya bashi kuɗi domin ya sayi abincin da zai ci don yasan yau Hafsat ba girki zatai ba. Nan ya ja kan motarsa ya fice da gidan.
Hafsat kuwa tsabar wahala ce ya sanya bacci walahane ya ɗauke ta batare data sani ba. Sai karfe tara da kusan rabi sannan ta farka daga nannauyan baccin daga ɗauke ta. Tashi ta yi ta zauna tana mai murza idanunta dubanta takai ga agogon dake ɗaura kan bed side drawer ta yi, ganin karfe tara harta gota ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tana mai dafe kanta, sakamakon sarawan daya ke mata. Mikewa ta yi da kyar jikinta na mata ciwo gaba ɗaya. Toilet ta shiga ta je ta yi wanka da ruwan zafi sosai Alhamdulilah yanzu kan ta ji daɗin jikinta, bayan ta fito daga wanka ne ta zauna gaban dressing mirror, Kamar yadda ya saba sai dai yauɗin in banda mai ba abinda ya iya shafawa a jikinta, shiru ta yi ta zuba madubin ido, tana kallon fuskarta wacce ta kumbura suntun, abin ka da farar fata, fuskar ta yi jazur idon ya kubura da kyar ta ke iya buɗe su, ita kanta nauyin su take ji dauriya kawai take yi. Tabbas a jiya tasha kukan da tunda tazo duniya bata taɓa irinsa ba "Wallahi Mus'ab ka ɗau bashi". Abinda ta furta can kasan makoshinta inda lokaci guda kwalla ya ciko fal idonta. Mikewa ta yi tana share kwallan ta zura doguwar riga da siket na kanti marassa nauyi............✍️
Taku har kullum
Zainab Ibrahim Gombe
09063406527
No comments