RAINA KAMA (BOOK 2) 5&6
~Book 2~ 👉🏻5⃣
..............Bayan
an idar da salla Galadima yace wanne office yakamata su fara zuwa?, mtn ko
glo?.
Shiru Nuren yay yana
tunani, zuwa can ya
kalli Galadima “Sameer mizai hana mubari sai zuwa gobe, kasamu kaje kad'an
kwanta ka huta, kaga yanda idonka yay jazur kuwa, ga jijiyan dukta tashi”.
Lumshe idanu Galadima yayi yana furzar da
huci mai zafi a bakinsa, “Nuren muje kawai, kona kwanta bazan samu nutsuwa ba,
kaga fa yanda suka jigata bawan ALLAHn nan”.
“hakane, amma karka damu muje kai dai
kawai”.
Galadima bai musaba, suka jera shida
Nuren zuwa wajen mota, bayan anbud'e musu sun shiga sai Nuren yacema Sarkin
mota suje hotel d'in daya sauka.
Galadima yanajinsu amma baice uffanba,
yayi shiru kawai yana kallon jama'a ta glass.
Koda suka isa hotel d'in sai Nuren yace
su sarkin mota suje abinsu, zuwa anjima zai kirasu su maida Galadima d'in gida.
Cikin girmamawa sarkin mota ya amsa da to,
yamusu sallama suka tafi.
Koda suka isa d'akin da Nuren ya sauka
Galadima cire rigar shaddar yayi ya kwanta dagashi sai dogon wandon da vest,
kwanciyar mintuna 5 kacal barci yay gaba dashi. Sosai tausayinsa yakama Nuren,
yanason d'an 'yar uwar mahaifinsa sosai, (Nuriddeen d'ane ga Abubakar yayan
Momma, babban d'an Sarki Abdul'fatah daya gaji sunan Sarki Abubakar kakansu
Galadima, mahaifin Nuren ayanzu haka shine mai jiran gado a masarautar su
momma, Nuren d'ansane na biyu, akwai yayansa Ballo, shid'in sa'an Galadima ne,
kusanma tare akayi goyonsu, amma Galadima ya girmesa da watanni 7 a duniya,
kunga d'an uwansane na jini kenan, ta 6angaren mahaifiya👌🏻).
Galadima ya jima yana barci, dan kiran
sallar la'asarne ya tadashi ma, wanka yasake yi, ya kar6i kayan Nuren ya sanya,
k'ananun kayane amma sun masa k'yau sosai, Nuren nata tsokanarsa, wai kayan sun
masa k'yau, inhar Munaya ta gansa bazata ganeshi ba.
Harara ya zubama Nuren, sannan yanemi
hanyar fita, “malam idan kagama surutun saika taho muje”.
“sorry sarkin gagara badau mai jiran
gado”.
tsaki Galadima yayi kawai yafice abinsa,
shifa haushin mai jiran gado d'innan yakeji idan aka ambata masa, sadai nemi
mai jiran gadonsu amma bashiba, mtsoww!!.
Wata mota dake fake a harabar hotel d'in
suka nufa, Nuren ya zauna a mazaunin driver, yayinda Galadima ya zauna gefensa.
A hankali Nuren ke tuk'in suna 'yar
hirarsu jefi-jefi, dayake kowanne akwai nutsuwa basuda yawan hayaniya, dan
shima Nuren d'in bashida surutu.
Tafiya mai d'an nisa ta kaisu wani
k'auye, bawani babban gari baneba can. Galadima ya kalli Nuren yana hararsa,
“wai Nuren bazaka saida gidannan ba dai ko?”.
Murmushi Nuren yayi, yad'an gyara zamansa
yana kallon Galadima, saikuma ya maida ga hanya. “brother kenan, ai yanzu ba
abinda kuke tunanin nake aikatawa ba a gidan, wlhy babu ruwana da 'yar kowa yanzun”.
“Humm Nuridden! nasan inhar kana tareda
Muzaffar bazaka ta6a daina neman mataba, nidai bazan gaji da gaya maka gaskiya
ba, inhar aure kakeso kawai kayi aure, bazaka gane llar zina ba saika auri
yarinyar da wani yagama Sani, saika haifi yara kuma, Nuren! Ba cika baki
nakeba, bakuma nafi k'arfin ALLAH ya jarabceniba, amma dana aikata zina ka
ganni nan gamma a d'auramin aure da mata hud'u a rana d'aya, please and please
d'an uwana, ka canja tun Kannada damar hakan, dukkanin ahalinmu basa son wannan
d'abi'ar taka wlhy”.
Nuren ya jinjina masa kai yana cije
la66a, “na gode d'an uwana, insha ALLAH nabari har abada, kuma kwannan zakaji
maganar aurena ta tashi, wlhy tun wancan lokacin da abunnan yafaru ban sake
mu'amulla da kowacce maceba, idan najima zan takura saina fara azumi”.
“tom ALLAH yacigaba da gadinmu muda
zuciyoyinmu, amma Auren shine tafi cancanta dakai, dan wani lokacin da mutum
yakai azumin ma zakaga komai yadawo,
kaga Auren shine cikakkiyar mafita kawai”.
“gaskiyane wlhy, ALLAH dai ya k'ara
shiryamu”. ‘Nuren yafad'a yana horn a k'ofar gate d'in katafaren gidan gonarsa
dayake kiwo’.
An bud'e musu gate d'in suka shiga,
ma'aikatan sai murnar ganinsa sukeyi, tsayawa yay da motar batare da sun
fitoba, sukaita zuwa gaishesu, bawani Sanin Galadima sukayi sosaiba, tunda
bawani zuwa wajen ya keyiba, Nuren zai fad'a musu wanene, amma Galadima yamasa
nuni da karya fad'a, hakkane yasakashi 6ame bakinsa.
******************************
Ran mama Fulani a 6ace yake kallon
manyan jikokin nata maza guda uku tayi, cikin isarta da k'asaitarta tafara
kiran sunayensu, “Talba! Wanbai! Matawalle!, kunsan dalilina Na taraku anan
kuwa?”.
A tare suka girgiza mata kai kawai.
Takuma gyara zamanta cikin tsantsar mulki da
izza, tace, “nakula mahaifinku har zuwa yanzu baison ciwonku ba, shi dole
yanaso ace masa adalin Sarki, shiyyasa kullum yake fifita d'an wani bisa Ku da
ALLAH ya bashi, Matawalle shekarunka dana Galadima kusan d'ayane, amma
mahaifinku nagani Galadima yay aure bai ta6a nuna damuwarsa akan kai kayiba
balle sauran 'yan uwanka, to yanzu matar Galadima cikine da ita, kuma tabbas ta
haifi namiji kuda sarautar gagara badau saidai kallo”.
A razane Talba da wambai suka zaro idanu
waje a zabure, matawalle kuwa murmushi kawai yayi yana girgiza kai da mamakin
wannan kakar tasu mai shegen son kanta.
Wambai yace, “haba Granny miyasa kike
fad'ar wannan maganar, yakamata bakinki ya fad'i alkairi mana, shi dan uban
cikin basai mun bari an haifesa ba, koshi uban cikin dayake tak'ama yana jiran
gado bai isa yayi mulkiba balle cikin da babu tabbas d'in haifosa, ni wlhy
kinma 6atamin rai”.
