RAGGON MIJI 6-10
*Dedicated
to SIS ZULAIHAT RANO*
a zaune kan
roba-robar shi kallo daya tai mashi ta dauke idanunta, jikin bango ta jingina
kanta na kallon sama ta cije baki saboda Marar ta data murda ,
Shi ko yana
ganin fitowar ta ya mike tsaye yana gyara riga ganin ta jingina a bango tana ya
mutsa fuska yasa shi jin badadi,
Bakomi yasa
faseelat dauke kai ba se dan ganin kara jiya da yau, shadda ce jikinshi fara
kall ya kawo farar hula akanta ga takalmi fari, wayaga balbela🤣
Shi gashi
baki abin se ya dagule, itada tafito ganin canji se taga gara jiya, shaddar se
sheki take tsabar fari.
Shi ko be
samu ganin fuskar taba saboda kanta na facing up ganin Sun kusa minti ukku
yasashi cewa "barka da fitowa"
Batare da ta
sauke kanta ba ta dan juya shi ta zuba mai jajayen idanunta wanda suka kumbura
saboda rashin barci da kukan da tasha ,
Yace
"subhanallah, faseelat lpya kike? "
Ta juya
sannan tace "ban lpya "
Cikin jimami
yace"miyasameki?"
Tace
"fever"tana tabe baki.
Yace
"ayyyah "da karfi wadda tasa seda ta mike daga jikin bango saboda
yadda gabanta ya fadi, Ya cigaba da cewa "Allah shi sawwake shi baki lpya
"
Faseelat
kamar ta dora hannu aka tasa ihu haka takeji, ashe ba karamar illa takeso taiwa
Kanta ba ko magana be iya ba, shi ga bahaushe wani abinda ta dan lura dashi
shine kamar maganarshi daga hanci take fitowa.
yakatse mata
tunani da cewa "ga wannan"
Ta kai
kallonta ga ledojin da yake miko mata, daya babba daya karama, dan dole ta mika
hannu ta amsa can ciki ciki tace "Nagode"yayi kamar be jiba sema yace
"dama zuwa nai mugaisa gashi bakya jin dadi yanzu ni zantafi se munyi waya
ga waya nan da sim da komi "
Batare da
wata murna ba ta kalli ledar hannunta ta yamutsa fuska.
Yace
"se anjima agaida ummi "
ta juya
kawai ta shige gida tana saka da warwara , yadda zata kuma ganinshi in ya dawo
dan kullum kara gano muninshi takeyi.
tana shiga
gida ummi tayi shimfida kan barandar gidansu kafafunta a mike tana huce gajiyar
hidimar da tasha, ta je ta kwanta kan kafafunta,
Ummi tace
"sannu faseelat kode mutafi asibity? "
Ta girgiza
Kai ummi ta kai dubanta ga ledojin da suke zube ta jawosu tana fadin "shi
ya baki wannan?"
Faseelat ta
daga kai idonta na kawo ruwa batare da ummi ta dubeta ba ta Fara bude ledojin,
daya cosmetics ne kawai ciki, danginsu perfume, Nivea lotion, roll on, powder
irin big pack dinnan wadda Zaka samu su concealer da foundation, da janbaki duk
a ciki, se lip gloss.
dayar kuma
waya ce ciki me suna infinix hot 6, ummi tace "aaa!masha Allah Allah yasa
alheri, faseelat kinga kaya ko? "
faseelat da
duk abinda zaa daga wani kululu ke tokare mata makoshi tace "ihhhhm "
Ummi tace
"to ga waya faseelat tunda wayarki tasamu matsala har yau alhaji babba be
aiko da wata ba toga khalil ya hutar dashi "
faseelat ta
mike tsaye zata wuce dakinta dantagaji da jin maganganun ummi, kawai wayar
tafara ringing, ummi tace "zo zo gashi har ya kira ashe a bude take "
Faseelat
takoma ta amsa kamar zatai kuka tashige daki tana shiga ta danna ta a key dif
ringing ya tsaya ummi duk a tunaninta faseelat ta dauki wayar ne, kiran na
yankewa shiru be sake kira ba faseelat ta tabe baki,
Ta haye gado
tana tunanin rayuwar da zatayi nangaba,
Hannunta ta
dora kan kirjinta taji yadda yake fat..fat ta fara hawaye.
