RAINA KAMA (BOOK 2) 1&2
*_♦RAINA
KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*
~Book 2~ 👉🏻1⃣
Yauma dai haka Na tashi banida wata
isashshiyar lafiya, Na tak'ark'ara nayi gyaran d'akin har zuwa falo, sannan Na
had'a ruwa mai zafi nayi wanka dashi.
Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a
k'ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k'arasa, sannan nace ta shigo.
“humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a
mirror kuwa?”.
Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli
jikina, nace, “kamarya?”.
Zama tayi a sofa tana 'yar dariya,
sannan tace, “wlhy kinyi k'iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata
madam”.
Nad'an fiddo idanu waje, sannan Na
harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”.
“tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na
fad'a, halan Uncle Sam bai ta6a fad'a mi ki ba........”
Ta k'arasa Maganarta da d'ai-d'ai saboda
shigowarasa d'akin da sallama ciki-ciki.
Suna had'a idanu ya watsa mata harara,
hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik'e ta fita, Nikuma
najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa.
Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo
d'aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid'e bisa fuskarsa.
“yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad'a cikin
tausayawa’.
Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka
a hankali zuwa gabansa, durk'usawa nayi a gaban nasa, a d'arare nasa hannu Na
najanye nasa dayay tagumi dashi.
Ya d'ago idanunsa da sukai jaa yana
kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar
zuciya nakuma fad'in “bakada lafiya yalla6ai?”.
Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji
yakamata ya fad'amin, kodan nuna damuwar danayi akansa......
Ganin yamin shiru nikuma saina yink'ura
natashi ina fad'in “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawab......”
Bankai k'arshen maganarba naji tattausan
tafin hannunsa cikin nawa.
Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da
tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare
hannun kawai ya fisgoni na fad'a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a
jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera.
Bansan nawani lumshe idanuba saboda
daddad'an k'amshin turarensa d'aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma
ya sauk'e 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a
gefen kafad'arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d'ina, mayun idanun
nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k'ok'arin
cire kannawa daga kafad'arsa.
Hannunsa na dama da nake jiki ya sak'alo ta
bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad'ar tasa, cikin muryarnan tasa mai
kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi
barciba gaba d'aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon
halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..”
‘yak'are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara
maganar’.
Wani matsanancin tausayinsa ne ya
ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya,
nima hawayen suka fara gudun fanfalak'e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai,
cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin
nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda
hard'e hannayensa a k'irji. duk da
kujerar tama tsawonsa kad'an, dan ma Love's chair ce.
Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye
na zirara daga idona har yanzun.
Shikam idanunsa a lumshe suke.
Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace,
“Yalla6ai kayi hak'uri, Abie d'inmu yana buk'ar addu'armu ne fiye da kukanmu,
sannan itace jarabawarsa, wad'anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin
ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu'oi Dana Sani, Nina kakanmu
ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana
zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya
gagaresa, kuma shine yace mu rok'esa zai amsa mana”.
Tunda nafara maganar bai bud'e idonsa
ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k'arshen zancen sannan ya
bud'e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar
zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Nima shirun nayi ban sake yink'urin yin
magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci
ya d'aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali.
Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama
fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai
yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da
Momma gsky, duniyar tunani nafad'a batare dana fargaba, tausayin Galadima da
families nashi yana cukurkud'ar ruhina, insha ALLAH nayi alk'awarin bada gudun mawa
a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k'are.
kaina na jingina da jikin kujera, nima
sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad'in jikina nakeyiba.
********
Bayan anma Abie allurar datake temaka
masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami
nutsuwa, dan yayi barci.
Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan
Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda
numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan
Galadiman ba.
Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d'an
uwanki?”.
Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta
yadawo ta farga babu Galadima d'in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya
fita, bara na duba”.
Bata jira cewar Momma ba tafito daga d'akin
da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak'ara tashi, fitowa tayi
harabar asibitin tana tambayar securitys d'in wajen.
d'aya ya sanar mata ya fita a rikice
gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba.
Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen
Momma ba tashiga mota tanufo gidan.
Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren
sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d'inku?”.
Samha tace, “yana sama Mummy”.
