RAGGON MIJI 1-5
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
1⃣
*In the name
of Allah the most beneficent the most merciful*
Alhamdulillah
ina rokon Allah yabani damar rubuta dede yadda nafara lpy Allah yabani ikon
gamawa lpy amin.
Sadaukarwa
ga *sis zulaihat rano* alherin Allah ya sameki a duk inda kike, kisani inayinki
bazan manta alherin da kikamin ba ina godiya da kulawa
faseelat
yarinya ce and she's not above 21yrs tana da kyau sosai babban jiki ne daita
fara ce sosai fuskarta is ready made ko ba tai kwalliya ba batada matsala
abinda yafi daukar hankali ajikinta shine kugunta tanada babban kugu da big
breast kusan ma sune suka sa ta kiban amma kibar ta me kyau ce saboda bata da
tumbi bata da fadi, faseelat kyakkyawa ce de sosai,
Gidansu
matsakaita ne ba masu karfi bane kuma ba matalauta ba, mamansu ita kadaice
awajen babansu su 5 ne mamansu ta haifa faseelat itace ta biyu kuma ita kadaice
mace ta taso cikin gayu tun tana yarinya har girmanta mamanta cikin gyaranta
take dayake ita kadai ce mace, yayanta sunanshi omer, se ita se abulkhair se
ishak se auta Mubarak,
Babansu
meson karatu ne sam be wasa da ilimi ta sauke kur'ani kuma tagama secondry sede
mamansu taki yarda tawuce makaranta, wai sanadin lalacewar yawancin yanmata
kenan, babanta alhaji maaruf yayi iyakar yinshi amma ummi taki wai sede tabari
setayi aure tayi,
Yanzu haka
faseelat bata zuwa koina se islamiya shima se weekend duk aikin gidansu itace
keyi batada hutu ko kadan, ta kware wurin sanwa sannan kwararra ce wurin gyaran
jiki saboda abinda mamanta ke koya mata ne, kullum ummi kamar yar 30yrs take
saboda bata wasa da gyara kanta duk abinda ya shafi gyara ko abinci ko kwalliya
wannan yasa abbansu yakasa yi mata kishiya dan ko kallon mace bayayi dan yasan
inyaje gida tashi tafita.
Har mazan
gidan suma basa yawace yawace unlike other houses da namiji se ma ya kwana ba
gida ba, su ko duk abunka karfe 10pm acikin gida takemasu.
Faseelat ba
mummuna bace bare ace shiyasa batada saurayi kawai Allah ne be kawo ba har yau
ba wanda ya taba tunkararta da kalmar so, wannan yana matukar damun umminta
saboda ita burinta ta ganta adakin aurenta lami lpya kuma shine gurin kowace
uwa akan yarta, shi ko abba be damu ba cewa yayi komi lokaci ne,
itama
faseelat abun baya damunta amma tanada buri a soyayya yadda take fara fari
takeso, tanada kiba to mijinta ya zama siriri dogo, tana masifar son saje a
fuskar namiji, yazama dole mijinta ya zama jarumi me karfin zuciya kuma sannan
ya zama yana da rufun asiri da ilimi to shine mijin aurenta kuma shine burinta,
So da dama
takan zauna da mamanta su tattauna akan aurenta itade faseelat abun mamaki yake
bata gani takeyi mamanta bata yarda da tarbiyyar da ta bata ba ,ko tagaji da
ganinta kusa daita,
Yau sungama
cin abincin rana itada ummi saboda tare suke cin abinci, ummi ta kalleta tace
"faseelat Allah yabaki miji nagari ki tafiyarki ki huta kullum addua ta
kenan ba dare ba rana "
faseelat
batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba,
Tasa bayan
hannunta ta goge ummi na ta kallonta da mamaki,
Faseelat
tace "ummi shin akwai ranar da zata zo ta koma baki maganar aure na ba?
