BARIKI NA FITO (BOOK 2) 20
BOOK 2
Rannan
saboda tsoro a toilet na kwana, koda asuba yayi da lambo na bud'e kofar toilet
din naga bata nan, naje nasa ma kofata key,...
Tun daka ranan ban cika fitowa ba, wata rana naje kitchen Zan d'iba
abinci sai gata ta shigo nan gabana ya fara fad'i amma sai naji Abu daban, inda
ta
Fara bani hakuri Wai Wlh shaidan ne ba halinta bane, ita bata haka kaza da
kaza tsautsayi ne wlh kunyan had'a ido takeyi dani, dan Allah in rufa Mata
asiri Kar in fad'ama kowa....... Ganin
harda kuka sai taban tausayi tare da fad'in Ummi ki nemi gafaran Allah akan ya
k'ara kareki daka fad'awa halaka, sannan babu wanda zan fad'ama wa, tunda har kin
gane kinyi kuskure..... Nan tai tamin
godiya.......
Tun daka
ranan na daina shige mata, dama ba wani shige mata din nakeyi ba, sai dai ita
ce ke k'okarin jana a jiki......
Wata rana
naje kitchen d'iban abinci, harna d'iba na fito naga Ummi a falo ita da wata
kawarta na gaida kawar wacce ta kuramin ido kaman tsohuwar mayya,, ummi tace
zainab Nayi coconut juice yana fridge Nasan kina so.....
Nace eh ummi
tare da komawa kitchen na d'auko a cikin fridge, d'akina na shiga na fara cin
abinci na, cikin kwanciyan hankali, nasha juice dina tunda ga lokacin ban San
inda kaina yake ba, tun wajan karfe biyu na rana, nidai na farka wajan karfe
goma na Safiya gabana Nata zugi kaman ansa min Reza an jimin ciwo, kafana duk
ciwo suke min kaman anyi dambe dani, jiki na duk tsami, dakyar na tashi nayi toilet
dan in samu inyi tsarki da ruwan zafi ko zanji sauki daka zugin da nakeji,
bayan na shiga toilet Wanda ban Lura ba kawai naga jini na bimin
kafana...... Abun yaban tsoro ya kuma
bani mamaki nasan dai bana al'ada sau biyu a wata kuma baifi kwana Goma dana
Gama ba, abun ya dauremin Kai, amma tunda nayi wanka tare da gasa wajan, nasa
pad, na fito ina tafiya dakyar.....
Abunda Yaban
mamaki shine yanda naga pad din bai baci ba, tunawa da nayi ance al'ada yakan
Zoma mace tako wani siga, wannan abun ne yasa na basar duk da ban taba yin
irinsa ba, ganin jinin baizo ba yasa nayi wanka na fara sallah
Lokacin da
dad dina ya dawo daka saudiya baiko nemeni ba, gaba d'aya tunda ya dawo ya
canza daka irin kulawan da yake min, da Farko Ina mamaki amma daka baya saina
Fara tunanin aiki sunyi mishi yawa, gashi ina son mishi maganan karatu na,
domin ni saudiya nake son zuwa karatu
ban son inyi a k'asar nan...... Wata
rana naje d'akinshi na sameshi akan maganan karatu na, ya nuna bai yarda inje
wata k'asa karatu ba, nai k'okarin in nuna mishi irin burina na son zuwa can
fad'a ya bini dashi abunda bai taba min ba a rayuwa, kuka nasa ganin haka Ya
fara rarrshi na akan inyi hakuri baya son yayi nisa dani ne, haka yaita
rarrashi na, duk da ina Lura da irin canza min din da yayi Sosai.......
Wani Tashin
hankali da damuwa daya rufeni shine rashin ganin al'ada dina harna wata biyu,
ga nonona suyi ta faman min zugi da rad'adi, gashi sun k'ara girma na k'ara
wani haske ....... Gashi gaba d'aya turare na da nake masifar so naji suna min
wani irin wari, gaba d'aya na zubar nace hala sunyi expire ne, nasa driver yaje
ya siyomin wasu irinsu ,shima dai naji warin yakeyi, abun bada ka nan ya tsaya
ba nida bani da wani cin abinci Sosai amma minti Goma na fara jin yunwa gashi
ci kaman jaka...... Duk wannan abunda
ake ciki Dad dina baya k'asar yana Ghana.
