RAGGON MIJI 31-35
3⃣1⃣
*Bismillahirrahmanirrahim*
*fans inajin
dadin comments dinku, naga yadda ku ka caccaki faseelat 😂,kusani faseelat yarinya ce ,kuma dan adam ajizine
kuyi mata uzuri mana inafatan zaku cigaba da biyoni dan jin cigaban labarin*
Yayinda
itakuma ta sunkuyar da kai kasa, ashe duk abinta na chart ne kawai yanzu gashi
ta ganshi takasa komi, gabadaya ya mata kwarjini bata kara sanin shi kyakykyawa
bane se yanzu data ganshi face to face.
Shi ko
kallonta ya cigaba da yi, yeah she's that girl to mi yakawota nan? yake
tambayar kanshi yana cigaba da kallonta tayi mai kyau sosai ba abunda yakara
burgeshi se shigarta in long hijab,
Zuwa can ya
dauke ido ya cigaba da aiki a system dinshi,
Faseelat
kamar kwai ya fashe mata aciki taja kafa taje ta samu wuri ta zauna, ta dan
saci kallonshi yana ta aikinshi hankali kwance, siririn hancinshi da dan
karamin bakinshi lebunansa pink color
ga abinda take mutuwar so sajen shi a kwance yana sheki,
Ta dauke ido
ta hadiyi miyau tana matse kafa, shiru 2mnt bawanda yayi magana cikin jarumta
irin tata tace "ina wuni "
Yayi banza
be amsa ba kuma yajita sarai sede ya dago suka hade ido tai sauri ta dauke
nata, ya kara kallonta na wasu seconds ya koma ya cigaba da aikinshi, kawai
yana mamakin Karfin halinta, yadda taiya yi mishi magana,
Faseelat
ganin shiru yasa ta fiddo waya ta kira maman amira,
Maman amira
da ke wajen saloon ta dauka tace "momyn amira yaushe zaki zo ne? Ko
kintaho?"
Faseelat
tace "anty gani nazo "
Maman amira
tace "ayya wlh bansan zakizo da wuri ba nazata seda marece, gashi ni ina
wurin saloon, zaaimin da wankin kafa, ita kuma amira ai mata kitso "
faseelat
tace "to bakomi anty bari natashi natafi se bayan salla in Allah yakaimu
"
Maman amira
tace "au kina ciki kenan, ashe daddyn amira ya dawo, to tunda kina ciki
kijira ni mana daman dan kar in shanyaki waje, ki bani 30 to 40 minutes inazuwa
"
Faseelat
tace "Tom anty se kindawo "
Ta yanke kiran
dan koda 2 hrs maman amira tace tozata iya jira saboda ko kamshin turaren fahad
kawai da ya mamaye falon yasa ta tsaya bare ga kyakykyawar fuskar shi tana
kallo,
Tunda tafara
waya yake kallonta se lokacin ya samu amsar tambayarshi wato kawar aisha ce, he
wonder ina ta samo wannan, ya meda kanshi kan aikinshi cikin ranshi yana cewa
"she has sweet voice too"
Faseelat tai
zaune dukda de adarare take amma she love the moment, a dan sace take samu tana
karemishi kallo, yana sanye cikin white shirt blue trouser, yayi kyau sosai ta
cigaba da satar kallonshi she don't think ta fishi da wani abu dan inma fari ne
har ya fita ,
Suna zaune
ahaka shima suna musayar ido da wannan ya dauke nashi se wannan ya soma,
Can de fahad
yameda hankalinshi kacokam kan system nashi,
Faseelat ta
rasa abinyi zaman yafara isarta seta jawo waya takira aisha, maman amira na
dauka faseelat tace "anty I'm feeling hungry "
Maman amira
tace "ayya I don't think zaki samu abinci amma ki bude fridge na hanyar
dining ki samu ko snack ne da drink kici "
faseelat
tace "ayya anty ni abinci nikeso fa "
Maman amira
tace "no be problem kishiga kitchen ki dafa abunda kikeso kafin na dawo
"
Faseelat
tace "OK I'm waiting "
Ta kashe
kiran ta tashi tsaye ta ajiye Jakarta takama hanyar kitchen fahad yabi bayanta
da kallo hijab din jikinta roba ce ta dan fito mata da shape kadan,
tana shiga
kitchen tabude freezer wow ga freez chicken nan ga fish, liver and kidney ga
chicken breast nan ma na company "
Ta danyi
tsaye tana tunanin mi zatayi, can zuwa tace "le me do yam porridge and
toastedchicken "
Ta fiddo
kaza da sauri da ice fish ta wanke tasa kasu a oven on law heat don Ice din dake jikinsu tayi melting,
Ta fiddo
kayan miya tai blending tadora tukunya a gas tafara soya su,
Ta fiddo
kazar da fish din har sunfara zafi ta ajiye tai grettin tarugu da albasa tazo
tai hadin kazar ta shafa mata ta kai fridge don tayi marinated ta cigaba da
aikinta for like 20 mnt ta fiddo ta ,ta saka a foil paper takara hada mata
spice tasaka a oven,
Ta koma ta
cigaba da hada faten doyanta for like 30 mnt da shigarta kitchen yaji kamshi
yana kawowa inda yake,
40 mnt dede
ta gama komi ta dan zuba wanda zata ci a plate ta zuba nasu a hotter takai
dining,
Yana zaune
yaga tafara zarya dining to kitchen yatashi ya dauki system dinshi ya haye
sama, faseelat na fitowa bataganshi ba,
Tasaki
murmushi "kagama duk wani jiji dakanka zaka shigo hannu ne "tafada
saboda karfin hali,yo karfin hali mana🤣
Ta zo ta
zauna tana cin nata hankali kwance tana gamawa takira maman amira, tana dauka
tace "anty har yanzu kusan 1hr fa kenan da zuwana "
Maman amira
tai dariya "sorry gamu kan hanya "
Takashe
kiran tana magana da amira "zakiga momy ko? "
Amira ta
daga kai tana murna,
Faseelat na
zaune amira ta shigo da gudu ta rungume faseelat, faseelat ta dauketa tana
jindadi, aisha ta shigo tana faraa tareda cewa "sorry I keep you waiting
"
Faseelat tai
dariya "bakomi anty "
Ta cigaba da
wasa da amira,
Maman amira
ta haura sama, ta samu fahad nata aikinshi tafada jikinshi tana fadin
"washhh! "
Tace
"yaya I'm very tired "tana shige mai,
Ya matsar da
laptop din ya kara jawota sosai kan cinyarsa yana Shafa kanta "kinyi kyau
sosai honey "
Aisha tai
Far da ido tace "thanks you my heart beat "
Ya na mata
kallon bukata yadora hannu kan boob's dinta yana matsawa yace "I want to
have you ..."