Talba yaja tsuka shima yana harare-harare,
“Granny ya akayi kikasan tanama da cikin to? wannan sarkin girman kai d'inne
zai iyama mace ciki?”.
Harara mama Fulani ta zubama Talba, “to
uban matanbaya, azatonka zai zuba mata idone yana kallonta kamar hoto ko
television a gida? ince kwana nan 4
kenan dabaro inda suke”.
Wambai yace “amma shine bakiyi
maganarba sai yau Granny?”.
“to ubana koyamin yanda zanyi”.
“ALLAH yabaki hak'uri”. ‘cewar wambai
yana k'unk'uni k'asa-k'asa’.
Matawalle dabaice uffanba tunda aka
fara maganar yay guntun murmushi, muryarsa a tausashe yace, “Ranki ya dad'e ni
banga amfanin wannan maganarba, ALLAH
shine ya azurta Galadima da samun ciki a jikin matarsa, wannan kuma abun farin
cikinmu ne amatsayinmu Na 'yan uwansa, shi dai mulki Na ALLAH ne, shike badawa
ga Wanda yaso akuma lokacin da yaso, bamuda tabbacin tsawancin ran ganin
gobenmu ma balle maganar gadar sarautar cikinma daba'a San miza a haifaba,
please musama zukatanmu sallama kodan mutuwa, nifa banga wani dalili dazamu ke
saka kammu a wahala akan mulkin da ubangijine kawai madawwami a mulkinsa, nikam
kunga tafiyata, ki gafarceni inada uzuri”.
Tunda matawalle yafara maganar Mama
Fulani da Talba da wambai ido suka zuba masa, harya fice ba'a samu mai iya
tanka masaba. haka yake shi, babu ruwansa da bak'in mugun abun masarautar, da
zuciya d'aya yakeson d'an uwansa, shi bama wani zaman k'asar ma yakeba sosai.
Wani wawan tsaki Talba yaja, yabi bayan
Matawalle da harara yana fad'in “lusari kawai, inkai bakason sarautar mu ai
munaso, shifa wannan ko sarautar ya gada wlhy lusarin Sarki mai lasisi za'ayi
anan, duk wannan wahalar akansa akeyinta danya zama magajin Abba amma
shashashan nan baya gani”.
“mtsoww!! bar banza d'an uwa, idan zai
bamu matsala kai basai ka zama magajin Abban ba, nifa harma tunani nake, anya
matawalle jinin gidannan ne?..........”
“kai ya isa haka, banason rashin tauna magana,
Ku k'yalesa zaima dawo hanyane, miye mafita yanzun?”.
“mafita d'ayace Granny a 6arar da shegen
cikin kawai, kuma ma ai Galadiman yazo jiya”.
Da sauri mama Fulani ta tashi zaune daga
kishin gid'ar datayi, “wambai kana nufin Sameer na a masarautar nan?”.
“kwarai ma kuwa, da safe nagansa zaishiga
mota a k'ofar sashensa, yanata faman d'aurema mutane wannan shegiyar fuskar
tashi da yakejin tafi ta kowa k'yawun gani”.
Wani k'asaitaccen murmushi mama
Fulani tayi tana fad'in “lallai yaronnan ya isa, kuje kawai, bayan nagama tsara
komai zan nemeku”.
atare suka mik'e suna fad'in “ahuta
lafiya ranki ya dad'e sarauniyar gagara badau”.
Murmushi tama jikokin nata tana gyad'a
musu kai.
____((____(((★)))____))____
Galadima da Nuren sun shiga ainahin
matsakaicin gidan Nuren dake a gidan gonarsa Na kiwo, sosai ya tsara cikin
gidan, dan ananne yake holewa da 'yammatansa a watannin baya, sai dai yanzu kam
alhmdllh yabari gaskiya, dan sai lokaci-lokaci yake d'an ta6awa, fatansa ma
yabari gaba d'aya, dama ta silar abokai ya koya🤦🏻♀.
Galadima ya zauna saman kujerar guda
d'aya yana sauke numfashi, har yanzu zuciyarsa tak'i nutsuwa waje d'aya, halin
da yaga Abban Munaya ya dank'are masa zuciya.
Cikin ma'aikatan wajen yay sallama daga
waje, Nuren yabashi izinin shigowa, kayan marmarine yahad'o ya kawo musu bayan
ya tsaftacesu, a saman center table d'in ya ajiye, sannan yakona yaciro musu
ruwa a freight d'in dake falon da cups Na glass.
Bayan fitarsa Galadima ya kalli Nuren d'in, “Brother wai miyasa ka
kawoni nan ne?”.
“cinikin kanka nayi”. ‘cewar Nuren yana
harar Galadima’.
“Wani k'asaitaccen murmushi Galadima ya
saki, yakai hannu yana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d'age kafad'a da la6e
baki yace “baka kai girman saida kainaba yaro”.
“uyim! Haka kace ko?”. ‘cewar Nuren yana
kallon galadima’.
“kaima kasan hakanne ai”.
Mik'ewa Nuren yayi yashiga wani d'aki yana
dariya, mintuna 4kacal saigashi tare da wani dattijo.
Galadima da yake kishingid'e yad'ago ido
yana kallon Nuren da dattijon, amma baice komaiba yacigaba da latsa wayarsa
hankali kwance.
Dattijo direban Alhaji balala ya zube
k'asa yana kwasar gaisuwa ga Galadima.
Galadima shi mutumne mai mutunta Wanda ya
girmesa, dan haka Yakuma d'ago kai yana kallon dattijon, fuskarsa ba'a d'aureba
ba'a sakeba, cikin muryarnan tasa ta isar masu mulki da k'asaita yace “no baba
zauna da k'yau, kabar durk'usamin banaso”.
Dattijo yace, “ai girmanka ne ranka ya
dad'e”.
Murmushi kawai Galadima yayi, ya ajiye
wayar hannunsa yatashi zaune sosai, ruwa ya d'auka ya zuba a cup sannan ya
d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallon dattijo.
“bawan ALLAH minene sunanka?”.
Jikin dattijo Na rawa yace “Barau ranka ya
dad'e”.
“humyim baba barau, koka sanni?”.
“sosaima ranka ya dad'e, wanene zaice
bai sankaba a wannan nahiyar”.
Galadima ya wani lumshe idanu yana cije
lips nashi, ya bud'e idanun akan Mal barau da duk yake a tsure, sosai kwarjinin
Galadima da cikar haibarsa suka rikita dukkan tunaninsa da kwarin guywarsa.
Galadima ya katse masa tunani da
fad'in, “Baba barau nasan akwai tambayoyi taf bakinka a gareni, saidai bazan
baka amsar ko guda d'ayaba, zan baka dama da sharad'i, Na farko shine kanada
damar fad'amin gaskiyar abinda kasani idan Na tambayeka, nikuma nabarka ka tafi
salin alin, Na biyu inada sharad'in ka d'aukarmin alk'awarin komai zai fito
abakinka ya zamto gaskiyar abinda Na tambayeka, idan kamin k'arya koka
yaudareni kuma.... Humm”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi batare da ya
k'arasaba’.