Da sassarfa ta haye step's d'in, itadai
Samha da mamaki taringa binta da kallo.
Ko knocking bata tsaya musuba ta turo
k'ofar ta shigo.
Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima
kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d'aya na bisa Kansa, yayinda shikuma
yarik'o d'ayan hannun munaya ya had'e da nasa ya d'ora kan kirjinsa, suduka
barci ya kwashesu a haka. cikin sand'a ta juya ta fita taja musu k'ofar tana
share hawaye dayima ALLAH godiya d'aya bama d'an uwanta mace tagari wadda take
kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar
dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar
masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai.
Momma ta kira ta fad'amawa dan hankalinta
itama ya kwanta.
Momma harda hawayen farinciki, tana godema
ALLAH.
Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin
itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.
*************
A k'alla munyi barcin 47minute's, Galadima
ne yafara farkawa, ya bud'e idanunsa a hankali, hannuna dake rik'e a nasa
yafara kallo, kafin yad'ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes
sannan yad'an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud'e idona, ido muka had'a,
kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan
nazame Wanda yarik'e d'in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani.
Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali
yacemin “thanks”.
Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba.
Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik'e tsaye. takalmansa kawai
yacire ya d'auki jallabiya a wardrobe d'insa yashige bayi.
A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda
janye idona daga k'ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na
kwanta.
Ya d'auki adadin wasu mintuna masu tsawo
kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi
batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon
alamar time d'in salla yayi.
Kaina kawai na girgiza na mik'e, zuciya ta
na mamakin hali irinna Galadima.
Shikam turare kawai ya d'auka ya fesa
yafice salla.
★★★
((★))(())((★)) ★★★
A gidanmu kam hankalin mamansu
yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa'eed babu labarinsa, kira Zarah
tamasa yafi 50 amma yak'i d'agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin
komai sai kuka, ga ciki.
Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata
gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad'i ainahin gaskiya,
danshi bai yarda ba itace ta d'auki kud'inba..
Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta
mak'iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya.
Itama da farko buris yay da ita, saida yaga
tanace sannan yace, “wai kekam Ai'sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu
da lamarin wad'anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke
cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”.
Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da
murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d'ayane a wajena, domin
kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka,
a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba'a son mace mai ciki da
shiga tashin hankali, muyima tufk'ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu
yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar
alhaji, dan ALLAH kayi hak'uri kaji”.
Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai
saka mata albarka da aminta da buk'atarta na kiran senator halluru da safe
insha ALLAH.
Innarmu tamasa godiya itama.
**********
“Babyna wai mike faruwane haka?”.
Da gyar Munubiya ta d'ago ido daga
kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar.
Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne
babu dad'i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”.
Zama yay kusada ita, yad'ago kanta ya
jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki
mana?”.
“a'a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa,
kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d'in”.
“Amma kuma k'ya zauna da ciwo, ki daure
dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”.
“babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na
d'ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”.
“Ana dai so aima Yaya wayo kawai”.
Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,,
takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon.
Binta kawai yay da kallo yana murmushi,
yana k'aunar matarsa kuma 'Yar uwarsa, gaba d'aya Munubiya ta canjashi, dukda
bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa,
komai a d'auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin
murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da
kawalwalniya a zuciyarsa.
Mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen
d'in danya taimaka mata da aikin, dan yau d'in weekend ne baije aikiba. dan
yayi resume tun last week.
((★))*((★))*((★))*((★))
Tunda na idar da sallar nazame a
wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad'i, jinake
kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d'ago ido na kallesa,
sannan na amsa ciki-ciki nima.
Frigate ya bud'e ya d'auki ruwa yakoma
saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad'a, saida ya
shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na
k'ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad'ago muka had'a idanu sannan nayi
saurin yin k'asa da nawa.
Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi
muje hospital d'in, daga nan saimu samo zam-zam d'in”.
Tunkan yakai k'arshen maganarma na mik'e
tsaye, hijjab kawai nasaka nad'an gyara fuskata, shikuma ya d'auki kaya yashiga
bayi ya canjo sannan muka fice.
