JAMI'IN DAN SANDA 5
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_5
...Kamar a mafarki yafara jin kukan Muneeba, da hanzari ya bude idonshi sannan ya tashi tsaye da k'yar , a Haka ya fito tsakar gidan yanajin kukanta har tsakkiyar zuciyarshi, ji yake kamar yaje ya shak'e wannan yarinyar Mai shegen shishshigin tsiya,
Truss yaja tsaya ganin Muneeba a hannun Inna tana Mata wanka Wanda akanshi ne take kukan , ajiyar zuciya ya sauke don harga Allah yaji dadin ganin Inna nayiwa Yar lelen tashi wanka , zamewa yayi a wajan ya zauna a hankali Yana sauke ajiyar zuciya , ido ya zuba masu har Inna tagama Yi Mata wankan sannan ta dauko madarar Shanu Mai dumi tafara Bata , Tasha sosai sannan ta dauko man shanu ta shafa Mata a matsayin mai,
jakar dake kusa da ita ta bude wadda ta kasance ta Hisham ce ta dauko Mata wasu riga da wando masu kauri ta Sanya mata sai ga Muneeba ta lafe ajikin Inna tana ajiyar zuciya tare bingirewa da dariya ,
Kallonsu kawai yakeyi cike da jin dadin ganin yarshi cikin farinciki, yanaso yace Inna tabashi ita Amma bakinshi yamashi nauyi , yanajin tunda wannan bala'in yafaru dasu maganarshi k'ayadadda ce Sam bayason yin magana ko Yaya ne ,
Sam Inna tabasan da zamanshi ba a wajan , Saida ta juyo sukayi ido hudu, Saida gaban Inna ya fad'i don harga Allah tsoron mutumin nan takeji , saidai ganin yau fuskarshi da d'an sassauci yasa tayi k'arfin halin cewa ,
"Akawo maka yarinyar ne "?
Kamar jira yake yace "eh" a hankali,
Inna zata tashi sukaga ta shigo Kamar an harbo kibiya , bata tsaya ko inaba sai inda Inna take , jikinta har rawa yake ta kar'bi Muneeba, sai washe baki take ganin yadda kayan suka k'ara fitowa da kyaun yarinyar, a hankali ta ce Mata
" *Bingel'am* sunan da take fadama Muneeba kenan ,
Inna dai sororo tayi tana kallonta kamun cikin harshen fillanci tace "je ki kaita wajan Babanta , ......
Kamun ma Inna ta rufe bakinta Hajar takai bak'in kofa tana Shirin fita take cewa bari nazo innata Zan nunawa kawayena ita ne,
Kasancewar duk da harshen fillanci sukayi magana yasa Hisham bai fahimci abunda suke cewa ba , Amma fa yacika yayi fam Kamar zai fashe idanunshi sun k'ank'ance tsabar bala'i sai huci yakeyi , Yana ganin yarinyar nan tayi bala'in Raina mashi hankali , to zaibar gidan nasu a yau din inyaso yaga ta inda zata sake ganin Muneeba ,wannan wace irin jaraba ce shida 'yarshi Amma ana Raina mashi hankali yakula kan yarinyar na rawa in batayi hankaliba sai yayi Mata saiti,
Tashi yayi da k'yar Yana taka k'afar a hankali yabi bayanta ,
Inna kuwa ganin yanayinshi yasa takasa Yi mashi magana don ita harga Allah tsoro yake ba , azuciyarta kuwa sai Allah Allah take kar yaje ya halaka Mata yarinya a banza don ta kula Sam baisan Kara ba , Ina laifin Hajar don tanuna k'aunarta ga 'yarshi , d'an tsaki tayi sannan ta tashi tafara ayukkanta duk da a k'asan ranta tunani take yadda za a kwashi Yan kallo tsakaninshi da Hajar , don tafi kowa sanin yarta da rigima akan yaran mutane ,
Duban duniya yayi Amma ko Mai kama da Hajar baigani ba , Kamar walk'iya ta 'bace mashi , dafe kanshi yayi cikin tsananin 'bacin Rai Nan take kanshi yafara ciyo Babu shiri ya Zame a wajan da yake ya zauna,Yana dafe da kanshi , jira kawai yake yaga ta inda wannan jarababbiyar yarinyar zata 'bullo ya kar'bi "yarsa ya k'ara gaba ,
Yajima awajan Amma shiru ba Hajar ba labarinta , a Haka Baffa yazo ya sameshi , da sauri ya k'arasa kusa dashi Yana cewa "
lafiya dai yaro mi kake anan "?