Ta katseshi
"but not now yaya kaga fa inada bakuwa plss kabari na sallameta sannan
"
Yayi
murmushi yace "who is she to you "
Tace
"just a friend "
Yace
"good"
Ta tashi
tsaye "let me attend her karta ga na dade "
Kallo kawai
yabita dashi har tafita, tana fita yasa hannu ya na shafar sajenshi tareda
furta "ahmmmmm"
aisha na
fita ta hangi warmers akan dining tayi gun ta bude tace "wow so delicious
"
Ta rufe
tafito tana zama tace "faseelat har wahala kika bawa kanki? "
Faseelat
tace "a, a bawata wahala anty "
Aisha tace
"thank you yau zamuci ur delicious cooking gaskiya kin iya girki "
Faseelat tai
dariya tana cewa amira "my angel kitsonki yayi kyau, anty nima fa naiya
kitso ni zanwa faseelat na salla "
Aisha tai
dariya "kinada kokari gaskiya Allah yakaimu, da inayin kitso da har ni
zakiwa to sede bana kitso daddinta bayaso ya fison ganin gashi haka "
faseelat tai
murmushi ta dubi agogo to 2 ta mike tsaye "anty bari nayi salla nawuce
"
aisha tace
OK, "ga toilet nan daga kofar fita kitchen, bari nakawo miki carpet "
Faseelat ta
juya ta tafi tayo alwala ta dawo tai salla suka dan yi labari ta tashi zata
tafi maman amira tamata kyautar perfume, ganin zata tafi amira tafasa ihu wanda
yasa fahad lekowa daga saman bene,
Amira tana
kuka tace "i want to follow you mommy "da maganarta da bata ida
gogewa ba, ta rikewa faseelat hijab,
Faseelat
tana rarrashi aisha nayi faseelat har suka fita, fahad na Sama yana kallo su
basuma san yanayi ba, suna fita ya saki murmushi,
Faseelat
tabar gidan sannan aisha ta dawo tanata wa amira wasa har ta samu tai shiru,
sega fahad ya sauko tace "yaya muje muyi lunch I'm hungry "
ya amshi
amira yana fadin "my blood what do you want ?"
Aisha tace
"rabu daita ta cika rigima "
Har kan
kujera ya zaunar da amira ya zauna aisha tai sarving dinsu ta zauna tafara ci,
spoon daya tayi ta rumtse ido tana fadin "yummy"tana juya kai,
amira tuni
take ta kai spoon baki tanacin abincin yana zaune yanata kallonsu, baya tunanin
waccan insane girl din zatayi wani abun kirki,
Can zuwa ya
daure ya kai spoon baki, wani dadi ya ziyarci kwakwalwarshi ya rumtse ido, inda
akabar aisha baya kenan ba ruwanta tana ma iyayin sati batai musu abinci ba
sede suje waje suci ko yayi musu da kanshi, tun tana gida mommy ta shagwabar
dasu komi se me aiki ce keyi baruwansu sede charting bacci da kallo,
fahad yaji
taste yakara dauko spoon yakai baki besan lokacin da yace "wow"
idonshi rumtse,
Aisha har ta
dau spoon zata kai baki ta meda ta ajiye wani haushi da kishi suka taso mata,
taja plate din gabanshi "girrrrr "
Ta medoshi
gabanta,
Ya bude ido
yana kallonta idanunta har sunyi ja tatashi tafara hada abincin cikin cooler
har da wanda amira keci,
Yana
kallonta idonta tab da kishi yace "aisha plsss mana kibari muci abincinnan
yamin dadi "
Ta watsa
mishi harara hawaye na neman fito mata tace "wlh baba tsoho zan kaiwa shi
bawanda zeci abincin nan "
Ta cigaba da
juye abincin, yahade hannu wuri daya yana kallonta, ta gama juyewa ta rufe kular
ta dauka,
Amira tafasa
kuka "daddy talk to mommy to bring my food back "
aisha
tawatsa mata harara tai waje,
Yabita da
ido ya girgiza kai, ya jawo amira yana tapping dinta yace "it's okay bari
muje restaurant muci kinji? "
amira ta
cigaba da kuka, yana cikin rarrashinta aisha ta shigo tana ta hade fuska ta hau
step din bene har takusa hayewa ya kira sunanta "Aisha! "
ta juyo
fuskarta da hawaye tana kallonshi......
[7/12, 11:00
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3⃣2⃣
*Bismillahirrahmanirrahim*
*dedicated
to yan amana 🤣*
Se yaji
badadi ganin hawaye fuskarta yayi alamar tausayi da fuskarshi, bata jira shiba
ta haye sama, yayi murmushin takaici ,bega wani laifinsa ba ita ta gayyato shi
cin abincin honestly speaking abincin yayi dadi b4 yafara santi she's the one
that begin, ya juya kan amira yace " angel muje mu rarrashi momy she's
angry with us "
Yaja amira
suka haye sama, suka shiga dakinta aisha tahaye saman bed tana rusa kuka
yanaganin abinda take ya dafe goshi, yaja hannun amira suka fita yakaita
dakinshi yabata game ya fito ya koma gun aisha,
Tana kwance
tana shan kukanta yazo yazauna kan bed din yajawota jikinshi, ta cigaba da kuka
don wani katon abu taji yatsaya mata a wuya,
Yana rungume
daita tana cigaba da kuka yace "ya Allah"yana rumtse ido dan jin
kukanta yake har cikin zuciya,
Magana
yafara mata "aisha plss stop this crying, kukan ki na tabamin zuciya,nayi
lefi kiyi hakuri plss, bansan zakiji zafi ba da bance abincin yayi dadi ba
"
Ta dago ido
tana cigaba da kuka tace "i love you yaya bazan iya hakurin abinda kayi ba
inajin ciwo a zuciya ta sosai "
Ya fara
share mata hawaye yana cewa "it's okay haka baze kara faruwa ba, nifa
nakine ke daya sweety dan haka just wipe your tears and stop this crying "
Ta dago ido
tana kallonshi yace "plss mana ko kinaso nima nayi kukan? "
Ta girgiza
kai yace "toki hakuri my one and only "
Yana kashe
mata ido daya, batasan lokacin da murmushi ya kufcemata, yayi murmushi shima
yace "that's my girl "ya kai mata kisss, ya riga yasan aisha akwai
kishi amma tana da saurin hakuri,
Yasamu ya
rarrasheta sannan suka tafi Chinese restaurant cin abinci,
Faseelat
tana isa gida tai ta juyi itakadai tarasa ina zata saka kanta don dadi finally
yau de taganshi ,
Ta zauna kan
kujera ta jawo wayarta ta tura mishi "kayi kyau sosai "
Ta ajiye
wayar tai shiru tanajin haushin kanta yadda tai da ta ganshi.
Ko da khalil
ya dawo da daddare take ce masa maman amira nagaidashi kuma tabata turare,
Yace
"Allah sarki tanada kirki sosai gaskiya "
Lokacin da
fahad yaga message din faseelat dariya ma abun yabashi yana tunanin yadda
yaganta a tsorace, se ya tura mata smiling face, tana gani ko seda taji dadi.