shin ummi kingaji da nine? Koko nikadaice wadda takai wadannan shekarun a gidan
iyayenta,? Ummi tunbana sa komi a raina har nafara zargin ko de baki yarda dani
bane? "
Kallon
mamaki kawai ummi kebinta dashi tace "haba faseelat burin kowace uwa taga
yarta gidan miji nasanki kaf ciki da waje nice mahaifiyarki ni na haifeki nasan
halinki bawai inafada bane dan ranki ya baci abinda ke gabana kenan banda Mace
se ke duk kanku ina alfahari daku kuma kullum ana yabon yara na dan haka kidena
zubar da hawaye kinji diyata? "
tajawo ta
akan kafarta hawaye faseelat ta share, ita fa bacin feeling da takeji ai bataki
tayita zama gidan suba, to shaawa tayi mata yawa so da dama tana yawan mafarki,
kuma dakinta ba toilet aciki tsakanin dakinta dana ummi toilet yake se can
farkon shigowa gidan nan dakunansu ya
omer suke suma da toilet tsakiya shi ko abba ciki da falo da toilet ne yakeda,
tun asuba take lallabawa tayi wanka inde tayi mafarkin sam batasan ummi tasani
ba ,shine ma yasa take kara son aurar daita dan itama ummi haka take da yawan
shaawa ,bare faseelat ga girman jiki tunda ko mata suka ganta sede suce
tubarkalla dan duk yaddda tayi tafiya kugunta da breast dinta rawa suke .
Ummi ta saki
ajiyar zuciya tace "Allah yamaki albarka faseelat duk aikace aikacen
gidannan ke kadai keyi kinhanani komi ni har tausayi kike bani "
Abulkhair ne
ya shigo agajiye yadawo daga school yana shigowa yaji yadda ummi kesawa
faseelat albarka,
Ya zauna
tareda fadin "wlh ummi bamu yadda ba kullum faseelat kadai kike sawa
albarka muko baruwanki damu, Allah ina tunanin rabon daki samin albarka tun kan
ki yayeni "
da faseelat
da ummi suka fashe da dariya
ummi tace
"abul inayimuku kuma ko ban bayyana ba, kaima Allah yamaka albarka dasu
gabadaya "
Yace"
amin ummina, ya faseelat mi kika dafa yau? "
tace
"aifa new student in university, abinda bakaso akayi danwake da souce
"
Yace
"nashiga ukku ni abul ummi ya zakuyi dani wlh nakusa karasawa lahira sora
kiris inbaku temaka min ba idawa zanyi "
Suka babbake
da dariya faseelat tace "katashi katube kashiga kitchen kawai "
Yace
"pls pls ya faseelat do help me "
Tace
"naki din "
Ya tabe
fuska "nide dama nasan yaya bakisona ko kadan "ya mike tsaye.
Ummi dake
dariya tace "itako ke sonka tayimaka rice beans se kaci da soese din"
Yasaka hannu
biyu a kirji yasauke ajiyar heart huuuuum "yaya Allah yabarminke inasonki
kamar rai "
ummi tace
"jeka de kaci kahuta tukun "
Yajuya
yatafi dasauri itako faseelat ta mike tsaye ummi tace "se ina? "
Tace
"wanka zanyi ummi kafin marece infito indora muku dinner"
Ummi tace
"bakigajiya da wanka faseelat to zakiga dilka saman windon toilet kidanyi
kafin wankan "
Tace
"Tom ummi se nafito "
[7/12, 10:57
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
2⃣
Dedicate to
*sis zulaihat rano*
A Al'adar
gidansu faseelat bayan asuba sukan hadu suyi murajia, bayan isha kuma suyita
fira basu cika kallace kallace ba, itada yanuwanta akwai kyakkyawar fahimta,ya
omer bayanan yana Niger karatu kuma can ne asalin mahaifiyarta asiya, sun hadu
da mahaifinta ne yaje kasuwanci a can kuma ya samu nasarar sace zuciyarta har
akamusu aure, sukan je niger amma ummi tafi yawan zuwa,
Bayan kwana
biyu
yau tun
asuba faseelat ta farka a firgice tasha mafarkai kala da kala
Cikin sauri
ta sa hannu ta shafo kasan pant dinta taji shi da lema, ta dafe goshi tareda
fadin "oh god"
Babban
tashin hankalinta sanyin da ake surarawa gashi dole tayi wanka, ta tsaya tana
ta nazari can dasauri ta dira daga kan bed ta jawo towel sauri -sauri ta sabule
rigar baccinta tai waje jin shiru dakin ummi tagane bata tashi ba, wuf tashige
toilet ta sakarma kanta shower yayinda take cudawa da hannunta sauri kawai take
kar ummi ta tashi.
Karar ruwan
dake sauka ne ya tayarda ummi daga bacci ta tashi zaune ta buga tagumi
tausayinta yakamata ko ita inde zatai wankannan takansa ruwan zafi, kamar
tatashi tafita se kuma tafasa dan karta bata kunya,
seda faseelat tagama wanka tafito tawuce
dakinta sannan ummi tafito jikinta a mace tashiga toilet itako faseelat salla
ta kabbara,
Ummi se sake
sake take bazata manta yadda tasha wahala ba lokacin da take budurwa don har
azumin dole takeyi,
Alwala tayi
ta kabbara salla tana ta adduar Allah yakawo wa faseelat miji nagari ,bayan
faseelat tagama tafito dakin ummi tashiga tazauna sannan ta gaisheta ummi ta
amsa tana lazimi har ta tashi ummi takira sunanta "faseelat!"
