RAGGON MIJI 11-15
Kukan nata
bame sauti bane ,zeyi wuya kaji shi inba dakin kake ba,
Tadau tsayin
minti 15 tanayi, se tafara magana da
zuciyar ta,
"ba
kince bazaki kara kuka ba to me kikeyi yanzu"
Dayar
zuciyar tace "i have to ko don na rage zafin da ke tsatstsafowa a
raina"
Dayar
zuciyar ta tace " you're only wasting your tear, ba abinda zaafasa, so you
better stop it"
"you
are right fa "ta sa hannu ta share hawayen nata.
Tambayar
zuciyarta take "to me yakamata nayi? "
Dayar tace
"don't ever take decision in haste, kibari ayi auren mana "
Shiru tayi
tana tunani
Can zuwa ta
Saki murmushi ita kadai tasan abinda ta kulla, se ta mike zaune, ta jawo
wayarta ta fara chart.
Bangaren
khalil ko seda cikin shi ya cika tabbb sannan yasha ruwa sukafara labari da
kanwar shi, har yabata number faseelat din kamar yadda ta bukata, shiru shiru
Hjyrsu bata fito ba seya fita zuwa wurin best friend nashi wanda suke tun suna
yara amma saboda irin yanayin khalil basa sharing problems nasu ma juna, ana
taren ne kawai.
Ummi na
komawa abba yace "ba matsala tunda ta yarda ki kira ita hjyar ki fadamata
yadda mukayi "
Ummi tace
"to "
Ta kira hjy
tafada mata duk da de hjy ba haka tasoba amma se tace "ai bakomi sati ai
kamar gobe ne "
Alhaji najin
yadda Sukai yace "to Allah yakaimu satin zanyiwa su yakubu magana dan su
shirya da sunbamu rana se suje "
hjy saratu
tai murmushin jindadi.
Faseelat na
tsaka da charting kiran siyama ya shigo ta dauka tai sallama, daga can bangaren
aka amsa,
Akace
"antinmu inawuni "
Faseelat
tace Anti kuma? Ai batada kanwa mace sannan bama haka ake kiran taba ta daure
tace "wa ke magana? "
Siyama tace
"kanwar mijinki ce siyama"
sora kirisss faseelat tai ta bargaza dan harta
hade baki da niyyar yin tsoki tai saurin fasawa, tace "ina yini "
Siyama tace
"lpy lau anty dama cema yaya nayi yaban number ki mugaisa "
Faseelat
tace "ihhhhn Nagode "
Siyama tace
"bakomi se anjima agaida su ummi "
Faseelat
tace "ihhhhm "takatse kiran ta turo baki gaba tare da cewa "Se
kuyi tayi ai nide nawa ido"
Kiran wata
number yashigo wayarta da alamu number Niger ce saboda digit din farkon number
din, tadesan baze wuce danginsu ba ko ya umar, yaushe rabon ma suyi waya
ankwana biyu
Ta daga
kiran ta kara wayar a kunne "assalamu alaikum"
Ta fada
,murmushi ya doki kunnenta akace "waalaikumussalam"
Tunda taji
murmushin ta gane me magana, yanayin yanda ya amsa mata sallama da zolaya ya
sata tafara dariya,
Tana dariya
tace "yaya na, kaine kamanta dani kwana biyu ko? "
shima yayi
dariyan yace "ina ni ina mantawa dake duk in mukayi waya da ummi ina cewa
ta gaidaki bata fadamiki ne? "
"Allah
ni bata fadamin"ta zumburo baki kamar yana ganinta.
Yace
"to laifin ummi ne ba nawa ba tunda kinsan bakida waya yanzu ma hakanan
nace bari nakira layinki se gashi tafara ringing, kice baba babba har ya siyi
wata, dan nasan ummi de bazata se miki waya ba tunda kudinta kaff suna karewa
ne wurin se miki cosmetics, kuma nasan abba baze siyamiki waya ba ya fiso ki
karatu besan shiririta "
Tace
"a, a ba shi yasiyamin ba fa "
Daga can
yace "to waye? "
Tadanyi
shiru sannan tace "yaya su ummi da abba are planning to get me
married"
Tai maganar
kasa -kasa.
yace
"very soon haka with whom? "
tace
"wani ne sunanshi khalil dangidan kawarta "
Yace
"to, what's in your mind did you like him "
Tai shiru
Yace
"faseelat are you with me? "
tace
"yeah ,honestly yaya bana sonshi but I will marry him, as they wish"
Yayi shiru
saboda problem da yaji daga wurinta can zuwa yace "will you... Se yayi
shiru "faseelat zama da wanda baka so, will not give you a good and
peaceful marriage life, akwai wani freind dina ya auri wadda bata sonshi at the
end auren mutuwa yayi dan ko 5 months ba suyi ba, "
Tace
"yaya tunda de ummi na so to zanyi hakuri in aure shi haka "
Ya fitar da
iska "huuuuuuh, to naji Allah yasa haka shi yafi zama alheri all the best
"
Tace
"amin, ina su dije su hanne su fatouma su kawu "
Yace
"actually i really don't know cos nayi Week banje gidajen su ba "
Tace
"kana nan wurinsu fadila sun rike ka "
Yace
"bahaka bane fa, I'm very busy we are about to start exam ,karatu ne kurum
ya hana .
tace
"to Allah ya bada saa, agaida ammah da su fadila da husna ka fadamusu ina
missing nasu "
Yace
"OK bye "
Ya kashe
kiran ta sauke ajiyar zuciya da ma ace kanwa na auren yaya da ya omer kawai
zata aura, ji yadda yake magana gashi kyakkyawa ga daukar wanka best dress dinta English dress, tace
"gaskiya yaya matarka ta mo re wlh"
Abba bugawa
baba babba waya yayi ya fadamasa abinda ake ciki, yace baya gari se next week
ze dawo amma yanzu zeyi sqeesing ya dawo, saboda shine madaurin auren faseelat,
Abba be yi
kasa a gwiwaba ya fadawa abokinshi yace Dan Allah ya masa bincike akan khalil
abokin nashi yace ba matsala, sannan ya wuce wurin kannenshi yafada masa shima
yace ze bincika abokinnashi har unguwarsu khalil yaje ya tambayi manyan mutane
gamedashi, hakan be isaba seda yaje yasamu principal din makarantar su ya mishi
bayani shima, haka suka dage bincike.