Jin gidan shiru yasashi d'aukar waya
yakira sashen bayin gidan, babu dad'ewa saiga d'aya acikinsu tazo.
Zubewa tayi tana gaishemu, ya d'aga mata
hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”.
“Ranka ya dad'e sunfita suda mummy”.
Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai
sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi
abaya.
Sai da yasakama k'ofar security sannan
muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri
suna gaishemu, hannu kawai suma ya d'aga musu muka shiga motar, suka bud'e mana
gate d'in muka fice.
Tunda muka fita babu Wanda yay magana
tsakanin ni da shi, yana aikin tuk'insa da sauraren redio daya kunna a motar,
nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a
redio d'in, tunda ba English baneba gaskiya.
Mun Isa wani babban shagon Islamic
camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.
Abinda ya kaimu muka shigayi, yad'ebo
zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad'in “saikuma mi?”?
Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata
muk'ara?, zuwa can nad'an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin
kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d'akkoshi,
(a tunanina idan mun dawo gidan zan d'auki hotunansu na turama Munubiya ta
bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.
Duk abinda nake yana a tsaye yana
kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.
Mun k'arasa wajen biyan kud'i, bayan
yabiya yaran shagon d'aya ya d'aukar mana zuwa mota.
Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har
lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji
dad'in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai
tsurama masa idanu da masa addu'oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne
Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.
Momma tayi farinciki da yanayin Galadima
d'in cikin k'oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin,
amma Alhmdllh yanzu gashi normal.
Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma,
ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.
Sauban ma yana dawowa daga school shida
Khaleel nan suka taho.
Bamu
bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk'atar Abie ya
kwana tare da ma'aikatansu.
Koda muka shigo Galadima sama ya wuce
abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.
A kunyace na mik'e domin cika umarninta.
Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da
baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga
wanka, nima natu6e nawa na d'aura zani nasaka hijjab tareda d'aukar kayan
barcina ina jiran fitowarsa.
Bai dad'eba sosai kuwa yafito, sanye
yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.
Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta
a bakin gadon a haka, k'afafunsa na k'asa, ya tsurama rufin d'akin idanu alamar
yatafi duniyar tunani.
Nikam ruwa mai zafi na had'a nashiga
koda zanji dad'in jikina, na dad'e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna
fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k'ofar
bayin, Amma babuni babu dalilina.
Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani
nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k'ofar cikeda basarwa.
Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin
barcina tun aciki, saina d'auki zani na d'ora a saman kayan nasaka hijjab nayi
sallar shafa'i da wutiri, bayan na idar nad'akko roban zam-zam d'in d'aya na
zauna nafara karatu Qur'an acikin ruwan zam-zam d'in. a hankali nake karatun
cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.
Har cikin 6argonsa da jini yakejin
sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi.
mik'ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa'i da witiri yay joining d'ina
muka cigaba da karatun a tare.
Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi.
(da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).
____((()))((*((()))*))((()))____
Yauma dai haka innarmu tadagema
abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma
lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d'aya xaka mata kagane abirkice
take.
Innarmu duksai suka bata tausayi, matan
gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy
Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d'in dad'i takeji, tanadai nuna
damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d'inne.
Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri
sukad'anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.
Hankalin Senator halluru yatashi, danshi
koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa'eed saiyaje gida yaci
abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.
Hak'uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy
shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa'eed d'in zaizo ya
d'auki matarsa.
Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma
bama d'an uwansa hak'uri akan lamarin.
Innarmu bata buk'atar jin k'arin bayani
dantaji komai, takumaji dad'i sosai.
()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()
Jikin Abie dai kam yayi tsanani a
tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu'a, dan baisanma Wanda yake
a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul'fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan
ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d'aukar kowa nasu,
duk da d'ar-d'ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake
zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni,
mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k'arema uwarsa tanadiba, ba
kamarma mu 'yan d'akinmu.
hakama sarki jalalludden shida
uwargidansa sunzo da mama Fulani.
Ranar momma har tausayi tabani, kai mama
Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid'a mulki a asibitin nan.
Hummm🤦🏻♀.
Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana
ya dage ya ya6a mata bak'a shikuma.