Tace
"naam ummi "
ummi tace
"dawo kizauna zamuyi magana "
tace
"to " tadawo ta zauna
Ummi tagyara
zama tace "faseelat ni ce mahaifiyarki ni na haifeki tambayar ki zanyi
kuma inaso ki bani amsa a matsayina na mamanki, dole ne yasa zan miki maganar
nan duk da tamin nauyi "
gaban
faseelat harbawa ya rika yi sosai da sosai,
Ummi ta
cigaba da cewa "ina kula da ke tun kina 18yrs na kula kina yawan yin wanka
akai akai kuma nasan dalilin hakan ,amma inaso kifadmin da kanki miye dalili
"
Hannu
faseelat ta dingi dannawa yana bada sautin kas -das
Ta sunkuyar
da kai, kunya duk ta cika ta,
Ummi tace
"dama nasan bazaki fadamin ba amma don Allah ina rokon ki faseelat kiyi
hakuri da yanayinki ki jure karki gurbata rayuwarki ki rike mutuncinki na roke
ki"
Faseelat
gabadaya jikinta yayi sanyi tace "ummi
banida wannan tunanin kuma namiki alkawari bazan taba zubda mutuncina ba
ki cigaba da yimin addua adduar ki nake so "
Ummi tace
"addua munanan munayi faseelat sede mukara akan ta"
shiru ummi
tayi sadaf sadaf faseelat tabar wurin, duk ji tayi jikinta ya mutu batareda ta
je wurin da suke karatu ba ta wuce daki ta kudundune,
Ummi bayan
ta gama addua tafita bayan Sun gaisa da
abba tawuce kitchen taga ba faseelat, ta girgiza kai tafara aiki, tasan dama me
wuyacine yau ta saki jikinta.
Suko su abba
karatunsu sukayi har xuwa 7am sannan suka tashi me bacci ya kwanta me zuwa
school yafara shiko abba shigewa yayi yafara shirin office.
bayan ummi
tagama hada breakfast suka yi suka fice gidan yayi tsit kamar ba kowa ciki,
Ummi wanka
tayi tashige daki, batareda ta waiwayi faseelat ba, itako faseelat bacci ne ya
dauketa,
Can wajen
10am ummi tafara jin sallama tana fitowa taga wata kawarta a aikin hajji suka
hadu matar ta girmi ummi nesa ba kusa ba amma jininsu yazo daya saboda a room
daya suka zauna lokacin hajji ita kuma ummi tana matukar girmama na gaba daita,
wannan yasa suka shaku da maman khalil, ko bayan Sun dawo daga saudiyya suka
cigaba da zumunci.
"maraba
maraba da maman khalil "
Hjy saratu
tana faraa tace "yawwa Hjy asiya "
Ummi tace
"shigo ciki mama naga kintsaya waje mushiga ciki "
Maman khalil
na murna suka shige ummi tanata nan nan daita takawomata pure water da zobo
taajiye sanan ta zauna ,"sannu Hjy ,sannu da zuwa, yasu khalil? "
Hjy saratu
tace "lpyarsu lau siyama ma na gaida faseelat"
Ummi tai
faraa da cewa "ihhhhn siyama kenan
kullum tana gida kamar ba macen aure ba "
Hjy saratu
tace "mijin tasamu me sauki shiyasa "
Ummi tai
murmushi
Suka cigaba
da fira can Hjy saratu tace "Hjy dama wata muhimmiyar magana nake tafe
daita Allah yasa zansamu abinda nazo nema "
Ummi tai
shiru tana saurarenta
Hjyar ta
cigaba da cewa "kinsan yara na biyu kacal khalil da siyama, siyama de tayi
aure gashi harda jikoki na samu, amma khalil shiru yaki ya fiddo mata gashi
yanzu har yana batun Shiga shekara 35 kuma bayada niyya na mishi magana baso
daya ba ba biyu ba amma shiru, to daga baya na Yanke shawarar zabar masa
mata,saboda shi mata basa gabansa kwata kwata.
nayi tunanin
,na duba na hango yarki faseelat ce ta dace dashi, batun yau ba ina fadamiki yaranki
na burgeni wannan yasa nakeso inhada Zuria dake, inaso yaro na yazo sugana da
faseelat in sun dedeta se ayi buki.
