RAINA KAMA (BOOK 2) 3&4
*_♦RAINA
KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
~Book 2~ 👉🏻3⃣
............Shiru
kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d'an hasken mai kalar jaa, sai fuskar
tabada wata kala data k'ara mata k'yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon
k'urilla irin haka, yadad'e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da
barci. hannu ya mik'a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d'akin, cikin
dabara yafara yunk'urin janye jikinsa, amma tak'i yarda, saima farkawa datayi,
tabud'e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad'an take kallon face nashi,
ta lumshe idon tasake bud'ewa.
“wannan d'aurin goronfa?”. ‘galadima yay
maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye
cikinsa da kallo’.
Sosai Munaya ta waro idonta yanzun,
ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana
matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad'i, dan ita
harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik'e kanta dake sara mata
tana tashi zaune.
Shima saiya tashi yana binta da kallo, a
mugun sanyin murya yace “bakida lafiya ne?”.
Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta
na rawa tace “kaina kamar zai tsage”.
Saida yaja 1minute kafin yad'an matso
kad'an, yatsunsa biyu ya d'ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya
janye ya d'aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d'ass d'ass
d'ass d'ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga
gadon gaba d'aya.
Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya
zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad'ago idanunta dake cike da
barci, sunyi d'anja sun k'ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta
maida k'asa tana cigaba da hawayenta.
Kad'an yad'an furzo iskar bakinsa, kafin a
hankali yace “mike miki ciwo bayan kan?”.
Saida takuma matso wasu hawayen sannan
tace, “duk jikina”.
“kin fad'ine?”.
Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da
tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu
dad'i, koba komai itad'in Friend nashice ai, kamar yanda yafad'a tun farko.
yad'an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik'e, bayi yashiga, mintuna
kad'an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace “taso kid'an watsa
ruwa, ko jikin zai huce”.
d'agowa tayi ta kallesa, sai taga ya
tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa
tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik'a mata hannunsa, alamar takama ta tashi,
ta d'ago ta kallesa ya d'aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun
tabbatarwa.
Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had'e
waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d'aya yamata ya kauda
kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda
surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba.
da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk'in kai irin nasa, ada kallon
mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara
fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu
ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai.
Koda ya fito saiya had'a mata tea, shi
dama baya rabo dasu a d'akinsa, magani ya d'akko shima ya ajiye, yakoma bakin
gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta.
Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta
ruwan, lallai naji dad'i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba,
inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d'auki zafi, towel naja Na d'aura, saidai
bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d'akin, kad'an
nabud'e k'ofar Na lek'oda kaina, yad'an juyama k'ofar bathroom d'in baya
kad'an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace “please
yalla6ai ka taimakeni da hijjab”.
Waiwayowa yayi ya kalleni, alamun
baijiba sosai, Na turo baki kad'an sannan nace “please yalla6ai hijjab”.
Baice komaiba ya mik'e, inda nake ajiye
hijjab d'in yaje ya d'ako, yazo inda nake ya d'oramin akan hannuna dana mik'o,
kallon ido cikin ido mukaima juna, kowa ya janye cikeda basarwa.
Bayan nasaka hijjab d'in nafito kamar wata
muna fuka, sai k'asa nakeyi da idanu nakasa kallonsa, shima idonsa a lumshe ya
jingina da fuskar gadon, wucewa nayi wajen akwatina Na d'akko wasu kayan
barcin, bayi nakoma Na saka, saina yafo k'aramin Vail Na cire hijjab d'in.
Yabud'e idanu kad'an a kaina, batare da
yayi magana ba ya nunamin mug d'in daya had'a tea a ciki. nad'an yatsine fuska
da marairaice murya tamkar xanyi kuka, “ALLAH yalla6ai banajin yunwa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saida yaja
kusan 2minutes sannan yatashi zaune sosai,
batare da yayi magana ba ya d'auki mug d'in da drug's d'in ya taso inda
nake zaune a kan sofa, saman k'aramin table d'in gaban kujerar ya zauna yana
fuskantata, d'an gaf d'in daya bari tsakanina dashi bai wuce tafin hannuba, Dan
har inajin saukar numfashinsa, baya nad'anja kad'an Na jingina da jikin
kujerar, amma hakan bai hana kusanci sosai tsakanina da shiba. babu magana babu
komai naji dirar cup a bakina, d'ago ido nayi tamkar zan fasa kuka, danni wlhy
banajin shan shayinan, yamin hararar data saka 'yan cikina harmutsawa, babu shiri
nabud'e baki na kar6a, ya had'e girar sama da k'asa, baibar ko k'aramar k'ofar
dazan kawo masa wargiba, haka naita kar6a ina hawaye, saida yaga Na shanye tas
sannan ya barni yana hararata, nidai yau babu k'arfin mayarwa, yabani maganin,
shikam babu musu Na kar6a nasha. ganin yanda naketa hawaye saiya zubamin ido
kawai yana kallon ikon ALLAH, nikam banida niyyar daina kukan nawa, kuma nima
bansan dalilin kukanba, kawai dai jinake hawayen Na tahowa.
