BARIKI NA FITO (BOOK 2) 21
BOOK 2
PAGE 21
Lallai dama
duk Wanda yabar Allah yana tare da tabewa da Asara, duk Wanda ya zabi sabama
Allah, amma babu komai zan jure insha Allah, zan d'auki duk wani hukunci ukuba
da Yarima zaiyi min...... Da sauri ta tuna da abunda habib ya Mata, lallai
habib yaci amanarta rayuwa
wanda ka yarda dashi shine mai cutanka...... D'auko wayanta tayi duk da dama Yarima ya
canza mata layi gab da bikinsu Tana da number habib dana su haulat ...... Kiran
habib tayi duk da lokacin wajan karfe biyar saura an kusa kiran sallah
asuba..... Cikin muryan bacci ya d'auka
daka gani baima ko duba sunan ba.....
Jin muryan
bariki yasa habib fad'in harya koroki ne???
Tace habib
kaci amanata Tana magana tana kuka, mai yasa kamin haka, duk irin yardan da
nayi maka??? Abun ......
Yace dakata
ki daina kaini jinsin da ba nawa ba Mlm,
Tace an
kaika d'an daudun banza da hofi..... Maci Amana
Habib yace
dakata bariki, miye zancan cin Amana??
Au dama bariki akwai Amana ne??
Toh gaskiya Indai haka kika d'auka bai kamata a dinga ce miki bariki ba,
karki manta kud'i na fito bid'a, kuma da Farko Aina rufe miki sirrinki, da aka
Biyani naira na dukan Naira har million biyar na fad'i gaskiya, sannan wacce
taban tace in kira Yarima in fad'a mishi gaskiya, Kafin ki fad'a mishi, sannan
ta tura mai hotunan ki da kikai da maza,
da sim d'inta na kira kuma ta wayarta ta tura hotunan, dan haka aikin
kud'i nayi, ke kina tunanin saboda in rufa miki asiri zanki amsar million
biyar, haba bariki ai kin yaudari kanki, Bariki babu Amana ko yarda..... Da Farko na ri'ke miki amana daka baya kud'i
yasa na canza, dan haka Kar kiga laifina.........
Bariki tace
abunda Kamin insha Allah sai kaima anyi maka, kaida wacce kuka shirya
hakan......
Habib yace
Ina ja miki kunne ki daina kaini jinsin daba nawa ba, sannan Bari kiji ita
wacce ta Biyani so tayi Yarima ya koroki ita ta aureki domin y'ar lesbians ce,
bari in fad'a miki sunanta, sunanta hjy Umaima abunda yasa na fad'a miki koda
Kema zaki Biyani ki nemeni dan ki rama, ko yaushe ina free Danni da kika ganni
y'ar kasuwa ce ya k'arasa maganan tare dayin shewa ahayye....... Ita haulat da
bata da k'ashin arziki Aida ita akaso ayi aikin ta Fara yima matar kwana
kwana.....
Bariki kashe
wayarta tayi domin bazata iya jin wannan tsinannan ba......
Kuka take
Sosai wato hjy Umaima itace tayi komai tare da amfani da habib, toh taya tasan
habib din?? Taya suka had'u?? Lallai haulat ya kamata taban amsa, kiran
Layin haulat tayi bata d'aga ba, k'ara kira tayi harya kusa tsinkewa sannan
haulat ta d'auka cikin muryan bacci.....
Da sauri
Bariki tace haulat maina miki keda habib da hjy Umaima.....
Haulat da
bacci ke idonta jin haka yasa ta tashi tare da cewa bariki, Kece?? Mai kike
fad'a haka......
Nan Bariki
ta bata Labarin abunda habib yayi mata
Haulat tace
Bariki wlh Wlh ban San hjy Umaima zatai miki haka ba, da Farko dai taso taje
wajan boka danta miki asiri ki yarda da ita, har nayi niyan taimaka mata a
lokacin, sanda na dawo kaduna in zaki tuna wata rana Aina amshi wayarki?? Toh Ina cikin duba hotunan da nake turawa sai
gashi an turo wani keda Alh madu tsirara, nan nima na tura, in baki mantaba
data dinki a kunne take ranan, ganin na tura na Alh madu saina had'a dana wani
da kika kwana a kirjinshi, ina gamawa na baki wayarki, dama Nayi magana da hjy babba akan Alh madu
ya bashi aikin ya gano wa zaki aura, yace yana son in tayashi...... Jin haka saina kira hjy Umaima akan Kar taje
wajan boka na bata labarin halinda kike ciki, akan auran da za kiyi akwai wanda
yake son rusa auran, harda hotunan dana tura cikin wayarki ta bu'kaci in tura
mata tunda na bata labari, nan na tura mata harda number din habib dan na fad'a
mata shine yasan komai da kike shiryawa......