Ummi hamdala
kawai take cikin ranta Allah ya amshi adduarta,
ta danyi
shiru sannan tace "..........
[7/12, 10:57
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
*Writing by
MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3⃣
*Dedicated
to SIS ZULAIHAT RANO*
Sannan tace
"naji dadin wannan maganar Hjy kuma inafatan zasu fuskanci juna Allah ya
tabbatar mana da abinda yafi zama alheri *
Hjy saratu
tace "amin amin Insha Allah gobe zezo su gaisa daita din saboda baniso a
dau lokaci"
Ummi tai
murmushi "tom madalla zansamu faseelat da maganar"
Hjy saratu
tace "ni tunda nashigo bangantaba nade san su Mubarak ana school"
Ummi
tace" inajin bacci takeyi, bari natado miki ita "
Hjy tace
"aa barta bari na tashi nawuce gida "
Ummi tace
"tom nagode kigaida gida "
Suka fito
ummi tayo mata rakiya suna fitowa tsakar gida sega faseelat ta fito zata shiga
toilet wanka tana daure da towel ,tana ganinsu ta sunkuya ta gaida Hjy saratu
dasauri tashige toilet, Hjy saratu ta bita da kallon birgewa sannan tawuce,
Ummi wasai ta
nufi kitchen ita kuma faseelat tai wanka tai brush sannan tafito neman abinci,
tana shiga kitchen ta tarda ummi na aiki batareda tace komiba ta debi kunun
tsamin daakayi tafita shaf shaf ta shanye ta dawo tace ummi ta bata tayi aikin,
ummi tace "a,a barshi zan dan tayaki se muyi tare "
Faseelat
tace "a, a ummi kibari nayi "
Ummi tace
"to" tasamu wuri tazauna tace "miko min albasa da latas din na
yanka miki "
Faseelat ta
mikomata ummi nayanka take magana,
"faseelat! "
Faseelat ta
juyo "naam ummi "
Ummi ta
cigaba da cewa "Hjy saratu ce tazo da maganar tanason danta khalil ya aure
ki shine ta zo neman izini zezo kugaisa kufahimci juna"
Faseelat tai
kasak'e can zuwa tace "to ummi "
Ummi tace
"gobe yana nan zuwa seki shirya sannan inaso Dan Allah badanniba ki
saurareshi "
Faseelat
takara cewa "to ummi "
Ummi ta
cigaba da cewa "Hjy saratu mutunniyar arziki ce tun bayan dawowarmu daga
saudiyya ta daukeni kamar kanwa tana sona da zuria ta baki daya, gashi
hartanason hada jini dani, Allah ina rokonka kasawa abinnan albarka"
shiru
faseelat tai ta cigaba da tsintar waken dake gabanta.
itama Hjy
saratu tana komawa gida tafadawa mijinta yanda Sukai yace Allah yasa haka shine
mafi alheri .
se 2pm
khalil yashigo gidan dakin Hjyar ya wuce yafada kan kujera "I'm very tired
hjy "
Ta harareshi
"se kace wanda yayi dako "
yace
"Allah Hjy barci ne a idona sosai bari na tashi naje naci abinci na kwanta
"
Har ya mike
Hjy saratu tace "kai dawo kazauna"
Yace
"to "yaxauna yana jiran mi zatace
"dazunnan
naje munyi magana da wata kawata zakaje kaga diyarta intamaka shikenan, tunda
kai kakasa fiddowa da kanka gwara ni na zabarma, kashirya gobe kaje kaganta
inka tashi kamin magana zanbaka address inafatan kagane? "
Tunda tafara
magana yake kallonta "amma Hjy kinaganin ba matsala ni da kinkara min
lokaci banfa isa aure ba gaskiya "
Hjy ta watsa
mashi harara "tashi kaban wuri "
Ya tashi har
ya kai kofa ya juyo "amma Hjy kinaganin ita yarinyar zata amince? "
Hjy saratu
takara watsa masa harara
Abinda
yasashi juyawa kenan ya fita dakin yanajin duk ta takura masa aishi be tashi
aure ba gaskiya shi ko kallon mata bayayi bare soyayya,kusanma tsoron matan
yake ranar kwana yayi beyi bacci ba ya nata saka da warwara Karon farko da ze
tunkari mace me zece mata? Mi zasu
tattauna shine tunaninshi kawai.
