Breaking News

TSANGAYAR MALAM 5-6

 _*‍👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️TSANGAYAR👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️*_

                  _(Malam)_

                       *Na*

_Maman Dr_

                5️⃣-6️⃣

Yan zun ma daga makewayin yadikko ta fito ta nufi chan gindin bishiyar mangwaro dake tsakiyar gidan ta zuɓe a ƙasa kanta na jingine da jikin bishiyar sai zare ido take tana ya mutsa fuska da alama cikin ta ke karta mata.

           A sittin wa saba'una Addah ta keto ƙafafun ta har harɗewa suke da junna dan sauri zanni a hannu ta faɗa bayi dai dai lokacin cikin yadikko ya kuma bada,"ƙuuuuuuuur,yadikkon ka ta miƙe a fusace ta zari butar data dangwarar a ƙasa sai hanyar banɗaki,gam gam garammmm yadikko ta shiga kokowa da ƙyauren ƙofar bayi Addah na ji ta fara.


"Ummmm'ummmm.


      jin yadikko bata da niyar dena kokowa da ƙofar yasa dole sai da Addah ta ce.


"Wai ni kam," wake ta nan gun,to mutum ne a shiki.


Duk maganar da Addah asma'u ke yi sam kunnuwan yadikko basu jiye mata ba tsabar ciwon ciki sai ma salati da buntsire buntsire da take tana ƙara buntsaro mazaunan nata baya a dai dai lokacin wani zawo ya taho wa addah bata san san da ta saki nishi da ƙarfi ba haɗe da cewa"


"Washiii aradu fitar zawo akwai shi da daɗi karaf a kunan yadikko da ta fara gudawarta a zanni,nan da nan wajan ya ɗauki wari ita kanta yadikkon toshe hancin ta,ta yi a lokacin ta tabbatar da tayi zawon ta a jiki,nan da nan ta saki jiki ta fara shatata abinta da mafi yawanci ma iska ce ke fita sai jifa jifan zawon wasu mutane su uku suka shigo da mutum a hannu yana"


"Wayyo Allah"wayyo cikina gashi nan gashi nan tahowa wayyo zai taho wayyo yama taho abun sa,kamar sabon kamu malam musa yake ihu da burgima a ƙasa riƙe da cikin sa dan tun da mutanan nan suka dire shi suka juya da gudu jin gidan na wani irin ƙamshin da in ka shaƙa kamar mutum yayi amai.


      Addah asma',u ce ta fito daga bayin jin ihun mutum kamar malam hancin ta yadaki wani shahararran ƙamshi daya sa hankalin ta ya kai kan yadikko da ke zaune daram a ƙasa ƙuda na binta ta ko ina sai ƙifta ido take tana mis mis da baki kamar me biyan karatu bata ma san Addah asma'u na wajan ba sai nishi take tana mis mis mis,ni shin malam musa ya kuma ɗauke hankalin Addah salati ta saki ko ƙarasawa batayi ba cikin ta ya kuma ƙarta mata ba shiri Addah ta koma bayi a guje tana nishi da ƙyar dan yanzu zawon ma yaƙi fitowa taji daɗi ga murɗawar da cikin ta yake yi.


      "Daga zaure zuwa ƙofar gidan ba ƙaramun bil adama aka tara ba daga wajen ko ina kana iya jiyo ihu da salatin yadikko da malam musa sai jifa jifa muryar Addah asma'u ke fita tana"" ataimako muni aradu shikena zai rabe"", yara da manya mata da maza duk an chake ana shawarar yanda za'a ɓullowa lamarin duba da gidan kansa ɗoyi yake bari su kan su masu zawon da ba ƙaramun namijin ƙoƙari mutum zai iya yi ya doshi inda suke ba a kai musu agaji,sale dake tsaye ya ce".


"A gaji a ina ai waɗannan bayin Allah shakatafin chan kaɗai za a miƙa su asamu sassauce dan Allah asibiti ne kaɗai zai iya da lamarin su abun nasu fa babba ne mu kammu da muke tsaye iska na yayimo warin yana bugar mu a cikin tsaka me wuya muke.


"Allah sule.



"Na rantse maka da Allah gali muma muna ruwa tsundum wai ni ba'ance wannan cutar ta ƙasar fararen fata da zawo take fara bayana daga cikin alamun ta ba.


Kai haba dai shima zawon yana daga cikin alamomin ta ne,sanar damu da wuri kafin taci ƙarfin mu,kusan mutum goma suka haɗa baki suka faɗa kowane na zara ido sule ya ƙara gyara tsaiwar sa ya ce"


To ko jiya sai da naji a radio ta burni wasu sun kamu ta hanyar shaƙar iskar zawo ina ji su malam musu sun shaƙa,bana ɗayan biyu kusan rabi da kwatar jama'ar dake wajan sun cika wandon su da iska sun fece babu kowa a ƙofar gidan gali shi yayi namijin ƙoƙari ya garzaya a guje inda Nafi'u ke zaman jiran shago ya shaida masa halin da ake ciki,kafin Nafi'un ya nufo gida sai da yafara zuwa ta wajan yaya manu ya shaida masa,yaya manu ya ƙwaɓe baki ya ce"


"Ban shirya mutuwa yanzu ba Nafi'u da saura na,babu inda zanje tunda kwarfin'19 ɗin tayi musu mugun kamu abarsu ka wai su wuce sun tafi a sa'a tunda duk da azumin su a baki.


"'haba yaya manu babane fa dan Allah ka taimaka mun muje mu kai su asibiti.


Na rantse da Allah ko buba ne babu inda zani ince har da yadikko a cikin gidan banje dan ita ba sai wani musu da yake yayana ya daɗe bai mutu ba ai bani na ɗora musu ba tsakanina da su du'a'i kowa na son ransa Nafi'u guda ɗaya ne kachal idan ka rasa shi,shikenan kuma tun da tasu ta ƙare ba sai a barsu su ƙarata chan ba kai kaji yaro da ganganci kai ma kayi ta kanka ba sani ko sabo wannan abar take da shi ba.


Idanun Nafi'u ne suka kaɗa sukayi jajir ya miƙe cikin sauri ya nufi hanyar gidan su da duk wanda yaga Nafi'u a hanya gudu yake ya kauce yana ƙoƙarin toshe hanci har ya shiga gidan bayan ya toshe hancinsa da hannu tsabar warin daya ke bugarsa har yunƙurin amai ya somayi a haka ya daure ya ƙarasa cikin gidan yaga yanda kowane ya fita daga hayyacin sa gasu cikin kashi dumu dumu,a guje Nafi'u ya fito yana kuka neman motar da zata kwashe su zuwa asibiti.


Duk wani me akori kura sam yaƙi yadda ya ɗauki su yadikko har masu babur ɗin ma lamarin da ya zagaya ko ina a garin gidan malam musa sun kamu da kwarfin'19 a cewar ƴan garin kowa ka gan shi hancinsa a toshe hunnuwan kuma duk sun sanƙame su da safa wasu ko ledar suka maka tafi biyar gudun ɗaukar cutta,a ƙarshe dai da ƙyar Nafi'u ya samo kurar ruwa da sharaɗi me tsaure akan sai ya wanke ta sau talatin da omo guda sitin ya kuma bada rabin kuɗin kurar Nafi',u ya amince da hakan ya nufo gida a guje yana hawaye..........





 _*A nan zan gintse inda Comments/Share*_

No comments