JAMI'IN DAN SANDA 6
👨🏻🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻🔧
🅿️_6
............"Alhajifa akwai matsala wallahi gaba daya narasa gane kan yarinyar nan , yanzu fa kwana ukku kenan ko ruwa bata sha ba numfashima nema yake ya gagareta , tayi maganar tana zubar da hawaye ".....
Zaune yake akan kujera gaba daya Ya had'a d'an k'aramun gajimare a wajan ,saboda tabar da yake ta zuk'a tun d'azu tada k'are zai kunna wata, ita kanta momy dauriya kawai takeyi amma gaba daya hayak'in ya dameta, ganin duk maganar da take bai kulataba yasa ta fashe da kuka tana cewa,
"Haba alhaji kanajina fa amma kayi shiru yarinyar nan ita kad'ai muke da ita a yanzu zamu iya rasata a kowane lokaci sannan.......... "Wata uwar tsawa ya daka mata wadda saida ta zabura , idanunshi da suka rine sukayi jajir ya zubamata yana mata wani shegen kallo na nuna tsantsar takaincinshi akanta,
"Waini Hindatu mi kikeso namaki ne da kike zancan Amna, ta mutu mana , d'ana mafi soyuwa a gareni ya mutu ma na hakura bare wata Amna , kina ganin saboda wani banzan bori nata zan kasa aikata abunda ya dace ne wallahi koke da kika haifi Zayyan kika mashi irin wannan abun irin hukuncin da zan maki kenan bare wasu banzaye ,
In taga dama ta ware in bata ganiba kanta , ba wanda zai mutu a yanzu ya dameni tunda har narasa Zayyan yayi maganar wasu zafafan hawaye na sauko mashi ,"
a zuciye ya tashi ya shige bedroom dinshi , yana shiga dakin ya zubawa wani makeken photon wani kyakyawan saurayi ido , saurayin yana sanye da k'ananan kaya irin masu matse mutum din nan , ya kafa wata shegiyar hula irin ta gayu yayinda ya zazzago wandonshi k'asa sosai irin dai wanda gayu ke yayi , wuyanshi sanye da sarkar gold hakan ma kunneshi manne da dan kunne irin wanda gayu maza ke sawa sai katon galss din da yakusa mamaye Rabin fuskarshi , photon kato ne kamar ka kira shi ya amsa , akalla sai da ya shafe awa daya a wajan yana kallon hoton tareda cin burika kala kala gefe daya kuma hawayene ke mashi zuba kamar anbude famfo,
Tashi momy tayi dakyar tabar falon zuciyarta kamar zata fashe yanzu in tarasa Amna ya zatayi da rayuwarta, su biyu kawai take dasu a duniya gashi ta rasa babban d'anta a sakamakon azzalumin mijinta wanda baisan komaiba sai zalunci , yanzu kuma ga halin da tilon 'yarta take ciki wanda batajin zata ta'ba yafe masa matuk'ar ta rasata,
dakin Amna ta nufa yadda ta barta haka ta sameta , tana kwance tazubama silin ido yayinda hawaye ke mata zuba ga kuma numfashinta da yake sama da k'asa kamar zata shid'e
Zama tayi kusa da ita ta dafa kanta tace ,
"Kiyi hakuri Amna ki kwantar da hankakinki insha Allah ko zan rasa raina sai sama maki farinkinki , nasan bamu kyauta ba ,munbi son zuciya gashi reshe ya juye da mujiya inason ki kwantar da hankalinki insha Allah zamu samu mafita don inaji ajikina nima yana raye kamar yadda kike fad'a,"
A hankali ta d'ago da kanta takalli momy tace "kinyi alk'awari momy??"
