RAINA KAMA (BOOK 1) 29&30
👉🏻2⃣9⃣
...........“Munaya taimakona nakeson kiyi
akan mijinki”.
'Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar
mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace “Umarni zaki bami Momma,
domin ke mahaifiyatace”.
Murmushin jin dad'i tayi kamfin takamo
hannuna cikin nata, “Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu
nakuma aminta Muh'd yasamu irin macen danake musu addu'a shida d'an uwansa,
ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana”.
Gabana yafad'i, a raina nace badai Na
yarjejeniyar ba?.......maganarta ta katsemin tunanin.
“Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine
yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k'addarar Muh'd ce
kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki
tarihin masarautar su Muh'd, da dalilin zamanmu wannan k'asar daba tamuba
tsawon shekara 24 kenan”.
Kaina na jin jina mata, nace “to Momma”.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji
dad'in fad'ar abinda ke a bakinta.
*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU
DASUKA SHU'DE🤔_*
Masarautar gagara badau masarautace mai
d'unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen
masana masarautar sarakuna a k'ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu,
wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud'ad'd'en
lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani
Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud'ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba
yake barin hannunka, a'a, da zarar anyi yak'i kayi sakakin da aka ci masarautar
tom dolenefa kayi murabus a nad'a wani kuma. kuma bawai cikin 'ya'yankaba,
saidai asamo wani hazik'i a masarautar a nad'ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka
kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada
wani d'a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin
da aka kawo musu harinnan ba'a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay
saurin had'a mayak'a suka tunkari wannan runduna, bak'aramin gumurzu akashaba,
sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata
Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu 'yan tsirarun mayak'a, ALLAH mai
iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka
babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad'a salisu. tundaga ranar takoma
*_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna
kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh'd kenan, mahaifin
su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun
mahaifinsa Yusufa.
Rana d'aya aka nad'a Abubakar Sarki
shida amininsa d'an sarkin kan karofi yarima Abdul'fatah, mahaifin Abubakar
Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d'aya suka yanke shawarar
yin murabus suka nad'a 'ya'yansu.
Sannan aka d'aura musu aure kuma a ranar
da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.
Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d'iyace
ga waziri Sama'ila k'anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres
bashida d'iya mace, dan haka ya d'auki mama Fulani d'iyar k'aninsa yabama
Abubakar d'an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya
d'auki Khadeeja (inno) yabama Abdul'fatah d'an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama
fulani) tana masifar son yarima Abdul'fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata
shi dama gimbiya Khadija (inno) k'anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama
Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad'a masarautunsu bata mata
magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya
nason yarima Abdul'fatah ba, sukayi wannan had'in aure. (Iyayen mama Fulani ma
sunso ta Auri yarima Abdul'fatah d'in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu
mai k'etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak'ura da
auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka
kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama
fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija
(inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d'aya sukeba hakan
yasaka mama Fulani bak'in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu
masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa
mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka
k'ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul'fatah. kamar atsare haka
sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud'u.
A masarautar gagara badau Mama Fulani na
zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar
yanada hak'uri da sauk'in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu
haihuba, sai mama Fulani keta zubo 'ya'ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta
Haifa d'anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud'u, duk da mama
Fulani itace da manyan 'ya'ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin
hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta
*Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo
har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki
Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an
acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi
tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba
mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma
bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji
Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine
tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1½ kuwa. danma
mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da
Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a
tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya
samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai
ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai
sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka mama
Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a
da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta
asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta
Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa
aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure,
shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala'i wai
munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.
Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan
atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai
tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAH😭.
Wannan shine silar aurena dana
Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da
kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon
abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa
kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin
yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi
hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa
(aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima
Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar
dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani,
duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina, amma
k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da
abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata
gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta
'Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne😆.
“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma
tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad'in.
Mama Fulani taso d'iayarta ta farko
gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki
Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata
dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura
sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar
mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama
jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba,
saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi
kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara
badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma
shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta
d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa
gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki
Abubakar har ma da jama'ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da
sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki
Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a
madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a
masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana
gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure,
dan Sarki baya zama da mace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A
rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani
tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu
kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a
karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza
mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara
badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden
zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba,
hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden
babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu
kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara
mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif
a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da
aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata
taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad
yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka
Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden
ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni
bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su
sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Sameer, dan
haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga
lafiyarsa, da yawa jama'ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta buga💔 ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.