Hakan yasaka jinin Malam barau rawa, yana
karkarwa yace, “insha ALLAHU ranka ya dad'e zaka sameni yanda duk kake
buk'ata”.
Nuren yace, “good daka fahimci hakan”.
Galadima bai sake cewa komaiba yacigaba
da latsa wayarsa.
Nuren ya kalli Malam barau yace, “malam
barau kasan wanene tsohon Sarki?”.
“eh kwarai ranka ya dad'e Na sanshi,
shine yake jinya a India yanzu haka aiko”.
“shin minene alak'ar uban gidanka da
tsohon Sarki?”.
A rikice Malam barau yace “ranka ya
dad'e miyasa zakamin wannan tambayar? Ku gafarceni, kuyi wata amma ba wannanan
ba dan ALLAH”.
Galadima ya d'ago idanu ya zubama Malam
barau su, jiyay zuciyarsa tana Neman fara hasala, har zaiyi maganar sai kuma
miya tuna yay shiru ya had'iyeta, maida kansa yayi yacigaba da latsa wayarsa.
Nuren ya bud'e k'aramar drowa dake jikin
center table d'in falon, saiga bindiga 'Yar k'arama ta bayyana, Malam barau ya
waro idanu waje yana kallon yanda Nuren ke d'ura Bullets a cikin bindigar.
Galadima duk yana kallon Nuren ta gefen
ido amma baice masa uffanba, saida Nuren ya gama sannan ya tashi ya koma
kujerar kusada Malam barau, cikin d'aure face yace, “nasan dai tsoron mutuwa ko
rasa aiki zai hanaka bamu amsar tambayarmu, to tabbas in baka fad'anba zan fasa
kwalwar kanka da wannan gun d'in, kuma ko k'arar fitar bullet d'inta baza'ajiba
ballema asan an kasheka, akuma cikin falonnan zan binne gawarka wlhy!!”.
Jikin Malam barau Na 6ari yarik'e
wandonsa, dan har fitsari yafara fito masa kad'an, yace, “ranka ya dad'e mi
kuke son sanine?”.
Galadima dake latsa wayarsa hankali
kwance, batareda ya d'agoba yace, 20 ga watan Yuli miya faru a masarautar
gagara badau”.
“ranka ya dad'e wlhy bansan komaiba,
amma tabbas ogana yafito ransa a 6ace daga wajen meeting d'in dasukayi da Sarki
shida abokansa. daga hakan bansan komaiba wlhy kaji Na rantse maka”.
Idanu Galadima ya d'ago ya zubama Malam
barau, yace, “malam Saminu kafadda!. koba shine ainahin sunanka ba? Na sanar da
kai karkamin k'arya, dan tunkan nakawoka nan nasan komai daya shafeka, amma a
tashin farko kamin k'aryar sunanka Malam barau, humm abin dariya, inason mutum
mai gardama dason ku6tar da kai. Malam Saminu shiga tarkon Muhammad Sameer ba abune mai sauk'iba, ina aiki da kwakwalwa,
kamar yanda gangar jiki take aiki da zuciya, karka yarda a maganarka ta gaba
k'arya ta shigo, idan hakan ta kasance saina binneka da ranka, wannan
tabbatacciyar maganar Muhammad Sameer Saifuddeen ce”. ‘ya k'are maganar da
mik'ewa tsaye yana had'a yatsunsa biyu ya buga a saitin fuskar Malam Saminu,
suka bada sautin d'as! d'ass!, sannan ya ra6a ta gefensa yafice’.
Nuren ya girgiza kansa, “dattijo kayi
kuskure kwarai da gaske, Galadima ya wuce dukkan tunaninka, tashi mu koma inda
ka fito, a yanzu kam bazai ta6a saurarenka ba sai kuma wani karon”.
Hawaye Malam Saminu yafarayi yana bama
Nuren hak'uri, “yalla6ai dan girman ALLAH ka kirashi, wlhy zan fad'a yanzu,
wlhy nagaji da zaman kurkukunnan, nasan hankalin iyalaina da mai gidana a tashe
take, ka taimakeni”.
K'ala Nuren baice masaba, ya dannashi a
d'akin ya maida ya kulle sannan yabi bayan Galadima.
★):(★):(★):(★)(★):(★):(★):(★):(★
Tunda suka tafi babu Wanda yay maganar,
saida suka shigo cikin gari sosai.
Nuren yace, “dattijonnan nakula zaiyi
taurin kai gaskiya”.
Murmushi Galadima yayi yana kuma lafewa
cikin seat, idonsa a lumshe batareda ya bud'eba yace, “mu wuce asibiti”.
Amsawa da to kawai Nuren yayi.
Sun isa asibiti suka iske duk 'yan gidanmu
suna nan, saisu Munubiya da Dady yace su tafi gidajensu hakanan, tundama ba
bari ake aga Abban ba basuga amfanin zaman nasuba, gashi mafi yawansu duk da
tsohon ciki, sai kuma Munubiya da Fauziyya da Haleematu dake fama da laulayi.
Haka ba dan sun soba kowacce takama
hanyar gidanta, wadda mijinta kuma yace ta jirasa ta zauna jiransa.
Suma su innarmu Yaa Anas ya kwashesu ya
maida gida.
Lokacin da su Galadima suka shigo asibitin
mafi yawansu duk sun wuce, sai mazan kawaine a asibitin.
Dan haka Galadima yasamu gaisawa da
Munubiya dake jiran yaa marwan yazo d'aukarta.
Munubiya ta tambayi 'Yar uwarta fa?, gaban
Galadima yafad'i, danshi yama manta su Munaya suna hanya, guntun murmushi yayma
Munubiya yace insha ALLAH suna hanya itama, maybe su iso cikin darene kokuma da
asuba”.
“ALLAH ya kawosu lafiya”. ‘cewar Munubiya
tana sharar hawaye’.
Tabama Galadima tausayi sosai, haka ya
k'arasa wajen doctor domin kumajin ko ansamu wani cigaba a jikin abban..
Doctor yamasa bayanin duk an gyara karayar
jikin Abba, hakama sauran ciwukan suna samun kulawa, kuma bugun zuciyarsa ta
daidaita bakamar jiya zuwa safiyar yauba.
Galadima ya jinjina kai, tareda sake
jaddadama doctor gargad'in kulawa da Abba d'in sosai.
Yad'an jima a asibitin sannan su sarkin
mota sukazo d'aukarsa, Nuren kuma daga nan hotel d'in daya sauka yanufa. ya
sauka hotel ne saboda basa buk'atar wani a masarautar su Galadima yasan da
Nuren d'in.
___________________________
Wajen misalin 2:30 na dare su Munaya
suka sauka, Sauban yayta wayge-wayge ko an zo d'aukarsu, amma baiga alamun wani
mai alak'a da masarautaba, ya kalli Munaya yana dariyar tsokana, “Aunty gimbiya
Honey d'inki ya manta damu, bai aiko d'aukarmu ba, kuma inatsoron mu shiga
motar haya azo a kwamushemu, kinsan yanzun kasuwancin kidnapping shine keda
tsada a 9ja”.