khalil yana
be koma gida ba se 2pm dan daganan school ya wuce,
Yana
shigarda mashin dinsa yayi hanyar dakinsa Hjy saratu da ke alwala zatai salla
tabar alwalar tana bin bayanshi da kallo har ya kusa shigewa Hjy tace "kai
zonan khalil"
ya juyo
yaisa wurinta dan slope din dakinta da take kai anan ya zauna tana kallonshi
tace "lpya kake naga ka dawo haka kamar marar lpya? "
ya cire
hular kanshi yana fifita yace "Hjy naje gidansu faseelat na sameta bata da
lpya sosai "
Hjyar tace
"ummm se akai yaya? "
yace
"shine nakeji nima bani lpyan "
Hjy saratu
tai kasake tana kallonshi shi kuma dagaske yake maganarshi ,Hjy tace "to
Allah ya sawwake ,saboda bata lpya shine kake wannan yaushin? kamar ba namiji
ba, tashi da Allah kaban wuri "
Memakon ya
tashi se yace "Hjy yaushe zakije ganinta? "
ta banka mai
harara "se ran da na shirya "
"to me
ze hana kije yau? "
Cikin haushi
tace "saboda ban ga dama ba "
Ze kara
magana tace "aa da Allah kyaleni fita xanyi yanzu idan na dawo zan biya
ingano tan "
yace
"tom "ya mike zakadai -zakadai ya shige dakinshi, wata kan jiya daga
jiya zuwa yau faseelat ta zama wani bangare na cikin jikinshi, ku jifa 😂kunsan irin su dasaurin shiga hannu ,
wayar shi ya
fiddo a aljihu ya kara kiranta bata dauka ba faseelat lokacin ma batasan inda
kanta yake ba dan gabadaya masassara ta
rufeta tana cikin bargo tana kyarma lokacinma ummi na wurinta zaune tana jiran
abba yazo su tafi asibity.
Koda kiran
ya tsinke ajiye wayar yayi shi a kaidar shi baya missed call biyu, (audu ka'ida
kenan)
Hmmm shifa
ba ordinary mutum bane shi rayuwar shi daban take da yadda aka saba gani kude
biyoni muji tasu salon soyayyar.
Au 😂nayi mistake, kaso a soka ai shine so, kaso a ki ka
fa?shi kuma me zaakirashi?
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LBBVKSXqmrj3oaalNYWqmS
➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
7⃣
Dedicated to
*SIS ZULAIHAT RANO*
Abba na zuwa
ummi ta kama faseelat da temakon kaninta abul saboda ko tafiya bata iyayi ga
zazzabi ga ciwon mara ga tension abun da yawa, har cikin mota akasakata,
babansu yana da mota amma ta kwana biyu sede batayi tsufa can can ba ,yayan
abba wanda sunansa salisu suna kiranshi baba babba ummi kuma na kiranshi alhaji
babba mutum ne me kirki da arziki duk da de bawani arziki ne me yawa ba amma ba
laifi tunda yana da zuciyar temakon yanuwan sa shi yakai su ummi hajji ya siya
wa abba mota shine ya dauki nauyin karatun ya umar, kuma a gidansa yake zaune a
Niger Republic din da yake shi alhaji salisun shima dan kasuwa ne yana yawan
zuwa can shine yayi aure kuma yabar matar a can kasar.
Shi kuma
abba tuni ya dena zuwa Niger din iyakar shi nan gida Nigeria duk da ummi can
duk ilahirin dangin ta suke amma alhaji be bari ya zauna a wani gida ba se a
gidanshi wannan kenan.
Asibiti suka
kaita da zuwan su aka sa mata ledar ruwa, bayan allurai da aka mata,
Se bayan
laasar ta farka likita ya shigo yana tambayarta mike damunta yanzu,
Jiki ba
kwari tace "ciwon mara da nan "
Ta fada tana
nuna setin zuciyarta likitan ya dan kura mata ido ta glass sannan yayi yan
rubuce rubuce,
Ya juya
wurin ummi da ke tsaye tanajin duk abinda ke faruwa yace "Hjy ire iren
ciwon marannan inba aure akayiwa yaranba zeyi wuya ya barsu, sannan batun ciwon
heart din rashin cin abinci ne da isashshen bacci wannan kesa ulcer ke kama
mutum wuf daya, se akiyaye duk abinda na fada banda abu me tsami ko yaji ko mai
da yawa arika bata abinci akai akai "ya juya bayan ya gama jawabin yana
kara kallon faseelat,
ummi tace
"insha Allah zaa kiyaye, kuma ankusa yin bikin ta ma "
Likitan ya
Mike tsaye yana gyara ta kaddun hannunshi, shi da har ya fara tunanin ya samu
ta ukku, matanshi biyu, ya killace a gida dukansu farare ne tass dan yanada
gurin ajiye fararen mata kuma dukansu a asibity suka hadu daya ma kauye take
daga amai da gudawa ya aure ta.
Fita daga
dakin yayi yana fadin ,"Allah ya sawwake, "
ko da abba
ya dawo hospital din samu yayi an sallame su dan lokacin kusan 6:40 ya biya
Bill suka wuce gida.
Bakin wani
pharmacy suka tsaya abba ya Shiga ya siyo magungunan da aka rubuta musu sannan
suka wuce .
suna isa
ummi takama faseelat suka fito har zuwa dakin ta ta kwantar daita malt da milk
ta hado mata tasha tasha magunguna ta kwanta baadade ba bacci ya dauketa.