Bayan kwana
hudu zuwan khalil gidansu faseelat ya ragu inyaje yau be zuwa gobe amma suna
yin waya tunda ta samu lpya shikenan se hankalinshi ya kwanta amma fa duk zuwan
da zeyi se ya ajiye mata bandir din 50 nera guda biyu da Alamu canzo kudi masu
yawa yayi, in yabata bata amsa shiyasa yake ajiye mata kawai ya tafi.
Bangaren
faseelat ba wani improvement saboda har yanzu de ba sonshi take ba watarana in
yan wulakancin na kai inyazo ko kallonshi batayi har yakara sa inda indarshi
yatafi.
bayan sati
baba babba
ya dawo shima yasa ammishi nashi binciken duk binciken da akeyi abu daya ne ke
fitowa bakinsu cewa "mutum ne me kunya da ibada kuma me yawan ambaton
Allah, gaskiya khalil ya samu yabo wurin
mutane,
Hjy saratu
ko tana nan ta zuba ido akan al'amuran khalil duk da de batason wainar da yake
toyawa bayan idonta ba,
yau ummi
takira ta tafada mata zasu iya turowa jibi
Hjy saratu
taji dadi sosai alhaji yana dawowa tafada mishi shi kuma yafadawa wakilansa,
Jibi nayi
sitting room din baba babba ya cika da manyan mutane su 5, akai gaishe gaishe
da ciye -ciye bayan sun gabatarda kansu, sannan suka bada nera dubu 100,
Alhaji babba
da yake dattijon mutum ne yace karsu kara kawo sisi duk radda suka shirya suka
wo kayan sa rana, daya daga cikin wakalan yace su ko yanzu a shirye suke buga
waya kawai zeyi akawo kayan sa rana,
Baba babba
da yake abba ya bashi labarin matsalar faseelat din ya amince ,akasa rana nan
da wata ukku, ko minti 15 baaiba se ga kwalayen biscuits da huhun goro biyu
manya manya ana shigowa dasu, dayake dama alhajinsu khalil yayi retire shine
yabude babban supervision store da kudin retire nashi.
da Faraa
abba yashigo gida ummi na masa sannu da zuwa tace "wai lpy kake ta faraa
"
Yayi dariya
"surukanki har sunzo sun tafi "
Tace
"eh se akai yaya? "
Yace
"uban diya har yasaka rana nan da 3month ran Friday "
Ummi farin
ciki ya lullubeta tace "to Allah yasa alheri "
faseelat na
kitchen tanajin abinda suke fada lokaci daya cikinta ya juya ji Kake
kululululu, ta tashi da sauri tatafi kewaye tafara fetsa zawo,
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣2⃣
*dedicated
to sis zulaihat*
Shikenan
yanzu tagane kowa baya sonta har shima baba babba baya sonta, ta dauki mintuna
kafin tafito,
Su abba ko
shigarta kewaye ba su gani ba dan Sun
riga sun shige daki,
Faseelat
wani dutse ne ya tsaya mata awaya, tana tuna firarsu da khalil ta jiya, wai ya
mata missed call daya da safe be sake kiraba se dare, ana cikin fira yake
tambayar ta wai bata ga missed call dinshiba? Tace tagani amma daya ne yace
dayan ai, ai ni bana missed call biyu innayi daya ba bukatar insake maybe Wanda
na kira yana busy "
Tace
"ko? "
Bakaramin
haushi maganar shi tabata ba, dazun da safe ma yakira bata daga ba, tariga tayi
alwashin seta sakashi ya rika mata many missed calls.
Lokacin da
khalil yaji labarin bakaramin farin ciki ya shiga ba wanda yakasa boyuwa ko da
akan fuskarsa ne,
Hjy saratu
ta banka mai harara tajin haushi tace "seka fara shirin biki bawai yin
wata hidima ba "
Ya sosa kai
"ai Hjy lefe ne kawai aiki na kinsan abba ya dade da bani wani gida da
yagina can a layout fenti kawai zaayi se kantoci "
Tace
"eh dukda haka lefen da Kake gani bakomi ba se yazama aiki, kai lefe fa
yana cin kudi sosai ,dan haka yanzu kameda hankali kawai akan abinda ke gabanka
"
Yace
"to Hjy "ya tashi ya fita, tace "shashan banza kawai kamar
anmasa bushara da aljanna ko kunya bayaji
mtsssw"
Shi ko
dakinshi yawuce ya ciro wayarshi yayi dialing number faseelat,
Faseelat na
kitchen stew ma ce take soyawa wayar na hannunta tana chart ya kira, harta
tsinke baa daga ba, ya ajiye wayar Ahankali murmushin dake kan fuskarshi
Ahankali ya bace, gashi so kawai yake suyi magana, yace "bari na bari zuwa
anjima"
Faseelat naganin
kiran ya tsinke tace"kasake kira in abun ya matse ka "
Ta koma
charting dinta, kawai se ga maman amira ta turo a group "slm yanuwa
inamaku bankwana zamuyi tafiya ni da mijina zuwa Cyprus, se Allah ya mana
dawowa I'm going to miss you "
Ta tura ma
group din da tasa akasa ka faseelat,sega best wishes Nata shigowa, wasu naturo
zamuyi missing naki muma da alamu ta dade da sabawa da yan group din, tun ranan
da sukayi saving contact na juna basu kara magana PC ba sede a gaisa a group,
se faseelat
ta bita prvt "anty tafiya zakuyi ne? "
Maman amira
ta tura mata "eh faseelat gobennan around 4am zamu tafi tareda mijina
"
Faseelat
tace "amira fa? "
Tace
"wurin momy nakeso mu barta nima nadan huta, inde daddynta ya bari"
Faseelat
tace "anty kitafi daita mana "
Maman amira
tace "ai duk takare dole mutafi Daita dan daddynta bana tunanin zeiya 3wks
