Breaking News

RAYUWAR BALKISU 5

Rayuwar Bilkisu

Part two

FREE BOOK

By

Nafeesat m.aliyu

(Feenah).

INTELLIGENT WRITER......

Juma'at Mubarak "yan uwa musulmi Rabbi ya maimaita mana,ya sadamu da alkhairan dake cikin wannan rana.ameen

Bissimillahir rahmanir rahim

♦️♦️♦️ page 5

Ta Dade zaune a falon yayinda zuciyarta ke sake sake daban daban game da abunda ya addabi zuciyarta da rayuwarta ahalin yanzu,sosai dare ya tsala  tana nan zaune ganin dai lokaci na tafiya ga bacci dake kawo mata farauta tana kwacewa ya sata tashi dole domin batada zabinda ya wuce mata hakan dukda tasan yin baccin cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba Abu bane mai sauqi.




Direct bedroom dinta tanufa yayinda wata zuciyar ke raya mata taleqa bedroom d'in nasa amma ina bazata nemeshi ba tunda shima ya manta da ita kulawar datake samuma daga gareshi ya dena duk asanadin wannan jarababban auren daya kafe sai yayi babu irin magiyar dabata masa ba da kuka akan ya hakura da hakan amma ya nuna tamkar bema san metakeyi ba.




Handle din kofar bedroom d'in nata tariqe tare da turawa tashiga yayinda tasa azuciyarta tabbas saita dau mataki.



Da wannan tunani ta kwanta kala kala har bacci yayi nasarar dauketa.



**

Washe gari



Sosai naji Dadin jikina sosai harma Dan zazzabi Dana kwanta dashi babu,tunda nayi sallah Umma tace nakoma na kwanta hakan kwa akayi,bani nafarka ba sai wajen 10:00am farkawata kuwa yayi daidai da shigowar Umma dakin,cike da kulawa Hajiya sauda ta kalli Bilkisu.




Tare da fad'in"Bilkisu kin tashi"Hajiya sauda ta fada cikin sakin fuska yayin da idanunta ke kan Bilkisu.



"Eh Umma na tashi"ta karashe maganar cike da sanyin murya"tom jeki wanka maza kizo kiyi breakfast gashi cen tun dazu yana jiranki"cikin girmamawa Bilkisu ta amsa tare da nufar toilet din cikin sanyinta.



***

11:00am

Muka hallara a bangaren Hajiya Kaka bisa umarninta,gaba dayan mu muna zaune bisa lallausan carpet din dake malale a tsakar falon,gyaran murya hajiya Kaka tayi bayan gaisheta da Surayya da Bilkisu harma da Dr......✍🏻



Pls kuyi manage da wannan zakujini gobe insha Allah.


More comment more typing✍🏻



Rabbi yasa mudace ameen🤲🏻

No comments