Can ana
kiran sallan ishai se ga Hjy saratu kamar daga sama tana sallama ummi da
fitowar ta wanka kenan ta amsa tana mata marhaba Hjy saratu ta shiga ummi tai
mata iso har daki,
bayan sun
gaisa take tambayar ummi ya me jiki?
ummi tace
"dasauki dazunnan ma aka sallamomu daga asibity dan seda suka saka mata
ruwa"
Hjy saratu
tace "Abu beyi dadi ba Allah ya sawwake ya bata lpy ai tundazun naso zuwa
se kuma na makara wajen fitar diyar kanwata ta haihu shine muka tafi suna
tundazu inata so na taho se yanzu Allah yayi ina rokon Allah yabata lpy "
Ummi tace
"amin"
Hiya saratu
tace "tunda Khalil ya koma naga ne ba lpya ba dan kamar kwai ya fashe masa
a ciki haka yayi "
Ummi tai
dariya "khalil kenan ai dazun da yazo ya cika faseelat da abun arziki
harda su waya a cikin kayan, Allah de ya kara budi na alheri "
Hjy saratu
tace "amin amin,bari naje na dubata na wuce gida"
Suka mike
suka fita zuwa dakin da faseelat ke kwance,
Har lokacin
tana bacci ummi tace "bata tashiba kila cikin drugs da aka bata akwai na
saka bacci ciki "
Hjy tace
"to ni zanwuce Allah ya kara bada lpy "
Ummi tace
"amin "
Ta na mata
tattaki zuwa bakin kofa seda suka kai can ummi ta dawo ta shige daki ta'ida
shiryawa, sannan tafito.
Ana gama
isha'i duk suka hallara ummi takawo masu babbar cooler datake zuba musu abinci
se plates da spoons suko sunbaje akan tabarma, kowa ya dibi nashi suka fara ci,
Mubarak yace "ummi ni de nakoshi tunda yaya bata lpya"
Ummi tace
"haba dan auta na, ka daure kaci ga faseelat can tana cin Nata itama
"
Yace
"dagasske ummi? "
Tace
"eh kai sauri ka gama cika cikin ka se kaje wurinta yace to "yafara
buga loma.
Su ummi basu
dade da barin dakin ba tafarka ba laifi massaran ta sauka tun asibity ciwon ma
ya lafa, sede ciwon da zuciyarta ke mata, baa jima ba taji wayarta na vibrate
taja dogon tsoki kamar ba marar lpya ba afili tace "dan wahala"
Hjy saratu
na'isa gida take bawa khalil labari tace "ashe haka faseelat ke jin jiki
?umminsu tace dazun har seda aka kwantar dasu asibity"
Yace
"Hjy suna asibitin yanzu? "
Tace
"a, a an sallamo su agida na samesu "
Ya tashi
tsaye daga shi se jallabiya ga zungureriyar casbahar shi yana ja yace
"bari na dawo hjy "
Hjy na
kallonshi tace "kai dawo nan ina zaka? "
yace "yanzu
zan dawo fa hjy gidansu zanje "
Tace
"Kai baka da hankali da zaka je
gidansu yanzu? "
Kawai ya
juya "sena dawo "ya fice
Niko nace
hjy barshi kinsan dogo dama be cika hankali ba 🤣🙊
Ya fidda
babur dinshi yaja akan hanya ya tsaya wata supermarket ya siyi chivita da
hollandia da malt da short cake da big biscuits gefen shagon ya siyi fruit
irinsu orange, banana da pineapple
daya wuce gidansu, lokacin kusan karfe 10pm
dan har Sun kulle gida ya yi parking machine dinsa ya fara kwankwasa gidan,
Be dade da
fara kwankwasawa ba ishak ya fito bema sanshi ba hakanan yace masa
"inayini "
Khalil yace
"lpya lau, ya me jiki? "
ishak yace
"dasauki "
Khalil yace
"Allah shi kara afuwa, ga wannan ka kai mata "
Ya mika masa
ledar ishak ya amsa yace "injiwa? Za a ce?"
Yace
"khalil "
ishak ya
juya yasaka sakata ya shiga cikin gidan abba da yake zaune shi ma yace
"waye ne ?"
Ishak yace
"yace khalil ne kuma yabada wannan yace abata "
Abba yace
"kai ma ummi tana can wurinta
Ya juya zuwa
dakin ummi kadai ya tadda tana gyara wa faseelat gado ita kuma tana toilet yace
"ummi gashi inji khalil yace yana gaida me jiki "
Ummi tace
"oh cikin darennan ya taso to kawo "
Ta amsa ta
ajiye shi kuma ya fita baa jima ba faseelat tashigo dakin,
Wajen
wardrobe dinta tawuce ta kimtsa kanta sannan ta dawo ta zauna kan bed.
Ummi tace
"ga kayan marmari ankawo me zakisha? "
Faseelat
tace "nakoshi ummi ruwan zafi kawai nakeso insha "
Ummi tace
"to bari in je inhada miki amma ki tashi ga ayaba nan kici ko kadanne
kinsan tana rage menstrual cramps "
Tace
"to "
Ta amsa ta
bare tana ci tana yamutsa fuska.