Ba gidan suka saukaba, a hotel suka
sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.
Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin
ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.
Nima k'asa na durk'usa na gaidasu su
dukansu har Momma da aunty Mimi.
Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo
na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k'urillar da Mama
Fulani kemin duk sai na takura.
Tad'an ta6e baki sannan ta gyara zama
idonta na kaina, tace “toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana?
daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india”.
Gaba nane yafad'i, dan nafahimci dani
take, saina rasa amsar dazan bata..
'Yan d'akin kam kowa ido ya zuba ma mama
Fulani har Galadima.
Aunty Mimi ce tace, “Ranki yadad'e Kodai
kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki?”.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali,
taji dad'in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad'an batason abinda
zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a
cikinsu.........
Wani munafukin murmushi mama Fulani
tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga
sama sukaji tace, “cikin namu wata nawane Galadima?”............✍🏼
E me🙆🏻 mama Fulani mai gani har hanji🤦🏻♀.
*_ALLAH ya
gafarta na iyayrnmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Haske writer's asso...._*💡
*_♦RAINA
KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻
~Book 2~ 👉🏻2⃣
..............Shiru
Galadima ya mata, da ace babu Momma daya
ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka
maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.
Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa
kallona duk sukayi, nayi k'asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen
tsohuwarnan yana son tsoratani.
Shigowar Sarki Abdul'fatah (papi) da
inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak'aita zancen. dan
daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima,
yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.
_____________________________
Misalin 8:pm saiga Sa'eed yazo
gidanmu, a time d'in gwaggon Haleematu da mamansu yaa Hameed suna ta hayaniyar
fad'a, wai mamansu yaa Hameed ce takama gwaggon Haleematu tana kallon Zarah
dake alwala a fanfo tana dariya.
Shinefa mamansu yaa Hameed tace gwaggon
Haleematu taci kanta tasha bak'in ruwa, karta lashe mata jika tun yana a ciki.
Wannan kalma ta mamansu yaa Hameed itace
tajawo fad'a, Dan gwaggon Haleematu tace mamansu yaa Hameed tace mata mayya
bazata yardaba. Fad'a sosai sukeyi suna cin zarafin juna da gori, dama kowa
kishi Na cinta a zuciya.
Matan gidanmu duk sunyo waje anrasa masu
dakatar dasu sai innarmu dake cewa suyi hak'uri Dan ALLAH, darene fa.
Amma Sam sunk'i saurarenta.
Innaro dataji hayaniyar tundaga gidanta
yasata d'akko fayafi tafito, kamar anjehota haka tashigo gidan.
Sa'eed da Sulaiman suna awaje a mota, duk
badak'alar da akeyi daga cikin gidanmu suna jiyowa, har shigar innaro kuwa suna
kallo. Dayake su Abbanmu suna masallaci.
Innaro tanata magana sunk'i saurarenta,
saiyi sukema kamar zasu fara danbe.
Mamansu yaa Hameed Na k'ok'arin kwalama
gwaggon Haleematu ludayin miya dake hannunta innaro takawo jiki zata kare sai a
goshinta, jikake kwarrrr!.
Tako dafe goshi tafasa k'ara..
Hakan kuma yay dai-dai da shigowar su Abba
gidan, su duka ukun, tunkan sushigo sukejiyo hayaniyar dama, dukansu rai a 6ace
suka shigo. Dan iskancin matan nasu ya ishesu hakanan, idonsu yarufe ko ganin
motar su Sa'eed basuyiba.
Ran Abba yakuma 6aci, Dan ganin duk
matansa ne ma masu hayaniyar, ga abinda sukaima mahaifiyarsa akan idonsa.
batareda yabi ba'asiba yace duk sufice su bar masa gida.
Ananne kowa yay tsitt, yadaka musu tsawa
yana fad'in wlhy idan basu fitaba zaisa a fiddasu, ko d'akunansu bai yarda wata
takomaba kuma.
Dole sai 'ya'yansu suka d'akko musu
hijjabai suna kuka da bama Abban hak'uri.
Amma yak'i sauraren kowa, daddy da baba
k'arami kuwa babu Wanda yay yunk'urin hanashi.