batare daita ba "
Faseelat
tatura smile emoji tace "yanzu se yaushe knan? "
Maman amira
tatura "2 to 3 months only "
Faseelat
tace "zanyi missing naki anty"
Maman amira
tace "ki dena kira na anty kila ma kin girmeni "
faseelat tai
dariya tace "yakamata ko insanki "
batare da
bata lokaci ba maman amira taturo mata pic dinta a kasam sa ta rubuta "my
name is aisha, I'm just 23 years old married with one girl name amira "
Faseelat na
bude pic din ta tsaya kallonta kyakkyawa ce black beauty gajera ce amma baso
saiba bata da kiba inde kaganta Zaka iya cewa shekarata 19 Daganinta tana
jindadi, ko kayan jikinta Sun isheka kallo,
Bata gama
kallon Nata ba taga Anturo wani ta bude
kasan sa an rubuta "baby amira "
Ta tsaya
kallon yarinyar yar 3yrs fara fesss irin farinnan ba ja ba gashegen kyau tana
sanye da gownt fara tasha twisting, bakaramin burge faseelat yarinyar tai ba,
tawani rike kugu ta sunkuya harda su turo baki gaba faseelat tace "duniya
inda ranka kasha kallo yaran yanzu da zamananci ake haifarsu jibi yadda tai
wani style "har cikin ran faseelat taji tanason amira, faseelat ta tura
"wow maman amira kibani amira mana inasonta sosai "
Aisha tace
"hmm faseelat da se me wannan diyar ya daureki, zande baki aro "
Faseelat ta
tura dariya "nide wlh inasonta kunyi kyau sosai, amma duk da haka kingirme
ni sunana faseelat b maaruf shekaru na 21 "
Ta tura
hoton ta,
Ta tashi
tafara zuba miyar da take soyawa a cooler dan tuni ta sauketa har ma tafara
kamu, tana juyewa ta bude wayar,
Ga reply din
maman amira "faseelat kina da kyau sosai inama ni ce ke danaji dadi
Kindace a komi ko a suna "
Faseelat ta
tura mata "Nagode sosai maman amira se anjima ko kuma ince Allah yamedoku
lpya"
Maman amira
tace "amin mommyn amira "
faseelat
bata iya tura komi ba saboda kiran
khalil da ya shigo, tai rejecting abun yabashi mamaki ko second baaiba
wani kiran ya shigo faseelat ta fashe da dariya "kai da kace baka kira
biyu yanaga haka? "
takara datse
kiran khalil besan lokacinda yakara kiranta ba ta dauka ta yamutsa fuska tai
shiru,
Yace
"haba faseelat mi yayi zafi da zaki rika rejecting kira na?"
faseelat ta
murguda baki "bakace bakayin missed call biyu ba? shine na ke gwadawa,
ashe abun naka bame daurewa bane "tai dariyar rainin hankali.
Yayi shiru
"ba da wata manufa nai wannan maganar ba faseelat ,baki fahimceni
bane"
Faseelat
tace "na fahimta mana "
Yace
"to kiyi hakuri in missed call din ne kikeso kinsamu shikenan? "
Tace
"bansaniba"
Yace
"to Allah yabaki hakuri se anjima"
Ya kashe
kiran kiran ta ma yayi ya fadamata abun farinciki amma tasako wannan batun.
maman amira
kau itama sauka tai tunda tagama rabawa duniya cewar zasuje Cyprus dukda ba
zuwanta waje na farko bane,
A sannu
lokaci ke tafiya abubuwa masu dadi da marar dadi na faruwa har anyi wata daya
dasaka baikon su khalil gaba daya yangidansu faseelat bawanda be saba da shiba dukda
de bai cika sakin fuska can-can ba,
Faseelat kau
gyara takesha daga sama har kasa, to da anyi na banza ma bare yanzu me dalili,
Lefe Nata
haduwa har ansiyi akwatuna anata zuba duk abinda ya samu akwati 6 ne setin
hello Queen, Hjy bata nuna komi dan itama burinta ta fita kunya dan tana daga
cikin masu zuwa ganin lefe gidaje inbe yiba aita surutu.
Bangaren
soyayyar khalil da faseelat kau abunde ba cigaba firarsu a waya bata wuce 2mnt
saboda besan firar da zasuyi ba, be iya tsara mace ba sam,
Inkuwa zuwa
yayi to befi yayi 20mnt ba kusan rabin lokacin duk kan kallonta yake tafiya.
Yau ya
kirata zezo danhaka tafito tana hadamasa abinda zeci dan ummi ce ta koya mata
yi masa girki da drinks in zezo.
[7/12, 10:59
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣3⃣
*Dedicated
to ALL RAGGON MIJI FANS*
Kuma hakan
bakaramin dadi yakemasa ba dan sakin jiki yake yaci abincin sa wanda hakan
bakaramin mamaki yake bawa faseelat ba,
Gaba daya
ummi tayi tayi faseelat tabar shiga kicin saboda gyaran jiki da ake mata,
faseelat taki ita bazata iya kwanciya ba mahaifiyarta kuma na aiki,
Dole ummi ta
siyo gas cylinder yanzu dashi faseelat ke girki, saboda gyaran da faseelat ke
samu har wani damshi damshi da maiko fatar keyi,gashi ta kara haske yanzu kam
faseelat kamar fitila ce .
Gas din
tadora shaf shaf tai masa alkubus da stew, tun jiya da daddare ta bada ishak ya
siyo mata banana, garin Katsina garin manoma zeyi wuya ka nemi wani naui daga
fruit ka rasa ko da wane lokaci gasunan bakin titi suna wali,
Banana
milkshake take so ta masa, shaf shaf ta Gama ta zuba a jug tai arranging
abincin a dakin ummi dan yan zu har cikin dakin ummi suke fira.