Ana haka aka
shiga watan azumi, tunda aka fara azumi shikenan khalil ko romance din ma
yadena yi da yayi bude baki ze cigaba da jan cazbi daganan yawuce masjid suyi
isha da tarawih ya dawo da yagama cin abinci ya cigaba da laziminshi itakuma
taita charting dinta da friends,
Har akayi
azumi 15 wani problem da faseelat ke fuskanta azumi ake amma ita shaawar karuwa
take dan ko baccin rana takeyi mafarki take,
shi ko
khalil gajiyar azumi da aiki ce tahanashi katabus,
Abun ya damu
faseelat ta rasa ina zata saka kanta taji dadi, atleast ma tasamu wanda
tafadawa zata rage wani abu,
Yau bayan ya
dawo daga tarawihi ya zauna yana lazimi, ita ko faseelat sede ta juya ta
kalleshi tayi tsoki kasa Kasa "waishi khalil miyake nufi ne?akace masa su
uztazan basa bawa matansu lokacinsu ne? Basa wata fira me tsayi be taba cewa
yana sonta ba sede aukin santi in yana cin abinci,
Hakanan taji
tana son sharing problem dinta da maman amira, akai saa tana online faseelat ta
tura mata "anty ansha ruwa lpy? Anty ina cikin matsala, shaawa tamin yawa,
mijina be damu dani ba "
Maman amira
na karantawa taji badadi tai mata reply "subhanallah, abu beyi dadi ba
kiyi hakuri "
ta tura mata
"anty shawara zakibani"
Maman amira
tace "shawarata kije ki sameshi ki masa maganar, mijinki ne fa ba wata
kunya tsakanin ku, ki masa maganar ku zauna kushawo problem din"
Faseelat
tace "to Nagode anty "
maman amira
tace "bakomi ai anzama daya "
Faseelat ta
sauka online tana tunanin ta ina zata fara, don gaskiya hakurinta ya tafi
karewa,
Har Sun
kwanta takasa mishi maganar can de tai ta maza ta fara kiran sunanshi ya amsa
yana saurarenta,
Tace
"khalil banajin dadin yadda muke having sex"
Tana inda
-inda tace "ni se nake ganin kamar baka lpya ya kamata kanemi magani
"
Yayi shiru
yana nazarin maganarta ya jawota jikinshi yace "I'm sorry faseelat,amma ni
lpyata lau banaso na fara shaye shayen magani nafiso ki saba dani ahaka,
faseelat bantaba koda rike hannun mace ba seke bantaba muamala da mata ba nike
ganin shiyasa abubuwannan suke faruwa haka kiyi hakuri zuwa gaba komi ze dedeta
"
Tai shiru ya
dan matse ta cikin wasa yace "kinji "
Ta daga kai,
yace "kuma cikin azuminnan wlh agajiye nake aiki yamin yawa shiyasa ko
feeling banaji amma kiyi hakuri bayan salla komi will be normal "
Tace
"to "tanajin haushi aranta itade tagama yarda da zuciyarta bashi
lpya,ya zaai yace rashin sabo ne wata 7 ba kwana bakwai bane, suna haka bacci
ya daukeshi while ita ko bacci batai ba,
Bayan kwana
biyu de abun na cigaba da damunta ta rubuta tambaya ta tafi daita wajen tafsir,
ta saka a akwati,
Kaidar
malamin seya fara karanta questions sannan afara karatu tana zaune aka karanto
tambayarta,
"Aslm
inama malam fatan alheri Allah ya shirya zuria yakara ilimi, malam munyi wata 7
da mijina amma be taba kusanta ta ba ,da abun ya daman namasa maganar yace min
lpyarshi lau inyi hakuri dashi ahaka, malam ina cutuwa sosai, har ya kai
matakin da bazan iya hakuri ba ina neman shawarar malam "
Bayan yagama
karanta tambayar yace "bewar Allah kina cikin jarabawa daga cikin
jarabawoyin duniya akwai shaawa, saboda tana saurin halakar da mutum, shawarar
da zanbaki ki hakuri ki cigaba da kame kanki, sannan ki kai maganar ga magabata
tunda kinmishi be gyara ba,inaba maza shawara kuji tsoron Allah kurika sauke
hakkin matanku na aure saduwa shine banban ginshikin aure bazaka ajiye mata dan
kabata ci da sha da sutura ba kace kagama mata komi, a, a akwai hakkoki da suka
rataya akanka daga ciki harda kawar mata da shaawarta, da zama daita kuyi wasa
da dariya bata labari da debe mata duk wata kewa da zata hanata ganin wani
namiji awaje, dan wasu mazan iyakarsu sex shikenan ba dariya ba magana me dadi,
mata suna bukatar kulawa sosai saboda masu rauni ne, muna miki fatan zaku
dedeta da mijinki Allah ya dedeta tsakanin ku, idan kuma anfada wa magabatan be
dena ba kina iya neman ya sakeki, saboda auren ya haramta tunda akwai cutarwa
ciki Allahu aalam "
Faseelat
tunda taji an amsa tambayarta memakon taji sauki se ma tashin hankali da
tashiga wa zata samu da maganar 'ummi? Gaskiya baxata iya ba gwara de ya
sawwake mata yafi, tai shiru tana tunanin khalil gaskiya yana matukar sonta
kuma yana da halin kirki sede tarin kayan haushin shi, tai shiru tanajin
tausayinshi,
tana komawa
gida takira maman amira awaya dan itakadai ce tasan matsalar kuma itama bata
fada mata gaskiya ba tunda bacewa tai be taba kusantar ta ba,
Maman amira
na dauka jiki badadi faseelat ke bata labarin tambayar da tayiwa malam da amsar
da yabada,
maman amira
cikin jimami tace "kiyi hakuri faseelat komi zewuce "
Tace
"nagaji ne maman amira haryanzu zuciya ta takasa sonshi har nafara son
wani daban "
Maman amira
tace "subhanallah gaskiya be dace ba tunda de kinajin bazaki iyaba ki
rokeshi ya sakekin"
Faseelat
tace "to anty Allah yatemakeni ya yarda"
Takashe
kiran ta zauna dabass kan kujera tanajin tausayin khalil,
bangaren
fahad ko yanzu sunfara charting da faseelat don yafara meda mata reply shima
hakanan yakejin wani feeling akanta saboda pic datake ta turomishi any how,
Kuma sosai
yakejin dadin adduoin da take mai saboda bayada me mishi addua, mommy batayi
befi tace mishi good luck ba a wayance, haka maman amira sede tace mashi best
of luck, ko safe trip ko something de,
Faseelat
sosai tasha kuka saboda batajin dadi kwata kwata hakanan taji bazata iya tarar
khalil da maganar ba,
Aranta tace
"kayi hakuri khalil dole se nayi abubuwan da zesa ka sakeni "
Anya ko
khalil ze iya sakin faseelat 🤔
[7/12, 11:00
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3⃣3⃣
*Bismillahirrahmanirrahim*
*Kad aflahal
muuminuun...... wallazinahum anil lagwi muuriduun*
*Dedicated to
golden pen writers, ko nima zansamu aban matsayin gimbiya😂🤭 kuzabe ni plss ni nacancanta abawa, 🤭ina maku gaisuwa da rokon iri👏🏼😂*
Wajen karfe
biyu khalil ya dawo gida don dukda ana azumi yakan dawo da rana ya dan huta,
har lokacin faseelat na zaune tana faman kuka da sake sake yana shigowa yaganta
zaune idanu jawur da sauri ya isa wurinta
,ya durkusa ya dafa cinyoyinta yace "faseelat lpya meyafaru? "
Faseelat
naganin yanda ya rude ganin tana cikin damuwa tana sheshsheka tace "bakomi
kawai azumin ne ke bani wahala "
Yatsaya
kallonta don be yadda da maganar ba,
Can zuwa
yace "faseelat karya bataimiki kyau ba, saboda baki sabayi ba kifadamin
meke damunki plsss" yariko hannunta .