Duk da Munaya tana tare da damuwa hakan bai
hanata yin dariyaba, tace, “kai yaa Sauban bakada dama, ina zamu samu waya mu
kirashi to?”.
Kafin Sauban yabata amsa sukaji magana a
bayansu.
“to maganannu, saikuzo mu wuce, wannan
surutun nakuma bayasa ayi kidnapping d'in naku ba”.
Gaba d'ayansu juyowa sukai suna kallonsa,
Galadima ne sanye cikin wando fari 3quarter da riga t-shirt pink mai gajeren
hannu. harya kwanta suka fad'o masa a rai, babu shiri yazari mukullan mota
yafito, bai tada kowaba a dogaransa saboda kasada irin tasa ya fito zuwa
airport, isowarsa baifi da 17minutes ba jirginsu Munaya ya sauka, tunda suka
fara fitowa daga jirgin idonsu a kansa, har tsayuwarsu da waige-waigen dasukeyi
na son ganin Wanda yazo d'aukarsu yana kallonsu. shagala yay da kallon Munaya,
wadda sai a yanzune yaga k'ibar da Samha ke fad'in tayi, ta murje tayi 6ul-6ul
da ita, har wani haske yaga ta k'ara masa, saboda hasken daya haske ko'ina a
cikin airport d'in. yadad'e tsaye a bayansu, duk gulmarsa da Sauban yayi akan
kunnensa ne.
Sauban ya k'araso da sauri ya rungume
d'an uwansa, dukda jiyane kawai suka rabu saiyaji yayi kewarsa.
Galadima yad'an daki bayansa yana fad'in
“k'aton banza, ka girma bakasan ka girma ba”.
d'agowa Sauban yayi daga jikin Galadima
yana dariya, yayinda Munaya da Galadima suka had'a idanu, gira d'aya ya d'aga
mata, itakuma tayi guntun murmushi tana kauda idonta gefe. (A ranta tace d'an
duniya).
Juyawa yayi batare da yak'ara magana ba,
Munaya da Sauban sukabi bayansa, Sauban ya shiga baya, badan Munaya tasoba tashiga
gaba kusada Galadima da zaiyi driving nasu, wannan ne karon farko da zataga
tuk'insa a k'asarsa.
Saida yatada motar suka fita daga airport
d'in sannan a hankali kamar bataso tace, “yalla6ai mun sameku lafiya?”.
Juyowa yayi kad'an ya kalleta ya maida
kansa ga titi, saida yaja numfashi sannan yace, “kunzo lafiya my Friend?”.
Kallonsa kawai tayi kad'an ta girgiza
kai, a zuciyarta tace su Friend anji jiki, zanbika a hakan kodan samun yanda
nakeso a kanka, danna cika alk'awarin danama mahaifiyarka insha ALLAH.
jin batace komaiba yakuma fad'in “ko
gajiyar tafiyarce?”.
“kusan haka yalla6ai”.
Yace, “to sannu yalla6iya”.
Ba Munaya ba har Sauban saida yayi dariya
da wannan suna, daganan motar ta d'auki shiru, har suka Isa masarautar.
Muftahu dake binsu abaya ya sauke ajiyar
zuciya, sannan shima ya shigo masarautar, tunda Galadima ya fito daga sashensa
akan idonsane, Dan haka yay saurin bin bayansa da mota shima Dan yaga inda
zaije. (Humm Muftahu😏).
Sosai Munaya kejin barci da farinciki,
yau gata tadawo k'asarta ta haihuwa, sun shiga sashen komai need tagansa, sai
k'amshi dake tashi kamar kullum.
d'akinta ta shige, Sauban da Galadima
suka nufi nasa. Sauban ya zube a kujera yana kiran “wash!”.
Galadima ya d'an hararesa, “amma idan
yawonkane aibaka gajiya”.
“yaya wlhy bazaka ganeba, nidai kawai
bani wajen kwana na kwanta wlhy”.
“Saidai ka kwana anan falo kuwa, kafin
da safe a gyara sashenku ka koma can”.
6ata fuska Sauban yayi, “haba Yaya da
gatana na kwana saman kujera, kadai katafi d'akin Aunty gimbiya ka kwana
gaskiya kabani gadonka”.
Galadima zaiyi magana Sauban yatashi da
gudu ya shige bedroom d'insa ya saka key.
Da sauri Galadima yace, “zan 6ata maka rai
fa Sauban”.
Ina, baima sauraresa ba, dafe kai Galadima
yayi kawai, wlhy baisan lokacin da Sauban yafara rainashiba, kodan yaga
tsawonsu kusan d'aya yanzu?. babu yanda ya iya dole yafita zuwa d'akin Munaya🤫.................✍🏼
Ho Sauban
aikinka yay k'yau🤣, su
Galadima dole a tafi😝, ba ruwana karya jini🤭⛹🏻♀
Readers kuma kuyi dariya a hankali fa🤫😝.
Barkanku da juma'a🙋🏻.
Musha
weekend lafiya sisters😁🙋🏻⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
~Book 2~ 👉🏻6⃣
............Har
ya fita ya dawo, laptop da wasu takardu ya d'auka a falonsa ya fita, zai zauna
a falonta saikuma wata dabara ta fad'o masa, bedroom d'inta ya nufa yana wani
ciccijewa (kaida zaka karoro, miye na fuska to yalla6ai?🤔😂).
Munaya Na tsaye tana ninke hijjab d'in
data rama sallolin dasuka risketa a hanya sai kawai shigowarsa tagani da
sallama ciki-ciki. k'ok'arin warware hijjabin tafarayi tana masifa ita kad'ai a
zuciya, haka kawai aita shigoma mutum d'aki babu izini, wannan wane irin
rayuwane.
Shikam Galadima kallo d'aya yamata ya
d'auke kansa, Dan daga ita sai zani d'aurin k'irji. Laptop d'in hannunsa da
takardu ya ajiye a bakin gadon, sannan shima ya zauna, batare da ya kuma
kalllon Munaya ba yace, “kinajin yunwa ne?”.
Ba yunwar takeji ba, amma dan Neman
magana kawai tace “eh”.
Kallonta ya sakeyi, bata yarda sun had'a
idoba, yace “Saidai kisha fresh milk kuwa, dan bani da abinci”.
Manyan idanunta ta waro masa waje, kamar
wadda akace tasha wuta, cikin dafe k'irji tace “yalla6ai fresh milk?”.
Da mamaki ya kalleta, danshi bai fahimci
ma'anar razanar tataba, yace, “uhmmm”....
“Na yafe wlhy”.
Tafad'a da
saurinta.
“To mine nawani birkicewa haka? fresh milk
d'in wani abune dashi?”.
“Humm”. Munaya tafad'a tana ta6e baki,
tace “yalla6ai nikam idan kaga nasha fresh milk d'in data fito daga d'akinka
saidai idan bana a hayyacina”.
Da tsantsar mamakin furucinta yake
kallonta, da yake basuda nisa saiya mik'a hannu ya rik'o nata, zatayi magana ya
fizgota ta zauna kusadashi, kad'an ya rage ta hau masa laptop, amma yay saurin
janyewa da d'ayan hannunsa.