Itama
faseelat batai bacci ba will he be like her dream guy? gaskiya bazata taba yin
aure ba harse tasamu muradin ta idan ya mata fine inbe mata ba bazata aureshi
ba ko,
Haka ta
kwana sake sake,
Washe gari
Bayan tagama
aikace aikacenta na yau da kullum sannan ta shirya tasa ka riga da sket ta yafa
gyalenta ta zauna jiran tsammani dan ummi sunyi waya da hjyar tace karfe 11
zezo,
agogo ta
kalla taga karfe 11 saura ta zare gyalen tana tsoki ta kwanta kan bed baccin da
bataiba ya dauketa 11 dede ya iso kofar gidan wata yarinya yasamu yace ta kira
masa faseelat, gabanshi nata dukan goma -goma.
Yarinyar
nashiga ummi tace kice gatanan zuwa, tashiga dakin faseelat ta
tadata"kitashi kigyara
fuskarki
maza "
shaf -shaf
ta sauka daga gadon ta kara kallon madibi bata tsaya kara shafa komiba tafita
she's eager to see him.
tana fita
kofar gidan ta diba hannunta na haggu taga roba -roba fa ke ,cikin ranta tace oh God ko yar honda
bedaita mtssssw.
Tayi sauri
ta juya hannunta na dama, se gashi tsaye yanata son ganin fuskarta tana waigowa
ya zuba mata ido itama shi take kallo daga saman sa zuwa kasa.
baki ne amma
not that black idanuwansa a bit tiny hancinsa gajere with medium mouth kayan
jikinsa kaftani ya taso hula gaba har kan goshi daf da ido tsawon shi takalla
dogo sosai shantaly kenan 😂🙊zufar dole ce tashiga keto mata,
*da akwai
matsala fa*🤣
in next page
zamuji ya firarsuzata kasance.
Inaganin
best wishes da adduoinku Nagode Allah yabar kauna
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
Writing by
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4⃣
*dedicated
to sis ZULAIHAT RANO*
*All praise
be to Allah*
Shi ko
kallonta yake saboda ta tafi da hankalinsa tabbas faseelat mace ce da inka
kalleta seka kara kallonta, kallon kallo suke wa juna and ita nata kallon
tanayi ne kawai amma hankalinta baya tare daita magana ma take da zuciyarta ga
abinda take cewa "allahumma ajirni fii musibaty wa aklifly khairan minha,
to musiba mana gabadaya tunaninta ya Kare akan mamakin tsawon sa dama duniya a
kuma Katsina akwai masu irin wanga tsawo haka? Ta cigaba da cewa ya Allah
kaceceni mu rabu da bawannnan naka lpya.
Shiko tashi
zuciyar tuni ta kamu da kaunar faseelat
,
Can zuwa ya
tattaro natsuwarsa bakinsa na dan kyarma yace "Assalamu alaikum"
firgigit ta
dawo hayyacinta still zufa na karyo mata se kace mejin kashi,
Tana mazurai
tace "sannu da zuwa shigo ciki"
Wani iri
yaji jin muryarta yayi tsaye itakuma tashiga cikin zauren gidan ya bita zalalo
zalalo kamar rakumi da akala.
Har cikin
zauren babban zaure ne dan already har an ajiye sit din roba biyu tai tsaye ta
juyo sannan yakaraso tana nuna masa kujera tace" bismilla "
Ya haye ita
kuma tasa gefen gyalenta ta share wata zufa data tsiyayomata ganin kafafunsa
Sun dan baud'e kadan,
jiki sanyaye
taja kujera ta zauna ta dukar da kai sam bata kaunar ganinsa, beyi mata ba, mi
zatayi da baki?dogo kamar ba samude sam baze yiwuba.
Tunanin ta
yakatse ne da yafara magana voice dinsa na vibrate saboda yadda yake jin tsoro
yace "sannu malama faseelat, Da farko de sunana khalil shekaruna 35 ina
teaching a all brighters academic, Hjy ta ta umarce ni nazo naganki mu dedeta
ina fatan zamu fahimci juna ni da ke "
wata iriyar
murya ce dashi gatanan de, ita kuma faseelat tana son miji me siririyar murya
shi ko gata de, kamar wadda aka mara tashiga jijjiga kai, shiru ne ya biyo baya
can ta tuna bata kawo masa drinks ba, ta tashi ta kawo masa dudu milk ta
tsiyaya a cup ta mika masa, yayi kurba daya ya ajiye shiru beda abin fadi kanta
na kasa amma duk dagowar da zatayi seta ga ita yake kallo,
Can zuwa
yayi karfin halin cewa "kibani no din wayarki "
Faseelat
gabanta na faduwa tana inda inda tace "ni banda waya"
yayi shiru
can yace" ba damuwa inafatan nasamu karbuwa? "
tai shiru
can zuwa ta daga kai
Yace
"Alhamdullilah se na sake dawowa ko? "
Haushi ya
kashe faseelat se tambaya yake kamar tsohon makaho ta dago tace
"ihhhhhh"
Aiko yayi
shiru ya tashi tsaye"ni nawuce "
Afili tace
"tow agaida Hjy, a Zuci tace agayas "
yajuya
yafita daga zauren takara bin bayanshi da kallo kuttt se yanzu ta lura rigarshi
ta wuce gwiwa tsabar tsawo
Ta kai minty
5 zaune sannn ta tashi tai cikin gida,
Shiko Karon
farko da yafara fira da mace dadi kawai yakeji yanda ya sameta ya tada babur
dinshi yayi gida.