Innarmu tamatsa kusadashi tana rok'onsa
karyayi haka, yazauna ya sauraresu tukunna, Hararar daya zuba matace yasata
jada baya tai 6am da bakinta.
Innaro kuwa maman safara'u ce takamata
ta zaunar, goshi harya fara kumbura🙆🏻.
(((+)))***(((+)))***(((+)))
Kafin mu baro asibitin nama manta da
maganar mama Fulani, saboda murnar bud'e ido da Abie yayi ta d'aukema kowa
hankali kuma, gaskiya ina tausayin bawan ALLAHn nan sosai.
yauma bamuyi k'asa a guywa ba wajen cigaba
da addu'oin damukeyi cikin zam-zam ni da Galadima, somuke muyi na 1week sannan
afara bashi.
Washe gari Alhmdllh jikin Abie yayi k'yau
sosai, Dan inka gaidashi yakan maka murmushin sa Na dattako, hakan ya sanya su
papi sukayi shirin tafiya da yamma.
Ni da Galadima da Sauban muka musu
rakkiya, sainaji tamkar nabisu. Harda 'yar kwallata kuwa. Inno tanata
tsokanata, Dan tsohuwar tashiga raina sosai.
Tunda muka d'akko hanyar dawowa
asibitin nakife kaina a cinya inata hawaye, sauban ne kawai ke tsokanata, amma
Galadima tamkarma baya cikin motar. hakan saiya k'ara tunzura zuciyata, nakuma
k'ara k'arfin kukan nawa.
Sauban yasamu guri yay parking, da hannu
Galadima yamasa alamar yaje.
Fita yay yana k'uk'uni da k'umshe dariya,
wai “su boss za'ayi lallashi shine aka koroni”. Saida yay nisa da motar sannan
yasami damar dariyar, har yashiga wajensu Momma.
Daga Momma har Aunty Mimi kalli
onsa
sukeyi,, aunty Mimi tace, “Auta lafiyarka kuwa?”.
Saida ya zauna sannan yashiga kora musu
bayani, dariya kawai sukayi, sunsan Sauban babu sauk'i wajen taso mutum agaba.
Tunda Sauban ya fita sai Galadima ya
gyara zamansa kawai ya zubamin ido, mutum ne shi dabaya son shiga hak'in wani,
ko kad'an baiso ace wane yana cikin damuwa ta dalilinsa......
Wayarsa aka kira, ya kalli wayar kafin
yakai hannu ya d'auka, salamar da akayi daga can ya amsa suka gaisa.
Jin ya ambaci Nuren nagane da Wanda
suka ta6a yin waya kwanakine, nad'an tsagaita da kukan ina sauraren mizasu
tattauna. Galadima naji yace,
“miya farune kakeson nazo Nigeria haka
da gaggawa Nuren”.
“no babu wani damuwa, driver da yarinyar
nanfa suna hannu, so yakamata ka shigo muyi abinda yadace ko?”.
“ok babu damuwa, insha ALLAH zuwa
Wednesday idan jikin Abie ya kuma lafawa zan shigo”.
“O right, ALLAH ya k'ara masa lafiya, a
gaishesu”.
“zasuji insha ALLAH, bye”.
Wayar ya ajiye a tsakkiyarmu ya maida
hankalinsa kaina.
Cikin wani salo yace, “Munaaya!”.
Wani Yarr naji a jikina, karo na biyu
kenan danaji sunana a bakinsa, sainaji sunan nawa ya canja kamar ba shiba,
danya iya sarrafa sunan a harshensa..... ganin ban d'agoba yakuma kiran sunan.
Kasa jurewa nayi nad'ago idona na kallesa,
ganin ya tsareni da idanu saina janye nawa. yad'an lumshe nasa ya bud'e a kaina
ya furzar da huci “kina ganin haka abokai yakamata su kasance? ni friend
nakine, miyasa bazaki iya fad'amin damuwarki ba? kiyi hak'uri nasan kina
buk'atar zuwa gida, last week naso maidaki Nigeria, amma sai jikin Abie Daya
motsa ya dakatar dani”.