Ya zuba tagumi abunsa yana kallona kamar
yasamu television. kallon dayake min saiya k'ara tunzurani, nafara kuka mai
sauti harda shashsheka.
Tagumin yacire yana wani k'asaitaccen
murmushi, ya mik'e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k'asa ya d'auka ya
jera a tsakkiyar gadon kamar d'azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama
k'afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan
hawaye”.
Harara Na zuba masa batare da Na
shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe
fitilar ya maida ta barci.
Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar,
amma sainaji duk babu dad'i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar
ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad'af-sad'af
tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci. Ashe duk abinda nake
yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana
jinjina irin rashin wayona.
Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan
naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad'an nafara zufa, alamar zazza6in
ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba.
Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke
numfashi a hankali alamar nasamu barci, k'aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin
yasake addu'a shima ya gyara kwanciyar sa.
★★★★★★★
Yau gidanmu sun tashi cikin tashin
hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na
kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta
tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad'ansu,
sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d'aga kai ta tsawatar
musu.
Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda
suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad'i zasu rud'e, amma
gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya
tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d'azun
tafara jin mamansu yaa hameed tana k'ananun magana akan tak'i fitowa ta aza
musu girki, maimakon sunga shiru su lek'o suji ko lafiya? A'a su babu ruwansu,
kawai a dafa abasu suci da 'ya'yansu...
Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta
kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki.
“wani cikinku ya d'akkomin wayata saman freight”.
Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa
ya dokarmin baki”.
“kukuka Sani, nidai nace wani ya d'akkon
waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”.
Aryaan ya d'akko mata wayar ya kawo
mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka
d'aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka
suna general hospital.
“innalillahi wa'inna'illaihirraji'un”
innarmu tafad'a tana mik'ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo
waje tana kwalama matan gidan kiraba.
Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu
wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d'ori d'afini.
tana hawaye ta sanar musu da abinda
yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro.
Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana
shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan
kwakwazon natane ya ankarar da jama'ar anguwarmu.
A rikice baba k'arami da Dady suka nufi
asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa.
Kafin wani lokaci jama'ar gidanmu sun gama
cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan
bak'aramin buguwa yayiba.
______________________________
Alhmdllh natashi jikina da sauk'i, Dan kuwa
babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo
massalaci, lokacin har gari yafara haske ma.
Na idar da salla ina zaune ina addu'a
yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue,
yana rik'e da k'aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa.
Kallo d'aya namasa Na d'auke kaina, shikoma
bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na
tsinkayo muryarsa yana fad'in “ya jikin naki?”.
Yanda yay maganar a cinkushe yasakani
d'agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d'auke kaina, nace “da
sauk'i”.
Bai sake magana ba, harya kammala yabar
gaban mirror d'in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na k'asa bansan hidimar dayakeba.
Koda ya d'auki kayan saiya koma bayi ya
saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na
kallesa, yayi k'yau cikin wani bak'in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan
style, nakula yanason kayan al'adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k'abilar
tasaba, sock's ya d'akko da bak'ak'en takalma sau ciki ya zauna saman sofa,
yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata 'yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike
da buk'ata?”.
Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake,
Na d'ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya
d'ago shima. Ido muka had'a saina janye nawa.
“kallon fa?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin
saka d'ayan takalmin’.
Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai
mizan kalla anan?”.
Banza yamin, saida yagama saka
takalminsa sannan yamik'e tsaye yana fad'in “hakanefa, Ashe babu abin kallo
anan”.
Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka
laptop d'insa dawasu 'yan abubuwa a k'aramar briefcase d'insa, ya zuge zip d'in
yana fad'in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”.
Da sauri nace “a'a kaje abinka, Indai
nice Na warke”.
Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma
nak'i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud'i akan gadon,
“ni Na tafi, a yafi juna”.
'Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin
kalmarsa ta k'arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya,
ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k'are maganar da d'aid'aya’.
Cak ya tsaya abakin k'ofar, saboda yanda
addu'ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a
hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had'a ido,
amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi, irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani
daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri.
Yabar zuciyata da luguden dabansan
dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na
dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin.
Bai dad'eba sosai a hospital yamusu
sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma
ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu'oin dawowa lafiya, yayinda shikuma
yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d'in
dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito.
Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu
ma shine yatafi kaisa airport d'in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso
zuwa 9ja.
Zaune yake kusa da window, yayinda wata
matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had'e
fuska, a d'age ma ya amsa mata sallamar data masa, yasaka belt tareda bud'e Newspaper yahau
karatu.
Budurwar sai satar kallonsa takeyi,
tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke
buk'ata?, yace Coffee.
Itama da sauri tace Coffee d'in. juyowa
yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi.
Janye idonsa yayi yanajan tsaki a
zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d'ayane Galadima yak'i yayi, ya
had'e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya
fad'o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan
jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan
yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani
murmushin yakuma saki...... haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar
tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata
yardaba adole big girl Ce.