Bariki tun ranan da kikai min wa'azi tare da nasiha Wlh daka ranan naji
jikina yayi sanyi tare dayin nadama, kuma harga Allah na cire hannuna daka son
cutar dake, wlh bariki ban taba tunanin hjy Umaima zata nemi habib ba, dan
tunda tamin magana nace tayi hakuri kawai ta bari kiyi aure in yaso daka baya
sai ta nemeki, na fad'a mata hakan kawai danta kyaleki Ashe bata hakura ba, kai
amma wannan matar ko y'ar iska amma karki damu bariki zan dau miki mataki Wlh,
Shima kanshi Alh madu da kanshi ya kira hjy babba yace a daina maganan ya barki
kawai.........
Bariki kashe
wayan tayi bata taba tunanin hjy Umaima ko habib za suyi mata haka ba, lallai
makashinka na tare dakai, ta yarda da habib amma yaci amanarta, lallai gaskiya
habib ya fad'a bariki babu Amana, sannan komai kayi sai Anci amanarka Indai a
bariki ne, jin kiran sallah asuba yasa ta tashi dakyar kanta kaman zai fashe da
ciwo, toilet ta nufa dakyar tayi alwala, tazo tayi sallah......
Bayan ta
idar gaba d'aya ta kasa bacci , ba komai take tunani ba sai irin matakin da
Yarima zai d'auka wanda ta tabbata za taji jiki, dan murmushi tayi tare da
fad'in indai wannan hukuncin da Yarima zaimin zaisa ya yafemin Zan jura, koda
zaiyi ta azabtar da rayuwa na Indai Ina matsayin matarshi zan jure.... Kuka ta
kuma saki tare da fad'in Yarima Ina maka son so, Sonka a jini na yake, zan
amshi duk wani horarwa daka gareka......
Tashi tayi ta fita falo da niyan ta Fara aikin bauta daka yau,tana shiga
taga Yarima kwance akan kujeran falon yana rawan sanyi, da sauri ta nufeshi
cikin Tashin hankali idonshi a rufe kaman yana bacci amma ba bacci yakeyi
ba........ Hannunta tasa akan goshin shi
taji zafi Sosai.. Ido ya bud'e a hankali
idonshi ya sauka akan Nata gaba d'aya kallon juna suke cikin ido...... Sunyi wajan minti uku suna kallon juna Kafin
ta tashi da sauri taje ta samo ruwa da towel tasa towel din tare da matsewa, ta
Fara k'okarin sama Yarima akai cikin murya irinta mara lfya yace don't you dare
try to touch me.
Cikin kuka
tace Yarima plz allow me to do it, you have a fever.....
Yana
k'okarin yin magana tayi sauri tasa Mai towel din akai tana d'an matsa Mai, jin
haka yasa ya kasa maganan da yake son yi.....
Amma cikin
ranshi babu komai sai k'una tare da tuna hotunan da aka turomai bariki akan
namiji tana kwance ga wani kuma yana tsirara ya ri'keta, da sauri yasa hannu ya
ture ta.......
K'asa tayi
ruwan dake kusa da ita ya zube, yace karki k'ara zuwa inda nake, I have told
you, I hate to see your face....
Kuka take
Sosai tare dayin nadama akan irin rayuwar data jefa kanta, dan kawai ta kuntata
ma Dad d'inta, wanda inta mutu bata da wata hujja, lallai dama irin bala'in
dake cikin zina harda rashin ganin k'imar mutum, sannan ba'a ganin darajan
mazinaci Wanda gashi shine take gani yanzu, ta tabbata bata ga komai ba yanzu,
sai nan gaba.....
Yarima ne ya
daka mata tsawa cikin tsana tare da fad'in I said leave from here.
Jiki a
sanyaye ta tashi tana kuka harta kusa shiga d'aki yace stop...... Cak ta tsaya
Yace zoki
goge wannan ruwan, wa kika bari ya goge??
And make sure ki cire carpet dinnan dan ruwa ya tabashi shima, kije ki
shanya a waje......
Kitchen ta
nufa ta d'auko mopper ta Fara goge ruwan, carpet din yana da girma kasa d'auka
tayi, duk abunda Zainab keyi Yarima na kwance yana kallonta, ganin bazata iya
d'auka ba yasa tace Yarima cikin dashewan murya bazan iya d'aukan carpet dinba
yayi min nauyi.....