Da sauri na kallo momma.
Ta d'aga min kai tana murmushin takaici,
“hakane d'iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..
Ranar wata litinin da asuba Sarki
Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad'i
ana tsaka da sallah.
A lokacin kafafunsa ne kawai basa aiki,
amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina
yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko'a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a
jikin takawa, tun ana kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a
lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time
d'in, a asirce batareda jama'ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu
Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin kawai ina rainon Sauban ne,
amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun
k'anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana
taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad'ewa aka maida
sarautar Saifudden akan Jalaludden d'an gidan mama Fulani, saikuma lokacin
jama'ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad'an ban damuba, danni ta lafiyar
mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin
mama Fulani dawasu kuma manyan attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki
Saifudden yayi dawasu attajiran k'asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga
yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk'aci wani Abu ya hanasu
kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida hankali akan wannanba,
mahaifina Sarki Abdul'fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma
da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan
Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d'aya a asibiti babu wani
canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya
d'aga koda d'an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa
allurar gubane, kuma guba mai had'ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar
da jijiyoyin jikine su daina aiki gaba d'aya, wannan yasaka jikin Sarki
Saifudden ya sandare😭.
Wani amintaccen likitanmune yabada
shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun
kulawa da tsaro a can.
Wannan shine silar dawowarmu wannan k'asa,
da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul'fatah, dan komai namu mukam ya k'are, duk
abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k'arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki
Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa maganar ta kud'ine. Wasu
sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk'atar kud'i muke sai
mahaifina yakafa wasu sana'oi da sauran kud'enmu, tanan muke samun kud'in
shiga. Karatun Muh'd da Haneefa kuma Mahaifiana ke d'aukar nauyi..
Tundaga primary har jami'a anan Sameer
yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani
saita dawo jlkan Muh'd gaba d'aya, kokad'an bata k'aunar ganinsa, kullum
tsakaninta dashi sai aibantawa da jifansa da kalamai masu had'ari ga yaro.
Tunda Muh'd yafara sanin Kansa, yaga
halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata
zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da burin d'aukar fansa.
Muh'd mai fara'a da barkwanci yakoma
mutum marason magana da azabar rashin d'aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai
dainaba, dan zakata masa Abu ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo
k'arshene zaka gane kurenka a wajensa.
Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine
yamatsa tun Muh'd na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan
acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh'd ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cikin son
had'a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had'a wani abun,
tunma ina masa fad'a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka
sunada Company na had'a wayoyi📱 da Computers💻🖥, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu business
domin dai muke samun kud'ad'en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan
babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh'd yayi Nigeria shine
aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai k'arfin gaske, dan sai
d'a mafi soyuwa ga Sarki ko k'ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da
sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma
wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko nace ya mayar musu amma sai
mahaifina yace a'a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har
tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai
zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke ganin sunfa *kashe
macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA.....*, basuyi
tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had'ari dake a tare dashi.
Shikuma Muh'd yafi karkata hankalinsa ga
jama'ar wajene sukama mahaifisa haka, koda akwai jama'ar masarautar gagara
badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad'ai nake zargiba, amma
yakasa fahimtata gaba d'aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi
zargin jama'ar waje, don mutananen masarautar suna 6oye musu ainahin fuskarsu
ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku
nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,,
daga nan na dukufa addu'a da neman za6in ALLAH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai
mahaifina Sarki Abdul'fatah (papi) yace Muh'd saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina
rok'on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki
iya canjamin Muh'd, dan banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin
walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke
macece, sai kin fishi zama cikin jama'ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar
halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan abinda yadace dashi. Inaji a
jikina zaki iya canjamin Muh'd, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama
zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki
rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masarauta
za'a koyar dake kinji”.
Kaina Na gyad'a mata, sannan a sanyaye nace
“Momma namiki alk'awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama
rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d'aya ne ban ganeba”.
“miye baki ganeba d'iyata?”.
“Abokinsa Muftahu, shima a masarautar
yake?”.
Murmushi Momma tayi, tace “daga Muftahu
har Harun duk 'yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had'a dasu Muhammad, da
kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh'd uwarsu d'aya ubansu d'aya,
shikuma Harun d'an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne,
saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?”.