Tausayi yabani, nad'ago na kallesa,
mutumne shi mai sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi ba zaka sameshi a
amurd'e, domin yanada wahalar sha'ani, hawayen dasuka ziraromin na goge,
muryata na rasa nace, “kayi hak'uri ina kewar su Munubiya ne, insha ALLAH bazan
sake yin kukanba amma”.
Murmushi yaymin yana jinjina kai, yad'an
shafa girarsa zuwa kai sannan yace, “kinada tsiwa, amma wani time d'in kinada
kirki”.
Bansan lokaci da dariya tazominba, nad'an
dara sannan nace kaima ai hakan kake, kanada tsauri kanada sauk'i”.
Yawani k'ank'ance idanu cikin wani salon
kallon yace, “really?”.
Gira d'aya na d'aga masa nima nace,
“yaah”.
Murmushi mai k'ayatarwa yayi yakwashi
wayoyinsa yabud'e motar yafita batare data sake cewa komaiba.
Ganin haka nima saina fito fuskata washe da
murmushi, kamar banice nagama kukan shagwa6a ba😉.
Tunda muka shigo aunty Mimi da Momma
suka zubo mana ido, Sauban kam dariyar shak'iyanci yafara k'asa-k'asa.
Momma tace, “ina kuka mak'ale haka?”.
Murmushi yayi yana zama kujerar dake
kusada Abie yace, “ba ko ina Momma”..
Momma tayi 'yar dariya tace, “shikenan
tunda ba'aso muji”.
Sauban da Aunty Mimi ma dariya sukayi,
nikam kunya tasani k'asa da kaina inad'an murmushi.
__((*))__((*))__((*))__((*))__
Abba dai bai yarda su maman yaa
Hameed su kwana a gidanba, a daren kowacce tanufi gidansu, yayinda baba k'arami
ya d'auki innaro zuwa asibiti.
Su Sa'eed kam zare jiki sukai suka koma
gida, zukatansu tab da mamakin wannan lamari.
A ranar zarah sai sashenmu ta kwana a tsohon d'akinmu ni da munubiya, saboda Aminu
ya sanar mata yaga Sa'eed da mijin Siyama a k'ofar gidanmu.
Gaba d'aya saitaji yau tanajin haushin
mamansu, dan daba ta tanka dariyar da gwaggon Haleematu tamata ba ai dabasuyi
rigima har Abba ya korasu gidaba, dayanzu gidanta zata kwana jikin mijinta
itama, wane irin abin kunyane wannan kai kana gida uwarka na gidansu itama🤦🏻♀.
%%%%%%%%%%%%%%%
Dawowarmu kenan ni da Sauban da Samha daga
zagaya gari, nagaji ovar, jikina sai ciwo yakemin, dama Yaya lafiyar giwa,
saman sofa na zube Ina sauk'i numfashin wahala, wani zazza6ima nakejin yana
neman rufeni, harna rufe idanu naji wayata na wringing, lalubowa nayi na duba
mai kirana, nasan dai duk Wanda zai kirani to daga Nigeria ne, dan su Samha duk
suna gida, Galadima kam bai ta6a kirana a wayaba, banmayi tunanin yanada number
ba duk da shine ya sayi layin.
Sunan munubiya dana gani yasani fad'ad'a
murmushina, saida nabari ya katse sannan na kirata.
Bugu biyu ta d'aga, jin muryarta can
k'asa sai hankalina ya tashi, nashiga tambayarta ko lafiya.
“sweetheart wlhy banajin dad'i, ko
school nakai sati banjeba, ya kuke?”.
“ayya sorry sweetheart, mike damunki?”.
“wlhy zazza6i, kema naji muryarki wata iri
ai?”.
“nima lafiyar sai a slow wlhy, ina yaa
marwan?”.
“tofa, ciwo a time d'aya mu duka? ALLAH
yabamu lafiya to, yaa marwan yafita gaida su mama, ya jikin Abie da Galadima?”.
“everything Alhmdllh dear, jikin Abie
ma yanata sauk'i, sun fara masa amfani da addu'oin, amma naji kamar doctors
d'inshi suna complain wai abar shafa masa abinda ake shafa masa”.
“karku wani sauraresu, Ku cigaba kawai,
ALLAH yasa muji alkairi”.