Da yake
khalil yafi zuwa da safe yau ma duk da be fadamata ba tasan bewuce yazo karfe
11 ko 12 ba.
Tana fitowa
wanka ta zauna bakin madubi tana kallon kanta, kumatunta ta dan latsa tasaki
murmushi, "wlh ni me kyau ce dubi yadda na kara haduwa "
Tace
"bari de natsaya na tsantsara kwalliya saboda gudun raini kullum yana gani
na ba makeup aise ya rainani "
Ta zauna ta
tsantsara kwalliya uban ubansu ta saka doguwar riga baka ganin doguwar rigar
dankwalinta na da girma se bata saka hijab ba, ta yafa gyalen rigar, ta tsaya
gaban madubi ta jujjuya .
Tana cikin
juyawa ummi ta shigo dakin tana ganin abinda take, se tai dariya tace "to
gashi can yazo seki fita karyaita jiranki"
faseelat ta
dauko turare ta kara feffesawa sannan tafita zuwa dakin ummi.
Tunda ta
tunkaro dakin kamshi ya sanarwa khalil faseelat na gab da shigowa dan haka ya
kurawa kofar ido, tana tafiyarta normal amma shi awurinshi kwarkwasa take, har
ta zauna kan kujera.
Ta sadda kai
sannan ta dagoshi a hankali ta Kalle shi, duk lokacin da yake mata irin wannnan
kallon bakaramin haushi yake bata ba, ta dauke ta ja gyalen sama sama ya rufe
mata rabin fuska,
Cikin
sanyayyar muryarta tace "sannu da zuwa "
yayi
firgigit tareda gyara zama, kusan 2mnt sannan yace "na sameki lpya?"
Ta yamutsa
fuska "lpya lau "
Yace
"ya hidimomi "
Tace
"suna wurinku "
"mu
suwa "
Tace
"ku manya "
yayi dariya
"to yayi "
Shiru na
wani lokaci, sannan faseelat tace "ga abinci nan bismillah"
Tai
zauniyyarta dama ba ita keyin serving dinshiba, yadanyi danne dannen waya
sannan ya zuba, milk shake din a copy tunda yakafa seda ya shanye yaajiye, ya
jawo kular abincin alkubus goma ne a kular saboda shikadai taiwa, ya zuba guda
biyar ringis ya zuba miya gefe, Cas...cas..cas karar cokali ne kawai ke tashi,
faseelat kau dukewa tai tana charting da wayarta, ya cinye biyar dinnan tas, ya
sake juye biyar din, suma tass ya cinye ya kara tsiyaya madarar a cup ya shanye
sannan yabuga uwar gyatsar sa wadda tasa faseelat dagowa ta Kalli kulolin
gabanshi kular alkubus bude take alamun bakomi ciki, ta kalli jug din taga yafi
half, ta daure fuska.
Shiko ba
ruwanshi handkerchief ya fiddo daga aljihu ya goge bakinshi, tare da furta
"alhamdulillah, gaskiya girkin yau yafi karfinki nasan bake kikayiba ummi
tayi "
Tace
"ihhhhm" ta yatsina hanci sama tana mai kallon wawa.
Ya jawo
wayar shi ya lallatsa bayan minti biyar ya medata aljihu ya kalleta "ni
zanwuce se na sake waiwayo "ya ajiye mata bandir din 100 guda daya.
Tace
"to yayi "
ya mike yayi
hanyar fita yanata mata kallon bankwana, har yakai kofa yaji tace "Allah
yakiyaye"
ya waigo
yayi murmushi wanda yasa bakinsa kara fadi ya juya yafita, faseelat tace
"kam wlh daace bakinka haka yake da ko kasuwa aka kaika bazaka siyuba.
yana fita
ummi ta shigo dakin, tana kallon faseelat, faseelat ta mike tsaye, zata fita
ummi tace "wai duk ya cinye alkubus din ina tunanin in ya rage inzo inci
naji kamshi Nata tashi lokacin da kina girkawa"
faseelat tai
dariya "waccan wawan ze rage sa ne? Ya cinye shi tass, ga sauran madara
nan yabar miki ki dan kora, wlh natsani namiji me yawan cin abinci kamar mace
ai mata akasani da ci, kuma shi ba kunya gidan surukai yasaki jiki ya tande
plate "
Tunda take
magana ummi ke hararta sede da yake ta juya mata baya bata gani ba.
Ummi tace
"amma faseelat baki da daa, ya kikeso ki meda kanki kina girma kina kara
rashin wayau, haka zaaimuku auren kije kitamishi yadda kika ga dama? To wlh kibari tun kan kishiga gidanshi, yo
inama laifinsa da kika samu yaci, da beci ba ai bazakiji dadi ba kema."
Cikin ran
faseelat tace "da yaci da kar yaci uwarsu daya ubansu daya " amma a
fili ta langabe kai "Allah yabaki hakuri ummi "
Tai sauri
tabar dakin ummi tabita da harara "shashasha kawai wadda batasan ciwon
kantaba, yaro nata miki hidima ke kina wulakantashi"taja tsoki taje ta
dauki kudin da yaajiye tai daki,
bayan sati
biyu, faseelat ce rike da troly tsakar gida ta rungume ummi tana kuka, ummi ma
hawaye take can zuwa ummi ta banbareta daga jikinta, tace "haba faseelat kamar
yarinya kinata kuka harnima kinsa nayi kukan ni wlh bacin yan hade -haden da
nakeso amiki aida bazaki tafiyar nan ba, kiyi hakuri mana "
Ta goge mata
hawaye sannan tace "ki gaida min so dijen da su ammah, ki tabbatar kin
zagaya dangi kinmusu bankwana kafin ki dawo "
Ta daga kai
ta juya ishak ya anshi trolyn suka fita tana rike da auta Mubarak.