Kaina Na girgiza alamar A'a.
Momma ta sauke ajiyar zuciya, “Munaya
saikin dage kinji, domin Na had'aki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma
sark'akiya, musanman akan halayyar Muh'd, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa
nan, koyaya Abu ya had'aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga
jerin wad'an da yake tuhuma. amma kekad'aice mafi kusanci da Muh'd yanzu,
zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa,
danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d'innanba,
yanzu haka kafin nasan matsalarsa 'Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa
(aunty Mimi), garama Sauban.
Nace “shikenan Momma ki tayamu da
addu'a kawai”.
“insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH
yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku
haifa”.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k'asa nikam,
ko azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk'awarin zai taimakesa kamar yanda ta
buk'ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma
gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak'iyane masu
fuska biyu. abinda kuma nalura da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai
yarda 'yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane
kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d'in dana gani a d'akinsace
tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin masu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da
tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum
shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak'uri Na yarda yanada hak'uri kam.
***********
Yau saida yamma mukaje muka duba Abie, mun
iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima
yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata,
yayinda sauban da aunty Mimi da Samha ke baya.
Maganar da samha ta fad'amin d'azun a
asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace
d'iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma
khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, bayan rasuwar mahaifin nasune suka
dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu
tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad'i shima, dan
ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ake zargin an
kasheshine saboda wani Abu daya gani.
Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a
baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.
Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya
sa6ashi a kafad'a muka shiga ciki, har d'akinsa ya kaisa. ni lokacinma harna
haye saman..........✍🏼
Barkanku da
juma'a.
Zanyi last
page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya⛹🏻♀⛹🏻♀.
Network
yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru☹
*_YA ALLAH
ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻3⃣0⃣
..................Da sallama ciki-ciki ya
shigo, nayi saurin maida zip d'in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni
yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.
Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan
mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d'agowa yayi yakuma
kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k'asaita, “k! Wai bazakima
Momma magana ba kikoma d'akinki?”.
Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi
batare da Na kallesaba, “inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi
son haka, duk nabi Na takura zama da Namiji d'aki d'aya”.
Banza yamin bai sake tankawa ba, saima
yamik'e yana jan k'aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad'in ka
iya fad'ar R kafin kamin mazurai.
Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe
d'insa ya d'auki kayan barci yanufi bathroom.
Murmushi kawai nayi, danni rayuwar
mutuminnan mamaki take bani, ina dad'i kabi ka k'untata kanka irin haka? baka
hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin
yanayiba, hakama wak'a banta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun
Qur'an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata 'Yar kanta dakecan gefe a
bedroom d'in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English
Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Momma tace anan India ya girma🤔). Wata zuciya tacemin su India
basuda musulmai ne?. “hakane kumafa” nafad'a a fili ina mik'ewa.
Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito,
daya fito saina shiga nima.
Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba
yanzun, dan haka hankalina kwance na zuge zip d'in rigar, na cireta gaba d'aya,
shima sket d'in nayi k'asa dashi yafad'i k'asa.
Juyowarnan da zanyi da nufin d'aukar towel
dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k'ofar bathroom,
hannunsa rik'eda k'aramin towel yayi tsaye yana kallona.
Bansan Na kwalla k'araba wlhy, Na rarumi
towel d'in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k'ofar a rufe take, dan
dawuya su Aunty Mimi sujini.
K'arata tadawo dashi daga sumar tsayen
dayayi, yawani kauda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun
tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi
shirin barcinsa a ciki.
Jinayi tamkar na makesa, d'an rainin
hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa baiga abin kalloba. hijjabin
sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.
Ina shiga yamik'e yana wani munafukin
murmushi, abin salla ya shinfid'a ya kabbara shafa'i da wutiri.
Nadad'e abayin nak'i fitowa, saida nabar
jin motsinsa duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya
kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya
bud'e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne
aciki.
Yad'an juyamin baya kad'an, dan haka cikin
sand'a Na rufe k'ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk
zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.
A ransa yace munafunci. cigaba yay da
aikinsa hankaki kwance, bai bar wajenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta
sainaga yashiga bayi ya d'auro alwala.
Nima har time d'in barci yakasa d'aukata,
maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima
kawai nakeyi.
Ina kallonsa ya kabbara salla. saida yay
kusan raka'a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d'auki alku'ani yafara karatu
k'asa-k'asa.