Murmushi
yayi tare da fad'in inda sex ne ai kina iya yi, harda kwanciya akan ko wani
namiji kin iya, kindai iya karuwanci......
Ido ta
lumshe domin maganan Yarima Aliyu ya dakar Mata zuciya, harga Allah Kalman daya
fad'a ta iya karuwanci taji Kalman har cikin zuciyarta, tunda take ba'a taba ce
mata karuwa ba tunda ta fito karuwanci Abun ya dameta, ita da takeso a dinga ma
kiranta da bariki, amma yau shine rana na farko da aka ce ta kware da karuwanci
Abun yayi mata ciwo.... Wani zazzafan hawaye ne ya zubo mata ganin in bata
fitar da carpet dinba zaiyi ta fad'a mata magana sai yasa ta Fara k'okarin ta
d'auki carpet din domin ta kaishi waje din, kaman yanda yace.... Fara ja tayi tana son tayi k'okarin ta d'auka
tasa akai, santsin tiles din wajan dabai bushe ba ya di'beta zata Zame, gaba
d'aya ta sadakar ta fad'i ji tayi an ri'keta, idonta dake rufe saboda tsoro ta
Fara bud'ewa a hankali idonta ya sauka akan na Yarima da shima din ita yake
kallo, sunyi wajan minti biyar a haka suna kallon juna , sannan ya d'agota gaba
d'aya tare da fad'in stop making and excuse da zaki dinga sawa ina taba wannan
kazamin jikin naki.....
Bata ce
komai ba shima yana tsaye yana kallonta, kokarin d'aukan carpet din ta
karayi......
Hannu yasa
shima tare da kama mata duk da baya jin dad'in jikinshi , har kofar waje suka
Kai ganin fadawa a wajan, gashi ko hijab balle Gyale bata saba sai dan kwalin
dake kanta na jallabiya, yasa yace sake carpet din kibar nan....
Bata musa
ba, dan in tayi magana zai iya yi mata ihu, ga fadawa kuma tana hangowa ita
yanzu tsoran halin Yarima take, d'auke roban ruwan tayi takai kitchen ta fito
kenan shima yana shigowa falon, kallonta yayi tare da kawar da idonshi daka
kanta, daka ya kalleta sai ya tuna irin karyan da tamai, Ashe duk ba sonshi
take ba, dan kud'i ta aureshi dan k'aramin tsaki yaja tare da wucewa d'akin da
yake matsayin nashi danya kwanta yabar ganinta domin wani irin tukukin ba'kin
ciki yake cika shi tare da mamaki Wai itace take da wannan munanan halin.....
Gimbiya
zinatu Tana farkawa ko sallah batai ba ta doka ma gimbiya Amina kira.......
D'auka
gimbiya Amina tayi tare da fad'in zinatu lafiya da asuba, badai Yarima bane ya
miki wani abu??
Tace ko
d'aya labari na kira in baki da dumi duminsa
Gimbiya
Amina tace bani inji kodai Yarima ya Kori Matar daya aura ne??
Gimbiya
zinatu tace kusan haka, nan taba gimbiya Amina Labarin abunda Ya faru.....
Gimbiya
Amina tace Kai amma wannan labarin yamin dad'i wlh, toh kodai ya sameta a bule
ne?? Hala ba budurwa bace an gama
cinyeta a waje, shine yaci yaji kofa a bud'e shine nasan yasa lokaci d'aya ya
tsaneta, amma labarin nan yasa ni nishad'i....
Su Yarima manya shidai Mata duk ba virgin....
Dariya suka
saki su duka, gimbiya zinatu tace ni tunani sunyi min yawa wlh, na farko dai
bamu tabbatar ko virgin bace ko akasin haka, kinga bamu da tabbas and sanda
yake kwance ita taje tayi magana dashi, har Dr
yana cewa tare da taimakon ta, yasa zuciyarshi ta Fara harbawa.... Wlh am compose
Gimbiya
Amina tace haba zinatu karki sama kanki tunani, ke dama miye burinki badai
Yarima yafi sonki bane, koma ya saki matar daya aura??
Zinatu tace
eh shine burina My love
Gimbiya
Amina tace toh ki cire tunanin komai, na kusa zuwa Zaria din insha Allah, zamu
shirya komai, yanda zata bar gidan gaba d'aya.......
Yarima koda
ya shiga d'aki kasa bacci yayi sai juyi yake, gashi kirjinshi na mishi mugun
zafi, ga zazzabin har yanzu yana ji, zainab ta gama dani, ta cuceni, but zan
rama abunda tamin Wanda nan gaba zata kiyayi yaudaran wasu.....