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By *MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
8⃣
Dedicated to
*ZULAIHAT RANO*
Lokacin da
ummi ta dawo har faseelat taci biyu, mika mata tea din ummi tayi tana fadin
"bansa sugar ba amma nasa miki citta da yawa saboda tana koro jini da wuri
"
Faseelat ta
amsa "Nagode ummi "
Ummi ta
zauna tana kallon faseelat tace "dazun Hjyarsu khalil tazo kina bacci tana
gaidaki da jiki "
Faseelat tai
shiru bata ce komi ba,
Ummi tace
"baki tambayi wanda ya kawo miki fruit dinnan ba "
Faseelat ta
kurbi tea tace "nayi zaton abba yakawo "
Ummi tace
"a, a khalil ne ya kawosu yanzu da darannan "
Kuts-kuts ta
zubdo tea din bakinta wani kuma ya sarketa tafara tari,
Ummi tace
"kibi a sannu mana inya miki zafi kibarshi ya huce tukun "
Faseelat ta
goge gefen bakinta taajiye copyn tea din tai shiru tana mamakin wane irin mutum
ne khalil itade ba sakarmishi fuska take ba sannan bawani sabawa sukai ba
ballatana ya dinga yi mata wadannan abubuwan,
Ummi ta
katse mata tunani da cewa "kind ace da miji faseelat alamu duk sun nuna
haka yaro me kunya da tarbiyya, duk dade bansan halinsa ba amma ina mai kyakykyawan
zato, Dan Allah faseelat ki saki jikinki sosai naga tunda yazo kike ciwo
bansaniba ko hakanan kika amsamin amma baki son auren shi "
Faseelat
tace "ummi gaskiya na amince ne saboda kawai kiji dadi ba dan inason shi
ba "
Ummi tace
"ai nangaba zakiso shi "
Faseelat
tace "hmmmmm "
ummi tai
dariya "kiyi magana mana nasan nangaba ko ance auren hadi akai muku mutane bazasu yarda ba danni nasan nabaki
many lessons daga tasowarki zuwa yanzu Wanda ko bankara da komi ba sunisheki
zaman gidan miji, kuma kina da komai da zakija hankalin namiji dashi inde har
kinmeda hankali mallake namiji baze miki wuya ba ,zaki so shi ki haifa masa
yara Kema kizama uwa me koyarwa kamarni"ummi ta'ida maganar da murmushi
fuskarta.
faseelat
batace komi ba batasan komi ze faru nan gaba ba amma bata tunanin zataso khalil
ko ta so shi bawani so sosai ba, saboda tadan fahimci wasu abubuwa dangane
dashi.
Ummi ta
katse shirun da cewa "ga kayanda ya kawo ki dauki abinda kikeso na kaiwa
yanuwanki sauran "
Faseelat
tace "ni nakoshi ki tafi dasu kawai "
Ummi tace
"to ki sha tea din kar yayi sanyi kuma "ta dauki ledar tai waje
Faseelat ta
yi tagumi ji yadda komi ya jagule mata lokaci daya saboda kawai ummi ta kamata
tana wankan janaba inda bataganta ba bazata matsa mata haka akan aure ba,
faseelat sede taji hawaye Sun zubomata anata abubuwa kamar gobe ne auren why?
ita tai
kanta haka ne haka Allah ya halicceta mata nawa ne irinta? Maza nawa ne Irinta
suma haka iyayensu ke matsa masu akan aure ko se ita dantana ya mace tilo gun
mahaifiyarta? Ta share hawayenta tana daga kai cikin zuciyarta tace bazan kara
zubda hawaye na akan batunnan ba zanyi kokarin hakan.
(yo anya
zata iya?)
ummi nafita
ta kaiwa abba kayan ya gani tace "me zaabaka? "
ya dauki
hollandia yace "wannan yayi "
Ta tashi su
ishak nata fira abul na gefe yana duba handout ummi ta zauna tsakiyarsu tace
"Mubarak kawo wuka"
Ya tashi
domin daukowa,
Abul ya
kalli kayan "wai ummi waye ya kawo kayan nan "
Tace
"kubakusan antinku aure zatayi ba? "
Ishak yace
"wannan kai "
abul yace
"yaakayi ne"
Ishak yace
"lokacin da na bude gida naganshi tsaye ya bani tsoro dogo ne sosai nazata
ma aljani ne "
Ummi ta
rumtse masa baki da hannuwanta tace "ubanka so kake ka kara tunzura
yayarku"ta juya tana kallon wajen dakinta
Abul ya kece
da dariya ,"ummi kibarshi ya ida mana"
Ummi ta
harareshi "kayi dede Allah yayi maka albarka "
daya daga
cikin sirrin ummi ko wane laifi zaaimata sede tace Allah yayi albarka bata taba
cewa komi fiye da wannan sede harara.
Mubarak ya
dawo da wuka hannunshi yana mita wai wukar can karkashin kwandon wanke wanke ya
ganta ummi tace "to me kauda kayan bata lpya se inta tashi tukun "ta
yanka kayan marmarin suka fara sha sunayi suna labari.