“wash hannuna”. Munaya tafad'a tana matse
baki.
Banza yamata, yakuma matsa hannun da
mugunta. tasaki k'aramar k'ara tana fad'awa gefen kafad'arsa.
Ya d'an kalleta ya janye yana ta6e baki
“ban fahimci zancenki daga nesa ba, maimaitamin”..
Cikin tunzuro masa baki tace, “yoni
babu abinda nake nufi fa, nidai bazan sha fresh milk d'in data fito daga
d'akinka ba wlhy. haka kawai aje asakama mutum abinda zai halakashi”.
‘k'asa-k'asa ta k'arasa maganar, amma yajita sarai’.
Shifa saima yanzu yagane inda zancenta
ya nufa, wani miskilin murmushi yasaki yana danne dariyarsa datake shirin
kufcewa, amma dukda haka saida taji sautin fitar murmushin nasa.
Munaya dake satar kallonsa idonta harya
cika da kwalla, a zuciyarta tace mugu d'an masa, dole fa kamin dariya.
Saida yayi dariyarsa a zuciya ya gama ya
kalleta, itakuma saiwani mar-mar takeyi da idanu wai zatayi kuka.
Murmushi ya kumayi, sannan yace, “wannan
bakin dakike tunzuromin ko, hummm.....”. ‘yak'are maganar da cije lips nashi’.
Yunk'urawa tayi zata mik'e, tace,
“yalla6ai ni wlhy barci nakeji fa”.
Dawo da ita yayi ta fad'o jikinsa shima
yana fad'in “nikuma gadinki zanyi ko? yalla6iya!”.
Tace “wayyo innarmu kice ya fitarmin a
d'aki please”.
“ko waya zan baki ki kiratane”. ‘yay
maganar cikin d'age gira d'aya’.
Munaya tai saurin janye idanunta daga
Kansa ga k'amshin turarensa ya gallabeta, barci takeji, amma takula mugunnan
soyake ya hanata ma.
Kamar zatayi kuka tace, “yalla6ai wai
mikazo nemane please? Wlhy barci na keson yi?”.
Shiru yamata, saida ya mula dan kansa
sannan yace “jikina fa”. ‘yay maganar yana kallon k'ugunta’.
Da sauri Munaya ta sauka daga jikinsa
tana k'unk'uni da tura baki.
Medical glasses d'insa ya d'auka ya saka,
tareda cigaba da aikinsa a laptop, a zuciyarsa yana fad'in yarinyarnan akwai
ruwan tsiwa, amma duk randa Na kama bakin tsiwarcan sai yamin bayani
dalla-dalla kuwa.
Ganin ya shareni ya cigaba da sabgarsa a
System, nima sai ban kuma bi ta kansa ba Na d'auki kayan barcina nashiga bayi
domin Na sanya. Sai dai zuciyata cike take da fargabar miya kawoshi d'akina?.
haka na fito kamar wata munafuka ina lallak'ewa jikin bango.
Duk yana kallona ta gefen idanu, amma yay
kamar baima San dani a d'akinba.
Sai zuwa can ya d'ago yana kallona,
yana wasa da pen d'in hannunsa kan la66ansa, “idan bak'yajin barci zokimin wani
d'an aiki nan”.
Saida gabana ya fad'i, a raina nace aikin
mi kuma?, a fili saina aro jarumta na yafama kaina, Dan nakula tsoron daya fara
gani a idona ne yake neman fara rainani da samin fargaba (🤣ho munayan shagali).
Takowa nayi inda yake, ina niyar zama
bakin gadon sai ya nunamin tsakiyar gadon, shima laptop d'in ya tura sosai kan
gadon ya haye tsakkiya yana gyara zamansa. kuma had'e fuska nayi ina wani
dojewa na hau nima na zauna, cigaba yayi da danna laptop d'in, kusan mintuna 3
ya jehomin tambaya.
“shin kinsan minene aikin Abba?”.
Da mamaki na kallesa, nace “wai Abbana
kake magana?”.
“uhmm”. ‘yafad'a batare da ya d'agoba’.
Shiru nayi alamar tunani, harya d'ago ya
kalleni bance komaiba, maida kansa yayi ga laptop d'in yacigaba da aikinsa,
zuwa can nace, “ma'aikacin gwamnati ne kawai tawani fanin kuma aikinsa yanada
Nasaba da jarida”.
Tunda nafara magana ya tsuramin idanu,
bakina kawai yake kallo yana taune lips nashi, saida nakai aya sannan yace,
“jarida?”.
Nace, “eh, wani abune ya faru?”.
Kansa ya girgizamin, “innalillahi” yashiga
maimaitawa a zuciyarsa, baya fatan zarginsa yazama gaskiya, cikin dakiya yakuma
cemin “kokin san abokansa? ina nufin cikin manyan mutane haka?”.
“eh to, akwai senator halluru garba, sai
kuma wani anacemasa Alhaji Mamman k'afur, last year yafito takarar shugaban
k'asa......”
Caraf ya kama hannuna, “kina nufin Alhaji
Mamman k'afur abokin Abban kune?”.
Ni tsoroma yabani, yanda yay maganar cikin
rawar jiki, na jinjina masa kaina a hankali.
Gani nai ya taune lips nashi da masifar
k'arfi, ya kaima iska naushi. da sauri na matsa baya Dan karya nausheni, ganin
kamar na tsorata sai yay murmushi, cikin k'asaitacciyar muryar nan tasa yace
“my Friend! Yanzu ne zamu fara aiki tare da gaske ni da ke”.
“kamar ya yalla6ai? wane irin aiki
kuma?”.
Murmushin takaici yayi, ya kalleni ido
cikin ido, kasa jurewa nayi nai k'asa da nawa. shima lumshe nasa yayi yana
fad'in “zaki gani”. daga haka ya janye laptop d'in gefe ya zame ya kwanta.
Binsa nayi da kallo tamkar wata sokuwa,
gaba d'aya ya kulle magudanar tunanina da wadda ke kaima kwakwalwata sakonni.
Medical glasses d'in idonsa ya cire ya
ajiye, sai kuma ya juyo gareni, hannunsa d'aya ya mik'amin yanamin alamar nazo
gareshi.
Idanu na d'an zaro, sai kuma na nok'e
kafad'a alamar nak'i din.
Wani murmushin da bako yaushe yakeyinsaba
ya sakarmin, ya juyamin baya yay kwanciyarsa. bai sake juyowa gareniba har
kusan 6minutes. nagaji da kallonsa da nazarin murmushinsa da tambayoyinsa na
janye idanuna, waishi guy d'innan mike damunsa ne? gaba d'aya ya canjamin daga
saukarmu zuwa yanzun, dubana nakai ga agogon d'akin. 3:27am, “ya salam” na
fad'a a hankali, muna Neman kwana a zaune. can k'arshen gadon na koma na
kwanta, zuciyata cike da tsoron ALLAH yasa bawani Abu ya shiryaminba, babu
dad'ewa barci 6arawo ya saceni.