Koda suka sauka baiko kalli inda
yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad'in “haba yayana babu
sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”.
Yana sauka daga step d'in k'arshe Na
jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad'in
“kozaka bani Number ka muke zuminci”.
Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba abinsa. tsaye
tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko
shid'in kurmane?. cikin matuk'ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d'aya sunyo
wajensa, daka gansu kaga jama'ar masarauta. da k'yar ta had'e yawun bakinta,
kenan shid'in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci
gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu.
Driver d'in da yazo d'aukarta yak'araso
inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k'ar6i handbag d'in hannunta. amota take
tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d'aya sukazo d'auka?.
Yace, “ma'am Galadima Sameer kenan, d'an
tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”.
Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina
ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d'inka Na fad'amin
abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Ma'am”.
Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta
karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number
babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d'inba yashiga
uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba.
*********************
Tun bayan tafiyar Galadima saina zama
wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai
nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani
al'amari yana shirin faruwa da rayuwata.
Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi
saida yay magana.
Bayan ya dawo school sai muka tafi
asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru
abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin,
narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana
yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa
yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa.
Shirun da Sauban yaga nayi shine ya
kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin
naki halan?”.
Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su
Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa
Sauban ALLAH a'a”.
Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata
murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”.
Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune
kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina,
saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract
d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni.
Haka nagama shirin barci Na kwanta a
gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e
ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai
zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na
kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na
d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar
innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa
kafin barci mai nauyi ya d'aukeni.
_____ .★. _____
.★. _____
Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba,
'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu
Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma.
Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito
yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba
a yau.
Sabon kukane yatashi, musamman ga
innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da
rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta..........
Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane
da yawa a wajen.
Munubiya tayi yunk'urin kirana amma
network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake
ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in.
Kowa zuciya babu dad'i suka tattara
suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer
aka bari a asibitin zasu kwana.
Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu
lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima
k'alilanne daga cikinsu suka yisa.
___________________________
Sosai hadimansa sukayi farincikin
ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud'in mutanene masu
muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa.
Kwance yake a bayan motar idonsa a
lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k'are masa a wajen
Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi
yunk'urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud'e lumsassun
idanunsa tareda furzo k'aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran
hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k'ofar sashensa suna jiran
isowarsa.
Dogarin daya bud'e masa k'ofar yafara
k'ok'arin d'aukar briefcase d'insa domin shigar masa.
Shima ziro k'afarsa d'aya yayi ta inda aka
bud'e masan, ya zuk'i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe
idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya
zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu
d'aci da rad'ad'i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid'in ba kowa baneba, inama
ace shid'in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za'ace yaza6i
rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka
kwanciyar hankali inhar yanada k'yak'yk'yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu
komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan
kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka
dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan
yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje
tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi
kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu
lafiyarsu sannan yashige ciki.
Ko ina k'al yake tamkar yanda yake
buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya
k'asar).
Zama yay bisa kujera yana fad'in “ya ALLAH!
Alhmdllh”.
Dogarin daya shigo masa da jakka
yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice.
Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa
da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin
isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in,
komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke
tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya
watsa ruwa.
Ya d'an jima a bayin sannan ya fito
d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya
d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a
hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa
turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune,
briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na
Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai
tashi yana fata komai ya dai-daita.
Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya,
amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya
dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi
barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili,
duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta,
Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya
kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract
fa?”. ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya,
daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana?
(danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu
zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi
samun nutsuwa, oh god🤦🏼♂”. ‘ya k'are maganar da dafe kai’.
Shima yajima baiyi barciba, sai can
dare yaja da nisa sannan ya saceshi.
Da asubahi da k'yar ya iya tashi,
alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki
da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa.
Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida
fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa
k'asa.
Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa,
sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida
Galadima d'in.
A hamshak'in falon mai martaba na farko
suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na
k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi
sallama..
K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da
butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug
k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl.
Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai
martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da
zuwa.
Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya
durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa
nuni dayaje abinsa.
Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa
sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje.
Galadima ya had'ama Mai martaba shayi
da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada
mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya).
cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa
murmushi, sannan yace “kaifa?”.
Girgiza kai Galadima yayi, yace “a'a
Abba, wannan sai ku”.
Mai martaba yay murmushinsu na manya
sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”.
Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin
tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha
ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga
guminmu”.
Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i
shayinsa sannan yace “tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya
jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah?”.
“jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan
tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”.
“to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo
kenan?”.
“a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala
abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”.
“to ALLAH ya tabbatar”.
“Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu
gaisa da jama'a, dan zan d'an fita”.
“ok, ALLAH yayi Albarka”.
“amin Abba, a huta lafiya”.
Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa,
Galadima kuma yafita.
Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa
domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo
k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu
hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye
da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa
abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.
Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa
tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan
yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin
mahaifinsa.
Ganin number ce sai abin yabashi mamaki,
bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.
_Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a
wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba
ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._✍🏼
No comments