Hjy najin
motsin mashin din khalil tafito waje seda yayi parking tace "kai dogore
seda kaje dinko? "
alhajinsu ya
leko tunkan khalil yayi magana "ai gwara da yaje zasu kara ganin yadda
take da mahimmanci a wurinshi "
Hjy ta rike
haba "ah to yayi ka ganta ko? "
Yayi shiru
ya shige daki.like mother like son wajen shegiyar tambayar yaya akayi aka haifi
uwarka.
The
following day.......
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
9⃣
Dedicated to
*sis Rano*
Ta kama ran
Friday salla day awurinmu musulmai, bayan ya dawo daga masallaci da asuba ya
shiga ya gaida Hjy ta amsa ciki -ciki yace "Hjy lpya? Ko nayi miki wani
abu ne? "
tai shiru ya
kara memetawa
Tace
"da Allah tashi kaban wuri "
"Hjy
dan Allah kiyi hakuri innayi miki laifi bada sani naba "
"bakasan
laifin da kayi ba kenan? Jiya ban hana ka zuwa gidannan ba da daddare amma seda
kaje, tunda kaje kaga yarinyar nan shikenan ba saura ba kingi duk ka zauce, aka
gaya maka haka akeyi ? ko dama can kana santa bansaniba?"
Maganganun
hjy sun matukar bashi mamaki yace "haba Hjy kefa kikayi wannan hadin ni
ina zan santa ma bare na so ta, kuma ni wlh hjy banga wani abinda nikeyi ba
dede ba, jiya kuma Banyi tunanin tafiya ta zata bata miki rai ba, kiyi hakuri
"
Tace
"to naji why kake ta kashe kudi har haka danna ce kai mata kyauta aiba
cewa nai kaita kashe kudi ba .
Shiru yayi
kanshi duke tambayar kanshi yake mi yasamu Hjyarsu.
can zuwa
yace " bawani kudi bane fa sosai waya kawai na siyo mata se cosmetics
that's all "
Ta Harare
shi "eh ba kudi bane masu yawa tashi kaban wuri, ai gwara ayi ai auren ko
kasamu kanka, ni wlh dama kauye naje nasamo maka yar yarinya"
ya tashi
tsaye ya shafi sumar kanshi can zuwa yace "Allah yabaki hakuri "ya
fita
Tace
"amin"
Khalil kusan
Karo sukayi da alhaji yayi saurin zukunnawa gaida shi alhaji ya amsa ya wuce
ciki.
Khalil ya
tashi ya tafi saboda shirin makaranta .
Alhaji yana shiga
yafara wa hjy fada "wato de sararu bazaki bar halinki na banza ba ko?
saboda nasan halinki fa shiyasa ban kara aure ba danna san duk wacce na aura
kashe ta kadai ke bakiyi, yanzu kuma ga matar danki zaki koma, to kibi Ahankali
wlh tun kafin yaronnan ya fahimci manufarki "
komi batace
ba ta tabe baki a ranta tace "aini ma bansan haka yake ba nazata ze cigaba
da halinsa na rashin son auren.
7:30 khalil
ya fito da shirin shi yau kam yayi kyau wani yadi ne ash color yasa mishi bakar
hula da bakin takalmi rigarde tazarce ce da alamu duk haka dinkunansa suke
hular ma tayi gaban goshi sosai shima da alama haka yake saka hular shi, ya
leka kitchen hjy se diminiya take dan kawai karyayi kalacin danwake ne zatayi
amma tai nan tai nan batare da ya damu da rashin hada kalacin ba yace "Hjy
natafi "
Tace
"Allah ya bada saa "fuskarta ba yabo ba fallasa.
Ko damuwa
beba ya bar gidan se sannan hjy tagama danwaken,
karfe 9
siyama ta shigo gidan tareda yaranta biyu "Fatima da farida "
hjy saratu
tace "oyoyo oyoyo yan albarka "
siyama tana
fara'a tace "hjy ina kwananku "
"lpy
lau ya jikin kwana biyu da kikai ba lpy kamar kin kwana goma wajen sunan ramla
se tambayarki suke "
Tace
"eh wlh hjy amma jiya na aika mata da sako kuma Bayan kwana biyu zanje
gidan na gano takwara, ai wlh naji jiki hjy danbana iya komi, abdulkadir ke
komi har girki "
hjy tace
"Allah yasa kaffara ne,"
siyama tace
"amin su yaya ana makaranta "
hjy tace
"uhm antafi ai yayanki ya kusa zama ango "
siyama na
murna tace "dan Allah Hjy wacece yarinyar "
Hjy saratu
tace "eh ba wata bace se faseelat "
Siyama tana
murna tace "faseelat de wadda nasani Hjy? "
"itafa
"
siyama tace
"gaskiya naji dadi hjy Allah yasa alheri ai faseelat full option ce komi yaji,
tana dariya tace "finally yaya zaayi aure "
Hjy tai
dariya siyama ta mike tsaye "Hjy mi zaa dafa muku yau ?"
