QANIN MIJI 5
5
Da sauri ya
zabura ya miqe tsaye har wayarsa tana faɗuwa a qasa tare da fisge jikinsa daga
na baturiyar da ta rungumeshi
Yatsarsa ya
nuna mata cikin fushi yace
"ke
dabba mahaukaciya, idan kika sake kuskuren taɓa jikina sai na ɓaɓɓalaki ke da
qasarku, duk tsiyar da za ayi a je ayi, 'yan iska kawai karnuka"
Ya ma mance
da ita wannan ɗin ba hausa take ji ba
Ita kuwa
baturiyar da take tsaye cikin kayan da bai fi tsirara ba, da mamaki take
kallonsa, domin ita na farko ba jin abinda yace tayi ba, na biyu kma ba tayi
tsammanin haka daga gareshi ba, musamman yadda ta ganshi wayayye, saboda
yanayin fuskarsa kawai ya nuna mata faɗa yake mata kan abinda ita ba ta ga
laifinsa ba
Rashin
hankali da fasali irin na matan turawa sai ta yi murmushi tace
"my
name is Tina, and you"?
Ta qarashe
da miqa masa hannu, mugun kallo ya mata sannan ya sunkuya ya ɗauki wayarsa ya
fara tafiya zai bar gurin, da sauri ta yunqura ta riqo hannunsa tace
"pls
can I help you"?
Cikin fushi
ya juyo ya kwasheta da mari tare da faɗin
"is
better for you to stay away from my life, don't put your self in trouble with
me, useless!!!"
Ya qarashe maganar
da ihu tare da tofa mata yawu ya taka cikin sauri ya bar gurin
Gaskiyar
magana a wannan rana Tina ta cutar da shi, saboda yadda ya ganta da surorinta
sun mugun ɗaga masa hankali, saidai alhamdulillah tunda ya banki qwaya ya samu
sauqi saidai ɗan feelings ɗin da ba za a rasa ba, hakan yasa shi kiran
fareedarsa domin ya kawar da wannan
yanayin ta hanyar rage zafi amma aka yi rashin sa'a wayar fareedah switch off,
haka yayi ta juye juye da tunane tunane har bacci ya kwasheshi
Ita kuwa
fareedah a nigeria da saninta ta rufe wayarta domin kiranta da yake yi cikin
dare yana mugun takurata, musamman yadda yake neman ya dinga ɗaga mata feelings
ɗinta a matsayinta ta ɗiya mace, ita kuwa a ganin ba qira babu abinda zai ci
gawayi, ni ko nace har ginkin matan kano😂🤭,
afwa...
A tunaninta
ba ita ta turashi ba balle ya zo ya dinga ɗaga mata hankali a banza da wofi ya
hanata bacci mai daɗi
***
NIGERIA
A ɓangaren
fareedah, tunda fa'eez ya bar qasar ta addabi kanta da tunaninsa da irin
rayuwar da take ciki, saidai hakan bai ɗau lokaci ba hafeez ya janye mata
hankali da wasannin da suka saba irin na qanin miji da matar yaya, kar ku manta
fareedah yarinyace me addini amma shaiɗan yana son yin nasara a kanta saboda
rashin kulawar miji, domin mu a muslunci wasan qanin miji haramunne, haramunne,
haramunne, manzon Allah ya haramta har ma ya ɗora da cewa ai shi qanin miji
mutuwane masu wasannin qanin miji idan kun shirya mutuwar toh kuyi tayi, Allah
tura shegu biyu kabari, munkar da nakir suna nan, akwai calugude🤣😂, daman ance lahirar da gumi
Saboda ko da
yaushe hafeez yana tare da ita yana bata labarurrukan ban dariya da nishaɗi
tare da ɗebe kewa, tsabar jin daɗi ma game ya haɗa musu a gidan na tseren mota,
idan ta kammala ayyukanta, shi kuma ya dawo daga school sai su cancaɗa kwalya
su hau buga game ɗinsu, kasancewar an fi cinye fareedah yasa take dasa masa
rigima tace yana mata wayo, shiko yayi ta tsokanarta da mata gwalo, hakan yake
sawa ta ɗauki filolin kujeru ta fara jifansa yana kwashe mata da dariya, wani
lokacin har remote take ɗauka ta wurga masa ya kauce, haka zasu yi tayi har