wani kukan
ya kufcemata cikin kukan tace "wurin waazi ne akai waazi akan azabar da
akewa yan wuta shine ya firgitani"
Ya dubi
hijabinta dake gefenta don tunda ta dawo take nan ya rumtse ido ya bude yakara
damke hannunta yace "idan anji waazi ba kuka akeba komawa ake ga Allah ta
hanyar kaucewa aikata duk wani sabo da kara kaimi wurin aikata alheri, ke mi
zesa ki daga hankalinki, kina karkashin inuwar aure, manzon Allah (S. A. W)
yace duk macen da ta mutu kuma mijinta ya yarda daita zata shiga, akwai hadisin
da kuma yace idan mace takiyaye sallolinta biyar, ta kiyaye azuminta da
farjinta da hakkin mijinta to zata shiga aljanna ta kofar da taga dama, me ze
dameki kina min biyayya bamu taba samun sabani ba kuma kina da yawan ibada, ki
shakuruminki ni dake duk yan aljanna ne gabadaya in Allah yaso, "
Ta kureshi
da ido tana jinjina maganganunsa,
Ganin takure
sa da ido ya sa hannu yana sharemata hawaye yana cewa "ki kwantar da
hankalinki mata ta yar aljanna "
Tai shiru
tana zazzare idanu wani mugun tsoro nakara shigarta.
Ganin tayi
shiru sannan ya tashi," bari naje na dan kwanta kitashi kiyi salla "
yawuce cikin
daki, har bayan 15 mnt da shigar shi faseelat takasa tashi, dakyar ta mike ta
shiga don yin salla,
Bayan tafito
ne wayar ta tafara ringing ta dauka tana dedeta maganarta ishak yace "yaya
kin sauke? Ni har nafara ta biyu "yana murna
Faseelat tai
dariya tana tabe baki "lazy boy dani kakeso kaja? Hhhh dasauranka ni kaga
nakusa sauke na biyu, ina ummi tayi ta farko ma? "
Yana dariya
yace "ummi najin azumi fa ta de kusa yin rabin sauka "
Faseelat ta
babbake da dariya "kafadamata se ta taho "
yayi dariya
"anti kina kokari asamu a addua "
Tace
"karka damu ka gaida kowa, kuma kafadamasu se suntaho "
Takashe
wayar tana dariya, wato su yar rige sukeyi a sauka cikin azumi wanda ya wuce
kowa ummi na mashi kyauta ta musamman,
Ajiye wayar
tayi tafara karatu seda akai laasar ta shiga kitchen,
bayan ansha
ruwa khalil ya tafi masjid ita kuma har tagama tata tarawihi ta dauko wayarta,
tana Bin chart dinta da fahad, duk reply dinshi bewuce thanks, ameen, i love
it, ko u look pretty good, tai dariya tana jindadi, ta rumtse ido tana tuno
yanda yake ta aiki a tsanake ranar nan yanzu muryar shi kawai takeson ji,
zataso taji ya voice nashi tasan jinta kadai zesa tai bacci cikin farin ciki,
Batare da
jinkiri ba ta bi numbers tai dialing my hope,
Fahad
dawowarshi kenan daga masjid yana cikin mota ko fita beba wayarshi tafara
vibrate,
yana ganin
number yagane number insane girl dinshi ce,
Ya dauka
yayi shiru jin andauka faseelat tai Kasa da murya tai sallama, ya amsa yana
lumshe ido tareda dora kanshi kan seat,
Faseelat
wani irin dadi muryarshi tai mata jitai kamar ba muryar namiji ba tsabar dadi,
Tadanyi jimm
sannan tace "inafatan kasha ruwa lpya? "
Yace
"yeah "yana mamakin yanda yakejin wani abu namasa yawo
tace "Allah
ya karbi ibada, ina anty da my meera "
Yace"they're
all fine "
tace
"naji dadin jin hakan, Inajin muryarka kamar honey or sweet ,nakirawo ne
naji muryar ka ko nasamu peace of mind, daddin amira tun ranar da naga pic naka
i fall for you "
yayi shiru
cikin ranshi yace, "u have nice voice too "
jinshiru
tace "I'm sorry na takura maka it's your love that make me gone crazy,im
sorry for all my disturbances, "
Yayi
murmushi me sauti wanda yasa taji wani abu na zubo mata yace "why do you
force me to start loving you, yeah you force me to fall for you ,u know what? I
love everything about you, ur smile ur voice , ur duas for me ur cooking and
your beauty, I love everything about you"
Saboda dadi
faseelat batasan lokacin da ta mike tsaye ba, sautin muryarshi nata kaikawo a
brain dinta,
Wata irin
dariya ce marar tsayi takeyi me cike da mamaki tana rufe baki tace "did
you? ....."
Takasa
karasawa, kamar yasan me zatace yace "yes I love you, I love you beauty
"
Dadi yakashe
faseelat da karfi tace "thank you so much I love you too "
Ta datse
kiran tana tsalle ,can zuwa takwara baki tace "I love you "
Saboda zafin
da ake tsakar gida take sallan, khalil tsayuwar mashin dinshi kenan yaji
maganar ta da karfi tana fadin I love you,
ya shigo
gidan don bude gate, tanajin karar kofa tai tsaye wayarta rungume da kirji,
Yana mata
kallon mamaki yace "kedawa kike waya kike daga murya haka? "
Tana inda
inda tace "ya omer ne munkwana biyu ba mugaisa ba shine yamin albishir
nakejin dadi "
Yajuya kawai
ya bude gate din yafita, tasaki ajiyar zuciya tana zaro ido waje ta shige daki,
Fahad jin
yanda take murna yakara sashi cikin wani Yanayi, Ya rumtse ido shikadai yasan
yanda yakeji gameda ita, brain dinshi tana hasko mishi irin murnar da takeyi
yace "be happy always my cutie,
Ya samu
yashige gida ya je ya sauke duk abinda yakeji gun aisha.
tundaga
ranar kullum se faseelat ta mishi barka da shan ruwa kuma suna chart suna
fadawa juna zafafan words da suke kara narkar da zuciyoyinsu.
Salla saura
5 days maman amira ta fadawa faseelat zasuje dubai acan zasuyi salla, faseelat
kamar tai hauka takira fahad, he was busy doing office work be dauka ba seta
turamishi message "zanyi kewarka my heart, inamaka fatan nasara akowane
abu da Kasa agaba Allah ya ya kaika lpya ya medoka lpya "
Seda aiki ya
lafa yaga miss call nata da message yana gama karantawa yayi murmushi ya tura
mata "why did you fell sad, we will continue chatting with each other and
I will call you time to time stop worrying your self we will only spend 10 days
only going to miss you too "
ya turamata
tana ganin message din tai murmushi,
ko minti
biyu baaiba yakirata yana rarrashi yace taturamasa account number dinta ta tura
masa nan take taji alert din 200,000.
kusan
zaucewa tayi tanata kara karanta zero zeron taga ko de bata karanta dede ba.