Wata rana na
fito ina zazzabi shima dakyar na fito na nufi kitchen dan naji yunwa na neman
kasheni, ina zuwa falo Nayi d'akina da gudu Ina amai domin warin turaren wutan
da aka sa a falon ji nayi kaman warin jaba...... Ina cikin amai saiga ummi da kawarta sun
shigo suna fad'in sannu maike damunki bari in kira Dr, ban damu ba dama ina da
bukatar ince a kira family Dr dinmu ta dubani domin dad baya Bari maza na dubamu...... Dr tazo tana tamin tambayoyi ina bata amsa
Kai tsaye tace bari ta d'iba jini na, na mi'ka mata hannu na ta d'iba, tace
zata koma tayi gwaji inta gwada ta gani zata Aiko da magani.....
Bayan Dr ta
fita na koma na kwanta ina jiran a kawo min magani, ina cikin bacci naji an
bugo min kofa da karfi, tashi nayi inga ko Waye dad na gani da Falmata, Dad
dina kallon tsana yake min ina mamakin ya akayi ya dawo yau,
Katse min
tunani yayi da fad'in uban wa ya miki ciki ??
Cikin razana
da fargaba nace Dad mai.....
Tas tas ya
saukemin Mari har biyu tare da fad'in kin cuceni Zainab, nida nake ma jama'a
wa'azi , yau gidana shine y'ata ta ciki na tayi cikin shege.... Allah ya isa tsakani na dake Zainab kin
cuceni, duk irin tarbiyan dana baki, jiya sanda ummi d'inki ta kirani tace in
dawo gida babu lafiya, Banyi zaton wannan mummunan labarin zan Tarar ba.....
Cikin kuka
na fara fad'in Wlh dad ba ciki gareni ba, kuma Wlh muje asibiti a duba, Niko
saurayi ma ban dashi W.......
Tas Falmata
itama ta sakar min wani gigitaccen Mari tare da fad'in shairi likita zata miki,
mutuniyar banza, wlh kin cucemu kaf zuri'ar mu babu wacce ta taba Abun kunya
sai ke
Cikin kuka
nace ummi Kema shaida ce banda K......
Tayi sauri
ta katseni tare da fad'in Yimin shuru munafuka
Dad dina
shidai shuru yayi inda Falmata take ta kalaman batanci akai na tare da fad'in
na d'auko musu Abun kunya yanzu taya zasu kalla mutane da wannan abun nawa.....
Falmata ta kalli dad dina babu ko tsoro tace naji kayi shuru kaman kana jin
tsoran yi mata magana gwara ka yanke hukunci tun Kafin mu kasa fita
Dad dina
yace in fad'i uban da yayi min ciki.
Ina tamai
rantsuwa akan ba ciki gareni ba, dan dai nidai nasan ban taba kwanciya da kowa
ba nida ko maza ban kulawa taya zan samu ciki, sai dai in a ruwa nasha.... Da
sauri nace Dad Wlh hala a ruwa nasha d...... Falmata ta saki shewa tare da
fad'in a ubanki gashi nan da yake gabanki kika sha...... Ko tsoran dad batai ba
ta dinga zaginshi Wai shine ya dauremin gindi ai yana nunamin so ya d'auki
dukiya masu yawa Yaban ba dole Inbi maza ba..... Kuka nake Sosai tare da takaici na tabbata
Falmata Nada wani mummunan Abu a kaina tun sanda Dad dina yace tun jiya ta
kirashi akan ya dawo, toh ni kuma yau Dr tazo ta dubani kenan tasan wani abu ko
ince ita ta kullamin shairi..... Tsawan da Dad dina yamin yasa na dawo cikin
hankalina da hayyacina yace na baki nan da zuwa gobe ki fad'amin wanda yayi
miki Inba haka ba za kiga fishina y'ar iska fuuuuuu ya fita...... Wannan itace mummunan Kalman dana taba ji Dad
ya fad'a tunda nazo duniya kuma ba'a kan kowa ya fad'a ba sai a kaina, Kalman
tayi min ciwo, nidai nasan namiji ko hannuna bai taba ri'kewa ba balle ince toh
taya na samu ciki kwata kwata na kasa ganewa..... Ina dai nan zaune inda nake ina kuka saiga
Falmata ta shigo tazo gab dani Tana fad'in Zainab kiban had'in Kai Indai kina
son Dad d'inki ya yafe miki.....