“insha ALLAH dear, dama haka Galadima
yace shima”.
“ALLAH ubangiji yabashi lafiya, bara na
barki ki huta, a gaida minsu”.
“ok sweetheart bye”.
Ina ajiye wayar na mik'e, bayi nashiga
nahad'a ruwa mai zafi nagasa jikina kozanji dad'i, haka nake kusan yini wanka
da ruwan zafi, wai ko zan dainajin ciwon jiki, amma a banza, danayi wanka bana
wuce mintuna talatin ciwon yake dawowa sabo.
Wani ash d'in wando da Riga na jawo na
saka, kayan basuda nauyi sosai, wandon kad'an yawuce guywata, rigar kam
hannunta iya kafad'a ya tsaya, kamardai vest d'in maza take, saidai daga gaba
tanada banbanci data maza. nasan Galadima bazai dawo gidan yanzuba saboda koya
tashi aiki saiya biya ta asibiti kafin yazo gida, yanzu kuma akayi isha'i nasan
sai zuwa irin 11, shiyyasa nayi tunanin sakasu ko zan ragema kaina nauyin
jikin. komawa nayi saman sofa data zama gadona na kwanta, amma sai naji dukna
takura, najujjuya naji babu dad'i kwanciyar, tsaki nayi namik'e nakoma saman
gadon na kwanta, insha ALLAH kafin maishi yadawo dai natashi😏.
Banfi 5minutes ba da kwanciya barci ya
d'aukeni.
*****
Kansa daya fara matsa masa da ciwone
yasashi tattara kayansa yabaro office, Dan yau sunyi overwork ne, suna shirin
fidda laptop sabon k'ira, saida yashiga office d'in vijeey da Alexander yamusu
sallama sannan yanufo gida, ko asibiti bai biyaba, Dan har wani jiri-jiri yake
gani a idonsa, yasan barcin dabasa samun yine ya haddasa masa ciwon kan, bama
kamarshi, Dan gara ni idan yafita nakan kwanta nayi barcin.
Da k'yar ALLAH yabashi Damar isowa gidan.
Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce
Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d'in
yafara cire bottom d'in Indian suit d'in dake jikinsa white color, burinsa yana
shiga d'akin yagansa a gado kawai.
Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana
kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun
mugun fito da surar jikina d'as, gashi sun bala'in min k'yau, yau da ace matar
dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan
kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik'e,
rigarma yakasa k'arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo
yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa.
Jin jiri na neman zubdashi a k'asa yay
saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi
buk'atar kwanciyar haka ya daure yad'an watso ruwa, sannan yafito yasha magani,
koma shafa'i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi.
Abin dariya, saiya jawo dogayen
filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k'arshe, shima
babu dad'ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad'o babu ruwana fad'ama fans
zanyi Galadima ya tik'o k'asa ehe😏🤨🤣🤣)
Can cikin barci Galadima yafara juye-juye,
yasaba shi kad'ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya
d'aukesu yayta wurgawa k'asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon.
Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum
biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan
da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba.
Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima
masu jera fillos a jikin munaya😂, d'umin jikinta yasashi kuma nanik'e
mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta
yamasa dad'i.
Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda
jin sanyi-sanyi da k'amshin turarensa kuma, sunbi sun k'adandane juna kaikace
ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d'an uwansa.
Humm, bara
na lek'o su innaro 'yan Nigeria suma🤗, mai tuk'ulluma a goshi ba🤭🤫, ni nama godema mamansu yaa Hameed🤣 dama k'afar suka karya😝.
_____________________________
Anbama innaro magani a wani camix suka dawo
gida, gidanta aka kaita, innarmu tad'an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka
k'aramin towel danta gasa mata goshin koza'a samu yarage tukullumar dayayi.
Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu
tijara.
Baba k'arami yay saurin tareta da fad'in
“haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad'anda suka miki abunma ko kallo
baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai'sha
agarekine?”.
Abbanmu da daddy suna zaune basuce
uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k'arami kawai amma batace komaiba,
itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata.
