Breaking News

WAYAR MIJI 3

*📱😱WAYAR MIJI😱📱*

        *Page 3* 

Wayarta ce ta shiga ringing, dubanta ta kai ga wayar ganin number aminiyarta Khadija ce ya sa ta yi saurin ɗaukar wayar. Bayan sun gaisa ne, Khadijah take sanar da ita yau da yamma zata zo, in sha Allah, ba sai gobe ba. Aiko ba ƙaramin farinciki Hafsat ta yi ba, godiya ta dinga mata domin dama gani take kamar ba zata iya jure zuwa gobe ba. Har sukai sallama, aje wayar ta yi tana mai sauke ajiyar zuciya. Can kuma sai kwalla ya ciko idonta bata ankaraba ta ji saukar su bisa fuskarta. "Oh my God!" Abunda ta furta tana mai goge kwallan da suka zubo mata.


Can ɓangaren Alhaji Mus'af kuma da fitarsa tare da yaran shi kai tsaye gidan Hajiyar sa dake unguwar Herwagana ya nufa. Hajiya dake zaune a falo ganin ƴan jikokin nata yasa ta yi farinciki matuƙa rungume su ta yi gaba ɗaya cikinfarin ciki ta ce "Ku ce yau an tuna da ni". Kare maganar ta yi tana mai kama hannunsu ta zaunar dasu bisa kujera inda ta ɗaura Ihsan kan cinyarta, sai a lokacin Hajiya ta kai dubanta ga Mus'af wanda ya ke zaune ya zuba musu ido sai murmushi ya ke. Ita ma Hajiyar sakar masa da murshi ta yi, cikin girmama ya shiga gaisheta. Cike da kulawa ta ke amsawa tana fara'a. Bayan sun gama gaisuwar ne ta sa Hajja mai aiki ta kawo musu kayan motsa baki, Duk da yaunwar da Alhaji Mus'af ya ke ji baisa ya ci abinci ba, ruwa kawai ya sha ya ce ya isheshi, ba yadda Hajiya ta yi akan ya ci amma fir ya ƙi dolenta ta hakura ta ci gaba da bawa ƴan jikokin ta kulawa. Gefe guda kuma suna taɓa hirar su tare da ɗanta mus'af, Inda ta ke kara jaddadar masa da bikin Kanwarsa Fati saura sati uku.


Murmshin Alhaji Mus'af ya yi tare da gyara zaman sa cike da kulawa ya ce "Hajiya ai ina sane, ina lissafima don jiya munyi maganan kayan ɗaki da Aunty Hauwa da taje gidana, to dai mun tsaida magana akan zata tambayi Fatima ko wani kala take so a sai mata, Sannan zan turo kuɗi ta account na ki in yaso duk abinda babu sai a saya idan kuma kuɗin ya kare sai amin magana, don wanna lokaci bana so Baba yasa koda Naira biyar game da hidimar bikin Fati, In sha Allah ni zan yi ko mai".


Tun da yake maganar Hajiya ta ke dubansa tana murshin jindaɗi matuka inda daga karshe ta dinga gero masa addu'oin karin buɗi tare da nasara cikin rayuwar sa. Kiran sallar la'asarne ya sashi ya mike tare da yi musu sallama sannan ya fice ya nufi masallaci.


Ita ma Hajiyar jan yaran ta yi suka shige ɗaki.


.....

Ɓangaren Hafsat kuwa tun idar da sallah la'asar ta fito falo ta zauna bisa kujera, tagumi ta yi hannu bibbiyu tare da ƙurawa kofa ido tana jiran isowar ƙawarta Khadija wacce a yanzu ta cire rai da zuwanta. Shiru ta yi kwalla fal cikin idonta, ita kaɗai tasan halin da ta ke ciki, Tabbas tsakanin jiya da yau ta jefa kanta cikin damuwa mai gusar da kwanciyar hankali., Tunani barkatai ta dinga yi, zuciyart na saka da warwara inda ta ke ji zuciyarta na kara tsanar mijinta, domin duk sanda ta tuna da abunda ta gani a wayarsa. Sai ta ji gaba ɗaya ta tsanesa, ta tsani zama da shi. Ta na cikin wannan zancen zucin ne sai ga ƙararrawar kofa ta yi ƙara, da sauri ta mike ta na sauke ajiyar zuciya cikin hanzari ta buɗe kofar, Malama Khadija ce tsaye a bakin kofar. Bata an karaba kawai sai ta ji Hafsat ta faɗa jikinta tare da sake wani irin kuka. Sosai gabanta ya shiga bugu, fargaba ya risketa lokaci guda ta ruɗe, da kyar ta iya maida kofar ta rufe, cikin tashin hankali ta ce "Hafsat lafiya? Wai meke damun ki ne haka?". Cikin ruɗu da ta shin hankali ta jero mata waƴannan tambayoyin tana mai ƙoƙarin ɗago kafa ɗunta, sai dai ina Hafsat ta yi nisa bata jin kira kuka mai sauti take. Malama Khadija takai maƙura wajen ta shin hankali, hannu Hafsat ta kama suka ƙarasa falo. 