Hjy tace
"komi kikayi yau de jumaa komiye de da miya zaki "
"ayi
taliya da miya NE? "
Hjy tace
"a, a kide yi shinkafa kinsan khalil beson taliya gwarama in anyita da
safe shima se anci saa kawai kiyi shinkafar se ki dafa masa wake, dan kinsan
shinkafar ma baya sonta ita kadai "
Tace
"to "tai hanyar kitchen.
Khalil ko
school ya wuce ,jss classes yake koyarwa duk jiki mace yake komi maganganun hjy
nata mashi yawo yanata kara nazarin su,, ga rashin lpyar faseelat data dameshi.
12:30 aka
tashi saboda sallan jumaa direct supervision store yawuce ya siyi su peak milk
, bournvita,cornflakes,block sugar, golden moon da tea bag, da different sweet
, kusa da wurin akwai oasis bakery ya saye big bottle ice cream da snacks ya
nufi gidansu faseelat .
yana isa
yayi dede da dawowar Mubarak daga school , Mubarak se kallonshi yake, khalil ya
jawo shi "abokina zo mugaisa "
Mubarak de
yayi tsaye yana kallonshi khalil hannunshi ya kamo yasaka a nashi yace
"ummi na gida?"
Mubarak ya
daga kai
Yace
"yayar ku fa ya jikinta "
Mubarak yace
"dasauki dan dazun naganta tafito zatai shara ummi ta hanata "
Yace
"good kaje kafadawa ummi cewa khalil yazo yana so ze shigo ya gaidata
"
Mubarak yace
"to"
ya shige
gida seda yafara shiga dakinsu ya ajiye jikkarsa sannan yaje ya fadawa ummi,
ummi tarike baki "Allah sarki yaron kirki ,jeka ce ya shigo "har ya
tafi tace "Mubarak dawo jirani "
tashige
dakin faseelat, faseelat taji sauki sosai dan wayar da yabata tasaka wa tsohon
sim dinta, tai checking balance babu kudi ciki tanayin Wanda ya kawo taga 1000
ta tabe baki ta siye data tayi download what's up tai installing messages
sunata shigowa ummi tashigo ,"ke ki tashi ki kimtsa ga khalil nan shigowa
"
faseelat
tace "khalil ?"tana zaro ido
Ummi tace
"eh ki tashi gashinan shigowa "ta juya Tabar dakin faseelat tace
"mtssww shikenan fa khalil khalil maganar kenan ta kalli riga da wandon
dake jikinta fakistan tace "ni shirye nake danban kara irin gayunnan
saboda shi "
Ummi nafita
tace yashigo tashige daki ta sako hijab.
Tare da
Mubarak suka shigo yana dauke da katuwar bakko,
Har bakin
dakin ummi yayi sallama ummi ta amsa tace "maraba ka shigo "
ya dan
sunkuya dukda tsayin kofar ya shiga memakon ya zauna kan kujera ya xube kasa, a
sannu ummi ta saci kallonshi tace "kambuu da wannan ne faseelat ke kushewa
ina laifinsa yanda mazannan sukayi tsada,
Ummi tace
"a, a katashi kazauna saman kujera "tana sunkuyar da kai na surukai,
Yace
"ina yini, "batare da yakoma ma waccan maganar ba.
Ummi ta amsa
akunyace yace "ya me jiki? "
Ummi tace
"dasauki "
yace
"Allah shi bata lpy dama zuwa nai nagaisheku"kanshi a kasa shima
kunyar yakeji
Ummi tace
" amin angode kwarai "
Dama da
shigowar shi ya jingina bakkon jikin cushion hannunshi ya cusa cikin aljihu ya
zaro kudi a kalla sunkai 10 ya ajiye sannan yace"ni zanwuce "
Ummi tace
"to angode bari na kira maka faseelat din "
Bece komi ba
ummi tafita Mubarak de na zaune ummi nashiga tacewa faseelat "ki tashi ki
shiga ku gaisa "
faseelat da
tunda taji sallamar shi taji zazzabi ya fara rufeta ta tashi tafita kamar me
koyon tafiya,
Ummi tace
"yar rainin hankali har ciwon ya dawo ko "
Faseelat ta
shiga da sallama bakinta, wani sanyi ya mamaye zuciyar khalil ya dago kananun
idanunsa ya zuba mata, kallo daya ta masa ta samu kujera ta zauna.
Yace
"inawuni malama faseelat,"faseelat ta kalli zungure riyar hijab din
dake jikinta tai shiru,
yanata
kallonta yace "ya jiki?"
ta lumshe
ido ta bude tace "naji sauki ai "
Yace
"da sauki zaki ce de, tunda baki warware ba "
Tai shiru
Yace
"to Allah yasa kaffarane "
Tace
"amin "kasa-kasa
Ta dago ta
saci kallonshi Sukai 4 eyes seda gabanta ya fadi ta rasa wane irin kallo yake
mata, shiko kallon luv ne yakeyi, to da yake de sabon shiga ne se kallon yayi
kama da kallon ruruwa🤦🏻♀Inajin harda kallon luv se kun koya mishi 🤣
Faseelat ta
kauda kai sannan ta dago ta kara kallonshi lokacin ya dauke ido yana magana da
Mubarak harda kudi ya bashi, wannan ya bata damar kallon dressing nashi a
zuciyarta tace not bad,
Ya mike
tsaye yana jifanta da wannan kallon yace "ni zanwuce "
tafara wasa
da hannunta,
yace
"ba bankwana?"