Tanama innarmu masifa dai har akad'an gasa
mata, aikam saigashi wajen yad'an saki, baba k'arami yamik'a mata kofin tea
d'in da maman fauziyya ta had'a.
Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma
saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta.
Basu bar gidanba saida tasamu barci, da
innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a'a tatashi suje
gida tunda ga habiba d'iyar gwaggo safiyya dabata komaba.
Badan innarmu tasoba tahak'ura, Dan
aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da
darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad'an yake jira a ta6ashi
ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma.
Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi,
innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d'akinta, abinda bayayi kenan, yakan
shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d'akin.
Tana yunk'urin tashi zaune zata tambayesa
lafiya? ya d'aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka
kwanta.
Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru
kawai kamar mai barci.
Kamar yanda Abba bai isashen barciba
hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu
Sa'eed.
Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon
Haleematu basu rintsaba dasukaje gida.
Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak'i
cewa komai, yakuma k'i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa.
Innaro harta fara samun sauk'i itama.
Sa'eed kam dadynsa ya taso k'eyarsa
washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad'i dukkan abinda zarah ke
masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin
iyayenmu ya harareta take shiru.
Nandai aka musu fad'a bayan itaba dad
d'insa yace tafad'i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita
baya mata komai, wannan yasa aka musu fad'a da nasiha kawai akace yad'auki
matarsa su tafi.
Dad'i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji
zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu
itama a dalilinta kuma🤕?).
Washe garin rana ta uku tunda safe saiga
mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai,
komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud'inma dashi suke tak'ama yanzun, duk da
mahaifinsu ya tara musu).
Abba dai k'in saurarensa yayi, saida
yaje ya kama k'afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne
yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai
innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin
zuciyar ko nuna gazawa.
Ansha fama akan Abba kafin ya
sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da
Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k'uruciya har
girma yafara kamasu sun k'asa canjawa, yabama kowaccensu damar k'arshe inhar
suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma
tatafi kenan har abada, Dan bazai duba 'ya'yan dake tsakaninsuba ma.
Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo
gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da
Kansa koya turo anbasu hak'uri.
Shikuma ya rantse saidai tayita zama
inhar saiyaje bikonta.
Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji,
Dan baba k'arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad'in barin gidan
gaduk wacce tasake fad'a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, 'yan
anguwa da makwafta sukaji kasiririt.
Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun
k'ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko 'ya'yanta basuda farinjini wajen
innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci🤣😝).
***************
Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa
marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti
tana kukan batason zuwa, amma yak'i saurarenta.
Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin
layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d'in samun
rabo na wata d'aya kacal (yaa marwan sharpshooter🤭, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi🤫🤣).
Wayyo zokuga murna wajen ogan
miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata
cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai
kunnenta.
Harda kukan dad'i tayi, ikon ALLAH kenan,
ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga
Munubiya wata 1 da sati d'aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya,
k'ila itama d'indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata
complain batajin dad'i. haka innarmu taita murnarta a d'aki ita kad'ai, babu
Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo
gidan sagani.
Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar
zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar
laulayi haka yakeji, Dan tana d'an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata
iyayi balle gyaran gida.
Hakanne yasaka mama rabi'a cewa yadawo da
Munubiya wajenta harta samu sauk'i.
Saiya fara fushi da rok'on tabarta Dan
ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita
taimakawa Munubiya da aikin gidan.
Mama Rabi'a tace a'a, Ayusher itake
taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki
take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai🤦🏻♀,
ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema
rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba😢, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy😭).
Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya
tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci
dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari.
Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama
Rabi'a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya
janyeta d'akinsa da wayo ya kashe arna😉😎.
Mama Rabi'a duk tana kula da su, amma
saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi
yake😂😜.
🤥kai jama'a mu koma India.🛫⛹🏻♀⛹🏻♀
....................................................
______________________________
....................................................
Zafin jikinane yafara masa yawa, dan
yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya
rungume haka? jin kamar mutum yasashi k'ok'arin bud'e idonsa dasukai masa nauyi saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar
munaya, hardai yasamu nasarar bud'e idon gaba d'aya a kanta🤫.................✍🏼
No comments