Numfashina dake sauka a hankali yasaka
Galadima gane nayi barci, juyowa yay yana kallona, yayinda zuciyarsa keta cud'a
amsoshin dana basa yanzun, tabbas mahaifin yarinyarnan akwai abinda yasani,
kwarai da gaske zaiyi amfani da ita wajen gano ko wanene mahaifinta?, minene
alak'arsa da case d'ina?, sannan minene alak'ar Muftahu da ita?, Dan tabbas akwai
manufar sako yarinyar acikin wannan tak'addamar, kuma Muftahu dashi aka shirya
komai. yasaki wani murmushin mugunta tareda nuna kansa, a fili yace _MAK'IYAN
MAHAIFINA SAINA ZAME MUKU_ *RAINA KAMA
KAGA GAYYA* tabbas lokaci yayi dazakuga wannan *Gayyar*.
Tofa masu
karatu, ana zaton wuta a mak'era🤔, mikuna yasako Abban munaya a rikicin masarauta? Kodai ba
masarautar kawai bace keda alhakin ciwon
tsohon Sarki Saifudden Abubakar🤔?,
shin tsakanin Galadima da Munaya & munubiya, innarsu Munaya. Wanene RAINA
KAMA...... d'in🤗?.
Kumuje zuwa kudai my Guy's😁, duk nisan jifa👆🏻,
k'asa zai fad'o👇🏻🤗
★___________________________★
Bayan shigewar su Galadima Muftahu ya fito
daga mota shima yana murmushin dashi kad'aine yasan fassararsa, jiyay kawai
handkerchief ya rufe masa fuska, yay saurin cirewa yana waige-waige dan dunba
wanene ya jeho masa, wayam babu alamar mutum a wajen, bai gama dube-duben ba
yay luuu zai fad'i, saigashi a hannun mutum, idanunsa sunriga sunyi nauyi,
dishi-dishi yake kallon Wanda ya tareshi d'in, dama gashi ya rufe rabin
fuskarsa ba'a gani, wasu samarine su biyu sukazo suka kama Muftahu tareda
wancan suka danna a mota, tun yanajinsu sama-sama har idonsa da jinsa suka rufe
baki d'aya.
🙆🏻tofa
suwaye?.
★__________★_________★
Tun kusan around 8pm Nuren yake
k'ofar wajen, a dukkan bayanan daya samu daga majiya mai k'arfi yarinyar
Minister ta shigo gari yau, kuma zatazo shan ice-cream wajen, wayarsa ya d'auka
yay wasu 'yan danne-danne, murmushi yayi ya maida wayar ya ajiye tareda dasama
k'ofar wajen idanu, dolene kafin tashiga ciki zai saceta, dan bincikrnsa ya
nuna masa cctv camera d'aya ce a cikin wajen kawai, a waje babu, dan haka bama
ya buk'atar ta Shiga, murmushi yayi saboda ganin motar da driver d'inta yamasa
kwatancen zasuzo aciki, saida driver n yaga motar Nuren sannan yazo kusada ita
yay parking, bud'e murfin gefen mai zaman banza Nuren yayi, hakan kuma yay
dai-dai da fitowar zankad'ed'iyar budurwa daga motar datai parking kusada ta
Nuren d'in, murfin ne ya daki gefen hannunta kad'an.
A fusace ta kalli motar Nuren, shikuma yay
mata murmushi, wani haushine ya kamata, banda rainin wayo ya bigeta amma yamata
murmushi saboda wulak'anci, yau saitaga wanene ubansa a garinnan?. da k'arfi
tabuga saman motar tana lek'a kanta ciki, “kai wawa bakaga abinda kayi bane?”.
Maimakon ya bata amsa saiya jefa mata
handkerchief d'insa saman fuskarta, janyewa tayi da sauri zatayi magana kanta
ya sara mata, da lalube ta dafa kujerar motar ta shiga ta zauna, sai faman
lumshe idanu takeyi. murmushi Nuren yayi, ya taimaka mata ta ida shigowa Sannan
ya rufe motar, komai akan idon driver n ta ya faru, bashida damar hanawa, dan
Nuren yasashi a tsaka mai wuyane. Agaban idonsa Nuren yaja motarsa yabar wajen
yana murmushin samun nasarar tafiyar plan d'insa yanda ya tsara. a wannan daren
yanufi gidan Galadima dake can bayan gari inda aka ta6a kai Munaya.
😱humm yau 'yar kidnapping akeyi kawai😂🤪.
------------(((★)))--------------
Galadima yariga Munaya farkawa, dama
bawani isashshen barci yayiba, tunani da damuwa suka taru suka hana idonsa
rintsawa sai gabannin Asuba. Ana kiran sallar farko kuma yana farkawa, tashi
yay zaune dafe da kansa, kusan mintuna biyu ya juya yana kallon munaya data
juyo tana fuskantar inda yake yanzun, da gani kasan barcin bamai dad'i
takeyiba, dan sai yamutse fuska takeyi a cikin barci. matsawa yayi kad'an ya
d'ora yatsunsa biyu gefen fuskarta, sai yaji zafi jikinta, ya janye yana
mamakin wai mike damun yarinyar nan kwana biyu haka? dolene yau yasata taga
doctor idan sunje ganin Abba. gabansa yad'an fad'i daya tuna har yanzu itafa
batasan komai ba, shi baima San ta yadda zai sanar mata abbanta yana cikin
mawuyacin hali ba, ya dafe kansa yana ambatar sunayen ALLAH kozaiji sassauci a
ransa. Da k'yar ya samu ya mik'e domin yin rakata ainul'fijir kafin akira
assalatu.
Bayan ya idar ya tadani, da k'yar na iya
tashi dafe da kai, dan barcin bai isheniba, muryarsa da alamun shima rashin
isashshen barcin yace, “time d'in salla yayi”.
Idona dake bud'ewa da lumshewa Na kad'a
masa alamar amsawa, yay saurin janye nasa saboda wata fad'uwar gaba da
tsirgawar wani Abu dayaji lokaci guda tun daga Kansa zuwa yatsan k'afarsa, bai
sake magana ba yafice. nikuma nakoma Na sake kwanciyata.
'Dakinsa ya shiga ya tada Sauban dansu
tafi massalaci.
Babu dad'ewa Sauban ya kammala alwala
yafito ya iskeshi a falo yana jiransa, harara ya antayama Sauban, shikuma ya
kauda kai gefe yana had'iye dariya (yo daga
taimako saiya zama laifi?).
Sarki yayi mamakin ganin Sauban, dan
yaron bawani zuwa k'asar yakeba saida dalili mai k'arfi, bayan yagama k'ar6ar
gaisuwa wajen jama'arsa Galadima da Sauban sukabishi zuwa sashensa.
Kasa 6oye mamakinsa yayi, ya kamo hannun
Sauban d'in dake d'ayan 6arinsa zaune kamar yanda Galadima yake, “yarona ne yau
ak'asarsa ba biki ba ba bikin salla ba?”.
Dariya Sauban yayi, yace “Abba nazo
gaidakune kawai”.
Sarki ya Murmusa yana kallon Galadima,
“Galadima kodai akwai abinda ke faruwane kuke 6oyemin?”.
Galadima ya d'ago kansa cikin damuwa
yace “babu abinda muke 6oyewa ranka ya dad'e. Mahaifin Munaaya ne yay Accident
shine suka taho da Sauban d'in”.
