RAYUWAR BILKISU 6
💓💓💓🧕🏻💓🔐
*Rayuwar* *Bilkisu*
*Part* *two*
♦️♦️♦️ Page 6
Cikin nutsuwa Hajiya tafara magana"dama bawani Abu bane yasa natara ku anan sai akan zan dan jamuku kunne game da wasu abubu"
"Tabbas ya zama dole kuyi hakuri da juna ku kasance masu kai zuciyoyin ku nesa domin gudun yawan samun wani abu wanda zai zama mara Dadi a tsakanin ku,Dan haka nakeso ko waccen ku takama kanta tasani cewa ibadar aure take"
"Bawai zamane na wucin gadi ba ko wanda zakiyi kokarin tado mana da matsala ko hargitsi a cikin family tabbas bazan dauki hakan ba
Mu zaman lafiya muka sani bawai tashin hankali ba kuma ina mai shawartar ku akan duk wacce take da futunar ta acikin ranta ko take kokarin yin wani abu dazai kasance bamai Dadi ba toh ta gaggauta
Dawo da nutsuwarta cikin jikinta domin kuwa ba anan ba,Kuma tabbas zansa kafar wando daya da duk wacce keda kokarin hakan
Kuma tabbas kika bari mukasa kafar wando daya dake tom ki kuka da kanki,da haka nake muku fatan zaman lafiya da zuri'a dayyiba,kuma Allah ya kauda futuna a tsakanin ku"
"Ameen" Dr.ya amsa dashi kafun hajiya Kaka ta juyo gareshi yayinda idanuwanta ke kansa"yauwa kaima nadawo gareka,banaso naji wata futuna da zata futo daga bangaren ka wacce zata iya zama ta dalilin ka inaso kaji tsoron Allah acikin zaman ku ka kasance mai adalci a tsakanin matan ka
Inaso ka kiyaye sosai kuma sarai kasan halina matuqar nasamu wani abu mara kyau daga gareka" wani qayataccen murmushi Dr.yasaki tare da fad'in"babu wata matsala daza'a samu ma insha Allah"
Yayinda tunda ya zauna babu abunda idanun sa keyi faman satar kallon Bilkisu wacce ke sanye cikin dogon hijabin ta ash color wanda yayi matuqar karbar ta,tunda ta zauna batayi wani kwakkwaran motsi ba dahar zata gane irin kallon da yake jifanta dashi,itadai kawai tana jinta a muqun takure.
Surayya kuwa ba qaramun gama quluwa taiba tabbas awannan lokacin tana ganin muqun kokarin da zuciyarta tayi da bata aikata wani abu mara kyau ba,domin sarai tana hankalce da wani salon kallo da Dr.ke jifan Bilkisu dashi,tabbas yarinyar tanada wani irin kyau na asalin jinin fulani,kallo Daya zaka mata ka fahimci baiwar da Allah zubawa halittar ta dama sanyinta wanda ke tsananin daukar hankalin mutane akan ta.
Saidai daga bangaren Surayya wata muquwar tsanar yarinyar ce ke Kuma shigarta a kowane bugu na zuciyarta,dukda itama ta kasance ba bayaba amma tabbas tana kallon yarinyar tasan ta hadu,hakan yasa tsanarta ke Kuma nunkuwa a zuciyarta.
Maganar hajiya Kaka ce tayi silar dawo da ita cikin wannan duniyar domin tariga tayi nisa a duniyar tunani"tom kutashi kutafi Allah ya bada zaman lafiya dama maganar kenan"Hajiya Kaka tafada yayinda take kishin gida bisa kujerar datake zaune.....✍🏻
Rabbi kaimana jagora ameen🤲🏻
Gaskiya inada complain akan ku Readers domin rashin ganin addu'oin ku da comment d'inku in kuma kuna ganin na dakatar da labarin baiyi muku ba tom
No comments