Faseelat
nashiga cikin gida da sallama ummi ta amsa, zuwa tai zata wuce ummi tashiga
daki ta kwanta ko ta samu ta dawo dede,
ummi tana kallonta
tace "zo nan faseelat"
Tana daga
kafa daya kan daya kamar wadda kafar taiwa dayi tazo gun ummi ta zauna,
Ummi tace
"ya kukayi"
Faseelat ta
sosa kai tare da cewa "naam"
ummi ta
harareta tace "eh "
Sosa kai
faseelat ta fara labbanta na kyarma tace "ummi beyi kama da mijin da
nikeson aure ba "
ummi tarika
jifanta da mugun kallo can tace "dan ubanki har wani kalar mijin da kikeso
kika tsara? wallahi faseelat ki shiga hankalinki tom,"
Faseelat ta
zumburo baki gaba "wlh ummi bani sanshi baki ganshiba beda kyau ko kadan
"
ummi ta rike
haba "faseelat? Dan kina ganinki fara shine zaki ce haka, ke kekikayi
kanki haka hala? To kamar yadda kike haka fara shima haka Allah yayishi baki
kuma haka yakeson ganinshi "
faseelat ta
matso hawaye "Allah ummi ni banisonshi "
ummi tace
"rufemin baki kar in mazgeki, dan kinsamu ze temakamiki ma wa yataba cewa
yanasonki? Dankawai ze rufa miki asiri? To barikiji wlh inkinga baayi aurennan
ba to abbanku ya binciko wani mummunan hali atare dashi ne ko in Allah ya
kaddara
Ke ba
matarshi bace amma ina tabbatarmiki se anyi bikinnan "
Faseelat ta
dora hannu akai "nashiga ukkuna ummi dan Allah ki temakamin "
Ummi tace
"temakon da zanmiki knan in aurar dake "
Faseelat
tafasa kara tana kuka sosai ummi ko tatashi tabata wuri tace "ai seki tayi
"
"wayyo
Allah na ni wlh bansonshi "
Hardasu
majina saboda kuka sallamar abbansu ne yasa ta gudu wurinshi ta rungume
"abba dan Allah banisonshi karku auraminshi "
cikin mamaki
yace "share hawayenki diyata "
Tasa hannu
ta goge still wasu na biyowa yace "bawanda ze miki auren dole kinaji ki
wuce kije ki kwanta "
Faseelat ta
wuce sundum sundum ummi tafito daga kitchen "amma de alhaji kasan bazanji
kunya nai magana biyu ba nariga na amsa musu yanzu mi kakeso nacema uwarsa ince
bata sonshi? "
Abba cikin
sanyin murya yace "haba asiya kibi komi sannu mana, wai ma duka Nawa
faseelat din take ne? Duka fa yanzu shaekararta biyu da graduate, kibari komi
asannu akebinshi ai yau suka fara haduwa may be su dedeta zuwa gaba"
Faseelat
dake labe tace "wlh aa banisonshi bazan so sa ba harabada "sede bawanda yajita dayake ta Shiga daki
Ummi tace
"hmmmm"
Tashige
kitchen
Shiko abba
ya shige daki yana girgiza kai, yarasa daliin ummi da ta kagara ta aurar da
faseelat.
faseelat kan
gado ta mike tanata sharar kwalla har bacci ya kwasheta.