Wani irin
kallo na Mata tare da fad'in da in aikata abunda kike bukata gara dad ya
yankani d'anya ya soya Naman jiki na, akan in aikata wannan mummunan aikin
wanda Manzon Allah ya tsine ma masuyi.....
Tace haba
zainab sau d'aya kawai za muyi in mukayi sai mu tuba....
Zainab tace
tir lallai tabewa da Asara sun tabbata a kanki, lallai irinku ne wanda ake cewa
kuna fita daka addini baku Sani ba......
D'aura
hannunta tayi akan nonona da sauri na wanka mata Mari Wanda dai dai lokacin dad
dina ya dawo d'akin ganin na mareta yasa ya fara salati tare da fad'in munanan
kalamai a kaina wanda zan iya rantsuwa sune suka bini harya kaini inda nake
yanzu domin bakin iyaye dafi ne, sai yasa koda wasa karka taba aibanta d'anka
domin addu'an iyaye kaman takobi take da kaifi..... Dad yaci gaba da fad'in
daka yau bani bake bazan zauna da wannan abun kunyar ba, wlh saboda ke bazan
fasa fita cikin al'umma ba , sannan harda marin ummi d'inki lallai wata rana
Nima zaki mareni,
Kuka nake
Sosai domin jin maganan dad nake Wlh kaman bashi yake fad'ansu ba, mutum Mai tawakkali, da ilimi
yau shine yake nuna da yaji kunyar duniya gwara ya rabu dani har abada, duk
irin sonda yake min ban taba tunanin zai min haka ba, yau koda cikin gareni
dagaske ina tunanin dad dina zai d'auka a matsayin kaddara amma gashi anyi min
shairi ya yarda
Gashi
matarshi sai zugashi takeyi shi kuma yana k'ara hawa yana aibanta ni......
Ranan cikin
dare mahaifina yace in bar mishi gidanshi tunda naki fad'an uban da yayi min
ciki, ina kuka inata rantsuwa akan banda ciki, inma ciki ne Toh a ruwa nasha,
har al'qur'ani na d'auko na dafa akan ban taba saduwa dako wani namiji ba amma
dad dina baiko saurareni ba, cikin kuka nace Dad na tabbata abunda kake min
yanzu kana yinshi ne cikin rashin bincike, dad kafi kowa sanin wacece ni, kafi
kowa sanin abunda zan aikata yau Dad koda ciki gareni ina tunanin zaka d'auka a
matsayin kaddara....
Cikin murya
irin ta fushi yace fita kibar min gida y'ar iska karuwa......
Lallai
wannan Kalman ta dad'e tana Yimin ciwo Sosai har yau inna tuna ina kuka
Mahaifina
ya'ki amsan kaddarata saboda Kar yaji kunyar duniya ace y'ar babban malami tayi
cikin shege, duk da a lokacin ban San inada ciki ba dagaske.....
Tafiya nake
cikin dare komai ban samu na d'auka ba, daka ni sai kayan jiki na, wata babban mota na gani ta lodo wasu kwalaye
na samu na shige duk da ban San inda za suba kawai Ina burin inbar garin abuja
dan nasan motar wani gari zata, ban dad'e da shiga ba motar ta tashi kaman ni
suke jira...... Aiko mukai ta
tafiya...... Munyi tafiya Sosai Kafin
motar ta tsaya inda na samu na fito na ganni a wani waje kaman kasuwa duk da
darene ga mata birjit, cikina naji ya fara ciwo Sosai tare dajin wani abu kaman
hanjin cikina zai fita, da sauri nayi wani wajan benci na zauna inata juyi ji
nayi wani abu kaman ruwa na fita daka jiki na, ina dubawa naga jini Sosai ga
wani irin ciwon ciki inaji Sosai, muryan wani naji a kaina yana fad'in na shiga
uku an fasa aurena Mai zan gani haka y'ar uwa??