Tai shiru
yace "to natafi amma plss ki rika daukar kira na i have called you several
times but you don't pick my calls why? "
Faseelat
seda murmushi ya kufce mata saboda
jindadi atleast de yana iya kwantar da murya wajen pleading kuma ya iya turanci
daya daga cikin abunda take so wajen mijinta.
akan idonsa
tai murmushin wani farinciki ya mamaye shi ganin smile a fuskar ta,
Yace
"I'm pleading I hope you will accept my request "
kawai ta
girgiza kai dariya tazo kufcemata ta jawo hijabinta ta rufe fuskarta.
yayi dariya
yafita ummi bata waje danhaka yawuce har kofar gida Mubarak ya rakashi khalil
nata masa labarai,.
Yana wucewa
Mubarak ya shigo gidan dede fitowar faseelat daga dakin taci dariyarta se kuma
daga karshe ta dinga buga tsoki,
sukayi
kicibus da ummi.
Mubarak yace
"gaskiya ummi yana da kirki sosai jibi kudinda ya bani "ya fiddo yan
200 guda biyar da yabashi sabbi fill
Ummi batabi
kan maganar shi ba hankalin ta na kan faseelat daketa murmushi ummi tace
"wai lpya kike ta dariya ke daya "
Faseelat ta
daure fuska "bakomi "tashige daki da sauri
Ummi tace
"hmmm Allah ya shirya ki "
Ta Shiga
dakinta, tana zare hijabin jikinta ta jawo bakkon ta bude kaya niki -niki, ta fiddo
Ice cream da snacks din ta ajiye gefe guda,
Kudin da ya
ajiye ta kirga nera dubu goma ciff ummi tai murmushi ta jawo wayarta tace
"bari na kira hjy saratu nai mata godiya "
Batare da
tunanin komi ba ta dannawa lambarta kira.....
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
🔟
Ringing biyu
Hjy saratu ta daga bayan gaishe gaishe ummi
tace "yanzu khalil ya fita yashigo har gida mungaisa, mun gode da abun
arziki "
Hjy saratu
tana ta faraa kamar duka knan tace "ah bakomi wlh ai anzama miye aciki
"
Sukai
bankwana ummi Nata godiya sede bata fada mata yakawo wani abu ba Hjy saratu tace
"hmmm yanzu haka wani abun ya kai musu, kowa na haramar tafiya masallaci
shi yanata surukai," taja dogon numfashi "nasan abinda zanyi komi
zezo karshe "
Shi ko
khalil masallaci ya wuce daga gidansu faseelat, hankali kwance, gabadaya jiyake
kamar bashi ba, soyayya ta fara sauya masa rayuwa.
Faseelat kau
seda ta shiga daki ta kara jan tsaki "komiye na mishi dariya ma? Nan fa se yayi tunanin tafara sonshi ne
"ta kara jan tsoki,
Ta jawo
wayarta messages sungama shigowa abinda ta lura groups dinta Sun ragu dama inka
dade baka online groups fita suke, bin groups din tafara yi taga wadanda suka
fitar daita,
Taga kusan
group bakwai ta fita, se tafara bin numbers dinta tayi wa friend dinta magana a
medata wasu ,akwai wani group sirrin mu mata, shi ta fara shiga saboda tanajin
dadin group din, messages din wasu Sun bude wasu basu bude ba, tatura sallama
,suka amsa tace "plss masu group suyi adding dina ko abada number ta asani
nadade bani online ne "
Se akafara
mata reply da welcome masu turo sticker na turowa, wata me suna maman amira
tace akwai wani group amma se kinbiya 500 ake adding naki ana karuwa sosai
ciki,
faseelat
tace "anayin share and self? "
Maman amira
ta turo mata "eh anayi, Ko kati ko
BTU ko transfer "
Faseelat
tace "kiban no din admin zantura mishi through share and self saboda banda
kudi "
maman amira
tace "ayya zan biyamiki asaki ki dan jira "
Faseelat
tace "amma de Nagode aunty Allah yaraya amira "
maman amira
ta turo mata smile face.
daganan
faseelat tai taganin new groups na matan aure wasu na novels ana sakata,
Seta bi
maman amira PC tana mata godiya maman amira tace karkidamu sister sunanki kawai
ya burgeni ,faseelat tace zan'iya adding number dinki?
maman amira
tace"yes zakiiya nima zanyi adding taki "
Faseelat ta
tura mata thanks you" (the Fateful relationship just begun)
Ko minti 10
baaiba akayi adding nata ta tura" slm "
Maman amira
taturo "you are highly welcome friend "
Faseelat
tace "I'm grateful "
Fitowa tai a
group din tafara bin status daya bayan daya sannan ta sauka online,
fitsari ne
ya matseta ta tashi tafita waje dasauri,
Ummi tagani
tafito daga kitchen hiyaki ya korota, tai sauri tashige toilet ta biya bukata
ta dawo, ta tafi gun ummi "ummi for god sake miyasa kikeson wahalar da
kanki nace naji sauki kibari nayi "
ummi tace
"ai gwara narinka shiga ciki ko na saba tunda tafiya zaki kibarni ni daya
"
Faseelat
tace "eh naji amma bari nashiga inbani nan kyayi din "
Ta kutsa kai
kitchen din duk da hiyakinsa inda sabo ta saba .