Masha ALLAH nafad'a a raina, danjin
yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda
kowane harafi cikin tsantseni da kwarewa. Tun ina saurarensa har wani barci mai
dad'i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.
Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan
haka shima yau a gida yayi.
Bayan ya idar waya ya d'auka naga yayi
kira.
Bayan an d'aga daga can sukayi gaisuwa, jin
ya tambayi ya Nigeria Na gane da 'yan can yake wayar. yacigaba da fad'in.
“Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a
inane yake haka?”.
Bansan mi akace masaba daga can, naga dai
yayi kwafa, sai yace “ya maganar Minister? dan nagansa wajen d'urin aurena, ban
kuma yi zaton zai zoba”.
Canma aka kuma yin wata maganar.
Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon,
dayake yana kan abin salla har yanzun. “kayi k'ok'ari Nuren, yanzu abinda
nakeso dakai shine, akwai yarinyarsa d'inan datake karatu a nan jami'ar Abuja,
inason a sacemin ita k'arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai
nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d'aukemin, dan bincikena ya
ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, kuma randa su Alhaji balala
sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani
Abu koda kad'anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar
wancan time d'in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da
Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso
Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata”.
bayan nacan yagama magana.
Yace “ok babu damuwa, zan turo maka number
yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anjima, ka gaidamin Mom d'ina”.
Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya
kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud'awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci
wayar tasaba gaba d'aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak'arsa da
Galadima kuma?.
Tabbas aikina bazai yuwuba saina San wanene
NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad'annan mutanen
biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d'in Na Abie
ne? kokuwa tasu dabance?.
Kwanciya ta na juya yanda zanji dad'in
tunanin da k'yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu,
kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d'in da rayuwarsa, na tuna maganar
Momma da tece “shi mutumne dabashi da yadda”. Mutum mara yarda kuwa yanada
wuyar sha'ani, kad'an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda
barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya
kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.
Sai around 11:30 na tashi, wani masifar
ciwo kaina yakemin, haka dai na tak'ark'ara nayi wanka, nagyara d'akin sannan
na sako k'asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama
nayi bisa kujera dafe da kaina.
“ranki ya dad'e lafiya dai?”.
Bud'e idona nayi a hankali, sai naga
jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk'urin tashi zaune, “wlhy kaina ke ciwo
jakadiya, halanma ke kad'aice ma a gidan?”.
“subahanalla, sannu ranki ya dad'e, bara
na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad'aice ranki ya dad'e su Sauban
sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine
shiyyasa tahana a tadaki”.
Nace “ALLAH sarki”.
Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad'ewa
saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad'in “gashi ranki ya dad'e,
kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti”.
Kallonta nayi da mamaki, “jakadiya waye
magajin gari kuma?”.
Tayi 'Yar dariya, “ranki ya dad'e ina
nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa”.
Murmushi nayi ina girgiza kai kawai, na
had'a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci
yakuma kwasheni.
Jakadiya na zaune tana gadina.
Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa
tareda mik'ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa, yad'an
saki fuska yana amsawa. d'aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya
sauka kaina.....
maganar da jakadiya take masa ce
yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.
“ranka ya dad'e akai kayan samane?”.
“no jakadiya kibari zan hau dasu, ai
sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?”. ‘yay maganar yana
maido idonsa kaina’.
“kanta ke ciwo ranka ya dad'e, amma
tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen”.
Ido yad'an tsuramin, kafin ya cije lips
d'insa kad'an.
Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad'ewa
tadawo da ruwa ta ajiye masa.
Sannu yamata sannan yad'auka yana sha,
itakuma tabar wajen.
Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida
kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya,
lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda
nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud'e idona a
hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune da sauri, tareda warware
d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai
santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama
yasan tun yaushe yake anan?.
Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes
yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada
kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman
mik'ewa saiya bud'e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin
kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da
tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da
zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya
kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu
Second's sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.
“kainane ke ciwo amma yama daina”.
maganar dayayice tabani mamaki.
Mik'ewa yayi yana fad'in “ba gulma tasaki
k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy
d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan
baya gani har hanji🤨?
nabishi da kallo yayinda yake taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa
d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke
ajiyar zuciya.
★*★*★*★*★*★*★
*_Nigeria_*
Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan
gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da
abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata
damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali
kwance.