Manage it 🤦🏻♀
[7/12, 11:00
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3⃣4⃣
She's very
happy, his gift is the best gift for her, can kuma setaji murnar duk ta tafi
she don't want his money she want him ,not the money he own, bayan 15 mnt da
turomata ta kirashi ya dauka yana driving to home, yace "menene kuma
cutie? "
Tai murmushi
"naji alert a account dina, bazance banyi murna ba saboda kyautar will
always be the best gift amma ni I don't want the money, kai nake so ba kudi ba,
zanmeda ma kudinka, Nagode sosai "
Yayi dogon
murmushi yace "naji kuma nasan hakan ,amma inkin medo min kudin bazanji
dadi ba, zama ki tabbatarminne bakisona kina fadane kurum "
Tace
"Tom bazan medoba dan banason ranka ya baci "
Yace
"kokefa yanzu I entered home se munyi waya anjima "
Tace
"wait nifa bansan me zanyi da kudinnan ba "
Yayi dariya
yace "kisa su a bola kinji ko "ya datse kiran yana dariya, yace
" you're not serious "
Tanajin ya
kashe kiran ta saki murmushi, ta rungume wayar,
Khalil yaga
sauyawar faseelat sede be dauki abun serious ba,
Da daddare
ya kirata don gobe ne zasu tafi ta dauka tana shagwaba shi kam dariya kawai
take bashi yanajin dadin yadda take shagwaba"plsss i don't want to you to
go there pleas"
Yayi dariya
"OK shikenan nafasa tafiyar are you happy? "
Tai dariya
tana zaro ido " wasa kake ko? "
Yaja
numfashi "dagaske nake munfasa tafiyar tunda bakiso saboda banason abinda
zesaki damuwa "
Tace
"a, a,kuje kawai kunriga fa kungama komai se kufasa? Na hakura kuyi
tafiyar ku"
shima yayi
muryar shagwaba yace "a, a ni de nafasa saboda kar masoyiyata tashiga
tunani "
Tafashe da
dariya tana zumbura baki tace "plss mana kutafiyarku"
Ya fashe da
dariya sannan yace "OK, OK zamuje tunda kince, me zaki bani na bankwana?
"
Tace
"kome kakeso "
Yace "I
want hot kiss from you "
Tai dariya
"how i will do it bayan bama tare? "
Yace
"muna tare idanuna suna hangomin yanda bakinki ke motsawa a yanzu da yadda
kike shagwaba, kiyimin kiss a waya I will feel like kamar azahiri ne "
Tace
"zaka samu fiye da yadda ka bukata, where do you want me to kiss ?"
Yace
"my cheek "
tace
"alright "
Muahw!
Taiwa wayar
kiss
Yace ash
yana dafe cheek dinshi alamun yaji dadin nan tai dariya tace "do you want
more "
Yace
"yes's "
Tace
"where I'm going to kiss now? "
Yace
"my lips "
Tai murmushi
takara jan wani deep kiss, wanda yasa fahad kusan haukacewa yanda yaji sautin,
Tana gamawa
tace "want more? "
Yace
"noo" muryarshi a dishe
tace
"why? "
Ya shafi
sajenshi yana rumtse ido yace "i will die if I have the third kiss "
Tafashe da
dariya yayi shiru saboda his Mood is totally change jiyake dama tana kusa he
want to squeeze her body, he's in need .
jin dariyar
ta nakara mishi kaimin jin desire the way she's laughing is different saboda
tanayi ne tana jan numfashi wanda yakejin shi kamar they're doing sex ne
takeyinshi,
Dole yatafi
gurin aisha yasamu relief,
Yacewa
faseelat "baby I'm going inside take care of yourself, I will call you the
time we have reach there "
Tabata fuska
sannan tace "miss you my handsome man "
Yace
"going to miss you too tace care bye "
Yakatse
kiran yanajin double feeling, yadan zauna ya dan dedeta kanshi sannan yashiga
gida,
Wannan karon
banda amira zasu yanzu tana gidan momy, yana shiga daki aisha nata charting
dinta, yaje ya zauna kan bed din yafara balle maballe, Aisha ta juyo ta
kalleshi tana ganinshi tasan what he capable of doing, ta sakarmishi murmushi ya
meda mata yana jawota jikinshi suka cigaba da kissing juna kan su afka ga
babbar sunnah,
Seda
sukagama tana kwance tana huce gajiya yamusu parking suka shiga toilet sukayo
wanka sannan suka kwanta don 12 jirginsu ze daga.
12 dede
jirginsu ya tashi going to Dubai
Faseelat
nagama wayar ta shige toilet don yin tsarki kaida ne inhar sukai irin firannan
se ta kama ruwa dan jikewa take jagabb,
Tana fitowa
khalil yashigo gidan taimasa sannu da zuwa ,yazo ya zauna ya aje ledar
hannunshi ya mikawa faseelat yace "kizabi kalar da kikeso guda biyu sauran
na hjya ne "
Tabude
ledojin atamfofi biyu da laces biyu, ta kara binsu da kallo ai wannan dama
yariga ya tsarosu da kaloli masu duhu da masu haske tasan masu duhunne dede
ita,
Ta dago ta
tabe baki tace "meyasa baka daukeni naje nazabo kalar da nakeso ba? Ni ko
agida nikeyin siyayyata bayimin ake ba, "
Tunda tafara
magana yake kallonta ya rasa meke
damunta ranshi ne yabaci ya tashi tsaye ze shige daki yace "ni agida na
mace bata zuwa kasuwa, ko super market ko wani wuri kingane ai "
Tace
"to wlh kaxo ka dauke kayanka bana bukatarsu kuma senaje super market din
sede kayi abinda zakai "
Har yazo
shigewa ya juyo cikeda mamaki yace "faseelat ni kike fadawa magana haka?
"
Tace
"anje anfada maka gobennan zanfita insiyo abinda yayi min, zaka wani
kawomin wadannan banzayen kayan kadauke abunka bani so, kahada su duka ka kaiwa
saratu ta dinka "
Gabanshi
yayi wani mummunan faduwa jin ta ambaci uwarshi kai tsaye, ya dafe zuciyarshi
sannan yace "faseelat kinsan abinda kike fadi? "
Tace
"bansaniba tunda ni mahaukaciya ce, sakarai kawai da komi nashi na
kauyanci ne bawani wayewa, harni zakaiwa kaya iri daya da hjya? Ai atleas ka
tambayeni wace color nakeso, ka kwashi kayanka bani bukata matsiyaci kawai
"
Jijiyoyin
kan khalil tuni suka firfito yayi tsaye yana kyarma yana kalonta tana xaune
tana shuka rashin mutunci hankali kwance jiya ke kamar ya rufeta da duka, ya
dunkule hannunshi yakaiwa iska naushi.
Kutstsss,
hhhhhh tafashe da dariya tana yamutsa fuska tace "ran yan maza ya baci, ta
kwashe da dariya "yo shi iska miye nashi nice nan nayi lefi azo a daken in
an isa "tana jinjina wa sekace inyazo bugunta zata iya katabus,
Rai bace
yabar wurin taja tsoki tace "mtswww wlh damma cikin azumine Allah yakaimu
bayan salla kasha mamaki "
ta hau
what's up ta danyi replying na messages da akaimata ta sauka don yanzu ko tana
online basu cika charting da aisha ba inde fahad na online.
Seda ta ga
dama sannan ta kwashi ledojin ta shiga daki
yana kwance yanata kallon silin hannu saman kai mamaki da bakin ciki Sun
addabeshi be ji shigowarta ba sede yaji kaya samanshi "ridididif "
Ya tashi
zaune zuciyarshi na harbawa da sauri yace "faseelat kina tsoron Allah
kuwa? "
Tana banka
mishi harara tace "inbanji tsoron Allah ba tsoronka zanji? "
Ta wani
murguda baki ta rike kugu sannan ta juya ta shige dakin ko minti biyu ba aiba
ta fito cikin sleeping dress ta wuceshi, yana zaune sede yaji ta bude dakinshi
ta shige da alamu can zata kwana.