“mu bamuda muhimmancin da zamu Sani
kenan ko?”.
“ALLAH ya huci zuciyarka ba haka nake
nufiba, bayan barina wajenka jiya nima aka sanarmin, lokacin dana shigo kuma
dare yayi”.
Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke, yace
“ALLAH yabashi lafiya, zuwa anjima sai su waziri suje dubashi ai, tana ina ne
ita d'iyar tawa?”.
“tana nan cikin masarauta”.
Jin jina kai kawai Sarki yay bai kuma cewa
komaiba, sai zuwa can yacigaba dayima Sauban tanbaya akan jikin Abie, shikuma
yana bashi amsa. Galadima dai Na jinsu bai saka bakiba.
*************
Saida gari yafara haske ALLAH yabani
ikon tashi, dan zazza6in kuma ya sauka, yanzu kuma haka yakemin, da dare yayi
zan fara zazza6i, lokacin da gari zai waye saikiji ya sauka. Sai dai ciwon
jiki.
Saida nayi wanka da ruwa mai zafi sannan
nayo alwala, sallar asubahi data kwacemin nayi, Na jawo handbag d'ina danazo da
ita Na d'akko wayata, sim card d'ina Na 9ja Na d'akko shima Na saka akan wayar,
massage suka turomin Na adadin awannin da suka bani sim card d'in zai d'auka
kafin ya cigaba da aiki. ganin haka saina ajiye wayar natashi domin gyara
d'akin, ina cikin kakka6e gado idona yakai bisa wayar Galadima. dad'ine ya
kamani, koba komai nakira wani d'an gidanmu Na sanar dasu nazo 9ja.
Wayar Na d'auka Na saka number Abbana,
dan yanzu nafi kwad'aituwa dajin muryarsa fiye da kowa, kodan mafarkai marasa
dad'i danakeyi a kansa, Mtn d'insa nafara kira amma a kashe, saina kira glo
d'in, shima switch up, ban kawo komai a rainaba na maida kiran kan innarmu,
bugu biyu aka d'aga, wani dad'ine ya kamani, cikeda d'oki nace “innarmu I miss
you”.
Aiyaan daya d'aga wayar yay dariya, aunty
ba inna baceba. Nine, Nima Na iya waya yanzun”.
Dukda naji dad'in jin muryar d'an uwana,
hakan bai hana zuciyata shiga fargaba ba, nace “Aiyaan Kaine? ina innarmu
d'in?”.
“Tana wanka ne zamuje asibiti wajen
Abba”.
Da sauri Na dafe k'irji, nace “Asibiti
kuma? miya sami Abban?”.
“Lah Aunty baki saniba? Ai accident
yayi fa, kuma innarmu nata kuka, hakama innaro dasu daddy”.
“Aiyaan!!...” nafad'a da k'arfi, kafin
nace wani Abu naji an rik'emin hannu ta bayana an zare wayar daga kunnena.
Kuma rikicewa nayi, Na juyo da hanzari,
cikin kuka naketa fad'in “abbana! Abba da gaske Aiyaan yake yi? Yalla6ai da
gaske Abbana yayi accident?”.
Wani tausayina yaji ya tsargashi, ya
dafa kafad'una, cikin sigar lallashi yace “cool down mana my friend”.
“to ka fad'amin da gaskene Abbana yayi
accident d'in?”.
Rasa mizaice min yayi, sai bin fusakata da
idanu yakeyi, ya cije lips nashi yana fad'in “inhar kinason na kaiki ki gansa
toki nutsu”.
Share hawayena nayi da sauri nace, “to na
nutsu muje”.
Yaja hancina, a hankali ya furta, “good
girl”. Sai ya juya kuma ya fita.
Binsa nayi da kallo hawaye na zuba a
kumatuna, kenan da gaske Aiyaan yakeyi Abba yayi Accident d'in, “hasbinallahu
wa'ni'imal wakil”. Na dafe kaina tareda zama a bakin gadon nacigaba da raira
kukana.
Shikam yana fita ya dunk'ule hannunsa yana
cije lips, yama akayi yabar wayarsa harta d'auka tayi kira dashi, ko kad'an
baiso hakaba. Baiso tajiba kai tsaye.
Saida naci kukana na gode ALLAH sannan
natashi na hau shiryawa, atamfa na saka zani da riga, bawata kwalliya nayi ba,
na shafa fauda kawai da lips gloss, turarema kad'an na shafa. ina cikin Neman
mayafi ya shigo, kamshin turarensa yasani juyowa na kallesa, sanye yake cikin
oxblood d'in shadda, hularsa takalmi agogo duk black, link d'in hannun rigarsa
yake sakawa, sai alk'yabba pink da ratsin milk a hannunsa.
d'auke kaina nayi naci gaba da neman
gyalena a cikin kayan lefena.
Baimin magana ba ya tako har inda nake,
hannu yasaka a kafad'una ya d'agoni, fuskarsa babu walwala ko kad'an, idonsa
akan fuskata, kusancin damukai da juna sosai yasaka numfashinsa ke sauka akan
fuskar tawa, janye idona nayi na maida kan design d'in gaban rigarsa, yayinda
shikuma ya warware alk'yabbar hannunsa mai k'yau ya sakamin, d'agowa nai muka
k'ara had'a idanu, ya jinjina min kansa kawai.
Jinai tamkar in fasa ihu, banason saka
alk'yabba d'in nan nidai, dan nauyi sukemin, garama wannan batada nauyi
gaskiya, dan tamkar riga After dress take, saidai suffar alk'yabba aka mata,
kuma tanada kaurin dabaza'a ga jikin mutumba.
Hannunsa yakuma d'orawa akan kafad'una ya
d'ago hular alk'yabbar dake kwance a baya ya sakamin, ni kaina koba'a fad'aba
nasan nayi k'yau, yanzunma baice uffanba ya juya ya fita yana nunamin agogon
hannunsa alamar time yana tafiya.
Handbag d'ita na d'auka da wayata nabi
bayansa, dauriya kawai nakeyi na hana kuka tasirin zubowa.
A falo na iskeshi shida Sauban dake zaune
a kujera shima cikin manyan kaya, dayake ba sakawa yakeba sainaga ya canjamin,
ya kalleni cikin halinsa na tsokana yana fad'in “kaga sarauniya gagara badau ta
gobe, takawarki lafiya 6auna mai tafiyar k'asaita.......”.
Harar da Galadima ya zuba masa ce ta
sakashi gimtse bakinsa yana had'iye dariya.
Nidai banma tankaba, dan yau zuciyata babu
dad'i.
Galadima ne yay gaba mukabi bayansa, tunda
muka fito hadimansa suke zubewa gaishemu, Sauban kawai ke amsa musu, shikam
Galadima saidai d'aga hannu, Niko ko kallonsuma banayi. Hakan yasa suka fahimci
har yanzu akwai matsala kenan, dansu bama Susan munzo nida Sauban ba.
Muna k'ok'arin shiga mota Harun ya iso
wajen, gaidashi Sauban yayi, nima na gaidashi, ganin ni da Galadima kowa fuska
a tamke sai abin yabashi mamaki, hannun Galadima ya kama suka koma gefe.