"Ba komai " yace da Baffah cikin hade gira don Sam baiso tsohon ya riskeshi ba yaso wannan yar banzar ta kawo mashi yarshi ya k'ara gaba , don yanajin nauyin Baffah sosai bazai iya tafiya a gabanshi ba ,
Kamashi Baffa yayi a hankali suka koma cikin gida , zaunar dashi yayi a tsakar gidan bisa wundi shima ya zauna Yana fuskantarshi, tuni Baffah ya karanci damuwarshi , yasan damuwarshi Bata wuce ta wannan yarinyar ko 'yarshi ce ko Kuma kanwarshi ce Allah masani, Amma dai kallo Daya zaka masu kaga tsantsar kamar da sukeyi da juna,
"Ina son ka gayamun sunaka, Baffa ya fad'a yana kallonshi,
"Sunana Hisham"
"To malam Hisham inason ka daukeni a matsayin mahafi ko wani abokin shawara ,in bazan takuraka ba ko Zan iya sanin abunda ya faru daku da rahuwarku,? Saboda na fuskanci kana cikin tsananin damuwa tareda k'unar zuciya , Ina kallon tsantsar tashin hankali da son cigaba da rayuwa acikin k'wayar idanunka , to koma dai minene Ni wannan yarinyar ita nake tausayi bansan abunda ya raboku da garinkuba kuka zo Nan Amma tabbas akwai matsala don zakasa rayuwar wannan yarinyar a garari , duk da bansan ya take a wajanka ba Amma dai kallo Daya na Mata nasan cewa jininka ce ,to Amma abun tambaya anan shine *Ina mahaifiyarta take*?? Mi ya faru dakai da har ka dauko wannan jinjirar ka rabota da mahaifiyarta, kayi hkr in na fada maka abunda baimaka dadi ba ,Sam banso shiga sabgarka ba to Amma abun Yana dauremun Kai kullum tambaya anan shine to ina mahaifiyar yarinyar nan take
Tunda Baffah yafara magana ya sunkuyar da kanshi tuni idonshi suka yi jajir yayinda jijiyoyin jikinshi dana kanshi suka tashi har wani rawa rawa naman fuskarshi keyi tsabar bacin rai tare da k'unar da yakeji a zuciyarshi ,
A hankali ya d'ago da kanshi ya dubi Baffa cikin wani irin yanayi yace,
"Kayi hak'uri , kuma yau zamu tafi naji sauk'i"
Zuba mashi ido Baffah yayi yana nazarinshi , haka kawai yakeji k'aunar yaron tareda tausayinshi , yasan koma minene ya raboshi da gida to ba k'aramun abu bane, nisawa Baffah yayi yace,
"Ka gayamun abu d'aya , shine inason insan matsayin wannan yarinyar a wajanka "
" *'ya ta ce Baffah"* a hankali kamar mai koyon magana ya fada kanshi a k'asa
" to shikenan Allah ya rayata akan sunna yayiwa rayuwarta albarka
a hankali ya furta "amin" tareda jin wata irin soyayyar dattijon,
Shirune ya ratsa wajan na dan wani lokaci kamun Baffah ya nisa yace ,
"Amma miyasa kakeso tafiya ne , ko akwai inda zakaje ? Sannan har yanzu baka gama warkewa gaba daya ba ko akwai abunda ake maka wanda bakajin dadi ne anan, ?
"Aa Baffah Kawai dai inason tafiya ne"
"To akwai inda ka nufa ne daga nan?"