Ya dade
zaune dan gabadaya gani yake kamar anmasa musanya, dakyar ya samu yayi bacci,
Dasafe tun
kafin tafito yabar gidan don wani mugun tsoronta ne ya shigeshi.
Yana zuwa
gidan hiya bayan sungaisa ya mika mata Nata kayan sallar, ta amsa ayatsine
tace?"Allah yasa albarka "
Badadi yabar
gidan kanshi na mugun ciwo,
Shiko fahad
karfe 11 da rabi na safe yakira faseelat yafadamata sun sauka taimishi ya
gajiya sukai sallama saboda azumi.
Haka
faseelat ta bullo da wasu sabbin abubuwa da suka rikita ma khalil kwakwalwa, da
yanzu tsoron shiga gida yake inko yashigo har kyarma yake wani lokaci ma da
yashigo sede kiji kwammmm! Mashin yafadi daga hannunshi saboda yanda hannunshi
ke rawa, ba ruwan faseelat da taji karar faduwar tai ta babbakar dariya se
tagama taja tsoki, gaba daya ya rikice idanunshi kullum awaje yana rarrabasu
more especially inya shigo gida.
Ranar salla
faseelat taci gayu ta turawa fahad, yayi ta kodata don bakaramin haduwa taiba
don seda taje kasuwarnan ta zabo materials masu kyau takai akamata dinki,
Yanata
aikomata da kisses daga karshe yakirata suka cigaba da waya,
Wan safen
salla, khalil ya dauki faseelat a mashin zasuje suyiwa su ummi barka da salla,
Hankalinta
kwance shiko yana tuki hannu na rawa, se warning takemasa "wlh kabini
asannu don inka kadani Kasa naji ciwo
wlh abakin aurenka don dolenka se ka sakeni "
Yayi shiru
sede hannunshi daya kara gafgaf yana rawa saboda bacin rai tana kallonshi tana
dariya kasakasa da farko tausayi yake bata intana mishi tsiya Amman yanzu
haushi da takaici yakebata tana ganinshi kamar ba namiji ba da wani ne da tuni
yabata red card dinta ahannu.
Tana ganin
an hau titin da ze kaika gidansu tace "dakata, dakata "
Yaja burki
ya juyo yazata ko zata gyara zama ne, yana kallonta ta tunzuro baki gaba ta
sauka tace "ina zakakaini ne naga munyi nan? "
Yace
"gidan hajya zamu fara zuwa sannan muwuce gidanku "
Tana mishi
kallon raini tace "wace hjyar? Wai hjya saratu? To banzuwa kaje ka gaida
uwarka nima inje ingaida tawa "
Rumtse ido
yayi da yanabiye zuciya da tuni yafara jibgarta,
Cikin tsawa
yace "faseelat !ya isheki kiyimin duk wulakanci amma karki kara ambatar
sunan mahaifiyata "
tace
"me zaka iyayi?innafada inba raba ido ba, "taja tsoki da Allah kakara
gaba inkaje ka gaida saratun "
ta juya,
cikin zafin rai yaja mashin yabi bayanta.
khalil ai
hakuri kar amedata gurguwa🤣
[7/12, 11:00
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
😂🤭
*ZINARIYAR GOLDEN👑*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🅿 3⃣5⃣
*hakika ina
cikin farinciki, na tabbatar ana so na anayi dani, jiya naga dubban comments da
wanda ma banganiba, kowa nata fadin raayinshi da hangenshi, ga ruwan adduoi da
na sha nida yarana, ina godiya Sosai Allah yabar soyayya*
Cikin zafin
rai yabi bayanta ya sha gabanta da mashin tai tsaye ta rike kugu da hannu daya,
Cikin
dauriya da fin karfin zuciya yace "ki hau muje gidan ummin"
Tana mishi
kallon up and down tace "kayi hanyar ka daban inyi tawa, bana bukatar ka
kaini kaji ko dan hjya "
Ta zagaye
shi Tawuce ya rumtse ido idanunshi tuni sukai ja sede baze iya bari tayi
doguwar tafiya a kafa ba , ya kara danne zuciyar yabi bayanta yakara shan
gabanta ,ta game fuska tana kallonshi tace "malan khalil kafara takura ni
nace katafiyar ka, aa ko ana dole ne?"
Cikin muryar
rarrashi yace "kiyi hakuri ki hau muje kalli titin nan ba abin hawa
doguwar tafiya zaki sosai "
Ta wurga
mishi harara "to ina ruwanka? Nace karabu dani "
Yace,
"Dan Allah ki hau mutafi "
Taja tsoki
ta hau babur din tana cewa "ande ji haushi ba zuciya ko kadan kare yariga
ya lashe"
Yana jinta
yayi kamar be ji taba ya juya yakama hanyar gidan ummi,
Yana zuwa ta
sauka ta shige, yayi parking ya kutsa kai shima,
Tana shiga
ta yaye hijab" ummi ga khalil nan shigowa fa "
Ummi tace
"to bari in dauko hijab dita, "
Khalil yayi
sallama ya shiga har cikin daki ummi ta shiga ciki suka gaisa da yatashi tafiya
ya aje mata bandir na 50 yace abawa yara,
Ummi tace
"to angode sosai Allah yakara budi, aitade hakuri shi zaman aure dole seda
hakuri da kai zuciya nesa Allah yabaku zuria dayyiba "
Yace
"amin "yanata sadda kai maganar ummi ta dan ragemishi zafin da yakeji
kamar tasan tsiyar da faseelat ke shukawa a cikin gidan ,ya tashi ya fita,
faseelat se wurga mishi harara takeyi beko damuba ya Saki murmushi yace
"ki shirya 6pm zanzo na daukeki "be jira amsar ta ba ya fita.
Shikadai
yaje gidan hjya bayan sungaisa take tambayarshi faseelat yace"ai tana gida
tundazu "
Hjya tai
shiru ta cigaba da hidimunta, tunda yazo ya zauna yaketa sake-sake da tunani,
wai miyake damun faseelat ne yau kusan kwana goma sha basa kwana daki daya, ba
magana me dadi, batayin duk wani abu da tasaba yi, yayi shiru yana nazari, seya
tuna last maganar su datake mashi korafi akan sex, tunanin shi da kwakwalwarshi
ya tsaya nan, se kuma ya cigaba da neman mafita, akarshe yayanke shawarar zuwa
wajen masu man power na Islamic, yana cikin tunanin hjya tashigo cikin dakin so
biyu kenan tana giftashi be sani ba har tazo kusa dashi tana kiran"
kai!kai ! "amma bejiba seda ta dafashi ya dago ta tsuramishi ido tace "wai
lpy kake? Dukkabi ka rame kafita hayyacinka mike faruwane? "
Yace
"bakomi hjya azumine ya medani haka "
tana mai
wani irin kallo tace "to yayi tunda bakaso naji damuwarka sede inaso ka
kwantar da hankalinka, banison ka shiga wani hali na rasa mahaifinka baniso na
rasa ka ,"
Yace
"hjya bawani abufa, Ki kwantar da hankalinki "
Tace
"Allah yasa "tana kara karemishi kallo,
Yadan kara
zama ya tashi yafita be zame ko inaba se alhayat Islamic center, yaje ya siyi
kati kasancewar salla ce ba layi yashiga gun malamin, ya mishi bayani a
kunyace, malamin yarubuta mashi
magugunan sa karfi na maza, khalil ya siya ya nufi gida ya dauki biyu ya shanye
su tass yayi kwance yana ta tunani abin duniya duk ya dameshi,
Karfe shidda
yaje ya dauko faseelat tunda ya daukota
batace uffan ba, saboda itama ummi seda tai mata tata yar nasihar,
Yana ajiyeta
yawuce masjid ita kuma ta shige gida, kusan karfe 7: 30 fahad yakirata sukai ta
fira har isha, shi ko khalil a daddafe yayi salla ya taho gida saboda yadda
yaji yana ta samun erection,
Ko da yazo
betsaya shigo da mashin ba ya shiga gida, sam faseelat batasan ya shigoba,
sunata firar soyayyar su da fahad,
Tunda khalil
yashiga dakin yaji wayar da take tana ta noke murya tana shagwaba da duk wani
abu da zeja hankalin namiji, hankalinshi ya tashi, kafafuwansa na kyarma ya
samu kujera ya zauna ya dafe kai da hannu biyu, yana tunani "meyasa?
Meyasa faseelat takeso ta lalata rayuwar aurensu? meyasa takeso ta jefa kanta
a cikin halaka? "
Tunanin shi
ne yakatse jin sautin kisses dinta ,ya mike tsaye yana kyarma,
faseelat
nakiran "good night have a sweet dreams "
Khalil
yashigo tai sauri ta kashe kiran ta mike tsaye tana raba ido dan bataji
shigowar shiba,
Tana ta
sadda kai shiko ya tsaya yana kallonta, da wani yabashi labari baze taba yarda
ba wai faseelat dinshi ce ke fira da wani,
Ya samu
dakyar yace "faseelat kinaso kigama da duniya lpya ko? da aure na akanki
kike waya da wani kato "
Faseelat ta
juyo dasauri ta daga mishi hannu "hehehee,karka kara cewa fahad dina kato
kaine de babban katon bashi ba "
Ta rika
murguda baki,
Ranshi ya
baci sosai, batai tsammani ba taji ya tura ta kan bed yabi bayanta ya fara kokarin cire mata riga
suka cigaba da kokawa har ya janye rigar ya danne mata hannuwa ya fara bin
jikinta da kisses ,tana ta kuka tana kokarin janye hannuwanta, ko minti daya be
dauka ba yayi hanyar shigarta ,abun mamakin shine yanajin shaawar beyi release
ba amma yana zuwa shigarta yaji abar ta kwanta, he was very surprised, ganin
baze iya ba yasa yatsa yafara kokarin yiwa kanshi hanya don yau yakudurci se
yayi sex daita,
Faseelat
sede taji yatsa na neman shigarta a tsorace ta kurma ihu yasa hannu ya toshe
bakin tadage cincin karfinta ta gartsa mashi cizo, yayi sauri ya dagata yana
duban hannun yana nishi, ita ko taja gefe guda tana kuka tana fadin "Allah
yaisa, banyafe ba mugu azzalumi, daniska "ta cigaba da kukanta yana samu
zafin cizon ya rage ya mika hannu ze kara kamota ta tashi da gudu ta shige
toilet
Tana cigaba
da kuka tana Allah yaisanta bata yakeba.
Yayi kwance
yana tunanin lamarinshi yanzu haka ga abar a mike, to me yahana ya shigeta?
Yanata tunani ,
itako tana
toilet tana cigaba da bankomai Allah yaisa, dukda shi masoyin bacci ne amma
bacci beyi gigin daukarsa ba saboda tashin hankalinda yake ciki, itama tana
cikin toilet tana kuka saboda yunkurin rabata da virgin dinta da yayi wanda
yanzu burinta be wuce takaishi ga fahad ba.
Har sha biyu
bata fito ba ya tashi yaje bakin kofar toilet din Yana kwankwasawa "kifito
faseelat dare ne fa kina cikin toilet for many hours ki fito plsss baabunda
zanmiki "
tana jingine
da kofar tace "baza a fito ba din mugu azzalumi kawai "
Yace
"eh naji kifito bazan miki komi ba, kinsan fa toilet matattarar iska ce
"
Tace
"yo ba kwara iskan ba da mugun abinda kakeson yimin dan zalunci "
Yace
"kifito plsss OK tunda bazaki fito ba ni natafi dakina acan zan kwana
kifito ni natafi "ya juya yabar dakin,
Seda taji
tsit sannan tafito dasauri ta sakawa dakin kuba, ta koma taita rizgar kuka
saboda ita kanta tasan abinda take badede bane amma takasa hakura wanda yanzu
bama zata iya kwana daya ba batare da jin muryar fahad ba,
Khalil
dakyar bacci ya daukeshi batare da yagano abinda ke damunshi ba, itama faseelat
dakyar tai bacci,
Da safe har
karfe 8 faseelat bata fito ba gashi yanason fita shago, yaje yana kwankwasa
mata, seda ya dade yanayi sannan ta tashi tana zumburo baki tazo ta bude tana
mishi kallon tsana,
Batare da
yadamu da kallon da takeyi mishi ba yace "ki sauri kihada min break fast
nayi late "yawuce cikin dakin
Ta tabe baki
tai hanyar kitchen, dukda yace yana sauri seta tsiri yin danwake, kuma it take
much time, har ya shirya ya zauna jiranta, se kusan 9 saura kwata takawomishi
abincin ta dangwarar da plate din Kasa ya dauka yana girgiza kai, don shi
dakanshi ke tausayin kanshi, yafara cin abincin,
Tana ta yan
gyare gyarenta, tana waiwayowa taga khalil yana cin abincin yana bata fuska
yana karkace baki irin ba dadin nan,
Beyi aune ba
yaji ta wafce plate din, ya kalleta yace "bani plate dinnan faseelat"
tace
"anki abaka ni zaka raina wa hankali insha wuya inmaka girki kazo kanaci
kamar yadda jaki keci to kaGama cin abinci na wlh daga yau kanemi wurin cin
abinci ko karika shiga kitchen da kanka ka girka "
Yatsura mata
ido yana memeta jaki,can yace "faseelat nine jakin? "
Tai dariyar
rainin hankali tace "ai gwara jakin ma da kai "
Tai waje ta
zubda abincin a dustbin dama dan tayi tsiya tai girkin ba dadi, ta dawo ta dora
plate din kan cinyarshi tace "kakai shi kitchen alaramma "ta shige
daki yayi galala da baki yana kallonta, ya ajiye plate din yatashi yabar gidan
gabadaya,
tagama
abubuwan da take tai wanka ta sanya wata yellow din gownt tana zaunawa kan
mirror fahad ya kira ta ,abun mamakin shine video call ne ba kamar yanda suka
saba ba, batare da wani laakari da ko dankwali babu kanta ba ta dauka ta ajiye
wayar setin ta,
Dukansu
kallon juna sukarika yi ba wanda yace uffan shi yana zaune akan wata resting
chair ne yana sanye da armless riga ,yanata aika mata da kallon love,
ya kure ta
da ido yana kallonta especially her boob's and her beautiful face and hair,
tayi matukar yin kyau,
Can zuwa ya
daure yace "hi! "
Tai murmushi
tana gyara gashin kanta da ya jike ya zubo kan fuskarta sannan tace "hi
"
Ya cigaba da
kallonta tai murmushi ganin be magana ba tace "kayi kyau sosai "
Ya danyi
dariya "kinga na kiraki video call ko? "
Tadaga kai
tana sunna kai tana mai wani irin kallo
Yace
"nakasa hakura ne har nadawo naganki, inason ganin motsin kyawawan lips
dinki da ganin ur beautiful body shiyasa na kira I hop banyi laifi ba? "
Tace
"laifi? Ai baka laifi "
yayi
murmushi "kinyi kyau sosai, se yanxu nasamu natsuwa dana ganki "
Tai dariya
tace "thank you "
Yace
"kinsan me? "
Tace
"a, a sekafada "
Yace
"jibi zamu dawo Nigeria "
Ta zaro ido
tana jindadi tace "wow im
Very happy
to hear that "
Yace
"and I want to meet you on that day"
Ta dan rage
faraar ta don batasan ko aina zasu haduba,
Seyaga duk
ta sauya yace "bakiji dadi ba? "
Tai dariya
tace "I'm very happy mana, that I will meet my handsome "
Yace
"good yanzu what do you want me to buy
for you ?"