Gidan baba
babba suka rakata zasu tafi Niger kanwar ummi ce ta ce taje can su gyarata
gyaran ze dauki lokaci shiyasa zasu tafi yanzu ,su ishak na ajiye kayan suka
juya danbasu son ganin tafiyarsu, kiran khalil ne yashigo wayarta, ta share
hawaye ta dauka tai shiru,
Yayi sallama
bata amsa ba, can zuwa yaji ajiyar zuciya, yace "faseelat kuka kike?
"
Tai shiru
yace "dukafa wata daya ne"
tai shiru
shima dauriya kawai yake maganar da yakemata, can zuwa yace "ganinan zuwa
muyi bankwana, kina gidan baba babban? "
Tace
"eh "
Yace
"ganinan zuwa yanzunnan"
Ta datse
kiran matar baba babba wadda suke kira baaba tace "amarya, amarya ki adana
kukanki se ranar da zamukai ki gidan miji sannan, "
Faseelat
tadan fadada bakinta, sega kiran khalil har yazo, ta tashi tafita, yana ganin
fuskarta tai jawur ya bata fuska kamar zeyi kuka "kiyi hakuri mana
faseelat,"
Faseelat ta
daga kai yace "ga wannan inkinje kinyi amfani dasu "
ya mika mata
wata leda ta amsa tadan leka cikinta sweet -sweet ne kala -kala se wasu yan
dubu -dubu dunkule kila sunkai ashirin ,
Ta rufe tace
"Nagode, ni zanwuce kar baba yafito "
Yace
"to Allah yakiyaye "
Tace
"amin "ta juya ta shige cikin gidan, tuni idanun mazaje yacika da
hawaye ya samu yayi ta maza ya shanye su, ya dade tsaye sannan ya tafi.
Be dade da
tafiya ba baba babba yafito daga sashensa cikin shirinsa, ya kalleta
"diyata harda kuka canma ai gida ne "
Ta dukar da kai
yace "to tashi mu wuce "
Lokacin
kusan karfe 10am na safe suka dau hanyar niger.
Faseelat a
niger........
Team khalil
on top 🤪
[7/12, 10:59
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣4⃣
*This page
is all for you sweetie*
*ina godiya
ga masoya na, ina ganin sharhinku kuma inajin dadi, insha Allah zakuji dadin
labarinnan dan bamuyi komi cikin shiba domin akwai doguwar tafiya a gaba,
faseelat na gaida masoyan ta all over the world, khalil kuma yace a fada maku
akwai ga garumar walima kuma yana gayyatar ku zuwa daurin aure*.
Tafiya ce me
dan tsayi ga wanda be saba yin ta ba,
suna tafiya,
baba babba yanata dan janta da labari
yace
"faseelat wace color ce best color taki?
"
Tai
murmushi tace "brown "
Yana kallon
titi yace "kin tabbatar? "
Tace
"eh baba"
Yace
"to ba matsala dama dan asiyo miki kayan daki irin kalar da kikeso dan
inaga duk lokacin da zaai wannan bakinan naji ance wata daya zakiyi "
Tace
"eh "
Yace
"Allah yakaimu, ai hakanan ma kike kuka nasan omer yana can yana murnar
zuwanki "
Tai shiru
itafa bata kaunar dan karamin abunda ze rabata da ummi ko da na kwana ne.
Bayan laasar
suka isa,
Wow Niger
garin buzaye garin rakumma garin sahara lol ,
direct
gidanshi ya wuce yayi parking faseelat tafito tana kara kallon garin rabonta
dashi kusan she Kara daya kenan,
Batare da
tabi kan trolynta ba tai gaba da sauri zata shige cikin gidan,
Baba babba
yace "zo zo faseelat dauki akwatinki ki wuce dashi ciki "
Se sannan ma
ta tuna da wani akwati ta dawo ta dauka tai cikin gidan.
Tana sallama
yaran dake nan suka ruga wajenta suka rungume ta ,tana ta raba ido taga fadila
bata ganta ba, sega ammah ta fito jin hayaniya tana faraa tace "sannunku
da zuwa amarya "
Faseelat tai
murmushi "ina wuni ammah"
ammah tace
"lpy lau ya gajiyar tafiya ?ki shigo ki ci abinci kiyi salloli "
Faseelat
"tace ina su fadila da husnah? "
ammah tace
"ai suna islamiyya amma nan ba da jimawa ba zaki gansu "
"yaya
omer fa? "
Ammah tai
dariya "yana school shima yakusa dawowa kishigo ki huta mana inje in kula
da mijina nima "
faseelat tai
dariya taja trolynta zuwa cikin dakin ta zauna kan kushin, ammah ta kawo mata
abinci a plate tafita, faseelat ta tashi ta shiga toilet ta yi bawali ta wanko
hannu sannan tafito ta zauna ta bude plate din shinkafa da miya da salad ce,
tasaka cokali tana ci a sannu,
Bayan tagama
ta yo alwala ta kabbara salla, dayake kasaru tayi shiyasa bata dauki lokaci ba,
ta dade tana addua,
Sallamar
fadila ne ya katseta, fadilan tana ta jindadi ganin motar babansu kuma mamansu
tace tareda faseelat zaya zo,
Dasauri
faseelat tafito dagudu fadila ta rungumeta "oyoyo yar uwa "
Faseelat tai
breaking hug din ta Kalli fadila sama da kasa tace "yar uwa Kin girma
hardasu kidayar dangi akafara "
Fadila ta
bata fuska "da ya kike so ne? "
Ta harareta
shigowar husna yakatse faseelat suka rungume juna suna murna, sannan suka shige
daki.
bayan kamar
15mnt omer yashigo gidan da sallama,aikuwa faseelat da gudu tafito ta rungume
shi se kuka,
Ba karamin
kashe mashi jiki tayi ba da kukanta, a sannu ya dagota yana goge mata hawaye,
"miye na kuka kuma? Ki shiru plsss kukanki na daga min hankali "
tai shiru
tana ajiyar heart yana tallabe da fuskarta yana kallon kwayar idanunta yace
"kinyi kyau kanwata "tai murmushi kawai ya Saki fuskar ya kama
hannunta zuwa dakinshi,
Tana zaune
ya rage kayan jikinshi ya rage daga shi se singlet da wando jumper ya shiga
toilet din dakin ya yo brush yadawo ya zauna cin abinci yana ci yana kallonta
itama shi take kallo kullum de bazata gaji da yabon danuwanta ba yayi a kowane
Fanni, ya katse shirun da cewa
"yasu
ummi da auta?"