shi ko malan
mudi da farin ciki ya isa gida,
Bayan ya
shigar da babur dinshi yawuce dasauri dakin Hjyarsu Hjyar na tsefe gashinta da
rabi yafara zama furfura ya shiga, Hjy saratu ta dago tana kallon fuskar shi
tagane yana cikin farin ciki,
Ya zauna
tare da cewa "Hjy kiniya zabe wlh tayi komi yayi dede, gata da kyau ga iya
wanka "
Hjyar tai
dariya" marar kunya kawai, aibaka isa aure ba "
Yayi shiru
yana dariya "toya ita faseelat yanayinta ta amince? "
yace
"eh Hjy "
"to
yaushe Zaka koma? Kukara ganawa, kafin atura su kawu "
yace
"gobennan Hjy "
Hjy tace
"hmmmm Allah ya kaimu, sede dan Allah ka natsu kuma ka rika yimata
kyautuka saboda takara sonka sannan kuma ka san maganar da zakurika yi "
Yace
"to "
Yakagara
gobe tayi
*nace da
akwai matsala kufa? 🤣*
[7/12, 10:58
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
Writing by
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
5⃣
*Dedicated
to SIS ZULAIHAT RANO*
Ya kagara
gobe tayi ko yakara ganin kyakkyawar fuskarta.
Wasa -wasa
har dare faseelat taki tafito waje, ummi de ta share ta su abulkhair suna ta
tambayarta sede ummi tace bacci take ,
Har abba ya
dawo gida bayan ishai ummi da abba suna
daki suna fira while ishak abul da Mubarak na tasu firar, dan auta ya kasa
hakura da rashin ganin ta ya leka dakinta tayi rubda ciki amma ba bacci take
ba, abin duniya ne kawai ya sha mata kai, ganin idonta rufe yasa yaja mata
kofar,
Dakin abba
ya shiga ya samu ummi ya zauna gefenta "ummi kode ya faseelat bata lpy?
Naga tundazu da rana bata fito ba yanzu naje dakinta na ganta kwance har yanzu
"
Ummi tace
"to bana ce maka bacci take ba? Ka tashi kaba mutane wuri "
Yace
"to ummi kode a tado ta ni wlh gidan ba dadi da babu ita "
Ummi tace
"kai kasani ai "
Abba yace
"wai tun dazu bata fito ba? Kuma kika kyaleta haba Hjy kinsan fa ulcer na
iya kamata "
"to ya
kake so na mata? Ko so Kake naje na rarraso ta tunda na mata laifi "
Abba yace
"yaro dan rarrashi ne in kika lallabata se ki shawo kanta amma bata haka
ba, kinsan faseelat na da saukin kai ai "
"Alhaji
kabarta kawai in yunwa ta kusa kasheta zata fito, nifa duk abinda nakeyi saboda
ita ne yarinyar nanfa da kake gani kusan kullum se tayi mafarki, taya kake
tunanin hankalina ze kwanta tana zaune gidannan gwara ai mata auren tun kan ai
abun kunya "
Abba yayi
shiru yana nazari,yace"eh ki de bita a sannu, wa ma ta gado inbake ba da
jarabar tsiya in baayi miki 3 rounds ba baki koshi "ya ida yana dariya
Tace
"eh naji din ai kai ma shine da har kake iya yin ukkun "
Suka sa
dariya Mubarak fa yadade da barin wurin tunda aka korashi.
Ummi nata
zuba ido faseelat zata fito cin abinci amma bata fito ba, se kuma tafara shiga
damuwa.
Itako
faseelat muguwar yunwa takeji ga, zazzabi da ya rufeta kwance kawai take tanata
tunanin yadda zatayi rayuwa da khalil.
Can 12am
samarin duk sunyi bacci ummi tafito daga dakin abba har zata wuce se kuma ta
shiga dakin faseelat,
Tana kwance
rubda ciki still ummi ta matsa "ke bana hanaki kwanciya haka ba?"
faseelat ta
birkita ba tare da ta dago ba
Ummi tace
"wai dani faseelat zaki fushi ?dan kawai ina fadamiki gaskiya? Ya kikeso
nayi ne? So kike nabarki na zuba miki ido? Bayan ga hanya Allah ya kawo, haba
faseelat wlh kinbani mamaki da har zaki bijirewa magana ta shi dake namiji ya
amince da umarnin mahaifiyarsa, amma ke kinkasa ".
faseelat ta
fashe da kuka tana sheshsheka ummi tace "aa kidena kuka faseelat bazan
takura miki ba tunda bazaki iya aurenshiba shikenan gobennan zankira uwarshi in
fadamata bakisonshi tunda burinki ki kunyatar dani, ni wlh daace kinada wanda
kikeso da baabinda zesa na matsa miki amma keda bakida kowa ihhhhm? Dama ace ke
lafiyayya ce amma kinada larura ki duba fa yanayinki faseelat, shikenan anfasa
auren ki tashi kije kici abinci "
Ummi ta juya
zata fita faseelat na kuka ta kira sunanta "ummi "!