Ganin na
kasa magana alaman ina jin jiki yasa ya kamani yana fad'in oh ni hjy babba sai
ku tashi ku kwaso ciki kuzo kusha maganin zubar da ciki kuyi ta juyi, sai a nan
na tabbatar da ciki gareni kuma Bari Nayi domin anyi mana bayanin jinin al'ada
a islamiyya kuma yanda wannan jinin yake zuba nasan bana al'ada bane, na shiga
rud'ani Sosai tare da tunanin a Ina na sami ciki, naci kuka tare da takaicin
wannan abun..... Wanna d'an daudun Mai
suna hjy babba shine ya taimaka min harna warke na dawo normal Ina kwana a
d'akinsa saiya koma d'akin abokanan sa y'an daudu...... Wannan shine silan komawa na gidan karuwai
har na fad'a wannan mummunan harkan tunda banda wani abu da zanyi sai shi,
sannan nakan je kofar gidan mahaifina ko in tura a ajiye Mai hotuna na da
shigan banza dan in kuntata mishi sai dai ban sani ba koya gani ko bai gani ba
oho, ina karuwanci ne saboda rasa mafita ko madafa iyayena sun koreni banda
wani gata.... Komai ya fado min shi zanyi tunda banda mafita duk da ina aikata
Abunne kaman dole sai dai banda wata hujja akai, amma na d'aura hujjata akan
ina son in kuntata ma Dad dina, duk da wani zuwa da nayi na ajiye hoto naga
gidan babu kowa , na tambaya akace sun tashi tun daka wannan ranan da naje naga
gidanmu ban k'ara tunanin in koma Gida ba ko in nemi iyayena ba...... Dan
Tsagaitawa tayi tana kuka tana rungume jikin Yarima taci gaba da fad'in Wlh
Yarima Ina aikata zina amma Wlh harga Allah cikin raina Ina mamakin haka..... Had'uwa na dakai shine yasa na daina, gaba
d'aya, Yarima Nasan had'uwa na dakai had'in Allah ne, na tabbata duk wannan
Abun daya faru dani kaddarace Wanda har yanzu ban son wanda yamin ciki ba,
Yarima dan Allah kaima karka juyamin baya kaman yanda dad dina yamin dan Allah
Yarima.......
Yarima Aliyu
dan janyeta yayi a jikinshi ya kura ma fuskanta ido na wani lokaci sannan ya
fara murmushi tare da fad'in wow wow nice story I wish dat am a director in
had'a film da wannan labarin naki Nasan zan samu kud'i, zainab I will never
ever trust you again, komai zai fito
daka bakinki karya ne, do you think dat I will believe you with dis ur fake
story....... Har kina danganta kanki da
babban malami kina fad'in shine dad d'inki??
Wani irin murmushi yayi tare da fad'in you always lies to me...... Bazan k'ara yarda dake ba in my lyf......
Tace Yarima
am telling you the truth........
Yace
truth?? Zainab komai naki karya ne, kina
tunanin wannan labarin naki zai sa in yarda dake?? You are wrong, this is not the same Yarima dat trust you
before, today wen I see d truth about you I have change.....
Cikin kuka
tace Yarima Wlh gaskiya na fad'a maka harga Allah, Wannan shine gaskiyan
labarin rayuwa ta......
Yace koda
gaskiya ne....... I won't accept you as my wife...... Zaki zauna a nan a matsayin baiwa Mai min
bauta...... I won't accept you macen da
kowa ya Santa, but before in baki aikin ki dole in miki HIV test in gani May be
kina dashi tunda anbi wancan anbi wancan so Kinga in kina dashi sai in San
Kalan aikin daya dace in baki......
Zainab I will make sure to hurt you, saina hukunta ki yanda nan gaba
bazaki k'ara yaudaran wani ba, you r lucky I make promise to my dad da yau sai
kin bar gidan nan but you will live here as my servant, I hate to see your face, make sure to hide
your face from me har sai na nemeki cheater, Yana fad'in haka ya ri'ke kirji
dake faman mishi zafi ya fita tare da bar mata d'akin...... K'asa tayi tana
kuka shikenan Yarima ya tsaneta duk da ta fad'a mishi gaskiyan ko ita wacece
kuka ta saki mai ban tausayi......
Daka yanzu
duk wacce take neman BARIKI NA FITO, daka farko taje ta duba Wattpad ko
facebook page d'ina MARYAM OBAM NOVELS... Dan gskya daka yanzu babu wacce zan
kara turamawa na gaji ga typing ga aikin ture ture haba Abun yamin yawa......
MARYAM OBAM
No comments