Tace
"lpya lau suke, suna gaidaka "
yace
"ai ummi takirani jiya tace zakizo in kula dake "
tai shiru
yace"kitashi ki shirya mutafi gidan dijen "
Ta tashi
tsaye ya dago ya kalleta har tafita ya girgiza kai a zuciyarshi yace
"tunda bazaki bi shawara ta ba ai shikenan "
he have been
advising her ta je ta fadawa baba Babba bata san auren amma taki a karshe ma
Cewa tai tafara son khalil din ,shiyasa ya kyaleta,
Yana Gama
cin abinci ya tashi ya watso ruwa ya shirya suka tafi gidan dije shi da ita da
fadila,
Suna isa
dije se murna take takawo masu abinci tai nan tai nan, su omer da fadila suka
barta suka koma gida a tare, domin shi omer tuni Sun dedeta da fadila wadda
dama can tasu tazo daya.
tun daren
ranar akafara gyaren faseelat taff,ko sati baaiba takara jin shaawa ta mata
yawa, abun mutum baze yarda ba domin har zuba takeyi kamar me mensis, nasan
wasu zasu ga cewar novel ne kawai amma it's happening wlh dan wani lokaci irin
wannan yanayin harda ciwon mara yake Saki,
Kiri-kiri
faseelat bacci nason ga gararta saboda shaawa, itaba abun ta dau azumi ba tunda
shaye-shayen da take wasu ma dasu take breakfast, dubarar da tayi shine tadena
zama ita daya kullum tana like da fatoum wadda tama girmeta, bata aikin komi
tunda taje,
*Bayan 3wks*
Lefe ya Gama
haduwa hjy ta kikkira danginta da abokanta da makwabta ganin lefe, ba lefi
lefen yayi kyau kuma de anyi kokari wajen kala 45 bag 5, 10 shoe's include
bathroom slippers, 6 hijab, kaya de sunyi.
Mutane
dodo-dodo ake zuwa ganin lefen dadi kam yakashe hjy domin ita macece meson ace
komi Nata yafi na kowa,
bangaren su
ummi kuwa tuni anje angano gidan faseelat matsakaicin gida ne, ciki da falo da
toilet se waje kitchen store da toilet na waje da dakin khalil falle daya,
tsakar gidan beda girma sosai se get dake makale da bangon gidan,
Baba babba
yariga yabada kudin yimata furnitures se nanda 10days zaagama kitchen plaza
kawai yaje yace ahada mishi all kitchen material, aka hada yana zaune ya Kalli
kayan yace akaro, irinsu food flask da jugs set 5, aka hada kayan kusan million
daya ba abinda babu har su gas toaster oven d. s.
Ya bada ATM
aka cire, suna da motar kai kaya danhaka har kofar gida aka kai kayan aka
zubasu a old garage nashi kafin ran jere.
Khalil kau
sukan dan taba waya da faseelat amma ba sosai ba saboda rashin lokaci dabata
dashi, gaskiya yayi missing dinta dan kullum da tunaninta yake barci.
Bayan sati,
yau faseelat
shirin tafiya kawai take, gashi motar haya zata hau dole ta fita da wuri yanzu
kusan 7am tana fitowa daga dakin tana kiran "dije.. Dije! Na shirya" sega ya omer
Yana
kallonta yadda ta canza yace "zuwa nai muyi bankwana, zan wuce school ne
kigaida ummi,Se nashigo daurin aure "
Bata iya
bashi amsa ba ta bishi da ido, ganin ranshi bace yake, seta fara tuhumar kanta
mima yasa ta fadamishi bata son auren gashi tabarshi cikin tunani, danuwa kenan
me hana kansa sukuni saboda matsalar dayan danuwan.
Baffa dan
yayar ummi shi yakaita tasha yanata tsokanarta wai ta kode tai kamar aljanna
karta je ta tsorata mijinta.
Yana kai ta
suka dau hanya,
motarsu ta
samu matsala a hanya ga shi cikin daji, sukayi cirko cirko suna jiran su samu
wata.
Da kyar suka
samu ana daukarsu da dai daya wannan yasa se Maghreb taisa, se murna kowa yake,
harta kwanta
kiran khalil ya shigo kamar karta daga se kuma ta daga, ya mata ban gajiya ta
kashe.
Washe gari
aka kai lefe gidan baba babba mutane suka fara zarya biyadin ma biyadin.
Seda yayi
kwana biyu aka kaishi gidansu faseelat, ko kadan lefen be mata ba ,ba English
wears ko daya se tarin atamfofi kamar me, haka de taje takai dinki.
yau saura
kwana goma auren, kamar daga sama sega wata kawar hjy da suka dade basu haduba,
bayan gaishe gaishe, kawar wadda ake kira rakiya tace naji ance danki zeyi aure
"
Ummi tace
"eh abu yazoma sauran kwana bakwai, "
rakiya tace
"naji ance diyar hjy asiya ce wadda ke can kofar durbi wadda kukaje hajj
tare "
Hjy ta washe
baki "aiko haka abun yake"
Rakiya tace
"kina aikinmi, Zaki hada jinin ki da nasu asiya, tobari infadamiki asiya
ko kara ta aje alhaji maaruf be tsallakewa nasanta sosai munyi zama unguwa daya
kafin su tashi, tariga ta mallakeshi, cewa ma akai danginsu wani lakani garesu
inde aka kusancesu to shikenan Sun mallake mutum se yadda sukace, ke mi zaki
hada jini da yan niger? Kinsan su da tsirface tsirface da shan kayan matan
tsiya kamar danshi aka halicce su, aiba hakanan suke ba "
Hjy tsoro ya
da baibayeta jikinta har kyarma yake yi saboda tashin hankali ,tace "aiko
wlh dole afasa aurennan, muddin ina numfashi bazaai aurennanba kawai? Wlh
rakiya tunda yaronnan yaje ganinta shikenan ya sauya ashe har an fara asirce
shi wlh bazeyiwuba sam "
ta jawo
wayarta ta kira alhaji,yana dauka tace "alhaji kataho gida ba lpya "
hularshi
kawai yasaka ya nufi gida a 360....