"Eh Amna namaki Alkawari don nagane ubanki bashida imani bashida tausayi to daga yau na dawo daga rakkiyarshi , zan tayaki bincike har allah yasa mudace ,"
Cikin matukar murna da farinciki Amna takama hannuwan momy ta rik'e gam tana zubar da hawaye yayinda fuskarta ke dauke da murmushin jin dadi , saidai takasa cewa komai don sam batada kuzarin da zata iya wata magana,
DA haka mommy tasamu ta lalla'bata ta yarda zata kaita asibiti, jikin momy har rawa yakeyi ta dauko wayarta takira daya daga cikin direbobin gidan don yazo ya kaisu asibiti, haka kuwa akayi wata tsadaddiyar asibiti sukaje inda dama acan suke zuwa ,
Ba 'bata lokaci ba likitoci suka rufu akanta tunda dama sun santa ,bayan sungama dubata sunmata duk abunda ya dacene suka bata gado suka daura mata drip da allurai sannan suka tafi ba a dauki lokaciba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita saboda alluran da akamata bayan sun gano bata samu isashen bacci,
Momy kuwa tana zaune tazuba mata ido tana kallonta yayinda zuciyarta ke tuhumarta akan alkawarin da tayiwa yar tata ta ina zata samu wanda yariga da ya mutu????🤔
*************************
A hankali ya furta "to shikenan Baffah nagode sosai Allah yasa hakan shine alkairi, Allah kuma yasaka maku da mafificin alkhairi,
Cike da farinciki Baffah yace "Amin amin Hisham naji dadin amincewarka , Allah yagani inajinka kamar d'an uwana , ina jin tausayinka sosai ganin irin halin da kake ciki duk da bansan abunda yake damunka ba amma nasan ba k'aramun abu bane zai raboka da gida da wannan jaririyar , bazan matsamaka don ka gayamun damuwarka ba Duk da inason jin damuwar taka, amma Duk lokacin da kaga yakamata ka sanar dani to ina maraba watak'ila bazan rasa taimakon da zan maka ba,
Yanzu zan tafi daji akwai magungunan da nakeson debowa zansa Habu da halliru su hada maka taka bukkar anan filin dake waje,
"To shikenan Baffah nagode sosai , "
Nan Baffah yamasu sallama ya fita ,
Inna dai na gefe tana wanki tana kuma sauraron maganar da sukeyi , itadai batajin dadin wannan hukunci na Baffah ba don wannan mutumin da gani zaiyi wuyar zama gashi kullum cikin muzurai kamar zaici babu , ita kam harga Allah tsoronshi takeji, sai dai fa itama tana son wannan 'yar tashi yara na burgeta sosai kasancewar tajima rabonta da haiguwa tun daga Hajar gashi har Hajar ta girma,
Shikam tuni ya lula duniyar tunani , yanajin zazzak'ar muryarta na dawo mashi cikin kunne , *" aa Hisham barin wannan aikin zaifi zama alkhairi a garemu saboda zaka iya sanya 'yan k'asa a cikin farinciki amma bazaka iya sanya ahalinka ba , zaka iya bada kariya ga mutanen k'asar nan amma bazaka iya bada kariya ga ahalinka ba Hisham*
Dariyar da Muneeba da hajar ke k'yalkyatawa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yashiga , a hankali ya dago da idonshi da suke fitar da wani irin yaji saboda tananin 'bacin rai ya zuba masu,
Ido hudu sukayi da Hajar aikuwa tuni tasha jinin jikinta nan da nan jikinta yafara rawa ganin wani birkitaccen kallo da yake mata, a hankali cikin tsoro tafara daga k'afarta tana nufar inda yake zaune ,
Har k'asa ta duk'a cikin rawar murya tace *"sannu Hamma* baice mata komai ba sai kallonta da yakeyi ,
Wasu yawu ta had'iye duk a zataonta fushinsa akanta ne a hankali ta ajiye muneeba a kusa dashi tace "gata Hamma dama najene na nunawa k'awayena 'ya ta" to to to shine yanzu nace bari na kawo maka ita ,tayi maganar.a tsorace sai faman k'yafk'yafta mayan idaunta masu kamar madara take,
Kallon mamaki yamata ,yana mamkin karfin halinta wai 'yar ta , bai kulata ba ya dauki muneeba ya tashi da kyar yanufi waje da ita,
Kamar wata zararra haka ta tashi tabi bayanshi cikin in ina tace Ham..mah..ina zakaje da ..ita,?
Juyowa yayi ya kalleta da rinannun idanunshi wanda babu shiri taja baya a tsorace ,baice mata komai ba yajuya yayi tafiyarshi,
zata koma binshi taji an rik'e mata hannu, juyowa tayi don ganin wanda ya rik'eta , ganin Inna tayi ranta a 'bace cikin harshen fillanci tace ,
"Wai ke hajar miyasa bakida hankali ne , ina ruwanki da inda zai kaita yarki ce ko yarshi , kincika shishigi wallahi ina jiye maki ranar da zai gaji da halinki don wannan da ganinshi bashida sauk'i ,"
"nidai innarmu ki bari nadubashi kar ya gudu da yarinyar " tayi maganar kamar zata fashe da kuka,
Cikin takaici inna tace to wallahi ba inda zakije maza ki koma ki zauna Allah yasama yayi tafiyar tashi inga yadda zakiyi,
Haka Hajar ta juya ta koma tana hawaye don gani take kamar Hisham dauke mata yarta zaiyi ya gudu (karfin hali 'barawo da sallama🤣)
Hisham kam can karkashin Wata babbar bishiyar gamji ya samu waje ya zauna yana yiwa 'yarshi wasa ganin yadda take dariya kadai ya sanyashi farinciki kadan kadan yakejin nauyin da zuciyarshi tayi mashi yana raguwa wannan dalilin yasa sam bayason yayi nesa da yar tashi ,don kallonta ne kadai ke sanyaya zuciyarshi a yanzu, yajima sosai a wajan kamun yakoma gidan Baffa wanda zuwa lokacin Hajar kuka take sosai gashi Inna ta hanata fita ,aikuwa tanajin sallamarshi Ta kwasa a guje taje ta babbanbare muneeba a jikinshi wadda tajima dayin bacci , bata ko kalleshiba ta shige cikin bukkarsu da munneba ,
🤦🏻♀️dafe kanshi yayi irin ta dameshi din nan kamun yayi tsaki ya gayar da Inna sannan ya shige cikin bukkar Baffa wanda anan ne suka saukeshi.