Ummi ta
waiwayo ta cigaba da cewa "Dan Allah ki hakuri baniso ranki ya baci karki
fushi dani "
"bazanyi
fushi da keba faseelat sede ki sani zaki sani cikin zullumi da tunani dan wlh
inde ban aurar dake ba banida kwanciyar hankali "
Faseelat
daga kwancen de take magana cikin rashin tunani tace "na yadda ummi zan
aure shi inde zakiji dadi "
Ummi tace
"dako kinfaranta min rai dan inada tabbacin bazaki kuka ba in Allah
yaso"
faseelat
tace "na amince ummi kuma kiyi hakuri da bata miki rai da nayi "
ummi tace
"bakomi Allah ya miki albarka ki tashi kici abinci karkijawa kanki
ciwo"
Faseelat
tace "bazan iyaba ummi masassara nake tun dazu "
ummi tace
"subhanallahi "tana hawa kan gadon ta fara tattabata gabadaya jikinta
rau yake har kafafunta, ummi tace "sannu kinji bari na kawo miki magani
"
Ta tashi ta
fita wani kuka ne yazowa faseelat ita kanta tasan ta amsa ne kawai amma tasan
haka zatai ta rayuwar hakuri harabada, tasa hannu ta share hawayenta yanzu de
koba komi ta farantawa mahaifiyarta rai da tun tasowarta tana ganin yadda take
fifita ta akan yanuwanta.
Motsin da
taji yasa ta kara goge fuskarta ummi
tashigo dauke da tray ta ajiye ta bude flask ta debo taliyar hausar da ta dafa
da daddare ta dora kan bed ta debi ruwa ta ajiye sannan ta zauna bakin gadon
tace "tashi ga abincin diyata "
Faseelat na
ciza baki ta yunkura ummi taida tadata zaunen jikinta har kyarma yake saboda
yunwa,
Ummi tafara bata abincin a baki da yake tana jin
yunwa taci abincin sosai sannan ta bata magani ta koma ta kwanta se sannu ummi
ke mata sede ta daga kai, tashi ummi tayi taja mata kofa tana mata seda safe.
ko bayan fitar
ummi faseelat kuka ta rikayi ga bacci ya kaura cewa idanunta,
Ba abinda
take tunani se fuskarshi da jikinshi tana tunanin yadda zasuyi rayuwa tare wuri
daya gida daya daki daya gado daya.
Se asuba
bacci ya dauketa, ummi na Gama azkhar taje ta gaida abba yake tambayarta jikin
faseelat da yake wurinshi ta amso maganin tace dasauki ta fita dubota, tana
shiga ta tada ta faseelat bude ido kawai tayi ummi tace "ya jikin
"tana tabata faseelat tace "dasauki "
Ummi tace
"naji haryanzu da fever din kitashi ki salla inje in hado miki tea kisha
kisha magani "
Faseelat
tace "I'm off"
Ummi tace
"kinada pads ne? "
Faseelat
tace "eh amma beda yawa "
"OK
anjima zanba Mubarak yasiyo miki wata tashi kije ki kimtsa ko kinji dadin jikin
"
faseelat
tace "to "ta mike ummi taga har tangadi take ummi tace "zakiiya
wankan kuwa "
Faseelat
tace "eh "tafara bin bango ummi takamata ta kaita toilet sannan tai
kitchen,
Da dai daya
yanuwanta suka rika shigowa suna mata ya jiki kafin su bar gidan, shi ko
Mubarak harda hawaye danba karamar shakuwa sukai ba daita.
Bayan tasha
tea din da magani ta koma ta kwanta,
Can wajen
12pm ummi nata aikace aikacenta wani yaro yazo yace ana kiran faseelat .
Ummi ta
danyi jimmm sannan tace "gatanan zuwa "
Yaro yaje ya
kai sako
itako ummi
tashiga dakin faseelat har lokacin tana bacci ummi tafara tapping dinta tana
kiran sunanta faseelat ta bude ido, tana kallon ummin.
Ummi tace
"ki daure kitashi ki dan kimtsa ga khalil can yazo "
Faseelat
gabanta ya bada dudum, tasan datace bata iyawa ran ummi ze baci dan dole ta
mike tsaye ummi tace "zade kiiya ko? "
Faseelat
tace "eh ta jawo hijab har kasa ta saka ai gwara tajema ta kara ganinshi
maybe jiya batai masa kallon tsaf ba.
Tana saka
hijab din tafita ummi ta girgixa kai tana kallon yadda take tafiya a kasalance.
Faseelat na
fita taganshi a.....
No comments