[7/12, 10:59
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣5⃣
Rakiya tace
"ni bansan me ya kaikiba duk matan da ke yawo a katsina ga sunan birjik in
auren hadin kikeso ki sama mishi a dangi mana amma kinje zakija jubo wa kanki
masifa, ke da danki sede kallo dan ita zata zama uwar ke kuma matai"
Hjy ta cire
dankwalin kanta tana fifita da hannu wani gumi ne ke tsatstsafo mata tace
" wlh rakiya kamar ammin asiri inata tunanin yarinyar da zan turashi
wurinta se ita kawai tafadomun kuma naji inason abun amma tunda naga yanata
rawar kai naji abun ya siremin, kibari de alhaji ya shigo bazaai bikin nanba
wlh "
Rakiya ta
tashi tsaye "to nikam zanwuce karya sameni anan Allah ya kyauta"
Dasauri ta
zuri ta kalminta tabar gidan.
Baa dade ba
alhaji ya shigo dasauri yanata tunanin me ke faruwa,
Yana shiga dakinta
ya ganta se kai kawo take tana hada zufa yace "wai lpya de? Mi yafaru NE
naganki hargitse "
Ba wani
tunani tace "alhaji so nike a fasa auren khalil, kuma a anso masa duk
kayansa "
Ya Saki baki
yana kallonta yace "kina da hankali kuwa? Yau saura sati biki kike wannan
maganar anriga angama komi se kice a fasa?
Ya jawo
hannunta ya zaunar daita shima ya zauna yace "inajinki "
Tace
"wlh alhaji se anfasa auren nan gabadaya duk gari fada ake danginsu yan
asiri ne ni kuma inason dana dan haka dole a fasa shi "
Ya game
hannunsa biyu ya saita su akan geme yana nazarinta yace "wannan ba magana
bace kide nemo wani abun fadin, kuma aure kamar anyi angama ne "
Cikin tashin
hankali tace "alhaji ya zakaimin haka? Inace ni na hada abun to yanzu na
raba ai shikenan"
Alhaji ya
zuba mata idanuwa he can't seee sense in her brain, yace "hjy are you out
of your sense ?"
Tace
"ni ban damu ko kakirani mad person amma a fasa aurennan kawai "
Ya tashi
tsaye yana tafiya yace "ni inada hankali na inke naki ya bar jikinki, wa
zan tura ya tunkari dattijon nan da wannan maganar? Mutane masu mutunci masu
halacci, ki gama duk haukanki ki dawo dede na gayamiki, ni na fita wurin
sanaata"
yayi tafiyar
shi da ido kawai tabishi ita yake kira mahaukaciya, toyayi kyau, ta jawo waya ta
kira khalil,
Yana school
yayi saurin baro makarantar saboda muryar ta da yaji some how.
Yana zuwa ya
shiga dakin yana binta da kallo dan haryanzu bata tashi daga zaunen da take ba
yace "hjy lpya? "
Ta sauke
tagumin da tayi tace "khalil ni na hada aurenka da faseelat yanzu kuma
banason kasancewar sa "
Yace"bangane
ba hjy"
tace
"nade fadamaka ka gaggauta zuwa kasamu alhaji kace kafasa "
Yayi sauri
ya tashi tsaye cikin tashin hankali, how he will live with out faseelat se
kawai ya duke akan gwiwoyinsa ya hade tafukan hannayensa yace "hjy Dan
Allah kiyi hakuri inma wani abu ya faru be dace kiyi wannan hukuncin ba, kiyi
hakuri dan Allah wlh inasonta hjy "
tatashi tai
kanshi ta falla mishi mari tareda cewa "shasha kawai katashi kaje kai
abinda nace tunkan in saba maka"
Idanuwan
khalil cike da hawaye hannunshi daya dafe da kumcinsa ya tashi tsaye ya fita
daga dakin yanata zazzaro ido saboda tashin hankali, direct shagon alhaji ya
nufa, alhaji naganinshi yasan ba lpy ba ya ja hannunshi ya fito dashi waje,
suka matsa can suka zauna kan wani slope,
Alhaji ya
fara magana "ka rabu da maganar saratu mutane kawai ke zugata, ita kuma ta
dauka ka kwantar da hankalinka ka je ka cigaba da hidimiminka "
Khalil yace
"tace dole se anfasa shi inde inason zaman lpy "
Alhaji yayi
murmushi "kayi hakuri da abubuwan da zatai tayi komi ze wuce, nide ne me
daura auren kuma se an daura "
Khalil jiki
sanyaye yabar wurin be koma gida ba har dare koda ya koma ta rufeshi da fada
alhaji ne ya saka ta dole tai shiru shikenan ta dauki fushi da khalil da alhaji
ta dena bacci da duk wata hidima,
Yau kwana
ukku kenan ana jidali amma da alamu de aurennan se anyi shi, danhaka ba bata
lokaci ta tafi gidan rakiya suka shige daki,
Hjy tafada
wa rakiya yadda ake Ciki rakiya tai shiru can zuwa tace "akwai mafita
"
hjy tace
"tame? "
Rakiya tace
"kawo kunnenki kiji "hjy ta mika kunne rakiya tafada mata, se hjy tai
kasake rakiya tace "Allah kuwa hankalinki kwance ba wani tension "
Hjy tace
"kuma fa kai Nagode kawalliya shiyasa nike sonki" suka tafa hannu hjy
tace "bari natashi na tafi se Kinzo har hankali na ya kwanta?"ta
tashi ta tafi.