*Washe gari*
Kamar yadda Baffa yace haka akayi Habu da Halliru harma da wasu daga cikn abokansu sani da sule suka had'a ma Hisham yar bukkarshi , acan filin dake bayansu kadan , bukkar ba a cikin gidan take ba hasalima akwai yar tazara tsakanin gidan na Baffah da inda bukkar shi take saidai suna hangen juna kasancewar wajan filine fetal,
Bayan sun gama komai ne suka sanya mashi gadon kara aciki sannan suka kwashe yan kayanshi suka kai mashi can tare da tarkacen maganinshi da yakesha , Inna kuma tabada wani zanen sak'i suka sanya mashi abakin k'ofa akayi labule dashi,
Bayan dawowar Baffa yaduba aikin yaga sunyi komai yadda ya kamata ,sai ya umurci Hisham da ya dawo nan da zama,
Sam Hisham bai yarda yabar 'yarshi ba tare da ita ya koma bukkar ,
Kwance yake akan gadon karan dake bukkar yana k'arama wajan kallo wasu hawaye masu zafi suka zubomashi yayinda gefe daya kuma yake murmushi wanda har saida gefen kumatunsa suka lotsa , mamaki yakeyi wai yau shine acikin irin wannan wajan a matsayin humallinshi lallai duk wanda baiji tsoron Allah ba yayi aikin Banza , ko a mafarki bai ta'ba tunanin yin wannan rayuwarba , lallai Allah mai hikima ne Allah ne kadai yasan abunda yake nufi da hakan , fatanshi daya Allah ya kare mashi 'yarshi daga idanun mak'iya masu son ganin bayanta, haka yayi ta tunane tunanen rayuwa da irin sauyin da tazo mashi dashi cikin k'ank'anin lokaci, ya rasa komai ya rasa kowa ,
Sannu a hankali rayuwa tana tafiya komai yana sauyawa , yanzu Hisham. watansa Ukku a garin su Hajar tuni yaji saukin k'afarshi Muneeba kuma tak'ara wayo sosai yanzu watanta shida har tana rarrafe , kuma har wannan lokacin Inna ke kula da duk wasu hidindinmunta iyakar Hisham agyarata a kawo mashi a wajanshi take wuni amma a wajan inna take kwana tun bayaso har doli ya hak'ura , don ko bai kaitaba sai wannan mayyar ta faki idonshi ta lalla'bo ta d'auketa ,...................✍🏼
*Pls ina bukatar comment inkuma book din baya maku dadine ku fada sa a sauya da wani amma rashin comment zai iya zama sanadin rashin post akan lkc*
*karki wuce baki karantaba*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
🅱️abu sama da yajin 'ya'yan citta a duk wani yajin maza da ake da 'ya'yan itatuwa, yanda yajin keda zafi haka namiji keda zunzurutun zafin sha'awa da jurewa saduwa na tsawon lokaci me yawa, haka zalika yajin 'ya'yan citta shine hade da itatuwan gargajiya mafi girma amaganin maza a kasar hausa wanda dai ake kira yaji, shine kuma ake kira (ginger seed) ku bincikashi, mun taba kawo muku abaya, anasha da shayi babu madara sannan kuma anasha lokacinda ake gida kamar bayan magriba, sannan yanda ake shansa kuma rabin cokali babba, bayan haka kuma koda mutum bayada aure zai iyasha, amma mazane zallah banda mata.
🅰️ana samun garin 'ya'yan citta, da dan kamaru, sai ginsine, da kwallon dabino, sai namijin goro, da farin gagai, sassaken marke, wadannan ana hadasu waje daya ayi garinsu, sai a tankade sosai shikenan an kammala hadashi,
No comments