magriba kafin su tashi su tafi sallah dan dukkansu babu mai wasa da sallah a
cikinsu
Abin haushi
da takaici, duk lokacin da hafeez zai ga fareedah da kwalya sai ya yaba mata ya
koɗata tamkar shine mijinta, hakan kuma yana mata matuqar daɗi a ranta tare da
qara wa zuciyarta shaquwa da hafeez, har tana Allah Allah tayi kwalya ya zo ya
gani ya koɗata ya kambamata
***
Yau ba
school a gurin hafeez, dan haka tun safe babu inda yaje yana gida, daman ko da
school ɗin ma yanzu yana dawowa baya qara fita da mota, sallace kawai take
fitar da shi masallacin unguwarsu
Tun da suka
yi break ɗin safe suka haɗa game sai yi suke yi cikin raha da barkwanci, gashi
suna zaune gab da gab kan two seater, duk wanda ya buge wani zai yi ihun murna,
tamkar dai wasu mahaukata, yayin da ɗayan zai yi harara, daga qarshe dai hafeez
ya buɗe wuta ya dinga doke fareedah, ganin yana ta cinyeta sai kawai ta jefar
da abin yin game ɗin ta tashi ta fara tafiya tana bubbuga qafa irin na rigima
ta juyo cikin muryar kuka da shagwaɓa tace
"ba za
ayi game ɗin ba, na qi ɗin, sai wayo kake min...😢"
Dariya ya
qyalqyale mata da shi yana mata gwalo da faɗin "woooh loozer"
Dawowa tayi
da nufin jifansa da filo shi kuwa ya tashi suka zuba a guje sai zagaye falon
suke yi ta kasa riskarshi yayin da yake ta qyaqyale mata da dariya
Haushine ya
kamata ta zabura za ta kai masa duka ya kauce ita kuma ta tafi zata faɗi saboda
taka remote ɗin da tayi wanda ta jefa masa ya kauce, ta tafi suuu zata kai qasa
hafeez kuma cikin zafin nama ya tareta yayin da shima kuma qafarsa ta bugu da
jikin kujera ta harɗar da shi saboda saurin da yayi gurin tarota, dan haka tana
faɗawa qirjinsa suka zube dukkansu a qasa😳
Tsabar
tsorata da fareedah tayi na mummunar faɗuwar da za ta yi a qasa yasa tana jin
jikin hafeez a nata jikin ta qanqameshi qam cikin tsoro tare da rufe idanu
Shi ko
hafeez jin tattausan jikin fareedah a jikinsa ya sa dukkan netwrk ɗinsa ɗaukewa
tare da tsinkewar laka da jijiyoyin jikinsa
Shine kwance
a qasa yayin da ita kuma take kansa qanqame da shi, duk buguwar da hafeez yayi
wannan qanqamar ta fareedah ta hana shi jin zafin, ko motsawa ma bai yi ba, dan
numfashinsa ya kusa ɗaukewa
Fareedah
kuwa tsoron na sake ta ta dawo cikin hayyacinta, hakan ya sanya ta sauri sakin
hafeez tare da zabura ta bar jikinsa, cikin jin kunya
Hafeez kuwa
idanunsa ma a rufe suke ko motsi ba yayi, cikin tsoro fareedah ta bubbuga kafaɗarsa
tana cewa "hafeez, hafeez!"
Idanunsa da
suka yi jajir ya buɗe a kanta yana binta da kallo, ita kuwa ganin idanunsa haka
ta ɗauka zafin faɗuwarne, dan haka cikin tausayawa tace
"sannu
hafeez, kayi hakuri dan Allah, ban san haka zata faru ba"
Shi dai bai
ce komai ba, sai ma binta da kallo da yake yi, hakan yasa ta shiga tashin
hankali ta miqa masa hannunta tace
"pls
hafeez kayi magana, kama hannuna ka tashi"
Sai a
lokacin yayi murmushi ya miqe ya zauna gurin yana mata wani irin kallo yace
"kalleta dallah, ke yanzu in na ce zan kamaki in tashi ba saidai mu sake
zubewa ba, wasshh amma gaskiya na bugu"
Ya qarasa
maganar da dafe bayansa, dariya ta yi tace
"kai
hafeez, kaman ba namiji ba, dubi idanunka yadda suka yi ja"
Hararanta
yayi yace "eh dole ki min dariya, da yake ba yayana bane ya faɗi ko?, da
yanzu kin rikice mana a gida da ihu"
Dariya ta
sake yi tace "toh ai shi wannan mijine, kai kuwa qaton...."