Shikenan
hankali kwance ta cigaba da hidimar biki. Se kuma lokacin ta sakarwa alhaji da
khalil mara,
Faseelat da
friends nata sunata shirye shirye kuma tunda ta dawo ummi ta cigaba da nata
gyaran ,gaba daya faseelat ta rame saboda tunani har yanzu ko digon son khalil
babu a ranta tayi adduar tayi adduar shiru haryanzu batajin sonshi, duk wanda
ya ganta se yayi tunanin ko rabuwa yasata rama kuma de it's normal thing mafiya
yawan amare na rama,.
Yau saura
kwana biyu biki yan biki tuni suka fara cika gida mutanen Niger su dije da
ammah dasu fadila duk har suniso, anata hidima faseelat tasha kunshi anyi mata
relaxer da kitso jelar gashin har kafada,tayi kyau sosai,
shima angon
duk ya rame yayi wuri -wuri dashi saboda hidima, abubuwa sunyi yawa,
Yau din kuma
akaje akaiwa faseelat jere, anata yaba kyan kayan har dakin khalil ansakawa
kujeru da karamin gado.
Gobe NE
daurin aure dukda de bawani event amma maza zasuuyi walima ita kuma faseelat
yau sukayi setting, wannan yasa duk suke busy khalil rabindshi ma da faseelat
tun jiya,
Can bayan
Maghreb alhaji yaji duk bejin dadi tunda hjy ta sako fitina hawan jininshi ya
tashi hakanan yake shan drugs be kwanta ba, yau abun yayi yawa gida ya dawo ya
shige daki ya kulle, bawanda ma yagansa
suna can ciki suna hidima,
Yayi kwance
yana dafe da zuciyarshi yana meda numfashi,
Sega rakiya
tazo hjy saratu ta jawota kofar dakin alhaji dan privacy, suna magana kasa kasa
rakiya tace "inafatan kinnyi duk yadda malam yace? "
hjy saratu
ta babbake da dariya "yo mi zanjira? Kede Allah yabarmu tare "suka
cigaba da magana alhaji yanajinsu, gabadaya tunda suka fara magana hankalin shi
ya tashi nan ciwonshi ya taso haikan, yanata meda numfashi yana fiddo, suko su
hjy suna Gama magana sukabar gun bayan Sun kamo wata fira daban,
Alhaji ko
zuciyarshi kamar zata fashe haka ya keji dandanan yafara karanto hailala yana
ta memetawa har ya cika,
Se bayan
ishai sosai wajen karfe 10 :30 hjy taje kofar dakin tasan de yanzu yaisa ya
dawo ta fara kwankwasa kofar shiru gata kuma a kulle daga ciki, se ta koma ta
window ta haska torchlight saboda ba haske dakin seta hango alhaji kwance, tai
ta kiran alhaji amma shiru ta kwartsa ihu "ni yau nashiga ukku na Lalace
ni saratu alhaji ya mutu "
ihunta yasa
duk kowa ya fito su siyama da sauran yanbiki duk suka yo out, kowa nata
sallallami suna leka windon itako ta zube kasa tanata ihu, siyama na kuka
takira khalil ta fada masa ,hankali tashe yayo gida da temakon zarto aka yanke
kubar suka shiga dakin, alhaji de ya mutu, kuka kawai sukeyi ba yaro ba babba
dandanan labarin mutuwarshi ta game dangi da yanuwa,
Su ummi
tunda akadamata tafara hawaye, Allah kenan me iko akan komi, shine kadai
yakeyin komi a duk lokacin da yaso,mutuwa bata
da notice kuma baajin alert ko wani sign zuwa kawai take, ana gobe daurin
auren dansa shi kuma ya mutu,
Allah
yajikan musulmai ya musu gafara.
Su faseelat
anbaje kan bed itada friends da dangi labarin aure kawai suke yadda zasu kula
da mazajensu se ga ummi da wannan labarin suma Sukai jingum jingum.
da karfe
bakwai aka kai alhaji gidanshi na gaskiya, sabon gida inda mutum ke girbar
abinda ya shuka.
tare da baba
babba akai janaiza bayan sunkoma wurin zaman makoki shi da daya daga cikin
wakilan khalil Sukai magana akan daurin aure zaa dagashi se next week,
Waccan
dattijon ya juya ya na kallon khalil da kanshi ke sunkuye hannunsa kan gwiwa
duk Bayan seconds yana share hawaye, ya girgiza kai.
Hjy saratu
da siyama sunsha kuka kuma suna kanshi gidan biki yazama gidan makoki ,bayan
kwana ukku da yawa daga cikin yanbiki suka koma gida kafin ran bikin yayinda
yan niger tuni sunkoma gida senanda 4 days din.
Tunda abun
Yafaru khalil ya sake komawa wani kala dan haryanzu a hurhurce yake, faseelat
de takirashi ta mai gaisuwa, har yanzu basu ga juna ba,
*************
Bayan kwana
hudu yau daurin aure yan biki tuni duk sundawo abubuwa ake da sanyin jiki,
Taro yayi
taro a masallacin abu ubaida, bayan gama salla aka daura auren khalil usman da
faseelat maaruf akan sadaki dubu 40 lakadan ba ajalan ba.
Ango khalil
ansha tsadaddun hill din corver shoe's hakan yasa ya kara tsayi yasha milk
shadda, as usual hular nan na kusa da ido se washe baki yake yana gaiswa da
mutane a bangare guda akai walima da hotuna.
Bangaren
amarya faseelat ............
yo Anya tayi
wanka ma ita 🤔
No comments