Tana
murmushi tace "everything kasan komi abunso ne aguna inde daga gareka ya
fito "
Yanata
kallon yanda take motsa lip dinta yace "I like ur lip "
Tai murmushi
"can I have a good kiss from you? "
Tai dariya
tana bin lip's dinshi da kallo tace
"where? "
Bece komi ba
yadora yatsa a lip dinshi,
Ta dan
sunkuyar da kai kasa yace "plss mana I'm watching"
Ta dago tai
kiss me sauti ta hura masa tana rufe fuska,
ya dafe
zuciya tare da fadin "ashsh "
tai ta
dariya yana kallonta ko kiftawa babu yace "I love you faseelat "
Tai tsit
tanajin dadi namata yawo koina,
Ahankali
tace "love you too dear "
yayi
murmushi tareda fadin "bye "
Bata iya
bashi amsa ba se yatsunta biyu da ta motsa alamun bye, yakashe kiran,
faseelat tai
zaune gun tana tunanin ta yadda zasuyi su hadu daga karshe taja tsoki, tace
"kawai anan ze sameni se me? "🤷🏻♀
Haka akai 2
days dinnan faseelat batawa khalil girki in ma ya dafa seta dauke ta cinye koba
dadi dan kawai yaji haushi,
Kuma kullum
se sunyi video call da fahad ba so daya ba biyu ba dan dukkansu jindadin ganin
juna sukeyi duk Sun dimauce dukansu,
Kafin ranar
da zasu dawo faseelat tasha dilka ta kara kilewa ya fadamata 11am zasu sauka
zezo wurinta da marece se dadi takeji kamar ta rafka ihu,
11 am su
maman amira suka sauka Nigeria, suna makale da juna as usual suka isa gida
sukai wanka suka fita zuwa dauko amira dan daddinta kullum cikin fadawa aisha
yadda yayi missing dinta yake, dukda suna waya yana ganinta
Sun dauki
lokaci agidan momy sannan ya daukosu suka koma gida, lokacin marece ne wajen
karfe biyar saura.
Ya fito daga
gida suna waya da faseelat har bakin kofar gidanta, yana zuwa few minutes later
tafito daga cikin gidan, tana hango mota Sabuwa dal tagane shine ba bata lokaci
ta isa gun motar ta bude ta shiga,
Hmmm kamshin
turarenta kawai ya rikita fahad se mayen kallo yake binta dashi itama seta
kalleshi tasaki murmushi,
yanajin
kamar yajawota ya rungume yace "me kyau kinason kasheni ne ko "
tai dariya
ta girgiza kai yace "se kara kyau kike miye sirrin ?"
Tai dariya
tace"ai kaine sirrina "
Yayi dariya
tace "ya hanya inafatan kundawo lpya? "
Yace
"lpya lau "yana lumshe ido
Tace
"ina my anti da daughter na? "
Yace
"suna lpya suma "
Tace
"alhamdulillah"
Duk sukai
shiru sunata kallon kallo can zuwa ya fiddo wani dankaramin akwati da kwalin
iPhone8s ya mika mata, ta karba tana duba kwalin wayar ta zaro ido tana kallon
wayar duka befi 3wks taga tallon ta a insta ba 500,000 ta kai hannuwa ta rufe
baki, sannan tabude akwatin sega haddadun zinare da yankunne da sarka da yan
hannu takara rufe baki tana mamaki shiko kallonta kawai yake kamar yau yafara
ganinta tace "all this for me? "
Ya daga mata
kai tace "thank you very much, Nagode Allah yakara tsaremin kai ya kara
buda duk kofofin arziki "
Ya lumshe
ido ya bude yace "amin my baby "
cikin kasala
dan gabadaya ta rudashi yace "me zaki bani? "
Tai karamin
murmushi tana sadda kai Kasa tana fatan kar yace tai kissing dinshi don bazata
iyayi ba a zahiri,
Yace
"koba za aban komi ba? "
Ta dago tana
kallon shi tace "me kakeso?"tana rufe fuska, yayi dariya
yace
"nothing but you "
Tana jin
kunya tace "I'm all yours "
Yace
"alright I need your hot kiss that always make me go crazy "
Ta zaro ido
ta tunzuro baki "plss not now, I'm feeling shyness ,"
Yace
"bazan samu ba kenan? "yana langwabe mata
Tace "I
will do that on the phone "
Yayi dariya
yana kallonta wai kunya takeji yace "alright bani wayarki naimiki exchange
na sim "don yasamu yadan taba ta,
Ta dauko ta
miko mishi yahada da hannunta sannan yajanye kamar irin mistake dinnan,yana
amsa ya rumtse ido again yadora kan seat jin soft and smooth na hannunta inaga
b..... Fa
Tana
kallonshi thinking that duk gajiya ce ya sauya mata sim card din yabata sabuwar
a hannu yasaka tsohuwar a kwali ya mika mata nan ma yasamu yadan taban batare
da damuwa ba tace "thank you "
ya kalleta
kawai tace "I'm going inside se yaushe? "
Yace
"anytime, "
Tace
"OK bye ka kulamin da kanka "
tana mishi
wani kallo me kara dulmiya mutum ta fita daga motar,ta shige gida yayi murmushi
ya girgiza kai yace "I love you my lady "
Yaja motor
yabar unguwar,
khalil
isowarshi kenan unguwar yaga faseelat tafito a motar ta shige gida dauke da
leda ahannu cikin daukewar wuta yabita da kallo har tashige yakuma Bin motar da
tafito daga ciki da kallo har tabar layin ,yayi wuf ya sauka daga babur dinshi
ko parking beyi ba yasaki mashin din ya fadi kasa, cikin sauri da bacin rai na
fitar hankali ya nufi cikin gidan yana kwalawa faseelat kira.
Toh fa
kaka,kara,kaka
ina kaunarku
yan golden pen nagaida kowa
No comments