**
Farhan ya
kammala karatu inda ya taso da maganan auranshi da haulat, nan hjy habiba ta
tasar da balli akan bai isa ba, babu yanda mijinta baiyi ba akan ta fad'a mishi
dalilin rashin yarda amma ta kasa bashi amsa, dan haka yace dole sai farhan ya
auri haulat......
Haulat tana
d'an waya da Bariki kuma tana neman shawaran bariki duk da bako da yaushe
bariki take d'aukan wayanta ba, wata waya da sukayi Bariki taba ma haulat
shawaran ta fad'ama farhan gaskiyan lamarin abunda suke ciki ita da mum dinshi
in yana Sonta may be ya aureta inko baya Sonta sai su hakura, inda bariki ta
fad'ama Haulat ita gashi karyan da tama Yarima gashi tana shan wuya yana nuna
mata tsana a fili, haulat ta d'auki shawaran bariki.
Farhan yazo
kaduna inda suka had'u da haulat kaman yanda bariki ta fad'a mata haka ta
fad'ama farhan, nan da nan idonshi ya kad'e yayi ja, baiko tsaya sauraranta ba
yayi gaba abunsa....... Koda haulat ta
kira bariki tana fad'a mata bariki tace aiki godema Allah da kika fad'a mishi
Indai har so gaskiya ne zai dawo, sannan zunubin da kika aikata keda mum dinshi
Kinga saiku nemi gafaran Allah tunda kince min kin daina yanzu ,
Bariki taci
gaba da fad'in ni saida na shiga gaskiya ta fito gashi ina cin ubana Kai haulat
da badan so ba dana bar Yarima kuka ta saki Tana fad'in ina son Yarima Sosai
wanda sonshi yasa nake jure irin azabtar dani din da yakeyi.......
***
Yarima Aliyu
ya warke babu laifi, amma har yanzu yana nunama Zainab tsana, yau Yarima Aliyu yaje
fada domin ganawa damai martaba, bayan yaje waziri ya fita Kafin in shiga aka
rufe kofa girib, wannan shine yasa ban
sami shiga ba 🙄 ban kuma San mai suka tattauna ba
.......
Koda Yarima
Aliyu ya fito direct gefen bariki ya koma domin duk irin abunda yake mata Indai
ran girkinta ne yana kwana a gefenta.....
Bariki na
zaune akan gadon d'akinta saiga Yarima ya shigo wanda rabon daya shigo d'akin
tun sanda aka kawota sukai rigima, sai dai su had'u a falo, Bariki kallo d'aya
zaka mata kaga ta rame Sosai, kallonta yayi tun daka sama har k'asa Shima ya
Lura data rame, yace ina son Kimin alfarma ko ince kiyi ma kanki.......
Da sauri
tace Yarima fad'i abunda kake so zan maka Indai za kaji dad'i.....
Yace ina son
ki kaini kotu ki nemi in sakeki........
Da sauri ta
kalleshi tare da hawaye dake zubar Mata a fuska..... Kai ta Fara girgizawa tare da fad'in Yarima
bazan iyayi maka wannan abun ba......
Yace
why?? Tell me why?? You don't love me, you marry me only for
money, ban San in baki wuya I try to send you away from me without hurting you
and you are telling me bazaki iya abunda nace ba??
Cikin kuka
tace Yarima zan zauna matsayin matarka har karshen rayuwa na koda zaka dinga
yankan Naman jiki na, Yarima kana ganin kaman baka min horo ba. Yarima kasan
rashin kulani da bakayi tare da maidani kamar Mai maka bauta kasan yafi min
komai zafi da ciwo........
Yace keep
quiet..... Don't try to show me
affection, you always telling me lies, Zainab you don't love me just go away
from my life.......
Tace Yarima
Wlh koda zaka kasheni bazan Barka b.....
Tsawa ya
daka mata tare da fad'in why tell m.......
Itama da
karfi tace because I love you.....
Da sauri ya
kalleta suka had'a ido, hawaye na zuba daka idonta taci gaba da fad'in Yarima I
can't live without you..... Yarima kayi
punishing dina dako wani irin hukunci zanyi accepting amma karka kara cewa in
rabu dakai, Yarima I will die without yo......... Da sauri yasa mata hannu a
baki alaman ta daina fad'in haka shima hawayen ke zuba daka idonshi duka kallon
juna suke cikin ido suna hawaye😞..........
MARYAM OBAM
No comments