Innaro kam kud'in da Galadima yabata suka
sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a
jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta
siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k'yauta tasaka mamansu yaa Hameed
kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka
suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe
kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi
shiru.
Kusan k'arfe hud'u na gamma saiga Zarah
wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar
gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.
Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka,
“innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'auka masa kud'iba, narantse
da ALLAH........”
Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin
kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k
mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?”..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta
a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki
kud'iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa
sai mamansu tajata suka shige d'aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u tayi,
tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita “to anfara da
bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......
Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e “yo mai kashi a
gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda
kema kinkai gidan wani”.
“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa
zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye
hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama
baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman
Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen
makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin
hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da
maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.
d'akin mamansu yaa hameed tashige domin
jiyo ba'asin dawowar Zarah n.
Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi,
wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan
sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene
tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki,
ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yakoma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata
kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane
ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma
dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen auren Malam
bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata
biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran
basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami
sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai
jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai
agidajensu.
Nace amin
innarmu😘👌🏻
★★★★
Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi
nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka
lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga
sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko
zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa
da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai ka aramin waya
dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya”.
Biris yay dani, sai zuwa can yad'ago ido
ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru
kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya
shigo da ita, wata k'aramar pink d'in souvenirs bag yamik'o min batareda yace
uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun
bag d'in k'aramine, dan haka hanunmu ya had'u waje d'aya, ni da shi kowa saida
yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d'in tayi k'asa zata fad'i
yay saurin kuma k'ok'arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da
sauri. Sai kawai na damk'e hannunsa kanmu ya gwaru waje d'aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda
hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d'in karta fad'i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji
zafi, kansa kamar kwakwa☹.
Hararata yayi yana fad'in “k wane irin
kaine dake haka?”.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai
nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace “kana niyyar
fasan kai, shine zaka maida abun kaina?”.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d'an bugi
bakina, “k kinma rainani wlhy”.
K'asa na durk'ushe kawai nasaki masa
kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d'an abin dayamin shine na
kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa”.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik'e
tsaye, tareda d'iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk
cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad'an shafa dan gaskiya
naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar
innarmu, amma tak'i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak'i tafiya, nad'an
ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad'ad'i yakemin, ina
cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad'anyi kamar zai basar saikuma
ya kasa, ya k'arasa jikin wardrobe d'insa yana bud'ewa, “har yanzu goshin zafi
yake?”.
Kamar zanyi kuka nace, “eh wlhy ”.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana
kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya
d'urk'usa, k'amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d'aura
bisa kaina, ya d'aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin
hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki
ina rik'e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, “please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai
zafi fa”, bai saurareniba, duk rik'e masa hannun danake saida ya mulmulamin
sosai sannan yamik'e yana hararata da ta6e baki, “halan kekam kina jaririya
ba'a miki wankan jegoba?”.
Baki na tunzuro masa, nace “ka kira
innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani”.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana
barin wajen. Kayansa ya d'auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik'e nakoma kan sofa d'in
ina bud'e bag d'in d'azun. kwalin wayane mai k'yau, wani dad'i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye
gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin
Brown d'in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k'ugunsa,
bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k'yau da aka zuba sandunan wasan
Golf a ciki🏑, guda biyu ya ciro, sannan ya tako
inda nake yana fad'in “bani wayata idan kin gama”.
Fuska na marairaice nace “ALLAH kagani
bamma yiba, tak'i shigama”.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya
d'an ta6e “k bak'auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k'asarkice?”.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace
“oh namanta saina saka + wlhy”.
Aljihu ya saka wayar, “saiki bari sai
wani time d'in kuma, yanzu sauri nake ana jirana”.
Da sauri nace “zan bika please, wlhy
gidan shiru babu dad'i”.
Yana fesa turare yace, “ba yauba, baga
jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d'akko khaleel a school ai”.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya
kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi
yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d'akko wasu album na
pictures har hud'u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi
sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace “wad'annan kayan nakine
ki duba”.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili
nace, “Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai”. (Kifad'a a gabansa
mana yarinya. 🤣🤭).
_______________,,___________,,,______
Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e
bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan
haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin
duka, “kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?”.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama
Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in “innaro wai
kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo
yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i
gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin
mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in
jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan
Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a
anguwar nataho gida”.
Innaro tarik'e ha6a tana fad'in “oh ni
marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke
kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?”.
“wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na
rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure
sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina
idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an
yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya
kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i
baneba😢”.
“kai amma wannan yaro anyi
wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su
Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,”.
“nidai babu wani court k innaro, kawai
akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy”.
“enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa,
nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma
yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki”. fuuu tafito tana
sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan
gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa
bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin
mata).
'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama
danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon
farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba”.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in “k
'yarnan da gaske?”.
“wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan
gidanmu suna maganar da Sulaiman”.
“to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya
mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar
family d'in, komai yaro yamaka ido nakai”.
“yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama
magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu,
toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni
miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata
Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”.
“eye, kice tafara miki hassada kawai
saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba,
karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito”.
“insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”.
“yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in
damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”.
“zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske
Munaya bata Nigeria? ”.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in
ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu
jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen
mijin nata”.
“aikam Momy indai da sunzo d'in to da
gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da
sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”.
“suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice
ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke
kin kasa sakashi ya kaiki”.
“lallai momyn nan, shikenan tunda laifina
kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata
jira cewarta ba ta yanke wayar’.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja
tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda
ya maido Zarah gida. (Fuska biyu😆👿).
*******************
Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow
irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na
wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na
d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau
bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba,
zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida
nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan
haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan
wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a
masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da
Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya
sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yara😄.
Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali
har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo
saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen
jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.
******
Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty
mimi.
Ina d'aki zaune har sannan ina kallon
pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar.
Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon,
d'an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik'e yashiga bathroom, kusan 1hour
sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (🚽🤭).
Yau saida na jirasa harya idar da shafa'i
da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace
“dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?”.
Batareda ya d'agoba yace “uhmm”.
Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, “shin
tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga
addu'oi haka?”.
Yanzun kam d'ago ido yayi ya kalleni, dama
tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar.
“lips d'insa yad'an cije, kamar zaiyi
magana saikuma yay shiru.
Nace “kayi hak'uri idan nashiga hurumin
daba nawaba”.
Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna
kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak'in ciki yace, “duk an
gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba,
saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k'ok'arin
sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu'oinmu akansa yake”.
Ajiyar zuciya na sauke, nace “ALLAH
yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan”.
“amin yafad'a a la66ansa”.
Dagani harshi babu Wanda yasake magana har
muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud'awa da kwancewa, har
gabannin asubahi kafin barcin ya saceni..................✍🏼
_To Alhmddlh
my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai
da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA..... PART ONE* yanda zamu tafi
a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma
za'a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima
kamar yanda Momma ta buk'ata, shin zai bata had'in kaima Kuwa? domin kunji
Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata
kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da
ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo
bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luv😍😍😍😘😘😘🥰👌🏻_
_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda
addu'oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk'ar sakani a
farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake
yasaka aransa yana can k'ark'ashin zuciyar Bilyn Abdull.🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘👌🏻🤝🏻._
_ga azumi
zamu shiga, 'yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da
k'autatama marasa k'arfi, marayu,, k'autata mu'amullarmu da jama'a dayin amfani
da abinda malamai zasu fad'akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa
tafseer amma bamu d'aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan
ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani
yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice ma😭, zata iya yuwa kece 'Yar uwa👉🏻😭, zata iya yuwa kaine d'an uwa👉🏻😭. dan ALLAH mu gyara please &
please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za'ikatul
maut, kowane rai saiya d'and'ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d'in da rundunar
mala'iku zasuzo d'aukar rayin nakaba,😭 mutuwa bata kwankwasa k'ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka,
kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana
aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairi😭, ya ALLAH ka d'auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH
ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._
_ina rok'on dukkan Wanda na 6atamawa a
yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema
kowa._😢👏🏻
*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason
yasakani a ddu'arsa ta cikin azuminnan koda sau d'ayane, idan munada Rabon
haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk'i
da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana
hak'uri da juriyar azuciyata😭👏🏻, ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu
baki d'aya._*😭👏🏻
Dan ALLAH ko sau 1 yane kar'a manta dani🙏🏻😊
Amin afuwa zan rage groups saboda yawan
groups d'in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d'aya ko sati bata
yimin take k'arewa🙏🏻.
Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa
munada rabon sake had'uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d'aya.
yabamu juriya da hak'urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1👌🏻.
No comments