Hjy saratu
kau alhaji ta dannawa kira, bayan ya amsa yace "lpy de ko kira gab Shiga
salla "
Tace
"eh dama so nike ince maka inason zamuyi magana inka dawo "
yace
"To saurin mi akeyi da antaso masallaci zanshigo gidan "
Ko to batace
ba ta yanke kiran,
Siyama ta
fito daga kitchen tana kai abinci daki har ta gama sannan ta zauna tana
"wash Allah na "
Hjy ta kure
ta da ido tace "wannan dan aikin? To ko de ciki gareki "
Siyama tai
murmushi batare da tace komi ba,
Hjy tai
dariya "to Allah ya raba lpy "
Siyama tai
tsit can tace "bari naje nai salla "
Hjy tace
"har lokaci yayi ne "
Tace
"eh karfe 1:40pm"
Hjy tace
"bari mutashi muma "
Ana saukowa
masallaci alhaji ya taho gida yana shiga da sallama bakinsa yaran siyama suka
gudu suka tarboshi ya tallabo kawunansu sukayi ciki, yanata jindadi,
Dakinshi ya
wuce kai tsaye ya rage kayan jikinshi ya dan kishingida sega siyama takawo masa
abincinsa suka gaisa ya mata ya jiki ta fita tareda yaran.
Yana
tsakiyar cin abinci Hjy tashigo ta zauna sannan tace "sannu da zuwa "
yace
"yawwa yana Kai loma bakinsa "
yace
"wai maganar mi cece da baajira na dawo "
Tace
"dama bawata magana bace seta khalil da faseelat "
Ya ajiye
cokalin hannunsa yace "inajinki"
Tace
"nace mi zaihana akai kudin neman aurensu tunda de akwai su, bayan ansa
rana se su cigaba da fahimtar juna kafin auren, nasan shima khalil din zeso
hakan."
yadanyi
nazari for some minutes sannan yace "yanzu de kifara yiwa mamanta maganar
duk yadda kukai se inji saboda kamar abun yayi wuri "
Tace
"haba bawani matsala amma bari na kirata "
ta kwalawa
siyama kira tace mata ta miko mata wayarta, takawo mata ta juya.
hjy tayi
dialing number ummi
Tadanyi
ringing sannan ummi ta dauka da sallama,
Hjy tace
"kinga na sake kira ko,dama maganar yarannan ce to munyi magana da alhaji
kiyi magana da abbansu in anbada izini zaaturo "
Ummi tace
"to ba matsala nasan yanakan hanyar dawowa Inya dawo zamuyi maganar duk
yadda mukayi zakiji "
Hjy tace
"to Nagode kwarai se na jiki "
Ta yanke
kiran
Alhaji bece
komi ba ya cigaba da cin abincinsa.
Khalil
siyama nafita ya shigo tafara zaulayar shi, yana dariya yace "siyama
bakiji ni kuma ake zolaya? Ni yayan. "
Tace
"hmm yaya kenan ,yanzu de kabar number anty ta mufara gaisawa "
yace
"zanbaki amma ba yanzu ba, kije ki daukomun abinci na tukun inna gama se
muyi maganar "
Ta kawo masa
abincin yafara ci dan mutuminnaku be wasa da k'oto.
Seda ummi
tabari abba yagama cika cikinsa da daddadan abincin da faseelat ta dafa sannan
tafada mishi yadda akai yace "kunde nace ga hadin nan auren hadi matsala
ne dashi in aka samu sabani, "
Ummi tace
"insha Allah bawata matsala"
Yace
"to yanzu de su bamu lokaci kamar nanda sati daya, dan inaso nayi bincike,
bama wannan ba ita faseelat din ta amince ne? "
Ummi tace
"eh mana ko akirata ka tambayeta? "
Yace
"eh kiramin ita "
Ummi tatashi
ta fita kiranta daga can bata dawo dakinba,
Faseelat ta
zauna "gani abba"
ya kalleta
sannan yace "kinji iyayen khalil zasu aiko me kikace? "
Faseelat
gabanta ba karamin faduwa yayi ba tai shiru ta sadda kai kasa,
Abba yace
"kin amince? Yanzu kina sonshin? "
Kuka ne
yazowa faseelat tai saurin rufe fuskarta da hijabin jikinta,
Abba yayi
tunanin ko kunya ce yace "to tashi kije? "
Ta tashi da
gudu tashiga dakinta ta fara kuka me cin rai.
No comments