Breaking News

ZAN FASA KWAI 19

 *ZAN FASA KWAI*

              *Page 19*


.......Wata irin Rashin lafiya ta Kama dungo uwar Kabir mashi ciwo irin Wanda Bata taba yin irin taba Amma da yake ta iya jarumta da hakuri haka take ta jaganiya da Yan yaran rainon ta yaran Babu Wanda ya shekara biyu ga Yar banzar rigima wancan yayi kuka ta rurruga wancan yayi fitsari ta wanke wancan yayi Kashi ta wanke ba zata taba samun sauki ba sai sunyi bacci ko iyayen su sun karbesu Amma Duk da haka ciwon da takeji Bai sa ta kwanta ba duk da kallo Daya zakayi Mata ka Gane Bata da lafiya matukar dai kana Gane lamarin Rayuwa sai dai Rashin kudi ya Hana Mata zuwa Asibiti inda ta Bari sai ta karbi kudin rainon ta idan anyi albashi sun karbi kudin su


Sai dai kafin albashin ciwo yaci karfin ta har ta Fadi kwance ciwo riris inda har rainon ma ya gagara

Wata daga cikin masu kawo yaranta me suna Jamila ta shigo gidan inda ta iske dungon kwance abin tausayi


"Subhallah ladidi Baki da lafiya ne? Wallahi kuwa Jamila Ina Dan gidana fahat? Yaron da take raino ya SHIGA dago Mata hannu Yana son ta dauke shi saboda sunyi sabo me karfi da yaran

Ta Mika hannu ya taho ta rungume shi inda Jamila ke kallon ta cikin tausayawa 


"Amma ladidi kinje Asibiti kuwa? A a Jamila banje ba saboda Babu kudi hannu na..........

"Karki damu taso muje in kaiki ai lafiya tafi komai 


Jamila ta kaita Asibiti aka dubata aka Bata magun guna suka juyo gida inda jamilar ta kashe kudi masu dama sama da dubu goma Sha biyar duka dawo gida gungo nata zuba godiya don gaskiya Jamila na mutunta ta ko abinci me Dadi tayi sai ta Aiko Mata bare ta dafa nama 


"Karki damu ladidi ai mun Zama Daya Babu komai ke dai Allah ya Baki lafiya

Ta amsa da ameen ya Allah

Haka Tasha magani har sauki ya samu

Inda wata ya cika Jamila ta dauki albashinta ta kawowa dungo hakkinta Amma dungo tace Allah ya sauwake wallahi ba zata karba ba Amma Jamila tace wallahi sai ta karba.....


"Haba Jamila don dai nice uwar marasa mutunci sai na karbi kudinki ?......

"A a sai kin amshe su wallahi banyi don komai ba sai don Allah da zaman tare  Allah ya Kara Miki lafiya ta aje Mata kudin ta dauko danta ta fito inda ta bar dungo da zubar hawaye Wai yau Dan da ta haifa ta wahaltawa shi ke gudunta yayin da can wasu da Basu hada komai ba sai musulunci da mutunci suke wahala Mata har suyi Mata abinda danta Bai yi Mata ba


Babu abinda yafi Kona ranta irin yadda ta taka har gida ta sanar dashi zubar bangon ta Amma har yau Bai tada Mata ba asalima an kusa shekara Amma har yau zuwan shi guda Kuma yaga yadda aka saka zana amma bai Kuma zuwa ba Kuma yanzu da mutuwa tayi ba lallai ya sani ba to in ta mutu ma Yana da asara ne?


Amma dayake tana mishi uzuri sai ta bar abin ya wuce ko aranta Bata aje shi ba taci gaba da rainon yaranta Wanda ke debe Mata kewa fiye da zato inda makocinta malam Ali ya shigo ya duba jikinta inda yake tambayar ta Kabir ya Zo kuwa? Tayi murmushi "Bai zo ba malam Ali , to Allah ya Kara lafiya da haka ya fice Yana mamakin wannan yaro da duniya ke rudu duk shaharar shi Amma abin haushi ya yasar da uwar shi sai tayi raino ta ke ciyar da kanta Amma shi Yana can cikin katon gida daga shi sai matar shi suke hutawa Anya kuwa Bai dauko hanyar lalacewa ba?


Uwafa? Uwar ma irin dungo wadda yasan yadda ta wahalta mishi har ya tako matsayin da ya tako? Babu wata riba ko nasara da ake samu ba ta silar uwaye ba koma an sameta to zata sulale saboda Babu albarkar iyayen sai yayi mishi adduar Allah ya shirye shi ya kuma shiryi Al ummar musulmi Baki Daya..........

No comments