A hankaki ya girgiza kanshi
Ajiyar zuciya Baffa ya sauke cike da tausayin wannan bawan Allah yace ,
" ina neman alfarmar da ka zauna anan na d'an wani lokaci saboda yarinyar nan karkayi sanadin rasa rayuwarta, in ka nausa wannan jejin bakasan iya inda zai kaika ba , jejine mai matukar girma da fadi da babu kamarshi anan Nigeria Sannan dajine da yake da matuk'ar had'ari mu kanmu ba abanza muke zaune anan ba , duk dama kowane lokaci zamu iyayin hijira daga wannan nahiyar zuwa wata nahiyar kasancewarmu fulanin yawo bamuda takamammen wajan zama , Yanzu lokacin da macijin ya sareka itama k'iris ya rage ya sareta Allah ya kawo Hajar ita ce ta kashe macijin kaga da bamusan abunda zai faru ba karkaci gaba da tafiya a haka kar kasamu kanka a inda bazaka iya kare kanka ba ma bare kuma wannan yarinyar,
Ina Neman alfarmar ka zauna anan na wani lokaci har yarinyarka ta k'ara wayo kaga a yanzu bata shan komai sai madara , zaka wahalar da rayuwarta in kaci gaba da tafiya da ita a haka koma ka rasata baki d'aya tunda bata iyacin komaiba ,
Akwai fili anan bayan gidan nan zansa amaka bukka anan saiku zauna , kamun muga abunda Allah zaiyi , don Allah karkacemun aa,
****************************
Tafiya take cikin sauri tana waiwaye tana sanye da bak'ar abaya da bak'i hijab fuskarta sanye da nik'ab yayinda hannayenta da kafafunta ke sanye da safa , abakin wani dan madaidaicin gida ta tsaya tareda ciro wayarta ta kira matar gidan , ba a jimaba kuwa aka bud'e mata k'ofar ta shiga,
Matar gidan na gaba itakuma tana bayanta har suka k'arasa falon gidan , zama sukayi akan kujerun dake falon ,
Sauke ajiyar zuciya matar tayi tareda cewa "wash Allah yau na gaji da yawa wallahi ,tayi maganar tana cire nik'abin fuskarta,
Hmmmm aike kikaji zaki iya ,wallahi Asmy yakamata ki rabu da wannan cess din hakanan tun kema ba a sanwaltar da rayuwarki ba , mutumin nan dai ko k'anen ubanki ne yakamata ace kin shafawa kanki lafiya hakanan tunda abun yafi karfinki,
Ta shi wadda aka kira da Asmy tayi tsaye ta cire hijab tareda abayar dake kijinta abun mamaki sai ga kayan *'yan sanda* sun bayyana ajikinta, firij ta nufa ta dauko lemu ta bude murfin ta kafa kanta ta shanyeshi tass sannan tayi jifa da goran , jakar da tashigo da ita ta dauko ta bude ta fito da laptop ta bude tafara danne-danne aciki ,
Tsakin maigidan tayi tace kefa tsiyata dake kenan tsabar iskanci mutum yana maki magana zakiyi banza dashi,
Nisawa Asmy tayi tace
"Hmmm Humaira bazaki gane bane , saifa nasan yadda akayi *yalla'bai* ya rasa ransa tabbas bazan saurara ba har sai nasamu gaskiyar abunda nakeson na sani koda kuwa nima zan rasa raina ne,
"Abunda nake nuna maki Asmy bakida k'arfi da ikon da zakija da mutanen nan , bance karkiyi bincikeba amma tunda kin gano abun yafi karfinki to yakamata kibarwa Allah komai tunda bazaki iya komai ba , "
"Aa Humaira zan jajirce inaji a jikina zanyi nasara , idan har dukkanmu zamuja bakinmu muyi shiru to tabbas bamuyiwa yallabai adalci ba , mutum jajirtacce mai aiki da dukkan gaskiya da rikon amana wanda samun irinshi yanada matukar wahala a yanzu , mutum ne da bashida tsoro ko kad'an wannan yasa ya jajirce don ganin mutane sun samu zaman lafiya wanda alokacinsa ne duk wani tantiri ya shafawa kansa lafiya , amma yanzu kiduba kika cikin lokaci kankani abubuwa da yawa sun canza yanayin tsaro da doka dakomai ya canza , tabbas munyi rashin *Jami'i* na kwarai 😢tayi maganar cike da damuwa da bakinciki,
Wayarta ta dauko takira wata number , hello Jabir ya ake ciki,?