Nikuma da Sauban muka shiga mota.
“Sameer babu fad'a miya kawo gaba?”.
Murmushi Galadima yayi, ya cije lips
nashi kad'an yana kallon Harun, “bazaka ganeba Harun, na iske abinda ya dagula
lissafinane kawai, naga kiranka jiya, amma ina cikin rud'ani a time d'in
shiyyasa ban d'agaba”.
“rud'ani? mike faruwa ne?”.
“mahaifin munaya ne yay Accident, a time d'in
ina hospital wajensa”.
“ya salam, ya jikin nasa to?”.
“Alhmdllh, zamuje canne bayan mun gaida
jama'ar gidan”.
“ok bara na k'arasa abinda zanyi kafin
Ku fito saimuje”.
Kai kawai Galadima ya jinjina masa.
Bud'e masa gefena akayi ya shigo, yad'an
kalleni, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Sashen mama Fulani muka fara Isa, amma
sai aka sanar mana tasha maganin mura ta kwanta, daga nan muka nufi sashen
matan Sarki, inda yafi ko ina k'awa da ado a gidan kenan.
Mun sami tarba ta musamman ga Uwar
gidansa, nidai matarnan tana k'aunata na lura, kuma tafi sakarma Galadima fiye
da kowa a Matan sarki, tanada kirki sosai, haka taita jan Sauban a jikinta,
nakula suma sunfi sakewa da ita.
Sosai ta nuna damuwarta akan Accident
d'in mahaifina da Galadima ya sanar mata, taita jinjina maganar tana lallashina
da jerama Abba addu'ar tashi cikin k'oshin lafiya.
Tasa aka kawo mana break fast wai
saimun karya anan, Sauban ne kawai yaci, amma Galadima cewa yay ya k'oshi, nima
nace bazan iya ciba. dan burina kawai naga mahaifina, gaisuwarma duk akan k'aya
nake.
Shima Sauban d'in bai wani ci abun kirkiba
yace ya k'oshi, mun fito muka shiga sauran sassan, amma ba ko inaba.
Sauban da harun sun tafi a mota d'aya, nikuma
ni da Galadima. Sai motar dogaran Galadima guda biyu, sai kuma kuyangi hud'u da
Uwargidan sarki gimbiya Zulfah tahad'oni dasu, wai kafin mu dawo nima a turamin
bayina da zasu ke kula dani, ni dai da to kawai na amsa, Galadima kam baima ce
uffanba.
Babu mai magana a cikinmu daga ni harshi,
sai saukar ajiyar zuciyata da share kwalla time to time danakeyi.
............................................
Innarmu na fitowa daga bayi Aiyaan ya
sanar mata na kira, da mamaki tace masa kodai Munubiya ce?”.
“wlhy Innarmu aunty Munaya ce, kuma
batasan Abba bashida lafiya ba”.
“ka sanar mata ne?”. tafad'a a rikice.
“eh innarmu na sanar mata, kumafa naji
tana kuka”.
“innalillahi Aiyaan wayace ka sanar mata?
da wace Number ta kira?”. Tayi maganar tamkar zata make Aiyaan.
Runtse idanu yayi yana k'ank'ame jiki
saboda tsoro. innarmu dukta rikice, tasan su Munaya da shiga Rud'ani akan Abu,
yanzu haka tana cikin damuwar Munubiya itama, dan jikinta yakuma janga6ewa, ga
laulayi ga wannan damuwar Abban.
K'ok'arin kiran Number tashigayi danta
kwantarmin da hankaki amma sai tak'i shiga.
Har suka gama shirin asibiti wayar bata
shigaba.
Koda suna mota taita gwadawa.
A asibitin suka had'u da mama Rabi'a suma
sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k'ok'arin fara kwantarma 'Yar uwarta
da hankali.
Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan
yayi.
“to Yaya ko su Munaya sunzo k'asarne?”.
Anya kuwa Rabi'a, naga jiya mijinta na nan
amma baiyi maganar zata zoba”.
“ito da wannan dan wanann, amma ai bama
fidda raiba”.
“hakane”. cewar innarmu.
Babu dad'ewa da zuwansu saiga gwaggon
Haleematu da matan k'annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba
ita). k'in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba,
amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka
shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi.
Koda suka fito harda kuka takeyi, matan
k'aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf 'yan gidanmu babu Wanda yace mata
danmi, kowama tasa ta isheshi aransa.
★★★★★
Tunda motocinmj suka shigo harabar
asibitin sai kallo ya koma sama, 'yan gidanmu dakeda yak'in Galadima ne kowa
tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama'a kuma da 'yan dubiya son ganin wad'anda
zasu fito sukeyi.
Sai da aka bud'e mana sannan muka fito,
suma su Harun duk sun fito.
Su yaa Hameed suka taho garemu sunama
Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu.
Kowannensu
fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar
da hawaye.
Cikin d'okin ganina Fauziyya tazo ta kama
hannuna itada Safara'u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu
da zuciya suma suka fara, sauran 'yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk
sun zo, ni kad'aice wadda nake nesa.
Saida baba k'arami yamana magana sannan
suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban
ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?.
Aunty khalisat tace “sunje ganin doctor
itada yaa marwan, dan batajin dad'i itama”.
Kaina kawai na jinjina, na k'arasa gabansu
innarmu na durk'usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata
ya hanya?, nace “Alhmdllh”.
Matan gidanmu kowacce kallona take da
mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d'akin
da Abba yake.
Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga
corridor d'in dazai sadamu da d'akin da Galadima yasa aka canjama Abba.
A ciki na iske Galadima da Harun da
Sauban, sai doctor da yaa Shafi'u yaa Hameed.
Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka
kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake
Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk'ushe ina sakin
kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon.
Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba,
Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na
mik'e tsaye, fad'awa nayi saman k'irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan.
Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka
shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d'ora ha6arsa saman kaina
yana lumshe idanu da cije lips. kad'an-kad'an yake buga bayana alamar lallashi.
d'ai-d'ai su yaa Hameed suka zare jikinsu
suka fice daga d'akin, aka barmu mu kad'ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta,
itama ganin sun fita saita fice taja mana k'ofar.
Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na
tsagaita da kukan sannan Galadima ya d'ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa
yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai
kawai yakeyi.
Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere,
da hannu ya nunamin hanyar fita.
Banyi musuba nabud'e k'ofar muka fito, ina
gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara
hajijiya dani, burina kawai nakai inda 'yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima
na samu na zauna.
Muna gab da k'arasawa wajen na dafe
kaina, sai nayi baya luuuuuu.
Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta
ta fad'o jikinsa, gaba d'aya 'yan gidanmu da mutanen wajen suka mik'e tsaye
cikin ambaton sunan ALLAH.
sosai Galadima ya tallafota jikinsa,
yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar.
Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da
ambatar su kira Doctor.
Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta
rikitashi....................✍🏼
*_Comments d'inku shike k'aramin k'arfin
guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya🤦🏻♀,
amma yanda kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba😃, ina godiya kwarai da gaske, I love you all🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻👍🏻❤_*
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
No comments