Hafsat bata yadda sun zauna a faloba har sanda suka shige bedroom, zama sukai bakin gado, har zuwa lokacin hawaye bai daina gudu kan fuskar Hafsat wanda da kyar ta samu ta tsaida su. Matsowa Hafsat ta yi ta na sharan kwalla ta haɗa hannunta dana Khadija, idanunta na fidda kwalla masu kuna da zafi, har zuwa lokacin gagara furta koda kalma ɗaya ta yi, sai sharan kwallar da take.


Khadija ganin lokaci na ja ya sa ta ce "Wai ni Hafsat me ya faru ne? Ki sanar da ni mana, amma kin zo kin sani a gaba kina kuka?". Duk wannan maganar da Khadija ta ke baisa Hafsat yin magana ba, sai kwalla kwai da ke zuba a idontan.


"Idan har kin san ba za ki yi magana ba, to ni kan zan tafi". Cewar Khadijah tana ƙoƙarin ta shi, da sauri Hafsat ta ƙara rikota cikin muryar kuka ta ce "Ki tsaya zan faɗa miki".


Shiru Khadija ta yi tare da zuba mata ido cike da tausayi ta ce "To ina jin ki, faɗi mai ya faru?".


Sa hannu Hafsat ta yi ta share kwallan dake zubo mata tare da gyara zamanta "Khadija a jiya na shiga wani tashin hankali wanda ya riskeni lokaci ɗaya".


"Subhanallah! Me ya faru?".


Ɗan shiru Hafsat ta yi domin har zuwa yanzu tana jin kuna abun a ranta, ware idanunta da suke lumshe ta yi, kwalla na sakko mata, da kyar bakinta ya iya furta "Wayar Abban Khairat na ɗauka!".


"Waya dai!" Cikin sauri Khadijah ta yi furucin tana mai dafe kirjinta, idanunta sun fito waje.


"Kwarai kuwa, Khadija wayar Abban Kharait na ɗauka wanda na jima ina bibiya sai jiya Allah ya sa na sameta, ina cikin binciken chart nasa na WhatsApp na tadda abunda ya ɗagamin hankali matuƙa, wayyo Allah na! Zuciyata na min kuna da raɗadi aduk sanda na tuna da wannan abun, wai ace mijina wanda ban ragesa da komai ba ya ke hira(chart) da mace a waya wai har ya ke ce mata, shi dai a sunan ya yi aure ne, amma ba yi da maraba da gwauro". Nan ta shiga bata labarin sauran hira masu muni data gani, wanda suka birkita mata tunani, daga karshe kuka ne ya kuɓce mata mai tsananin kunan rai. Cikin kukan ta shiga faɗin "Wallahi namiji bai da amana, Khadija namiji butulune, bayan nagi da idona na kuma karanta, amma wai shine zai zo ya dinga ban hakuri akan bazai ƙaraba, kiji rashin kunya irin ta maza. Ni Mus'af zai yi wa haka, ina matarsa ta suna". Fashewa da Kuka ta kuma yi tamkar wanda ranta zai fita, duk wanda ya ji sautin kukan sai ya tausaya mata.


Sororo Khadija ta yi tama rasa mai zata ce, gaba ɗaya abun ya rikece mata, ƙara matsuwa ta yi kusa da Hafsat tare da tallafo kafaɗunta cikin muryar lallashi mai nuna alamun tausayawa ta ce "Ki yi hakuri Hafsat". Tsagaita wa da kukan Hafsat ta yi idanunta na tsiyayar ruwan hawaye masu zafi ta ce "Khadija raina na ƙuna, ji nake kamar zuciyata zata fashe, aduk san da natuna, ban taɓa sanin haka halin Mus'af ya ke ba, wai ni Hafsat mijina ya ke chart irin wannan, harda hoton mace. Khadijah Mus'af ya sharyar dani ruwan mamaki matuƙa wanda ban taɓa zato zai min haka ba, zuciyata na kuna da raɗaɗi". Kare maganar ta yi tana mai dafe kirjinta, hawaye na ziraro mata. Khadija dai bata iya cewa komai ba sanda ta tabbatar da ta rarrashita ta hankali ta ya dawo jikinta ta nitsu waje guda sannan ta gyara zamanta, ta dubi Hafsat cike da mamaki ta ce "Tirka shi! tabbas abinda Mus'af ya yi bai kyauta ba, ya yi matuƙar ban mamaki, dole hankali ya tashi Hafsat". 


"Zuciyata na kuna na rasa yadda zan yi, khadija wai har ni Mus'af zai furtawa haka, bayan kusan shekarun takwas da auren mu, yara biyu, amma Mus'af ya buɗi baki ya faɗawa wata gardiya ƙatuwar mata, wai shi da sunan yana da aurene, amma bayi da maraba da gwauro! Tabbas namiji ya kai maƙura wajen iya butulci, dana ci karo da wannan kalaman kwalla jifa nai da wayar ta tarwatse". 