Ba ta qarasa
ba ta rufe baki, wani irin kallo ya mata yana murmushi yace "qaton banza
ko"?
Girarta ɗaya
ta ɗaga masa cikin tsokana tace "yesss..."
Murmushi
yayi yace "toh shikenan qaton banza ya gode"
"yi
hakuri kaide wasa nake maka mijin" tace tana murmushi
Lumshe idanu
yayi ya buɗe yace "ya wuce matar, amma fa yau ya kamata mu ɗan zaga gari
ko, wallahi ni dai zaman gidan nan ya isheni, haka kawai an min kulle kamar
wata mace, an hana 'yammata ganin babban yaro mai qtr million, mu ɗan fita ko
shan ice cream ne matar"
"lallai
fa babban yaro, amma dai duk tsiyar mutum bai kai mijina haɗuwa ba balle a min
iyayi"
Harararta
yayi yace "toh kin ji na sako mijinki ko neman magana, ki faɗa masa kawai
da yamma mu je mu kashe qwarqwatar idanu"
Miqewa tayi
tana tafiya tace "wai dai na tuna makane, ka daina mantawa akwai kyawawa a
gabanka, zan mishi magana, sai mu fita 4:00, nima na gaji da zaman gidan
wallahi"
Bai amsa ba
sai bin bayanta da yayi da kallo har ya daina kallonta sannan ya tashi yayi ɗakinsa
***
Cikin shiga
ta alfarma fareedah ta fito ta sha kwalya iya kwalya domin ta ɓata lokaci gurin
yinta, sai wani dal dal dal take yi tana wani wal wal wal
Qaran
takalmantane ya janyo hankalin hafeez da yake zaune yake duba saqonninsa na
istagram
"wow........"
Hafeez yace
tare da miqewa tsaye yana mata kallon up and down, ita kuwa sai murmushi take
yi domin ta san yba mata zai yi
"matar
ke kin ganki kuwa, ke kin san wutar da kika bayar kuwa?, kai matar da ana
kallon hurul'een a duniya sai ince ke jinsinsu ce, mashaa Allah, gaskiya na
sara miki, ke sarauniyar matace, daga kin fito kike daqushe haskensu, kai ki
gode wa ubangijin da ya qeroki cikin gwanayen iya kwalya da tsara ado"
Cikin
farinciki da jin daɗi fareedah tace "kana koɗani da yawa mijin, na gode,
mu je ko"
ɓata
fuskarsa yayi yace "kin gode kawai zaki ce min, kullum ni sai na yaba miki
ke kuma ko sau ɗaya"
Cikin muryar
lallashi tace "tuba nake nawan, ai bama haka da kai, wallahi kayi kyau,
kuma daman kai kyakkyawane, ga iya gayu tamkar jinin sarauta"
Ai ko ya ji
daɗin yabawar, murmushi yayi tare da godiya sannan suka fice tamkar miji da
mata
*
Sai da suka
je gidan su fareedah suka ɗauki kboy sannan suka wuce, yawo sosai suka yi tare
da saye sayen banza da wofi suka yi ta zuba hotuna abinsu sannan suka mayar da
kboy gida tare da tsarabobinsa sannan suka dawo gidansu cikin nishaɗi da
walwala, domin dukkansu babu wanda bai ji daɗin fitan ba saboda wasannin da
sukayi da yadda suka yi ta hotuna a gurare daban daban, hoto ɗaya kawai suka
tura wa faeez shine wanda fareedah da kboy suke kan lilo suna dariya, hafeez
kuma na ta lilasu
Suna shiga
cikin gidan kowa yayi ɓangarensa da sauri, saboda yau sun yi missing sallar
magrib cikin jam'i
*
Ko da faeez
ya ga hoton dariya suka bashi, duk da sun masa kyau, sai da ya kira kowannensu
a waya yace musu lallai baku da aikin yi, wasa dai wasa dai, sana'ar kenan, toh
Allah kyauta muku, kamar sun haɗa baki kuwa, kowanne dariya ya masa suka manna
masa, ni ko nace yo toh me za su ce😂
**
Yau watan
faeez ɗaya a can da kwana biyar, zuwa yanzu baya samun daman wuni a hotel ɗin
saboda taron nasu ya fara ɗaukan zafi, sai dare yake dawowa ko daf magriba,
amma fa har yanzu wannan yanayin yana tare da shi na saurin motsawar sha'awa