Daga can 'bangaren Ya amsa da cewa ,
"Madam har yanzu ina kan bincike amma har yau bansamu wata alama da zata warwarema zare da abawa ba, "
Dan Jimm tayi sannan tace " to shikenan kaci gaba da sa ido sannan ban yarda da kowa ba duk abunda zakayi kayi acikin sirri,"
"To shikenan Madam ko mi ake ciki zan kiraki,
"Aa Jabir ban yarda da kira ba ni zan kiraka in bukatar hakan ta taso "
"Yes ma"
Daga haka sukayi sallama itakuma taci gaba da dannar laptop dinta,
**************************
Innalillahi wa inna ilaihin raji'un don Allah Malam ka cire damuwar mariya a ranka Shin da wanne kakeson muji da rashin mariya ko da wannan ciyon da yake damunka , sanin kankane wanda ya mutu bazai dawo ba zaluncine anriga an zaluncemu ba abunda muka iya saidai mu barwa Allah,
Tari yake sosai da kyar yasamu ya lafa mashi , yana sauke numfashi ,gefenshi kuma sulaiman ne da Hadiza sai shemau wadda itace k'arama a gidan ,
Cikin galabaita yafara magana yana cewa
" doli in damu Inno sun cuceni sun kashemun 'yata da banida kamarta sun rabani da farincikina ,yarinya mai nutsuwa da ladabi da biyayya , mutuwarta ba shine abunda yake tayarmun da hankali ba kamar sanadin mutuwar tata , saboda zalunci suka rink'a yi mata *fyade* har sukayi ajalinta wannan wane irin rashin imani ne, bazan ta'ba yafe masu ba , kullum burinta tayi karatu mai zurfi amma yanzu sunyi sanadin mutuwarta ba tareda ta cika burinta ba ya karashe maganar yana zubar da hawaye duka yaran kuka sukeyi to bare kuma inno ,
Tunda suka rasa mariya sukayi k'aura da farinciki duk da ba mutuwar ke k'ona masu raiba sai sanadin mutuwar,............✍🏼
*Rashin comment dinku zaisa in ajiye book din nan gsky bana bukatar stecker ko tnx comment kawai nakeso inba hakaba zan ajiye don inada aikinyi zanbata awa ukku ko hudu inyi typing amma bazaku iya bata minti biyar ba kuyi mun comment*🤔🤔🤔
*KI KARANTA ZAKI KARU SIRRIN HUNTU KO NACE GONGOLI*
🅱️abbar ciyawar maganin gargajiya daga yankin kudu masu yamma na yankin afurka musamman kasashen renon kasar faransa, haka zalika wannan magani daya shahara a kowanne fanni musamman wajen tsaftace gaban mace kamar mejego wanda take bukatar kamshin gaba idan kuma matsi akeso ana hadashi da gabaruwa da saiwar kalgo ana tafasawa ana zama acikin ruwan, wannan ya inganta a bangaren maganin gargajiya tun ba yauba, asalin sunansa kuma da yaren faransa GONGOLI
🅱️ayanin yanda yake warkarda cututtukan gaban mace kuma ana aiki dashi da lemon tsami da ganyen gwaiba shine ake jikasu su jika sosai ana tsarki da ruwan, baya bari wata cuta ta shiga gaban mace, wannan koda mace tanada abokan zama masu daukeda ciwon sanyi bazai shiga jikintaba domin akwai babbar garkuwa a tattare da wadannan magungunan wanda haryanzu an tabbatar basu da wani illah ga lafiya matukar aka kiyaye aiki dasu,
🅱️angaren shahara da yayi kuma a yanzu ya zagaya duniya ta yanda wadanda basu dashi ayanzu ya iskesu, harma yanzu ana amfani dashi kadai dinsa ta hanyar jikashi da ruwa anasha domin riga kafin kamuwa da cututtuka maza harda mata
🅱️ayan wannan ana hada maganin samun ni,ima dashi, da wanke mara yanda ake ana tafasa shi da zobo da kanunfari idan ya tafasa atace ruwan asaka Zuma ko mazar kwaila anasha.
*KU TAYA YARONA ASLAM DA ADDU'A YAU YA K'ONE DA RUWAN ZAFI*😭😭😭😭😭😭😭😭
No comments