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!Hafsat abun na ku abin dubawane, to amma ke mai ya aike da ɗaukar  WaYAR MIJI?".


"Kamar ya Khadija?" Cikin rashin fahimta Hafsat tai maganar.


"Hafsat a wannan zamanin da muke ciki, mata bata ɗaukar WAYAR MIJI"


"Akan wani dalili zai sa mata bazata ɗau WAYAR MIJI ba, bayan mijin nata ne kuma ace kar ta ɗau waya?".


"Hafsat idan har mace na son zaman lafiya cikin gidan mijinta to ta guji ɗaukar WAYAR MIJI shine kawai, domin ɗaukar WAYAR MIJI bala'i ce mai gusar da farinciki da jindaɗin rayuwar aure, wanda kema sheda ce tunda kinga zahiri da idon ki".


Dogon numfashi Hafsat ta ja tana kara duban ƙawarta ta ce "Tabbas a bunda kika faɗi gaskiya ne, na kuma yadda sai dai kuma bazan iya daina ɗaukar WAYAR MIJI ba, idan har shi ba zai daina ba, ni ma bazan daina ɗauka ba".


Da kallon mamaki Khadija take bin ƙawarta dashi har ta gama maganar. Kama baki ta yi tana gyaɗa kai ta ce "A lalle Hafsat ki naso ki jawo wa kan ki masifa, da bakin ki ke furta baza ki iya daina ɗaukar WAYAR MIJI ba".


"Kwarai ma kuwa, ƙawata bazan iya dai nawa ba, don idan har nace bazan dauki WAYAR MIJI na yi bincike ba hankalin ba zai taɓa kwanciya ba, barin ma Abban Khairat dana fahimci mai ya ke aikatawa, ai dole naci gaba da bincikar wayar sa."


"Hafsat da zaki ji shawara da kin hakura da ɗaukar WAYAR MIJI, tunda kin fahimci abinda ya ke ciki sai ki guji ɗaukarta".

Girgiza kai Hafsat ta shiga yi hawaye na sakko mata ta shiga faɗin "Kai ina, Khadija idan har wannan ce shawara gaskiya ba zan iya ɗauka ba!".


"Ba zaki ɗau ba kika ce fa". Cewar Khadija cikin mamaki.


Tana kallon khadija ta ce "Kwarai ma kuwa, ke de ki naimo wata shawara amma badda wannan. Don  bazan ɗauke ta ba, haka kawai zan daina ɗaukar WAYAR MIJINA na yi bincike acikin 

ta, ni da WAYAR MIJINA abinda ma bazai yi wuba, don idan har na yi haka naƙara basa kofar ci gaba da abinda ya ke, don haka dole na ɗau waya na yi kuma bincike". 


"Ya salma!" Kalmar data fito daga bakin Khadija, don ta rasa ta ce wa domin ƙawarta ta yi nisa bata jin kira, tama rasa ta inda zata ɓullo mata tafahimci babban illace ɗaukar WAYAR MIJI.


Cikin nitsuwa ta furta "Hafsat binciken WAYAR MIJI ba shi zaisa ya daina abinda ya ke yi ba. Tunda ke kin ga da idon ki, ya kamata ki guji ɗaukar wayar".


"Ni bazan iya ba gaskiya, bincike wajibi, kuma yanzu na fara, zanga ni da shi wa zai gaji".


"Ok, tunda kika ce haka Allah ya zabar da abinda ya fi alkairi, amma bazan fasa baki shawara ki....."


Da sauri Hafsat ta tari bakin khadija batare data jira ta ƙarasa abunda zata faɗa ba, ɗaga mata hannu ta yi tare da cewa "Kin ga Khadija bana bukatar wannan shawarar ta ki, idan zaki canja ki canja kawai". Kare maganar ta yi tana mai share hawayen da suka sakko mata. Ci gaba ta yi da cewa "Bincikar WAYAR MIJI dole".


Sake baki khadija ta yi na tsantsar mamaki, girgiza kai ta yi azuciyata ta ce "Hafsat ina jiye miki wataran, domin WAYAR MIJI bala'i ce bincikarta". Sauke ajiyar zuciya ta yi tare da mikewa tana duban Hafsat ta ce "Tun da dai kince haka, nikam kinga tafiya domin banda wata shawar bayan wannan".


Hafsat itama mikewa ta yi tana gyara ɗan kwalinta ta ce "Idan har ranki ƴa ɓaci ki yi hakuri". A sanyaye ta kare maganar.


Murmushi khadija ta yi domin tasan za ai haka, don inda sabo ta saba da halin Hafsat "Ni kam bakomai Hafsat".


"Na gode" cewar Hafsat tana murmushi.


Ficewa falo sukai, har harabar gidan Hafsat ta yi mata rakiya inda ta bata abu abakar laida. Godiya khadija ta dinga har suka rabu.........✍️




Yawan comments

               👇

      Yawan typing ✍️



Zainab Ibrahim Gombe

09063406527

No comments