saboda yanayin sanyi da kuma yawan kallon tsaraicin mata a ko da yaushe, ya
shiga damuwa sosai, da har ya so ya faɗa wa fareedah ta biyoshi sai kuma shaiɗan
ya hanashi da wasiyoyinshi na banza, kullum yana nuna masa bai dace ya kawo
fareedah wannan qazantacciyar qasar ba, saboda zinace zinacen kan hanya da yake
gani, sannan kuma ya kan tuna masa ga tablet yayi ta sha kawai, amma fa bai
tuna masa yin azumi ba dan mugunta
Yau ya dawo
hotel ɗinne cikin muguwar sha'awar da bai taɓa jin irinta ba, sai kuma aka yi
sa'a a yau ɗin harabar hotel ɗin cike yake da tantirai ana ta tantiranci,
abubuwan babu kyan gani, da qyar ya kawo kansa ɗaki saboda jiri da yake ta ɗebansa,
burinsa kawai ya je ɗaki ya sha tablet ɗinsa ko zai ji relief, saidai neman
duniyan nan yayi wa tablet ɗin ya rasa, sai daga baya ya tuna da cewa sun qare,
ragwaf ya kwanta a gado tare da riqe kai, yana son fita ya je ya sayo tablet ɗin
amma baya buqatar sake ɗora idanunsa a kan baɗalar da ake yi a wajen, don haka
yayi lamo a kan gadon, ya ɗau lokaci a haka kafin ya tashi a daddafe ya je yayi
wanka ya sanya kayan barci ya zo ya sake kwanciya ruf da ciki
A hankali ya
sanya hannunsa ya ɗauko wayarsa ya fara dialing number fareedah, cikin sa'a
kuwa wayar ta shiga, hakan yasa shi juyowa yayi rigingine yana kallon seiling,
fareedah da ba ta daɗe da kwanciya ba dan yau basu yi game ba saboda hafeez
yana da test mai zafi a school, wayarta ta janyo ta kara a kunnenta ba tare da
ta duba mai kiran ba
Abin da ta
ji ya fara faɗa kawai shine "fareedah wallahi nayi begen wannan daren ace
muna tare, gaskiya neman halak da wuya, ina cikin wani hali"
Muryar da
yayi amfani da ita sai da ta ɗaga mata kaf tsikar jikinta, sosai ta rintse
idanunta, duk da haka sai da tayi magana cikin kasalalliyar muryarta da ta gama
narkewa tace "haramun ɗin ma ba baya bane fa'eezzz...."
Sake
burkitashi muryar fareedah tayi, cikin mawuyacin hali da kasalalliyar murya
yace "fareedah pls, kiyi duk abinda ya dace ki samar min da nutsuwa plss,
fareedah......."
Qofar ɗakinsa
ya ji an turo, bai san lokacin da wayar hanunsa ta zame daga hanun nasa ba,
saboda teena da ta shigo ɗakin cikin tsaraici, daga ita sai wani ɗan jan qyalle
daga iya qirjinta zuwa kan cinyarta, ko pant da bra babu, sheɗaniyar tana gani
ya zuba mata idanu sai kawai ta janye qyallen, ta fara takowa gurinsa,
subhanallah
*
A nigeria
kuwa, yadda faeez ya burkita fareedah da muryarshi kuma ta ji yayi shiru alamar
yana sauraronta, sai hakan ya ba ta haushi ta datse kiran tare da jefar da
wayar gefe, ji take kamar ta ja masa Allah ya isa, haka tayi ta jan tsaki tana
juyi a kan gado ita kaɗai, maimakon ta fara ambaton Allah ko ta tashi ta fara
nafila, sai ta qanqame kanta a kan gado
tana jin wata muguwar sha'awa tana taso mata tana bibiyar duk wata magudanar
jininta, can wata dabara ta faɗo mata, a kasalance ta tashi, shi ko oga shaiɗan
la'anatullahi yana ta zugata, tunawa tayi da wani littafi da ta ji ana
labarinsa a wtsp groups da take, saboda abubuwan da ta ji ake labari na book ɗin
ta san in ta karanta ita ma za ta samu sassauci kan yanayin da faeez ya jefata,
ta gane hakan ne daga comments ɗin da ake yi a kan book ɗin, hmmmm
Anya kuwa
tusa za ta hura wuta readers?
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments